Author : Khadija KMU Category : Love
suna gama soyawa
suka tattara komai suka tafi gida.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: í ¼í¼šMasarautar Qamar
By Khadija (KMU )
Page 5&6
lokacin da suka dawo anata kiraye kirayen sallah magriba Don Hurriya zaiyi wuya takai bayan magrib
a wurin suyar Awara Bintu tayi alwala sannan ta shigo dakin kallon Hurriya dake kwance saman
katifar tana jin waka tayi idonta a lumshe suke Bintu ta kalleta tana admiring irin kyaun da Allah yayi
mata long lashes dinta da suke kwance kamar tayi fixing dinsu dogon hancin ta sai kuma cynical
mouth dinta banda glowing ba abinda fuskar ta take because of her smooth and flawless skin a
hankali ta kalli shafefen cikinta wanda kamar bata sanya mashi komai Hurriya is extraordinary
beauty duk wanda ya kalleta yasan tana da kyau kuma har ka gama rayuwarka da ita baza ka lura da
wani muni nata ba saboda kana kallonta a kullum tana kara maka kyau irinsu ne wanda ake gasar
kyau dasu kuma tayi imani da cewar idan daHurriya zata fito gasar kyau ba abinda zai hanata cin
wannan gasar irinsu ne za’a iya biyansu ko nawane don su kasance manya manya models irin nasu
france da america Everything about her is screaming perfection with nothing left to criticize Â
Sallah Bintu ta kabbara har tagama sallah Hurriya bata matsa konan da can ba Bayan Bintu ta gama
addu’a ta kalli Hurriya tace Hurriya ki tashi kiyi sallah lokaci na tafiya Hurriya kam da batajin Mai take
cewa don ta kure volume a burin yar garuwarta Bintu kara mata magana tayi shiru tayi Bintu da taga
kamar batajin mi take cewa sai ta sanya hannu ta taba ta Aiko kamar an tsunkuli Hurriya din da a
firgice ta tashi tana Bintu wani irin mugun kallo ta Hurriya kallon take sosai Bintu kam da tasan
yadda Hurriya ta tsani wani ya tabata don tanada tabbacin idan wani ne ya tabata ba ita ba to saukar
mari ne kawai zaiji Hurriya tace Bintu don’t ever repeat this mistake again Bintu tace ki tashi kiyi
sallah lokaci na wucewa Hurriya ta daga mata kai sannan taje tayi alwala da sauri tayi sallah don
Bintu kallon yadda take sallah kawai sannan girgiza ta kai kawaiÂ
Hurriya ta kalli Bintu sannan tace kina jin yunwa Bintu tace inajin yunwa HurriyaÂ
Hurriya daure gashinta tayi saboda wanda tayi taji yana damunta so take tasamu lokaci ta rage
gashin don ya kara taruwa da yawa gashi bata san takura tana gama gyaran gashin ta kalli Bintu tace
bari na samo manah gari can shagon Bintu tace zan rakakiÂ
Tare suka jero suna tafiya su biyu duk inda ta gifta kallonsu ake ba Kamar Hurriya don crop top ce
jikinta pink sai wani bakin wando gashin kanta ta da yake a bude sai sheki yake har suka zo shagon
da ake saide saideÂ
Da murmushi a fuskar shi yace Hurriya mi za’a baku gari tace ya sanya masu na dari sai sugar na
hamsin gyadar hamsin Hamza da murmushi yace su Hurriya gari za’a sha wani kallo Hurriya tayi
mashi ai sai ya fara to to sannan ya miko garin da suga da gyada Bintu ta amsa sannan tace mun
gode Hurriya dai banza tayi dasu dukan su.
