KISHIN BALBAL BOOK 3 HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   6 / 10

15K to 18K   out of 28.9K words

zaka yarda ka tozarta wanda kake so? Sannan kin yi maganar mayya ce matsafiya? Daman akwai maita? Ko za ki iya kawo mana dalilan da ya sa kika ce matsafiya ce?"
Fatiti ta hau soki burutsu ta yi gaba ta yi baya.
Mahaifin Usman ya ce "saboda wannan dalilin ya sa kika tafi Bauchi kika yi fada da ita, ba tare da izinin mijinki ba?"
Fatiti ta yi shiru dan ta rasa amsar da zata bayar.
Malaman nan suka bayar da cikekken labarin larurar Mufidah da kuma yadda suka je suka taimaka mata har ta sami lafiya. Aka sake dawowa kan Usman aka dinga jero masa tambayoyi a dole ya bode baki ya fara magana. Ya fadi abinda ya sa ya rasa aiki da yadda Mufidah ta taimake su da yadda shima ya taimaka mata wajen larurar ciwonta, sai kawai Fatiti ta dauki zafi.
Ya ci gaba da bada labarin Jaliliah da kudin da suke bin sa, sannan ya fadi abubuwan da ta aikwatawa Mufidah da Jalilah da ta tafi Bauchi. Sai kowa ya dauki salati.
Mahaifiyar Usman ta fusata ta yi masa tsawa ta ce "kai ba namiji ba ne dan ka na so ka qara aure sai ya zama fada? Tsoronta kake ji ne da zaka kasa fada mana ka hadu da Mufidah kana so ba?"
Baban Fatiti ya ce "Usman in ka na son Mufidah ka aure ta izini nake baka ba shawara ba."
Fatiti ta kwalla qara ta ce "Baba da bakinka ka ke cewa ayi min kishiya?"
Usman ya yi shiru ya kasa magana.
Mahaifinsa ya ce "ka kira Mufidah a gabanmu ka fada mata za ka aure ta nan da wata guda."
Usman ya hau lalube-lalube kamar mai neman wayarsa alhali gata nan a hannunsa. Cikin fargaba ya kira Mufidah a waya, nan da nan ta amsa zata yi masa kalaman soyayya yayi sauri ya katse ta,ya ce mata " ina tare da mahaifana ne sun ce in kira in sanar da ke zasu zo neman aurenmu. Abuja zaau je ko Bauchi? su na so a daura nan da watannin uku."
Mahaifin Usman ya ce "jiran me zaa yi har na wata uku? Wata daya ya isa."
Mahaifiyar Usman ta ce "ya na buqatar lokaci, mutumin da baya aiki. Dan haka a ka bari akan watanni ukun.
Mufidah tana ta mamaki tana tsaye sai ta zauna ta ce " ok babu damuwa, zan sanar da su."
Usman ya yi godiya sannan ya kashe waya.
Fatiti ta dauki salati "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun, daga iyayena har surukaina babu mai bin bayana. Wallahi in.ya qara aure mutuwa zan yi.
Su ka ce kin dade a ki mutu ba, aure kamar an qara an gama.
Babu mai jin tausayin Fatiti a wajen sai mahaifiyarta da alama bata ji dadin wannan hukuncin ba. Ta ce " ayi mata fada akan abinda ta yi ba sai an sa yayi mata kishiya ba."
Haka dai aka yi.kan fatiti aka dinga yi mata fada, kuma aka gindaya mata sharudda kala-kala na zaman lafiya ko kuma a dauki matakin da ya fi wannan.
Aka ce su tashi su tafi gida baa so a sake jin wannan maganar.
Fatiti ta na ta runguza kuka, su ka fito suka tafi gida.Ta dinga roqon Usman akan ya janye maganar auren Mufidah zata gyara halinta.
Ya ce "ai auren nan ma ke ce kika hada shi, kuma ke ce kika jawo zaa daura shi, kika gayyato mana mutane, kika sanarwa iyayenmu cewa na ce zan yi aure, kika fada musu zan yi aure alhali ban taba furtawa kowa ba, ke kika sa nuna Mufidah kika fito da ita kika haska ta kowa ma ya santa. Dan haka na gode miki sosai zafin kishi yayi min rana."
Kwanakin da yayi ya ga canji, ta saduda ta fara biyayya, saboda ya janye ya fasa. Ko ruwa zaa bashi sai ta durqusa har qasa, haka abinci kala-kala take dafa masa. Ruwan wanka ma sai ta kai, a raka shi da tawul har bakin bandaki. Duk dai dan ta lallashi shi kada ya qara aure.
