Author : Khadija KMU Category : Love
falon da yake link da bedroom dinshi yana kallon
football babu wanda yake da access din shigowa wurin anyhow sai hassan dinshi wato twin brother
dinshiÂ
 Ammar tasowa yayi ya kalki danuwanshi wanda suke da matukar kama sannan ya bashi side hugÂ
Tunda ya kalleshi yasan cewar mood dinshi ba Daidai bane don haka yace twin mi yake faruwa dakai
ne
Don’t tell me har yanzu saboda sabuwar maid dinka kake wannan frowning face din dariya Ammar
yayi mai kulewa sannan yace haba young prince kada fa ka bada mu ka saki ranka mana don AllahÂ
Zamuyi maganinta ta isa ta taba min husain dina ta zauna lafiya kada kacwani damu i will punish her
myselfÂ
Dadin baki Ammar ya rinkayi mashi har ya samu Imad yayi dariyar da bai shirya ba daman dariyar
tashi a iyakar ta wurin Ammar din sai kuma kannenshi shi kuma Ammar daman baida matsala yana
da fara’a sosaiÂ
Fitowa sukayi tare wanda duk bala’en ka baka iya ganesu saboda matukar kamar su don wata irin
kama sukeyi ba kadan ba they are identical twins kamarsu har tayi yawaÂ
Duk inda suka wuce durkusawa ake ana cewa Allah ya taimake ku Allah ya kara maku nasara har
suka fito inda motoci suke parked iri iri cikin hanzari aka bude masuÂ
bayan wata red Bentley flying spur sannan bakaken convoy suka biyo bayansuÂ
Hurriya kallon kala biyun da idan tagama wankesu to shikenan tagama wankin
 tayi kololuwa wurin gajiya don daurewa kawai takeyi ga yunwa da take nukurkusartaÂ
Tsotsar bakinta tayi sannan ta maida hankalita ta cigaba da wanki shanya taje tayi har ta fara tafiya
taji ana mai kyau mai kyau mai kyau tana haki har ta iso inda Hurriya take tasha gabanta Hurriya
kallonta tayi kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru yar kyakyawar yarinya karama wadda ta zauna
kusada Hurriya kafin ta fara wanki dazu tace ina maki magana shine ki kayi shiru Hurriya again
batace mata komai ba dariya wasba tayi sannan tace mata sunana wasba kefa ? Hurriya ko kallon
inda take batayi ba ta kama gabanta.
Wasba kallon inda Hurriya ta bari tayi sannan tayi murmushi ta nufi gidansu dake cikin masarautar.
Hurriya kam tundaga nesa taga bakin dakin wurin ya cika yayi fam cike da mamaki ta karaso tana
kallon mutanen da suka cika famm kamar hadin baki kuma suna ganinta sauran mutanen duka suka
juyo suna kallontaÂ
Hurriya kam takawa ta cigabayi a hankali tana karasowa don ita haka Allah yayi ta idanun mutane
basu takura mata saidai su kara mata confidence don haka ta tsakiyar su ta ratsa don duk kallon da
ake mata ko ajikinta saidai wata fitinanniyar tsawa da aka buga mata wadda ta shiga duk wanda yake
wurin Hurriya ita kanta tsawar ta shigeta saidai ta maze ta dago idonta cike da rainin wayau ta zuba
ma wanda ya jefeta da tsawar tana zuba mashi idanunta masu masifar kyau.