Suna shigowa suka ga talatu a zaure itada tasi’u hannunshi sanye cikin rigarta tana ta dariya kasa
kasa kwata kwata basu lura dasu Hurriya ba da suka shigo don Bintu ba karamin tsorota tayi ba don
sauran kadan ta fadi Hurriya kallo daya tayi masu ta dauke kanta tayi gaba har ta sanya kanta taji
maganar su kasa kasa tasi’u yace ya za’ayi da yarinyar can ne ni wallahi duk unguwar nan ba wanda
yake burgeni Kamar ta yarinya shigar banza kuma Kamar tsohuwar baturiya Amman ace duk
unguwar nan gani nan bari ina da burin in lasa wannan yarinya nima tasi’u yace ma talatu dariya tayi
sannan tace Hurriya ai karuwa ce ta karshe kawai dai ta iya allontaÂ
Ganin Hurriya da tayi a tsaye saida gabanta ya fadi wani irin mugun kallo take mata fuskar nan
kwata kwata babu emotion tana a yadda take kamar kullum tasi’u ta kalla cikin ido hannun tasi’u
dake cikin rigar talatu ta kalla sannan cikin muryarta mai dadi ta kalleshi sannan tace nima ka sanya
hannunka cikin rigata tana kallon tsakiyar idanunshi tsotsar bakinta tayi kadan tace ka sanya
hannuka cikin rigata manaÂ
Shiru tasi’u yayi yama kasa kallonta duk ya daburce don wani irin kwarjini da tayi mashi kilan saboda
kyaunta take da irin wannan kwarjini frowning face dinta tayi in a mocking way tace kai dan akuya
ne? Are you mad kallon shi tayi sannan tace kaje ka kalli kanka a madubi sannan tazo saitin talatu
kallon cikin idanunta tayi sannan tace miye ma’anar karuwanci shiru tayi talatu tace ina tambayar ki
shiru tayiÂ
Hurriya tace sana’ar kice keda tabawa and please stop sleeping with young boys masu empty
pockets idan zaki kwanta da namiji gwara ki nemi baban tasi’u yadda idan yagama zai baki koda dari
biyu ce wadda zaki iya cin tsire wawaye makwadaita.
Earpiece dinta ta maida tayi cikin gida abinta kamar batayi komai ba she hate nonsense mutanen
yanzu you’v to stand and for yourself ita batama ga dalilin da zaisa mutum ya zageta tayi shiru ba she
doesn’t care ko waye kai zata kalli tsabar idonka tayi maka daidai abinda kayi mata Amman dai ba
ruwan ta da kowa kawai miskila ce ta karshe and don’t talk behind her back saboda Allah ya bata
wani irin ji sosai kilan shine baiwarta Don tana iyajin magana daga nesa Sosai wadda nisanta ya
wuce tunani Amman cikin ikon Allah zataji lokacin da bata ma iya hausar ba Sosai don ko magana
taso ta fada ma mutum marar dadi to ba lallai yaji mi take cewa ba saboda she’s using British and
Amacharic Amman yanzu idan ta yanko maka magana kamar daman asalin yaren hausan takeji don
duk kalmomi mararsa dadi ta iya amfani dasu.
Bintu kam har ta jika masu garin tanata jiran Hurriya din tazo domin susha suyi sallah su kwanta
Bintu ta kalli Hurriya tace ina kika tsaya ahankali tace waje tasan bata cika san magana ba don ta
tsani unnecessary zance don haka Bintu taja Bakinta tayi shiruÂ
Tare suka sha garin don ita Hurriya a hankali take sha don har tagama shanye nata Hurriya bata
shanye ba tanajin waka tana kada kanta Bintu murmushi tayi sannan ta fita ta wanke kofin tayo
alwala sannan ta kabbara isha’i tana gama sallah tana lazimi saiga sallamaÂ
 Hurriya idonta lumshe Amman duk abinda Bintu suke cewa tanajin su Bintu ta kalli Hurriya tace
Hurriya na tafi baba ya dawo yace a kirani tana goge dan hawayen da ya zubo mata Hurriya tayi shiru
kamar bataji mai Bintu take cewa ba sannan Bintu ta fita tana dan gyara ma Hurriya labule.
