KISHIN BALBAL BOOK 3 HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romance

Chapter   1 / 10

1 to 3K   out of 28.9K words

??????>?? ?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????[? ???bjbj???? ;J?????C???????????MMM????aaa8???a
3


NA














JAMILA UMAR TANKO
(JUT)

Matashiya:
Assalamu alaikum wararahamatullah. Tsofaffi da sababbin masoyana masu bibiyar rubutuna. Ina yi muku Albishir da fitowar sabon labarina mai tafe da sabon salo , mai fadakarwa da nishadantarwa wato KISHIN BAL-BAL part 1 ,2 and 3.

Godiya:
Bismillahi Rahmanir Rahim
Na fara da sunan Allah mai rahama mai jin qai. Dukkan godiya ta tabbata ga ubangijin talikai mai kowa mai komai. Ina addua yadda Allah Ya bani ikon farawa Ya bani ikon kammalawa lafiya. Allah Ya dora alqalamina akan rubuta daidai ya kiyayeni da rubuta kuskure.Amin.

Sadaukarwa:
Ga dukka matan da suke yiwa mazansu uzuri, su ka iya danne da saita kansu wajen fito da mugun kishi.

An fara rubuta shi ranar 24/06/2022.
Qarfe 8:30am.








Su Fatiti an tafi Kano gashi bata san abinda yake faruwa da Usman ba kuma.
Usman yayi waya da mahaifinsa sannan ya yi waya da manyan Malamansa game da neman haske da shawarwari akan matsalar Mufidah. Da su ka tambaye shi meye alaqar dake tsakaninsa da ita sai ya ce musu maqwabciyarsa ce, abokiyar aikinsa, kuma aminiya ce. Ya takaice musu cewar ta taimake shi sosai a rayuwa, ya na so shima ya taimake ta, ace ya zamanto silar samun lafiyarta don ta samu itama ta yi aure ta hayayyafa dan a yanzu shekarunka sun kai ashirin da bakwai zuwa da takwas ko maganar aure bata son ji.
Sun tausaya mata matuqa kowa ya bashi ta sa dubara ta yadda zai bi da aljanun wajen ruqiyya da tofi a cikin ruwa a watsa mata ruwan, sannan ta sha, sai turaren aljanu masu qarfi da kuma turaren almiski masu korar shaidanu.
Sai dokokin da zata kiyaye kamar yawan zama da alwallah da kuma suturce jikinta da daina jin kide-kide ta awaits jin karatun qur'ani. Wasu suka aiko masa da magunguna ta tasha, wasu kuma ya shiga kasuwa ya hado a nan Bauchi. Sai dai ta yadda zai tunkaro Mufidah da wadannan kayan aikin ne bai sani ba.
Ya ci gaba da tura mata hayaqi a bakin qofarsa in da ta yi boda da qofarta, sai ya shige gida ya bari anan. Sai ya kasa kunne ya ji yadda take shige da fice tana buga qofofin gidanta. Ko bacci take sai ta farka tun tana ta atishawa a cikin gida har sai ta fito bakin qofarta ta tsaya sai ta iske babu kowa, ya dauke kaskon ya shige cikin gida da sauri ya rufe qofarsa.
Sharar safe da ta daren ma ta daina, idan ta tafi wajen aiki dakyar ta ke daurewa ta dawo gidan saboda turaren nan. Ta na dawowa gida, idan ya ga shigarta sai ya tuqaqa wannan turare ya shige gidansa ya kulle, ko ta fito ba za ta ganshi ba. Ta na cikin gida kamar zata yi hauka, hawaye da atishawa da murza ido baa magana.
Usman ya fito daga masallacin qofar gidansu bayan sallar magruba. Wani kamilin mutum ne yayi masa sallama a bayansa, ya juyo da sauri ya amsa gami da miqa masa hannu suka gaisa.
Mutumin ya tambaya "kai ne Usman?"
Sai Usman ya cika da mamaki ya amsa "eh nine."
Mutum ya gabatar da kansa shi ma ya ce " sunana Imam malik Hamza ni yaya ne a wajen Bar.Mufidah Hamza wato maqwabciyarka."
Sai Usman ya ji gabansa ya fadi ya tabbatar a kwai magana. Imam Malik ya nemi da su koma gefe zasu yi magana, haka kuwa aka yi su ka koma gefe.
Imam Malik ya na ta bayani yayin da kan Usman ya daure ya kasa fahimtar maganar da Imam malik yake yi.
