Author : Jamila Umar Tanko Category : Romance
yi fushi kuma za ka jawo min ciwon kai."
Ya zabura ya miqe tsaye ya ce "Ah bari in ci ko da zan amayo da shi, kada gimbiya ta yi ciwon kan nan dan Allah a rufa min asiri. Ciwonki dafi ne a cikin zuciyata. Ba na so ki yi ciwo, fatana ki sami lafiya."
Ta ji duniyar ta zame mata tamkar a aljanna dan gaba daya baqin ciki ya gushe mata. Ta bubbude masa jerin abinciccikan da su ka shirya masa, ya zazzabi abinda zai iya ci marar nauyi. Itama abinda ya zaba ta zaba ta zuba su ka zauna su na ci.
Ya kalli farantin gabanta ya ce "me yasa kika zabi duk abinda na zaba?"
Ta yi dariya ta ce "haka kawai na ji nima raina su yake so."
Ya ce "idan na sake zabar wasu fa?"
Ta ce "su zan zaba nima." Ya ce "saboda me?"
Ta ce "ikon Allah ne kawai." Su ka yi dariya su dukka daga nan suka gangaro hirar Yaya Imam Malik.
Ta ce "Yayana ya na sonka sosai saboda taimakon da ka yi min, kana da labarin duk duniya Imam babu abinda yake so sama da ni.
Usman ya ce " ya gyada kai ya ce ya fada min haka da bakinsa, ai duk duniya babu wanda ya taba taimakona irinsa, da yayi min hanya, ya yi silar da na zo na zama nine silar nemo miki maganin ciwon nan har muka saba muka fara gaisawa. Kin manta ada kin tsane ni daga harara sai tsaki?"
Ta sunkuyar da kai qasa saboda nauyi da kunya. Can ya dago ta dube shi ya ce "ka yi haquri amma ban taba tsanarka ba a raina, tun ranar da na fara ganinka a duniya na ce wow he is gentle and handsome."
Su ka yi dariya su dukka ya ce "kai ban ga alamar hakan ba kuwa, sai tsana. Cab ke kin ga yadda kike hararata kamar za ki mauje ni."
Ta ce "ai kai ma kana ramawa."
Ya ce "kadan na ke yi miki ai, shima sai a gaban madam nake dan tabukawa. Kin taba ganin mutumin da ku ke tsakiyar fada amma kuma.ya ceto rayuwarki, ya yarda ku mutu tare? Dan tsabar zafin zuciya irin ta ki, mu na cikin dan fadanmu ina jin dadin muryarki kawai kika nufi tirela za ta kashe min ke. Ai Godwin har yau haushi yake bani da ya qi zuwa ya kamo, a dole ni din dai na tafi."
Ta ajiye cokalin hannunta ta zuba masa ido, tana kallo har tsawon lokaci.
Ta ce "ka san haka yayana ya ce min kuwa? Haka ma Murjanatu ta ce wai kai ai baka fada da ni, qaunata ma kake yi in har zan ka gan ni zan halaka amma ka ceto ni."
Ya kalle ta kallo mai taba zuciya ya ce "cab in kin ji an ce qauna ma ai daya kenan qaunoni."
Su ka bushe da dariya ta ce "da gaske kake wai?"
Ya girgiza kai ya ce " me zaki bawa kanki amsa ai ba ni ba."
Da ya tashi zai tafi ta dauko masa himilin ledoji alewa da biskit sai da ya tsorata, ya cika da mamaki marar misali.
Ya ce "gaskiya ba zai karbi dukka ba, ai sai a dauka kanti zan bude."
Ta ce "ai kuwa dukka zaka kai musu."
Ya yi shiru ya ce "amma fa madam zata tuhume ni."
Ta tabe baki alamar kishi dan ta ji haushi, sai ya gigice ya durqusa a gabanta ya riqe kunnuwansa biyu ya ce "afuwan zan dauka dukka in kai musu. Shikenan?"
Farin ciki ya lullube zuciyarta ta ce " Ah ka tashi tsaye na hakura, kar kasa a zo a kama ni, ace na saka babban mutum tsallen kwado."
Ta raka shi har bakin qofarsa ta ja ta tsaya,anan ma suka bude sabuwar hira ji suke kamar su hadiye juna. Dakyar suka bawa zuciyoyinsu haquri suka yi sallama kowa ya shiga gida. Amma fa a ranar dakyar kowannensu ya yi bacci, juyi suke su na ta tunanin juna yayin da dukka hirar da suka yi ta dinga dawowa kwanyarsu.