Bintu na isowa kofar gida gabanta ya fadi don batasan mi zata tarar ba a gidan a hankali tasa kanta a
soron Gidan tana tafiya kamar munafuka lalu da suka shirya abunsu da larai daman yasan dole zata
dawo gida shiyasa ya tsaya zaure ya tarbeta saboda ya lalubi rabonshiÂ
Daidai inda take yazo yana wani munafukin dariya yace wa naka ma matsowa ya farayi tana matsawa
baya yana Dariyar har saida ya kawota karshen bango riketa yayi gam yana dariya yellowing
hakoranshi suna bayyana kugunta yarike yana kokarin sanya mata hannu cikin riga tureshi tayi yayiÂ
baya ya kalleta sannan yace ni zaki ture to yau Mai rabani dake sai Allah kugunta ya rike aiko suka
fara kokowa karfinta ne ya fara karewa sosaiÂ
Hurriya da take kallon ikon Allah zuwa tayi daidai inda yake ta dauke lalu da mari a harzuqe ya dago
da niyyar sauke ma kowaye ya mareshi ruwan tijara saidai da kyar ya iya hadiya maganar shi da
kuma yawun dake bakinshi kallonta yakeyi da yar crop top din da ko cibi bata rufe mata ba sai bakin
wandon dake jikinta gashin kanta kam ba’a daure ba tunda lalu yake bai taba ganin halitta mai kyan
mahnoor ba saidai kyawawan idanunta da Allah ya basu matukar kwarjini Hurriya ta janye bintu daga
wurin lalu tana mashi wani irin banza kallo da kyawawan idanunta cikin muryarta mai dadi da tace
duk randa na karajin wani Abu makamancin haka ya faru sai kaji a jikin ka sakarai mai karamar
kwakwalwaÂ
Bintu kallon Hurriya tayi sannan tace nagode Hurriya kam baka iya karantar yanayinta don ta kwarai
wurin shutting emotions dintaÂ
Tare suka shiga inda suka tarar abbanta na kwasar tuwo larai na kusa dashi Larai na lura da
shigowar su ta saki wani munafukin murmushi Abbanta da ya kula dasu aiko zumbur ya taso da
hannunshi duk miya zai mari Hurriya cikin sauri ta rike hannunshi tana rikewa ta saki don kamar ta
rike kashi tana kallonshi Abba da ya harzuka yace daman kina wurin wannan shedaniyar marar
tarbiya marar addini.
Hurriya a kalleshi sannan tace babban shedani ya wuce bayanka wanda har zai tsallake kafa ya tafi
gantali ba tare da tunanin halin da diyarshi zata fada ba a hannun kishiyar uwa bakasan mi taci ba
bakasan mi tasha ba baka san wazai lalat maka diya ba kallon Larai da tabata fuska tana kallonta tayi
sannan tace koda yake ba abin mamaki bane tunda duka jikin ka daure yake da asiri.
Rashin addinina da Rashin tarbiyata duka dauka nayi a wurin wanda baisan hakkin diyarshi ba ido
cikin ido tace sakarai wawa mijin tace Bintu da take kallon komai tasan a haka Hurriya na ganin
mutuncinta tasan idan tayi wani abun ba zataji dadi ba.
Hurriya ta kalli Bintu sannan tace ai baki jin yunwa ko Bintu ta daga mata kai tace muje dakinki
Hurriya na gaba Bintu na baya har suka zo dakin kallonta tayi mata da ido ta shiga kuka take shirin yi
Hurriya ta nuna mata alama da tai shiru.
Abba da Larai kam sunsan halin shegiyar Hurriya ldinan da ta zame masu karfen kafa a cikin garin
nan don bata da mutunciÂ
Hurriya tazo ta kallesu sannan tace idan har naji ko harar Bintu kunyi to zan kira maku hukuma ta
kada kai ta bar gidan lalu da yake boye yana kallon su duka ya fito yana kallon Larai yace wacece
wannan Larai ta kalleshi tace fitacciyar marar kunya kenan don haka duk abinda tace to ba mamaki
zata iya aikata shi.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: í ¼í¼šMasarautar QamarÂ
By Khadija (KMU)
Page 7&8
Gida Hurriya ta koma tana shiga ta kwanta a katifar tana tunani bata gama tunanin ba bacci ya
dauketa sai karfe bakwai ta tashi ruwa ta dan kashe sannan ta juyeshi cikin bucket tayi wanka kanta
ta fara wankewa sannan wanka tayi alwala saida ta sanya gashin kanta saitin fan ya bushe tukunna
scissors ta duba inda take ajewa bata gani ba dubawa tayi sosai bata gani ba tsoki tayi ta gyara
gashinta ta daureshi kawai don taso ta yankeshi saboda gashin ya fara yi mata yawa wani dan
karamin box ta fiddo can cikin kayanta ahankali ta bude tana kallon sarkoki guda biyu masu masifar
kyau Rufe box din tayi ta maida sannan ta fiddo wani jeans blue ne sosai Amman yanada dan fadi
kasan shi sai tsagar dake a cinyoyin wandon da gwiwar wandon shiryawa tayi cikin wando ta sanya
bakar riga yau kawai taji tanason ta sanya dan kwali don haka ta zaro wani blue and black vintage
scarf ta daura ma kanta saida tagama shiryawa tsaff sannan ta dan murza dan oil turaren ta mai
saukin kudiÂ
Saida tagama komai sannan ta kabbara sallahr asuba don har takwas da mintuna tayi da sauri
tagama komai ta nufi gidan mai anguwa .