Imam Malik ya ci gaba da cewa "Mufidah dai ita kadai ce qanwata a duniya da nake ji da ita, bana so komai ya dame ta, na tabbatar bata da neman tashin hankali tana zaune da kowa lafiya. Amma ta na yawan kawo qarar Usman da Fatiti su na takura mata dan haka ma take so ta tashi ta bar gida."
Usman ya tambaya "kamar me da me ta ce ana yi mata?"
Imam Malik ya ce "abubuwa da yawa amma a cikin satin nan dai sunanka take ta kira wai ka takura mata, ta rasa in da zata saka kanta."
Usman ya yi murmushi ya ce "baka tambaye ta dame na takura ma ta ba? A iya sanina Mufidah ba ma haduwa, ba ta zuwa gidana, ba na zuwa gidanta, ba ma gaisawa ko a hanya. Toh me zai hada ni da ita?"
Sai imam malik ya yi shiru can ya ce " babu wata hayaniya da ta hada ku a cikin satin nan?"
Usman ya ce "wallahi ko daya babu abinda ya hada mu."
Da Usman ya ga Imam Malik ya shiga dimuwa sai ya fitar da shi.
Ya ce " Na san ka san matsalarta ta aljanu ai ko? Toh ni kuma mai ruqiyya ne ina cire aljanu, wataqila turaren aljanu da adduoi yi gidana su ne suke damunta. Kuma a a gidana nake yi ba gidanta nake Shiga in yi ba."
Wannan karon Imam Malik zabura yayi ya kama hannun Usman ya na karkarwa ya ce "Usman! ka taimake ta, ka yi mana wannan jihadin, ka raba ta da wannan masifa. In akwai abinda ya dame ni a duniya bai wuce ciwon Mufidah ba, dan duk malaman da nake kawowa har su yi su gama bata taba yin motsi ba SSI su kwashe kayansu su tafi su ce na ta manyan ne. Sun hana ta a aure, ba ta son maganar namiji ko kadan. Yanzu na gane dalilin fadan na ku ai sai ta yi ta cewa ka takura mata amma ta qi fadar takurar."
Usman ya yi murmushi ya ce "zan taimaka iya qoqarina, nima na fahimci hakan."
Su ka fara shawarwari ta in da zaa bullowa al'amarin. Mufidah dai ta na gida da akwatunanta a gaba, ta ce yau qafarta qafar yayanta ba za ta zauna a gidan ba.
Su ka dinguma suka shiga gidan, Mufidah tana zauna ta buga tagumi idanuwa sun yi mata jajawur saboda kuka, sanye take da baqar abaya da dankwalinta yau an yi shiga ta kammala saboda babban yaya.
Ta na daga ido ta ga Usman, sai ta ji ranta ya baci, ta zabura ta miqe tsaye ta tare gaban Usman a fusace, bata yi magana ba dai amma alamu sun nuna ba zai shigo mata gida ba.
Imam Malik zai yi mata tsawa, Usman ya sa hannu ya dakatar da shi, alamar yayi shiru.
Usman ya yi murmushi ya ce mata "na zo ne in baki haquri akan laifukan da na yi miki wadanda na sani da wadanda ban sani ba.
Da alama zuciyarta ta yi sanyi sai ta koma ta zauna, ta dora qafa daya kan daya tana ta girgiza. Usman ya zauna akan kujerar da yake fuskantarta aka hau kallon kallo.
Imam Malik ya samu kujera ya zauna a gefensu ya na ta kallon kowannensu. Usman ya yi bismillah ya fara karatu.
Mufidah ta daka tsalle ta miqe tsaye ta ce "ka rufe mana baki Malam, mun fi karfinka."
Imam Malik ya yi masa sigina alamar ya ci gaba. Usman ya ce bari ya je gida ya dauko kayan aiki.
Mufida ta shiga cikin dakinta da sauri wannan karon ta canja kamanni, ta canja shiga da mucizai guda biya ta fito a rataye a wuyanta daga ita sai riga shima da wando dogo jeans.
Imam Malik ya zabura ya daka tsalle ya bude qofa zai arta waje da gudu, sai ya ci karo da Usman yana shigowa.
Usman ya umarce shi da ya shigo ya zauna babu abinda za ta yi masa. Imam Malik ya ga bala'i can kuryar falon ya je ya tsaya dan yana tsoron ya zauna. Sannan ya ce kada a datse qofa saboda ko abin gudu ne ya taso ya samu hanya a sauqaqe.