Mufidah bata taba sanin yadda zaqin soyayya take a rayuwarta ba, sai akan Usman. Shima ya ji kamar bai taba jin irin wannan soyayyar a cikin dan qanqanin lokaci ba sai akan Mufidah.
Ya tabbatar ashe baya son Jalilah ne shiyasa zuciyarsa ta qi karbar ta, ya dauka ya tsufa da yin sabuwar soyayya ne ko kuma qaunar Fatiti ce ta hana shi qara son wata, ashe ba haka abin yake ba.
Da asuba ya tashi yayi wanka ya shirya, ya so ya fita da asuba dan ya isa da wuri amma sai ya ji ba zai iya wucewa ba ba tare da ya ga fuskar Mufidah ba. Dan haka sai da ya jira gari ya waye ya ji motsin shara ya tabbatar ita ce sai yayi wuf ya fito. Ita din ce kuwa ba Patient ba ce,
Kamar daga sama ta ji an ce "kawo in taya ki sarkin sharar."
Tabbas shigar da ta yi yau bata so ya ganta a haka ba, duk da rigar baccin tana da rubi biyu ta ciki da ta samanta, kuma ta dan sauko mata ta wuce guiwar qafarta kanta babu dankwali.
Ta yi murmushi ta duqa ta gaishe shi.
Ya ce "amma kin yi min laifi na hana ki yawo babu dankwali. Ki koma gida ki saka hijabi ki zo ki raka ni bakin mota zan tafi."
Ta wuce kanta a sunkuye ta je ta saka hijabi ta zo ta iske shi a tsaye a bakin qofarta yana jira, suka dunguma suka sauka tare da alama su dukka basa kunya ko tsoron a gansu tare.
Dr. Isa ne yake tsaye yana karkade motarsa, Usman da Mufidah ya gani sun sauko tare, su ka tsaya suka gaisa. Ya hau kallonsu, kallo na mamaki da rashin fahimta saboda duk wanda ya san Usman ya san Mufidah ya san arnan gaba ne.
Dr.Isa ya bi su a baya har bakin motar Usman dan ya tabbatar shin Mufidah rakiya tayi masa ko kuma wucewa ta zo aka yi katari shima ya sauko.
Mufidah ta harari Usman ta ce "saqon yaran ka baro shi a sama ko?"
Ya ce "ai ban isa ba tun a daren na sauko na zuba su a but, akwatina kuma tun jiya na saka a but a gabanki ko?"
Dr.Isa ya tambaya ya ce "za ka dade ne a Kano?"
Usman ya dubi Mufidah itama ta dube shi.
Dr.Isah ya ce " au ashe fa madam zan ya kamata in tambaya ba kai ba ko?"
Ta gyada kai ta ce "ka san mu lauyoyi akwai mu da adalci ba kamar likitoci ba. Sati guda zai yi acan ya dawo."
Su dukka dukka su ka yi dariya, sannan Usman ya fara jan mota a hankali kamar baya so ya tafi yayin da Mufidah take daga masa hannu. Gaba daya hankalinta a a tashe kamar mai shirin fashewa da kuka.
" ikon Allah. Ikon Allah." kawai Dr. Isah yake ta ambato, dan mamaki ya damqe masa zuciya. Bai san sanda haka ta faru ba. A iya saninsa Usman baya boye masa komai sai gashi har abu ya nuna bai sani ba.
Usman ya kama hanyar kano, zuciyarsa babu dadi rayuwarsa da Mufidah dan haka sai ya saka karatun qur'ani yana ji. Mufidah ce a ransa duk da ya na farin ciki zai je ya ga iyayensa da yaransa har ma da Fatitin. Amma daga ya tuna bacin ran da Fatiti ta cusguna masa a hanyar Kano sai ya ji duk ta fita a ransa.
Mufidah ta hau sama ta shirya zuwa wajen aiki, tana aiki tana hasko Usman a zuciyarta, sai a lokacin ne ta tabbatar ta yi kuskure da ta yi qauron baki bata karbi lambar wayarsa ba. Duk da ma ya taba kiranta a lokacin da ta dauki yaransa amma bata yi saving lambar ba dan babu abinda zata yi da ita a lokacin da ake tsaka da yin fada kenan.