Tadan makara yau wurin aiki tana shiga laminde tace kina raina Hurriya yanzu nike da niyyar daman
In sanya a Duba ki ko lafiya Hurriya ta share tambayar da tayi mata tace ina kayan murmushi
laminde tayi ta fiddo mata kayan yau cikin sauri take komai saboda yau zata kwashi adashenta kuma
tanaso ta siye kaya saida ta tabbatar tagama komai don ko laminde ko Bankwana batayi ma laminde
ba ta fitoÂ
Hurriya kam saida taje gida ta fiddo asusunta har ta maida wurin maida asusun ne wani dan box í ½í³¦
ya fado a hankali ta bude tana kallon sarkoki guda biyu da banda kyalkyali ba abinda sukeyi maidawa
take kokarinyi kawai sai a ranta tace bari ta sanya it’s been a long time a hankali ta warware sarka
guda daya wadda plain ce kawai Amman gold ne a sarkar ta sanya Kallon dayar sarkar take wadda
kamar diamond ce Amman stone din anyi mashi carve da H Maidawa tayi a box din sannan ta sanya
shi a aljihun wandonta Emotions din da taji ya fara taso mata ne ya sanya kawai ta cire kudin asusun
wanda suka kama dubu takwas ta tafi gidan Asabe wadda ta kasance uwar zubin adashen Hurriya ba
sallama ta shiga gidan a tsakar gida ta iske asabe tana shan rake
Asabe saidai ganin mutum tayi a kanta don ta tsoro ta matuka Hurriya ta kalla daga sama har kasa
tace Nagode ma Allah kece cikin gidanan namu da ace bake bace da sai anjimu dake yau Hurriya
kallon Asabe tayi fuskar ta babu alamun murmushi ko daya tace nazo kwashe kudinaÂ
Dariya Asabe tayi sannan tace oh kece fa kwasar karshe kusan kowa yasan halinki shiyasa duk
angama maki zubin adashen ki tun kafin ma kizo ta ida maganar da dariya hurriya batace mata kala
ba saidai ta jawo kujerar dake kusa da Asabe ta zaunaÂ
Asabe tace kinga bari na dauko maki kudin ki labule asabe ta daga ta shiga daki sai gata tafito da yar
lalitar tsaff ta kirga ma Hurriya dubu sha biyar da dari takwas tace ga kudin ki kece daman zaki ida
zubin yau shine zai kama dubu sha shida kenan Hurriya amsar kudinta tayi daman hannu biyu tayi
zubin na wata biyu kenan kuma itace kwasar karshe ta hada da dubu takwas din da ta fiddo daga
asusun ta wanda suka kama dubu ashirin da uku
Amsar abunta tayi ba tare da tace ta gode ba asabe har zata wuce asabe tace yawwa Hurriya ga fa
irin kayan da kike sawa gwanjo ki duba Hurriya alama tayi mata da ta miko cike da murna asabe ta
shiga daki don tasan indai Hurriya ce sai ta siye kayan kusan dubu biyar indai tanason Abu zata siya
gashi ita bata taya kaya duk yanda aka batasu saye takeyiÂ
Kulli guda asabe ta fitoda kayan tana nuna ma Hurriya murmushi tayi tare da bude kayan tace kalla
Hurriya kallon da Hurriya take ma kayan kawai zai tabbatar maka da cewar sun burgeta a hankali ta
fara zabar kayan masu kyau har kusan kala goma sai hula kala uku Asabe ce ta kalleta sannan tace
Hurriya gafa wata jalabiya zatayi maki kyau ki hada da ita Hurriya kallon jalabiyar tayi sannan tace ta
sanya mata da murmushi asabe ta sanya hada wani dan kwali Mai silbi sai hijab Mahnoor kallonta
tayi sannan tace nawa ne duka kudin kayan Asabe ta gyara tsayuwa sannan tace dubu shida Hurriya
ba tare da bata lokaci ba ta kirgo dubu shida ta bama asabeÂ
Asabe kam dadi kamar ya kasheta daman tasan Hurriya bata da bakin ciki indai tanason Abu zata
siya à yadda ka batashi leda ta dauko ta kwashe ma Hurriya kayan sai zuba kam godiya take da
addu’a Hurriya bata bi takanta ba ta fito daga gidan ta nufi gidan mai unguwa cikin aljihun wandonta