Usman ya na zaune yana fuskantarta tun yana karatun qur'ani a hankali har ya fara yi da qarfi, tun tana hararar sa har ta ji ba zata iya daurewa ba daga ita har mucizan ta sai mutsu mutsu suke, ta ja dogon tsaki ta tashi ta shiga daki.
Imam Malik ya na magana cikin rada ya ce "mu bita cikin dakin."
Usman ya girgiza kai ya ce "ka barta kawai."
Usman ya kunna gawayi cikin kasko ya dinga bunkuda turaren aljanu, sannan ya tura kaskon cikin koridon da dakunan suke, ko mintina biyar baa yi ba sai ga Mufidah ta fito tana layi kamar zata fadi, wannan karon ita kadai ce babu mucizan.
Usman ya cewa Imam ya dauko mata hijabi ya saka mata, nan da nan ya Shiga daki da sauri ya dauko ya zo ya saka mata, sai kuma ya riqe ta dan tana qoqarin faduwa. Ta fusge ta tafi ta fada akan doguwar kujera, Usman ya sami damar yi mata karatu a kunnuwanta da qarfi. Ya na ta yi har aka samu su ka fara yin magana, masu gardama na yi sai da suka ji wuya suka fita masu saukin kai su ka fita salin alin gami da yin alqawarin ba zasu dawo ba har abada. Sun kwatanta wannan rana ita ce rana mai kama da tashin qiyamar su dan gaba daya sun gigita wasu sun kama da wuta.
Imam Malik ya fashe da kukan dadi dan ya ga alama an kwato qanwarsa daga hannun wadanda suka kwace ta tsawon shekaru masu yawa. Bayan fitar aljanun Mufidah ta jigata, sai da ta yi baccin awanni kafin ta farka Usman ya bawa Imam Malik magunguna na mai kala-kala ya shashshafa mata a qofofin hanci da kunnuwanta.
Ta farka da salati da kalmar shahada a bakinta, haman ya nuna aiki ya yi kyau kenan. Ta bude ido ta dubi Usman ta juya ta dubi yayanta, sai ta fashe kuka ta qanwame yayanta. Shima hawaye yake yayin da tausayi ya sa kwalla ta cikawa Usman idanuwa.
Usman ya yi hamdala ya ce " aiki ya yi kyau yanzu abinda ya rage shine ta shiga ta dauko mucizan nan da duk sauran kayansu ta zo mu je cikin daji ta ajiye su."
Da alama bata gane halinda ake ciki ba sai da Imam Malik ya ja hannunta suka shiga daki ya yi mata bayani gami da lallaba ta sannan ta dinga zaqulu terkace kala-kala wanda suka saka ta, ta siya ta ajiye musu, irin su wata kwarya me nono, su tulu da tukwanen qasa da layu da fatar mucizai, fatar kuraye, fatar zaki da dai sauransu.
Aka cika manyan jakunkuna ta dauki kwaryar mucizai su dukka su ka shiga mota aka yi ta tafiya mai nisa a cikin daji sannan suka tsaya aka zubar da mucizai aka qone wadannan tarkacen.
Tabbas ko baa fada maka ba kowa ya ga Mufidah ya san ta canza. Ita kanta sai ta ji ta saqayau, dan ada ji take kamar a daure take.
Da suka dawo Usman ya ce yayi waya da wasu manyan malamansa guda biyu su ne ma suka koya masa yadda ake yin ruqiyyar, ya na so su zo su sake bincike ta ko akwai wasu sannan a toshe dukka qofofin da suka huda a jikinta dan kada wasu su shiga.
Nan da nan Imam Malik ya amince ya na ta godiya sannan ya tambaya ko nawa zaa tura musu kudin mota? Usman ya ce a bari zai biya.
Washe gari da rana sai ga malamai sun iso, a cikin falon Usman suka zazzauna bayan sun yi sallah sai ya fita ya siyo musu suka ci, sannan ya kira Imam Malik a waya.
Ashe ma a gidan Mufidah ya kwana tare da ita sai kuma daya daga cikin masu aikin Murjanatu Bibi itama ta zo mai su na Patient. Dan ta kula da ita sosai wajen dafa abinci da sauransu.
Nan da nan Imam ya ce su shigo gidan, kafin su fito ma ya bude musu qofar falo. Sannan ya je har daki ya lallaba Mufidah ya ce ta fito, zazzabi take ta yi da ciwon gabobi, tabbas dole ta ji a jikinta irin wannan aljanu da suka yi mata sansani a jikinta shekara da shekaru.