Imam Malik ya kira shi a waya ya ce zai shigo Bauchi wani satin, ya na so su zauna su yi magana..Usman ya ce kafin nan shima ma ya dawo Bauchi.
Usman ya na yawan fita daga gida ya tafi ya sami waje mai nisa ya zauna ya yi ta yin waya da Mufidah. Soyaya ta nuna kowa yana sauqi.
Sai da Usman ya yi sati biyu a Kano sannan ya shirya komawa Bauchi. Tunda Fatiti ta san zai koma tun ana washegari ta kasa rintsawa, ta yi ta kuka har ta gaji, kukan da ba zai yi mata amfani ba, dan Usman ya daina damuwa da hannayenta.
Ta shiga roqonsa akan ya mayar da ita Bauchi kusa da Mufidah, gara dai in su na ganin juna. Ko amsa bai bata ba, ya fice.
Gidan mahaifansa ya je su ka tattauna akan yadda zaa je gaisuwar aure. Su ka ce Malaman nan sun tabbatar musu yarinyar nan 'yar mutunci ce ita da yayanta sun san darajar dan adam.
Usman ya sanar musu rashin aikin ne ba zai bari ya yi auren da wuri ba amma zai je ya nemi abin yi. A nan aka tsaya yayi musu sallama ya basu kudin abinci kamar yadda ya saba ya tafi su ka bishi da addu'a.
Da ya zo zai tafi sai Fatiti ta kusa hadiyar zuciya, tana magana ta na sheshsheqa kamar zata shide, ya san tuggunta dan haka ko kallo bata ishe shi ba.Ya ajiye mata kudi cefane ya fita. Yaransa ne suka bashi tausayi har sai da idanuwansa suka cika da hawaye. Sun saka shi kwalla saboda kukan da suke ta yi, su na cewa sai sun bi shi.
Da kyar ya samu ya tafi, yana tuqi yana kuka. Ya ce a ransa "in ba dole ba yaya zaa yi ya rabu da yaransa?
Ya isa Bauchi da rana bai je gida ba, gidan abokin aikinsa Sulainan ya wuce, dan ya ce yana nemansa akwai wani labari daga wajen aiki.
A gidan Sulaiman ya ci abincin rana, suka fara maganar aiki. Sai Usman ya cika da mamaki da jin abinda Sulaiman yake fadi.
Sulaiman ya ce an fara qishin-qishin dawo da kai aiki dan rannan aka dauko file dinka aka dinga cike-cike, an ce daga can sama ne aka yi magana aka bayar order aka ce a dawo da kai aikinka sannan a baka dukkan haqqunanka na tsawon shekarun da baa biyansa. An ce sanatoci guda uku ne suka yi magana a akan case dinka.
Usman ya bude baki yana kallon Sulaiman, duba na rashin fahimta kuma ya fara tunanin ko Sulaiman ya na buqatar ruqiyya ne, ko kuwa ya fara shan kwaya ne? Dan da alama ya fara kwanccewa.
Sulaiman.ya lura da irin kallon da Usman yake yi masa, na rashin yarda.
Ya ci gaba da cewa "shiyasa ban fada maka ba, dan mun hadu sau biyu da kai na ji baka yi min maganar ba. Amma ka jira za ka ga kira kwanan nan, za ka tabbatar da maganata gaskiya ce."
Usman ya yi dariya ya ce "ai dole in tsaya ina kallonka mana, ni Usman ina na san wani kansila ma.balle sanatoci har guda uku. Wataqila wani Usman din ne suka yi kuskure suke tunanin nine. Ni din wa? Ina ta addu'a dai, Allah da Ya halicci bawanSa shi ya san ta inda zai kawo masa mafita. A hakan ma Alhamdulullah na riqe Allah kuma Ya na ta rufa min asiri, ban tozarta ba."
Su ka kwashe da dariya suka tafa hannu. Usman ya yi masa sallama ya shiga mota ya nufi gidansa.
Bai fadawa Mufidah zai dawo a yau ba, dan yana so yayi mata ba zata. Kuma bai manta da yi mata tsarabar gurasa ba, sabuwar yi mai dumi, mai laushi dan sun taba hirar ta ita ta nuna masa tana son gurasar Kano sosai.