Da alama shima bai yi saving lambarta ba a lokacin kuma shima da ta ga bai tambaye ta lambarta ba shiyasa itama bata tambayi tasa ba, bata san ko baya so ta kira shi ba, musamman shi da zai je wajen matarsa din nan mai ahegen kishi.
Usman bai yiwa 'yan Kano waya ya ce zai ba, bai cewa kowa komai ba, zuwan bazata yayi, kwatsam suka gan shi. Bayan ya shigo garin ma sai da ya gama yin duk abubuwan da zai yi a garin sannan da yamma ya tafi gidansa.
Fatiti na zaune a tsakar gida kan qatuwar tabarma ta hada tawagar qawayenta kai ka ce gidan biki ne, ana ta sharhi akan yadda zaa dinga bi da miji dan kada ya qara aure idan ma mijin ya riga da ya qara auren toh ga hanyoyin da zaa abi a casa kishiyar a hana ta sakat.
Ya jima a labe ya na sauraronsu, muryar Fatiti ce a sama ta fi kowa kaudi tana bada shawarwari akan su daina sakarwa miji fuska ko barinsa ya sami sukuni dan kada ya qaro aure.
Ya cika da takaici ya rasa yadda zai yi Fatiti ta waye ta san zamani an ci gaba akwai abubuwa da yawa a gidan aure ba maganar kishiya ba ne kadai.
Ya yi sallama bayan an amsa ya shiga sai kowacce ta hau saka hijabi ana ta sussune kai qasa bayan sun gaishe shi sun yi masa sannu da zuwa sai suka fara harhada kayansu zasu tafi. Za ka iya ganin mamaki marar musaltuwa daga idanuwan Fatiti ga murna ana yi amma ana shan kunu irin jan ajin nan dan yayi mata laifi fushi take.
Shi bai san kan gidan ba bai san falo ba, bai san daki ba, ya rasa ma in da zai nufa. Ta miqe tsaye tana kallonsa,
Ya harare ta ya ce "ki kai ni daki mana kin tsaya kina kallona."
Ta wuce gaba ya bi ta a baya suka shiga daki, ya ga daki shar kamar na amarya ya sha sabuwar leda da fenti ga sabon gado.
Ya dube ta yayi murmushi ya ce amarya amma dakin namu yayi kyau."
Ta tabe baki ta ce "eh dole ka ce haka mana saboda ka kai ni ka baro ni, an zubar da ni an wulaqanta ni."
Ta fice a fusace ya bi ta da kallo cike da takaici. Ya koma gefen gado ya zauna babu abinda ya fara fado masa a rai sai katafaren gadon Mufidah da qamshin dakinta. Ya tuna irin fara'ar da take tarar sa da ita, ya lumshe ido, sai yanzu yake da na sanin da ya yi saving lambarta a wancan lokacin da Dr.Isa ya bashi kuma da kunya yanzu ya kira Dakta ya ce ya bashi lambarta bayan dazun nan suka yi masa ba zata suka bashi mamaki.
Qawayen Fatiti su takwas suka yi mata sallama suka watse. Gashi gidan babu abinci dukka baqin sun cinye, bai ce mata zai zo ba bata dafa da shi ba.
Da ya ji sun fita sai ya fito tsakar gida yana hararar bola da tarkacen da aka barbaza a tsakar gidan kamar ba gidan.mace ba.
Ta gane da hakan sai ta hau fada tana cewa "ai baqi na yi kuma su na da yara ba laifina ba ne."
Ya tabe baki yayi tsaki ya ce "ina yaran nawa suke da kike rainon 'yayan wasu? Ban ga nawa yaran ko daya."
Ta fada a fusace "sun tafi gidan Auti Rabi acan suka.wuni."
Daga nan ya tabbatar yayi kuskire da ya kama gida a tsakiyar unguwar iyayensu, ba zasu rabu da yin baqi ba, ba zasu rabu da gulma da -yan saka ido ba, haka yaransa zasu koyi yawo dan duk inda suka waiga gidan.dangi ne shiga kawai zasu.
Ya fusata ya ce "ki yi musu waya a kawo min yarana."
Ta jawo wata qaramar waya Nokia ta matso lambar Rabi, ashe har waya ta siya amma bata taba kiransa ba. Bayan sun gaisa da Rabi ta ce "a kawo yara yanzu ga babansu ya dawo."