Ta fito sanye da hijabinata har qasa ta zauna a hankali akan kujera, sannan ta gashe su. Su ka ce ta zo gabansu ta zauna a qasa a kan kafet, ta na zauna su na ta karatu da tofi sai ta yi miqa ta kwanta, ashe da sauran aljani guda daya shine bai fita ba, babbansu ne uban gayya shine ma wanda ya aure ta.
Aljani ya ce ba zai fita ba ai matarsa ce, sadaki ya biya. Aka dinga fafatawa an sha wuya daga qarshe dai sai bayan sallar isha'i yayi mubaya'a ya yarda zai kwashe kayansa ya fita, kuma ya fita bayan ya qone.
Daga nan su ka yi mata addu'oi har sai da suka tabbatar an toshe duk wata hudar da aljanu ba za su sake iya dawowa ba.
Mufidah ta tashi daram ta zauna idanuwanta sun rusuna ta daina kallon nan da take yiwa kowa ido a tsatstsaye.
Su ka yi mata nasiha, suka yi mata wa'azi akan ta riqe addua musamman azkhar ta safe da yamma. Su ka bata shawarwarin yadda zata dinga kula da kanta da kare hakkunan Allah ta hanyar shari'ah, ta suturta jikinta ta yadda aljanu ba su isa ya dawo jikinta ba. Su ka bata magunguna na turare da wanka da sha da shafawa.
Ta karba ta yi godiya sannan ta tashi ta shiga daki da alama kuka take ta yi ba qaqqautawa.
Ashe abinci kala-kala Imam ya sa Patient ta daddafa, ga kaji ga shinkafa, ga tuwon shinkafa, ga sakwara da miyar ganye ta sha naman kaji, jan nama, Kifi da ganda. Ga lemo kala-kala, ga shayi da kunu. Aka cika kan tebur da abinci suka hau su dukka suka ci, suka qoshi ana ci ana hira.
Tabbas Imam malik ya ji Usman ya kwanta masa a rai musamman da suka yi hira sosai ya tabbatar Usman yana da ilimi na boko da kur'ani, sannan ya na da nutsuwa, ga ladabi da biyayya.
A cikin hirar ta su dai da tambayoyin da yake ta jero masa, Usman ya shaida masa ya na da mata daya da yara hudu kuma shi mutumin Kano ne amma bai ce masa baya aiki ba yanzu.
Naira dubu dari-dari Imam ya bawa Malaman nan guda biyu, Usman yayi-yayi kada ya basu komai. Ya ce ai bai isa ya biya su ladan abinda su ka yi masa ba, ya basu kudin mota ne dai kawai.
A gidan Usman Malaman su ka kwana, da sassafe Usman ya kai su tasha suka tafi Kano, bakinsu ya kasa rufuwa saboda murna su na ta godiya, Usman ya na godiya su ka tafi.
Imam Malik yayi-yayi Alan Usman ya bashi account number sa zai saka masa kudi amma Usman ya hana , sannan ya yi qoqarin bashi kudin a hannu shima ya qi karba ya ce yayi ne saboda Allah. Dan haka yayi masa godiya sosai ya yi masa sallama akan zai koma Abuja dan ya baro aiyuka da yawa ya taho babu shiri,sai an kwana biyu zai sake ziyartarsu.
Ya damqawa Usman amanar Mufidah akan ya kula da ita, ya saka mata ido sosai akan lamuranta, sannan ya dinga kula da yanayin jikin idan tana yawo babu dankwali ko ta shagala da jin kida ya tsawatar mata ko ya kira ya fada masa. Usman ya amsa masa ya amince ya karbi amanar.
Haka kuma Imam Malik ya yiwa Mufidah fada da nasiha akan ta bi maganar Usman, shi makwabcinta ne kuma malaminta ba maqiyinta ba. Burin Usman akan shine ya ga ta sami lafiya, ba dan ya musguna mata ba ne.
Ta yi amanna ta ce yanzu ta gane ba cutar da ita yake niyyar yi ba taimako ne, ada bata gane ba ne ta dauka dan su kore ta daga gidan ne yasa suke takura mata.
Bayan tafiyar Imam malik da wasu kwanaki Usman bai ga giftawar Mufidah ba sai dai ya ga Patient ta na shara a matattakala kullum, sai su gaisa ya wuce.
A yau dai ya kasa daurewa da Patient ta gaishe shi sai ya kasa daurewa ya tambaye ta ko ina Mufidah? Lafiya kuwa dan baya ganinta? Kafin patients ta bashi amsa ido hudu suka yi da

1 / 10