Kallonta yake tundaga tafukan kafafunta har zuwa kan dogon bakin gashinta kallonta yake yana
hadiye miyau da kyarÂ
Hurriya kam lura da irin kallon da yake mata mai cike da zallar iskanci ya sanya tayi tsoki tace dan
akuya maye ta nufi inda zai sadata da kofa saidai bata ida karasawa ba taji an kifa mata bulala mai
matukar zafiÂ
Juyowa tayi aiko taganshi tsaye yana kallonta da idanunshi wadanda basu da kyaun ganiÂ
Kallonta yayi sannan yace ke tsinaniya yar gidan matsiyata da ubanwa kike takama dashi duk
masarautar nan da har zaki kona ma barira fuska tsotsar bakinta tayi sannan ta kalleshi ido cikin ido
tace da ubanka nike takama a masarautar nan tana kallonshi shima yana kallonta wani irin kwarjini
takeyi mashi don kwata kwata taki sauke idonta har lokacin idonshi na cikin nashiÂ
Kowa kallon dramarsu yake ana jiran kaura ya jawota yayi mata dukan da bazata iya gane ko kanta
ba bare har ta zagi kaura ko ta kona mashi budurwaÂ
Shikam kaura he was lost in thought because he had never seen a beautiful human being like her
she’s beautiful beyond words she’s just beautiful yadda take komai yake sanya mashi ganin
kyauwunta gyara tsayuwar shi yayi domin ya bugeta kawai saiga kuyanga daga sashen ImadÂ
Kallonsu tayi tace mi yake faruwa ganin duk sunyi shiru ya sanya ta kalli Hurriya tace muje hakimi na
kiranki Hurriya ba wanda ta kalla acikin su tabi kuyangarÂ
Suna zuwa suka shiga chamber hakimin wanda yana can ciki kwance a saman sofaÂ
Abinci ya gama ci sannan ya sanya aka fidda mashi kwanonin abinci wayarshi yake latsawa kafin
bacci ya daukeshi mai matukar dadin gaskeÂ
Hurriya kam tunda ta sanya aka gaya mashi Amman har lokacin bataji anyi mata iso ba don haka taje
balcony ta zauna tayi shiru tana kallon masu wucewaÂ
Duk kuyangin dake wucewa kallonta suke da mamaki irin kujerar prince kika zauna tabb kina ruwa
ba wanda ta kula bare tayi mashi maganaÂ
Lumshe idonta tayi sannan tayi crossing legs dinta banda yunwa ba abinda takeji don duk wunin
ranar bata sanya ma cikinta komaiÂ
Baccin gajiya da taji ya fara daukarta ya sanya ta tashi ta koma ciki kitchen din ta shiga wanda tayi
sa’a ba kowa kallon kulolin abinci tayi wanda aka jera abinci ne a table din kitchen island ba tare da
bata lokaci ba ta shiga budewa abinci ne kala kala ga yankakun fruits wani plate mai kyau ta jawo ta
zuba abincin ta faraci ahankali saida taci ta koshi don wanda ta rage baifi ace loma daya ba wanda
har ta koshi sosaiÂ
Mama RaBI ta shigo kitchen din tare da zubaida dukansu bude baki sukayi da mamaki suna kallon
Hurriya da tagama cin abincinta hankali kwance salati mama rabi ta farayi tana kallonta sannan tace
waye ya baki izinin cin abincin nan kinsan abinci waye kuwa kallonta Hurriya tayi da idanunta masu
haske ba tare da tace komai ba ta dauki ruwan da yake jere a saman tray din ta fita.
Mama RaBI kam ba’a tabayi mata irin abinda Hurriya tayi mata baÂ
Kallon zubaida tayi wadda har lokacin bakinta bude yake sannan tace wai ina aka samo wannan
shegiyar yarinyar ne mama rabi kinga wani kallon banza datayi maki sannan ta juya ta tafi shiru
mama rabi tayi sannan ta Sauke ajiyar zuciya tace lallai yaro baisan wuta ba sai ya taka sannan ta
kyalkyace da dariya zubaida wata dariyar gefen baki tayi itama sannan suka bar wurinÂ
Mama RaBI taji haushi sosai da hakimi bai basu fuskaÂ
Ko kara bai basu damar wani ya kaimashi bare munafunci da tsaegumiÂ
Da wallahi sai tagaya ma Imad kaskantaciyar mai-aikin shi taci mashi abinci kwata tayi sannan tace
ajuri zuwa rafi watarana tulu zai fasheÂ
Hurriya tafiyar ta Tayi wanda gari har ya fara duhu magrib ta gabato saida tayi tafiya mai nisan gaske
sannan tazo bangarensu ta shigaÂ
Ta gaji sosai don ba abinda take bukata irin tayi wanka tayi bacci kallon bintu da take zaune tana