ta sanya kudin tabo aljihun tayi kawai sai taji dan karamin box dinta tsoki tayi ta maida kudin a dayan
aljihuntaÂ
Da isowar ta kofar gidan mai unguwa taga kofar gidan cike da motoci fararen bus ne na hias masu
kyau ga yara da iyayen yara shake a wurinÂ
 A hankali Hurriya ta kutsa kai gidan mai anguwa samudawan dogarai ta gani sai mazurai suke da
idanu frowning face dinta tayi ganin su da wasu uniform ga kuma rawani daure a kansu hango
laminde da Hurriya tayi ne ya sanyata kutsa kai har inda take ganin ta , Duka wurin kallonta suke ba
tare da ko kyaftawa laminde kam kallonta take tana mata alama da ta fita Amman Hurriya ba tare da
ta kula kallon da ake mata ba ta iso har inda take fuskar ta sai fidda wani irin kyau take Amman
kwata kwata babu murmushi ko sauki a fuskar ta laminde ta kalla sannan tace namanta ban amshi
kudin aikina ba laminde tace oh oh bari na dauko makiÂ
Mai unguwa kallon Hurriya yayi cike da tausayinta saboda ya tabbata baza ta koma gida ba yau don
kallon da dogarawan kadai ke mata ya isa ya baka amsa laminde ta fito da Dari biyu ta bata tana
kallon ledar hannunta da kuma wuyanta gaban laminde ne ya fadi ganin sarkar gold din da ta fito
baro baro a wuyanta tasan zalincin dake masarautar Qamar don haka a hankali tazo saitin Hurriya
gabanta na faduwa saboda kada wani ya lura da abinda zatayi itadai Allah ya Sani tana kaunar
Hurriya har cikin ranta duk da ita bata nuna wata alamar girmamawa amman a haka take kaunarta a
hankali tazo ta gyara mata wuyan riga tare da zurma sarkar cikin riga Hurriya kam wani irin kallo take
mata murmushi laminde tayi sannan tace kada ki yadda wadanan dogarawan suga sarkar dake
awuyan ki a hankali tayi mata magana yadda ko mai unguwa da yake nesa dasu bazai iya ji ba ki kula
da kankiÂ
Hurriya .
Hurriya a daga kai tayi tana rike da ledar kayan ta ta doshi hanyar fita wata tsawa aka daka mata
Daidai ta kai kofar akace ke yar matsiyaciya ina zakiÂ
Hurriya cigaba tayi da tafiyar ta wata tsawa ce aka kara daka mata ke kaskantarciyar karuwa ina zaki
Hurriya bata taka ba kuma bata juya ba tsaye tayi tana jiran isowar ko waye da yake mata tsawa har
haka don tun lokacin da ya fara tasan da ita yakeÂ
Salati laminde takeyi ta kalli mai unguwa dake gefe sannan tace ka taimakeni ka rufama yarinya asiri
kasan halin Hurriya Daidai take da duk wanda ya kwana ya tashi kasan masarautar Qamar basu da
imani mai unguwa shiru yayi
Kowa ma shiru yayi yana kallon ikon Allah Hurriya da take tsaye fuskar ta blank baka iya cewa ga
yanayin ta Kumurci yazo saitin ta sannan ya daka mata tsawa wadda saida ta girgiza kusan kowa a
wurin Amman Hurriya ko gezau duk da saida yan hanjin cikinta saida suka kada Amman tayi kokarin
gyara tsayuwarta tana frowning fuskar ta Mai fidda zallan kyau tana kallon cikin idanun kumurciÂ
Kumurci kallonta yake da mamaki sannan cikin daga murya yace kaskantaciya yar gidan matsiyata
wadda tarbiya gabaki daya bata wadata iyayenki ba har suka baki ba yana magana cikin hargagi da
wulakanci yana kallon ko ina na jikintaÂ
Hurriya tace Are you mad kana hauka ne cikin zazzakar muryata mai dadi da dadin sauraro saboda
yanayin maganarta hankalin kowa ya dauku ya dawo kanta tarbiya bata wadata iyayena ba kai kuma
jahilci ya wadata naka iyayen tunda gashi kana juya abinda suka koya maka cikin doddar kwakwar ka
Animal Asshole
Kumurci banda radadi ba