Ya shigo cikin get din gidan, Tanimu ya gaishe shi sannan ya wuce wajen da suke ajiye motocinsu. Ya na ta waiwaye amma bai ga kwankwatsatstsiyar motar Mufidah ba, ya na so ya ga barnar da aka yi mata.
Ya na fitowa daga cikin mota sai ya ji an rufe masa idanuwa da tafin hannu daga bayansa, kamar irin wasan yaran nan. Wani hannu ne lallausa gami da wani qamshi mai dadi ne ya daki hancinsa. Ya zabura ya bambare hannun da sauri sannan ya waiwaya dan ya ga wacce yayi masa haka. Da alama dai hannun mace ne.
Ya fi zaton Mufidah ce amma anya Mufidah zata iya taba shi a cikin mutane haka? Ai bata da irin wannan rawar kan, ita din nutsatstsiya ce mai kunya ga kamun kai. Amma idan ita ce tabbas bata kyauta masa ba, bai kamata ta yi masa haka ba ga masu gadi, ga makwabta. In suka gani yaya zasu dauke shi kenan?
Murjanatu Bibi ya gani tana dariya. Dan haka sai ya daina mamaki ya san sai ita din, za ta iya yin abinda ya fi haka ma.
Ya yi tsaki ya rufe qofar mota da sauri zai bar wajen, sai ya ga Mufidah ta tare gabansa, Murjanatu ta tare bayansa suka saka shi a tsakiya dan haka sai ya juya ya tsaya cak ya dora hannayensa a saman motar, yana ta huci ya sha kunu.
Murjanatu ta ce "na fada miki mutumin nan fushi yake yi da ni, baya amsa wayata amma kin ce ba haka yake ba wai Usman baya fushi. Nima a sanina da shi baya fushi amma dai yanzu na yarda yayi fushi da ni."
Mufidah ta fada cikin sanyayyiyar murya "sannu da zuwa angona. Ka yafe mana, ka yi mana afuwa, mun yarda mun yi maka laifi. Qawata ta ci albarkata ka yafe mata, ta ce bata san ma abinda ta yi maka ba."
Murjanatu ta ce idan bai yi dariya ba zata yi masa cakulkuli, da gaske take kuwa dan har ta kawo hannayenta gefen cikinsa zata yi masa cakukkulin, ta san Ustaz ne ba zai bari ayi ba. Sai ya yi sauri ya goce, su dukka suka yi dariya.
Ya bude mota ya dauko qatuwar leda mai dauke da gurasa ya miqawa Mufidah. Ta cika da mamaki ta durqusa ta karba ta yi godiya. Usman ne ya hada ido da Safiya tana leqensu ta wundon dakinta. Ya fada a zuciyarsa "wahalallu ku na bawa kanku wahala bayan babu abinda zaa fasa.
Su ka dunguma suka haye sama, a falon Mufidah suka zauna, sai da ta juye a kwano sannan ta ga ashe gura ce, ta yi ta murna ta sake yi masa godiya.Ta yi mamakin yadda Usman ya gane abinda take matuqar so.
Murjanatu Bibi ta zauna suka yi magana da Usman ta fahimta, ta ce ta rasa dalilin da ya sa ta ji wani tsoro da fargaba a duk sanda ta hango shi, bata iya tsayawa da shi sai ta ga kamar ta ga zaki.
Murjanatu ta ci gaba da cewa "amma da na fadawa Mufidah yanayin da nake ji dan a lokacin na kasa zaman gidan nan ma, sai ta ce min ba kya yin addu'a ne, ki riqe azkhar an raba ku ne. Ka san qawata wani lokaci in ta ga dama ta na fadar abubuwa, in bata ga dama ba kuwa ko an tambaye ta ba zata fada ba. Ka san idanuwanta guda goma ne. Yanzu Usman ka yarda haka kawai zan hau gudunka?"
Ya yi shiru ya na tunani a cikin zuciyarsa yana ta tantance maganar Murjanatu akwai qamshin gaskiya, tabbas biri yayi kama da mutum, a wannan lokacin ne Fatiti da Safiya suke yin qaryar zuwa seminar. Daga baya ya gane babu wata semina, asiri suka je aka yi musu aka farraqashi da Murjanatu da Mufidah hakan ne kuma ya jawo matsalarka ta girmama, Dan babu abinda aka yiwa Murjanatu ta bar gidan kuma daga lokacin bata qara yarda sun hadu ba. Gara ma Dakta shi daga baya ya ce su na waya kuma yana zuwa gidansu su gaisa. Tabbas Fatiti ta dade tana cuta ta tana rugurguza min ci gaban rayuwata."