hamma tayi wanda dama ga dukkan alamu Hurriya take jiraÂ
Wuri ta samu ta zauna Bintu ta kalleta tace sannu Hurriya kindawo ne kinci abinci ? Daga mata kai
Hurriya tayi batace ma Bintu komai baÂ
Bintu kallonta tayi hamma tayi sannan tace saida safe daman jiran dawowar ki nike bari in tafi har ta
juya tajiyo sautin muryar Hurriya daga bayanta tace kinci abinci da wata irin murna Bintu tajuyo tace
naci a hankali Hurriya ta zaro naira dari biyu ta mika mataÂ
Bintu amsa tayi tana kallon Hurriya domin jin karin bayani lumshe idonta Hurriya tayi sannan ta
tsotsi bakinta saida ta dauki lokaci sannan ta bude idonta masu kyau ta zuba ma bintu su tace idan
kina bukatar wani abu ki siya can kasan makoshin tace ki kula da kanki sannan ta kara rufe idonta
kamar mai bacciÂ
Bintu murmushi tayi tana kallon Hurriya da zallar kauna a idonta wadda idonta suke rufe dan tsalle
Bintu tayi kamar karamar yarinya tace Ina kaunar ki Hurriya sannan ta juya ta tafi dakinsuÂ
Saida Hurriya taji tafiyarta sannan ta mike ta nufi babban kitchen din da ake dafa ko wani irin abinciÂ
Dubawa tayi ko zata ga matar jiya saidai akasin haka baba haule reza tagani don duk tafi kowa zama
kusa da ita don haka ta nufi wurinta da bokitin baba haula reza kallo daya zakayi mata kasan cewar
masifarfa ce ta ajin karsheÂ
Hurriya bokoti ta ajiye ahankali sannan ta kalleta in a commanding tone tace ruwa zaki zuba minÂ
Baba haule reza ta dago idonta a kankance ta fara surfa mata ashariya Hurriya bata janye idonta
daga kallonta ba kuma batace mata kala baÂ
Har saida tagama kumfar bakinta kowa kallon baba haule reza yayi acikin kitchen din sannan kowa
ya cigaba da hidimar shi don inda sabo ta sabaÂ
Hurriya saida ta tabattar da cewar baba haule tagama masifarta sannan ta zaro naira dari ta ajiye
mata tana kulleta da idontaÂ
Baba haule kam kamar an daure mata baki don dauke darin tayi a inda Hurriya ta ajiye tana saka
kudin cikin skirt dintaÂ
Bokitin ta janyo ta zuba ma Hurriya ruwan zafi masu yawan gaske ba tare da Hurriya tace kala ba taja
bokitin ta nufi toilet ta gasa jikinta sosai da ruwan zafi.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: í ¼í¼šMasarautar QamarÂ
   A story about a mysterious palaceÂ
By Khadija (KMU)
Page 21&22
Bata wani dauki lokaci sosai ba ta fito daga toilet din tana mai ya mutsa fuskarta don duk batajin dadi
don kayan dake jikinta sune ta maida dalili kam da akwai zanen tatoo a bayanta bata kaunar ko wani
dan mutum yaga tatoo din sam she’s not comfortable cikin masarautar Qamar don kwata kwata
batada yancin dan adam kuma ita a rayuwarta ba abinda takeso irin yanci don haka ta tashi a
rayuwarta tunda ta taso ba wanda ya taba depriving right dinta tanada ko wani irin freedomÂ
Tana da matukar tsafta don kaya basu iya mata 24hrs ajikinta bare kuma ace kuma tayi wanka ta
maimaita kaya saidai da ace ta fita da daurin zani wanda duk zanen dake bayyane a bayanta zai
bayyana ga idon mutane gwara ta maida kayantaÂ
Don haka da kayan ajikinta ta fito sannan tayi alwala ta shiga dakinÂ
Cikin natsuwa ta Cire kayan jikinta kallon inner wears din da ta siya dazu dasu sabulun wanka da
brush tayi har da turare mai sanyi kamshi batasan ana kasa haja ba sai dazu da safe inda har tazo
wucewa taga haule reza ta kasa kaya masu kyau har ta wuce ta dawo haule reza ba abinda bata
saidawa saida Hurriya ta bata kudi sosai wurin siyen abinda takeso don saida ta tabbatar duk abinda
take bukata ta siya sannan ta nufi bangaren ImadÂ
under wears ta sanya masu kyau sannan ta shirya cikin wata blue half gown da iyakarta gwiwar
kafarta ta tsayaÂ
doguwar hijab dinta ta sanya sannan ta kabbara sallah rama sallolinta tayi duka bayan tagama