Usman ya shiga falo ya zauna, tana kallon kujeru masu kyau har sun fi na su na Bauchi kyau. Fatiti tana ta cuku-cukun gyaran tsakar gida da dora girki, wayar ta ce ta yi qara tana dubawa ta ga Safiya ce.
Ta dauka da sauri ta amsa cike da murna ta ce "qawata yaya Bauchi? Na yi ta ganin missed calls dinki kin san kano ana ta hidima, bana rabuwa da baqi, ina ta so in kira ki daman."
Safiya ta gyara zama ta fara kwararowa Fatiti wani labari wanda ta ji gaba daya ta fita hayyacinta, ta ji kamar a mafarki take ba a ido biyu ba.Yadda Usman ya ga ta shigo falon zani yana ballewa, dankwali a hannu sai ya tsorata, wayar ce dai a maqale a jikin kunnenta tana sauraron baqin labarin wanda gara a bata labarin mutuwa da a bata irinsa. Sai zufa take ta hadawa, ta tsaya a kan Usman ta riqe qugu tana ta girgiza ji take kamar ta kifa masa mari. Ta yi salati wani lokacin ta saki babban ashar duk ita kadai. Bai tashi fahimta ba sai da ya ji an ambaci sunan Mufidah sannan ya tabbatar munafukar ce ta kawo labari.
Ya ji gabansa ya fadi dan ya tabbatar yau ba zaa bari ya kwanta haqarqarinsa ya huta ba, gashi ya gaji.
Ta dora hannu aka ta kwalla qara sai ta baje akan kafet ta yi zaman 'yan bori, ta dauki kuka kamar wacce aka fadawa saqon mutuwa.
Kafin ya tambaya sai da ya kawo mata agaji, yana qoqarin ya daga ta tsaye, sai ta mauje hannunsa.
Ta ce "yau sai an yi bala'in da baa taba yi ba, ni da kai. Cin amanata za ka yi ashe shiyasa ka kore ni ka tafi ka zauna tare da waccan mayyar har ana ganinku tare.
Sai na kashe Mufidah, sai dai ka zaba ko ni ko ita."
Usman ya daka mata tsawa ya ce "kin kuwa san me kike cewa? Daga ta fada miki gulma a waya ai sai ki tsaya ki yi bincike ki sani hakan din ne ko ba haka ba ne, ba wai ki yanke hukunci ba."
Ta ce "babu wani bincike daman an ce su Malam babba sun je Bauchi har sun samo naira dubu dari-dari wai ka yi musu hanya sun je saukar karatun qur'ani ashe ruqiyya suka yiwa waccan matsafiyar dan ka samu ka aure ta. Wallahi sai dai dukka a rasa daga ni har kai babu mai zama a duniyar in dai ka yi aure."
Ya fada a bayyane "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. ki na da hankali kuwa?"
Wani saurayi ne ya shigo mai suna Nura tare da yaran, su ka hau tsalle da murna da ganin mahaifi. Bayan Nura ya gaishe suya tafi. Usman ya fita mota ya dauko musu himilin alewoyi da biskit ya na raba musu. Kallo daya Fatiti ta yiwa biskit da alewar ta tabbatar irin wacce Mufidah ta saba raba musu ce, dan haka ita ce ta bashi ya kawo babu ko tantama.
Ta yi kukan kura ta dinga cilli da alewoyi nan da biskit, dakyar Usman ya riqe ta. Ta haukace gaba daya, yayi-yayi ta tsaya ta saurare shi ta qi.
Mayafinta ta dauka ta fice daga gidan da alama ta yi yaji, ta bar shi da yara. Ya ma fi son ta tafi in ta huce sai ta dawo dan ba zai iya hana ta abinda take yi yanzu ba, ranta ya riga da ya baci.
Waya ya dauko ya kira qannensa 'yan mata Amal da Aisha ya ce su zo su taya Fatiti aiki su shiryo su zo da shirin kwana, sun zaci raguna ya yanka zasu yi suya, suka harhado da sauri suka taho cike da murna, sai suka iske shi, shi kadai daga shi sai yara.
Ya gargade su da su yi shiru kada su fadawa kowa su kular masa da yaran zai fita ya dawo. Da ya je gidan su Fatiti sai ya iske bata nan,