Murjanatu ce ta katse tunanin da ya tsunduma yana yi. Ta ce "an fi watanni biyu da Mufidah ta takura min akan sai na yi magana da manyan da na sani akan a mayar da kai aikinka. Na ce ta bari in zo qasar amma ta ce ina daga nan ma ta san zan iya yin komai.Ta hana ni bacci ta ce sai na taimaka dan ta ga alamar ka shiga wani hali, yaranka basa zuwa makaranta, ga kudin hayarku ya qare Godwin ya takura muku.
To a dole fa na dauko waya na yi ta bubbugawa wadanda na san zasu iya taimakawa, ina ta bibiya.
Na yi magana da sanatoci guda uku, dukka sun yi min alqawari za su sa a mayar da kai aikinka kuma a biya ka dukkan haqqunanka da aka riqe."
Sai yanzu ya gasgata maganar da Sulaiman yake fada masa dazu tabbas gaskiya ya fada masa ashe. Farin ciki ya rufe zuciyar Usman nan da nan ya warware ya fara murna yana godiya.
Murjanatu ta ga fuska ta ce da wa Allah Ya hada ni in ba da ku ba, ta dinga yi musu tsiya akan yadda dambe da fada da tsana ya juye soyayya a tsakanin su. Ta dinga yi musu dariya tana mayar da labari.
Da alama basa so ta dinga tuna musu baya. Mufidah dai ta qi kulla ta tana ta qoqarin hadawa angonta abinci kala- kala da kanta dan Patient ta tafi. Ta kawo masa wannan ta ajiye a gabansa, ta hado masa wancan.
Shi dai yana zaune ya rasa ma abinda zai ce, ya na ta bin ta da kallo, ya ji sonta ya qaru a ransa kamar zai hadiye ta.Ya ji ta sake shiga ransa tunda ta yi masa wannan jahadi ta sa zaa mayar da shi aiki. Abin mamakin tun ba a yanzu ta fara kokarin nan ba, tun a baya ne, a lokacin da suke tsakiyar yin fada. Duk da fadan da suke yi amma ta damu da halin wahalar da suke ciki tana so ta taimake su.Ya tabbatar wannan tausayin ne ya sa ta biya masu kudin haya. Ka ga masu yi dan Allah.
Fatiti ta yiwa matar nan qazafi ba dan kadan ba, babu wani qaton arnan da Mufidah take kawo gida, bayan yayanta Imam Malik babu mai shiga gidanta.
Ashe shine mutumin nan mai rungumarta ya na share mata hawaye idan tana cikin damuwa. Nima har na yarda da sharrin Fatiti na shiga zarginta.Tabbas idan Mufidah bata yafe mana ba sai mun ci wuta."
Kwalla ce ta cika masa ido ya na damben mayar da ita. Hannun Murjanatu ya gani ta na dagawa daidai fuskarsa.
Ya zabura ya dube ta da sauri, ta yi dariya ta ce " kai ka kafawa qawata ido, har ka fita daga cikin duniyar da muke, ka fada kogin tunaninta."
Wannan karon kallon juna suka yi shi da Mufidah suka yiwa juna murmushi.
Ya gyara zama ya ce "ai dole in bi ta da kallo Mufidah abar a kalla ce, ba ki ganta ba ne? Kyakywa masha Allah. Ina yiwa Allah godiya da Ya bani ita. Ba ta gajiya da yi min hidima, lallai ana ji da ni. Tun yanzu na zama dan Lele. Toh ina ga idan na zama angonta kuma?"
Murjanatu ta daka tsalle ta miqe tsaye ya ce "wallahi ba zata sabu ba, ba zata yarda ba a kira Dr.Isa itama a zo a gama maganar nan. Sai a lokacin ta sanarwa Usman su ma soyayyarsu ta nuna.
Da kanta ta kira shi ta ce ya zo ana nemansa a saman Mufidah ga Usman ma ya zo. Dr. Isa ya cika da murna yana rawar jiki ya ce nan da awa daya gashi nan zuwa.
Wani abu ne ya bawa Usman mamaki, Jalila ce ta dinga kira, sai ya qi dauka kasancewar wayar a silent take daman. Sai ta turo masa wasu sakonni da bai gane kansu ba. Sannan ta sake kira wannan karon sai ya amsa yayi shiru yana sauraronta,

6 / 10