sallarh ta kishingida jikin katifar ta lumshe idonta ba bacci take ba Amman dai tayi lamo
Sunanta taji ana kira saidai ko motsawa batayi ba bare tayi tunanin bude idonta saida tayi mintuna
Sosai kafin ta bude idonta ta zuba ma zubaida su da take tsaye wanda tagama kulewa don tunda
tazo tasan ba bacci take ba Amman don bakin rainin wayau ace tanajinta tayi shiru ta kyaletaÂ
Zubaida ta kalleta tace Lallai ma Hurriya shine zaki zo ki kwanta wakike tunanin kinbar ma aiki sai ki
taso tunda ba bayi kika ajiye baÂ
Don ana bukatar ki a Aikin dare shiru Hurriya tayi batace kala ba don yaddda tayi kamar ma da dutse
ake maganarÂ
Hurriya magana fa nike inji zubaida shiru Hurriya tayi saita lumshe idontaÂ
Zubaida kam iya jin haushi takai don cikin zuciyarta banda la’anar Hurriya ba abinda take saidai tayi
mata wani irin mugun kwarjinin da bata iya maida mata maganaÂ
Gajiya tayi da tsayuwa zubaida taja tsoki tayi tafiyar taÂ
Hurriya kam shiru tayi don saida tayi kusan minti talatin kwance idonta kuma rufe kamar mai bacciÂ
Tashi tayi ahankali cikin yanayin natsuwarta ta sanya takalminta ta fita
A hankali take tafiya wadda idan ka kalli yadda take tafiyar zaka dauka jinin sarauta ce dogayen
kafafunta da suke bude sai salki suke sai tulin bakin sumarta wadda baka iya ganin jelar gashin saidai
kwantaccen gashinta wanda ya fara tundaga goshinta farin wata ya haskata wanda ya taimaka wurin
fito mata da tsantsar kyau na hallita duk wanda ya kalleta ya kara kallonta yasan mai kyau ce wato
mai asalin kyauÂ
Kallonta ake gabas da yamma kudu da arewa duk da kasancewar dareneÂ
Daidai saitin su barira da suke zaune a tabarma suna shan rake tazo zata wuce tanajin duka
idanunsu dake yawo a kanta Amman ko a kwalar rigarta ta cigaba da tafiya tayi abuntaÂ
Muryar Hansa’u ce ta doki kunnenta wadda take cewa barira gafa mutuniyarÂ
Barira shiru tayi tana kallon bayan Hurriya da dogayen kafafunta lashe baki tayi ta gyara zamanta
batace komai baÂ
Wasila ce tace har yanzu bamu dauki fansar abinda tayi maki barira ba Amman na rantse bataci
banza baÂ
Don ko yadda ta bata mana suna sai mun gyara mata zama sai na wulakanta yar matsiyaciyar can
wulakanci mai muni sai kuma na hada mata tuggun da bazata iya warwareshi ba duka rayuwarta a
masarautar nan sai na wulakantata wulakanci mafi wulakanci sannan in kaskantata kaskanci mafi
kaskanciÂ
Sannan tazo har gadon baccinki barira sai yadda kikayi da itaÂ
Dukansu dariya suka sheke da ita tare dayin na’am da alkawarin da tayi kuma Dukansu sunce zasu
tayataÂ
Hurriya duk tanajin abinda suke cewa duk da kam tafiya takeyi kuma tayi masu nisa kallon sakarkaru
marar sa aikinyi tayi masu ta cigaba da tafiyartaÂ
Saida tayi tafiya mai nisan gaske kafin ta kawo chamber ImadÂ
Ahankali ta shiga kitchen din wanda tana shiga kamar hadin baki duka ma’ikatan da suke aiki a
kitchen din suka jiyo suka kalleta acikin su ba wanda bai bude baki ba yana kallonta ba tunda daga
sama har kasaÂ
Amman Hurriya shin ita ko ajikinta don idanun mutane basu daureta kwata kwata ko alama itadai
Allah ya bata wani irin confindence wanda ba ko wani dan mutum yake da irinshi baÂ
Hurriya bata fasa tafiya ba don tsakiyar kitchen din tazo sannan sai taga tukunyar da ake shredded
beef din don haka cikin natsuwa taje ta fara motsa tukunyarÂ
Zubaida ce wadda ta kasa yin shiru cike da rashin kunya da wulakanci tace wai casu zaki ko coci
Hurriya dagowa tayi ta zubama zubaida idonta masu kama da zaiba sannan ta tsotsi bakinta a
hankali tace casu zamuje nida tsohuwarki da tsohonki idan mugama sheke aya sai mu tsaya ta coci
muyi ibadaÂ
Tayi maganar hankali kwance tana kallon kowa acikinsu wanda fuskarsu take dauke da mamakiÂ
Dukansu ba wanda bai saka wani abu acikin ranshi ba
Wasu kuma cewa suke daman tana magana?
Hurriya bayan ta tabbatar da shredded beef din yayi ta juyeshi a cikin food flask sannan ta dauki
tukunya ba abinda ba’a nuna mata ba a bayani don haka tasan inda komai yakeÂ
Ruwa ta zuba a tukunya sannan ta shiga store ta debo basmati ta kunna gas ta daura tukunya
hadaddiyar biryani tayi masu don tana abincin tana rera waka nike gani tanayi tana dan juya kugunta
har ta gama don kamar abincin na tura mata memories don tana enjoyingÂ
Tazo ta kwaba pancake dinta ta soyashi mini sannan ta dauko chocolaté tayi dizzling dashiÂ
Tana aikinta tana wakarta tanajin idanunsu a kanta Amman kamar babu kowa a wurinÂ
Saida tagama yin komai ta dauko kula ta juye don abinci bai dauki wani lokaci ba tagama saboda
karfin gas din dake da ci sosaiÂ
Hadawa tayi a tray don dakanta ta jeraÂ
hada wanda mama rabi tayi da wanda tayi don abinci suna da matukar yawa mutum ashirin zasu
iyacin abinci don different varieties of food ne a wurinÂ
Bayan tagama sai ta nufi hanyar fita mama RaBI kamar tasan niyyarta don haka tace Hurriya kune
zaku tsaya har su hakimi sugama cin abinci koda suna bukatar wani abu sai ku mika masuÂ
Bata matsa ba kuma bata dawo ba Amman ga dukkan alamu maganar ta shigeta zubaida da mama
rabi da wasu kuyangu guda ukku suka fara fitar da tray din abincin da drinks da wasu manya manya
non alcoholic winesÂ
Hurriya zuwa tayi ta dauki trays din wanda yake cike da wasu matsiyatan plate ta shiga parlon saida
ba kowa a parlon it looks like Dukansu suna parlon gaba don haka Bata wani Bata lokacin ba ta shiga
ba excuse ba sallama kallon mutanen dake zaune a tsakiyar parlon tayi duk twins ne kusan set uku
masu matukar kama da juna.
Liya wadda ta daura kafafunta saman jikin Neela in an annoying way itace ta fara lura da Hurriya
kallonta take from head to toe shiru tayi batace komai ba duka sauran hankalin su yana akan abinda
sukeyi Neela hankalinta duka yana Akan wayarta sai Amrah da imran da suke playing ps 5game duka
hankalisu yana a wurin game dinÂ
Liya kam satar kallon Hurriya kawai take wadda take jera abinda ta shigo dasu a dining kutt The girl is
unparalleled beauty su zubaida duk sun dukar da kansu da kuyangin da suka shigo tareÂ
Kallon kafafunta wanda suke bude tayi tana kallon sumarta da take bude fuskar nan a hade take
kamar an aiko mata da sakon mutuwa tanayi tana cije lebe wanda ga dukkan alamu sararta ce Liya
kasa janye idonta tayi daga kallon Hurriya don tunda take masarautar Qamar bata taba ganin halitta
mai kyaun Hurriya ba saidai gabanta ne yayi mugun faduwa tunawa da tayi ana jita jitar cewar masu
kyaun masarautar su mutuwa sukeyi don ko a ma’aikata indai matane to ba’a cika kawo marar sa
kyaun hallita ba saidai tunda take bata taba ganin Mai kyaun da ta kama kafar Hurriya ba wane
subira an dade acikin masarautar Qamar ana bama subira sarauniyar kyau Amman wannan yarinyar
tayi ma subira fintinkau don indai za’a hada kyaun subira da Hurriya to subira zata iya samun
30percent ita kuma Hurriya 70percentÂ
Babu abinda Allah ya rageta dashi don ita jikinta irin na models ne wanda turawa suke iya barnar da
ko nawa ne garesu saboda su mallaki irin jikintaÂ
Sauke ajiyar zuciya tayi farar daya tausayin yarinyar yana kamata don tana da kyaun da ba kowani
namiji bane zai iya dauke ido akanta ba sai kuma babban kalubalen dake masarautar duk da jita jita
ne Amman ta dade tana tunanin anya abun ba gaskiya bane don itama ta rasa ma’aikantata Sosai
wanda suka shaku kuma ta saba dasu saidai duk idan hakan ta faru akwai abinda jakadiya take fada
mata saidai tun tana yadda har tazo tana putting Question mark.
Imad ne ya shigo kallonsu yayi Dukansu sannan yace guys let’s eat dinner ku tafi kubar min part dina
don duk kun cikamin part dina Ammar ne ya ajiye wayarshi wadda take hannunshi sannan yazo
Daidai inda Imad yake ya dafa shi yace ya akayi ka kosa MU tafi kodai kodai sannan ya fashe da
dariya Imad daure fuska yayi dagajin maganar Hurriya don yarinya ta bata mashi rai kuma ta rainashi
shida ma’aikatan masarautar Qamar ke shakkar shi Amman yarinya yar Qarama tana Neman
rainashi har sanyawa fa yayi a kira mashi ita kuma dagagan ya shanyata so yayi sai tayi awa