Masarautar Qamar Hausa Novel

Author :  Khadija KMU Category :  Love

Chapter   5 / 13

12K to 15K   out of 36.4K words

masarautar kuma wahala zata sha
don ko bata durkusa ma ma’aikata ba ai akwai ubannin gidansu da dole suyi masu biyyaya tana fatar
dai Allah yasa kada su sha wahala don ganin Hurriya tana wahala tamkar itace take wahalar bazata
iya dauka ba.
Murmushi tayi ganin Hurriya ta  tsotsi bakinta sai kuma ta turo bakin tana bata fuska alamar
shagwaba magana tayi da wani yaren Bintu da take kallonta taji tana magana tana bata fuska da
wani yaren da bata taba ji ba 
Don tasan yaren dai gaskiya babu kalar shi a Nigeria 
Kallon kyaun hallitar fuskarta takeyi yadda tayi ma fuskarta kamar wata baby magana takeyi cike da
shagwaba murmushi Bintu tayi tace naga ranar da Hurriya zata daina daure fuskarta tana shagwaba
haka tabb akwai ruwa da kankara ranar.
Bintu bacci ta faraji don Haka ta kalli Hurriya ganin ta dukunkune wuri daya kuma ga space nan da
yawa don haka ta raba gefenta ta kwanta nesa sosai da ita don kada cikin bacci Hurriya taji ta a kusa
da ita ta tureta 
Addu’a tayi sannan ta runtse idonta bacci mai cike da gajiya ya dauketa .

Karfe bakwai  Bintu ta tashi har lokacin Hurriya bata tashi daga bacci ba ta makara don haka
agurguje ta kama ruwa hade da alwala tazo tayi sallah .Tana gama Sallah taje inda taga sauran yan
uwanta karime tayi ma magana tayi banza da ita don haka tayi ma uwale magana tace miye akeyi
anan uwale tace zamu tafi ne za’a araba mana aiki bata ida magana ba saiga Uwar bayi tazo Kallonsu
tayi tace saifa kun kula kubi a hankali kuskure daya a masarautar nan zai iya zamar mutum babban
kalubale a rayuwarta, kowa amsa mata yayi sannan suka bi bayanta tafiya sukayi Mai nisa sannan
suka iso katon wuri inda mazan dasuka zo duk sunja layi suma layi sukaja suna kallon kyawu da
tsarin masarautar da babu wani Abuna more rayuwa da bai wadace ta ba.
Kwance take a lallausar katifa wani Abu dake gefenta kamar wasan yara ya fara kara bude idonta tayi
masu cike da bacci kokarin komawa take Amman karar ta hana ta karar wayarta ta hade da karar
abunda yaketa wakar yaran tsoki taja tana maganganu da kuma mamakin wani marar sa’a ne ya tada
ta daga bacci Amman bari Taga kowaye tana jawo wayar wani call din na kara shigo mata kallon
wayar tayi da wani bacin Rai cikin muryar ta maidadi tace oh my God sannan ta ziro dogayen
kafafunta wani Abu ta latsa saiga kuyangi guda Biyu sun shigo suna dukar da kansu kasa sannan cike
da mugun girmamawa sukace Allah ya taimake ki Allah ya kara maki Nasara Allah yasa wannan Rana
tazamar maki Ranar farin ciki da Albarka Batace masu kala ba sai da tagama Shan kamshinta sannan
ta kallesu Dukansu ba wanda baisan ma’anar kallon da tayi masu ba don haka da sauri daya daga
cikin kuyangar ta shiga toilet dinta ta hada mata ruwa Daidai yadda tasan tana amfani dashi kullum
ta zuba mata flowers masu kamshin dadi ta wanke mata brush ta sanya mata macline Mai kamshi ta
fito tana durkusawa tace Allah ya taimaki Batatuma Angama 
Dayar da take tsaye wacce har ta dauko pink towel dan dora mata towel din tayi  sannan ta zame
mata rigar tareda rumtse idonta  ta yadda kada a samu matsala taga wata siffa ta jikinta cewa tayi ya
isa don Haka ta juya Neela ta ida daura towel dinta ta shiga toilet din saida ta farayin brush tadan
shafa wasu abubuwa na skin care sannan ta shiga bahon da aka hada mata ruwan wanka lumshe
idonta tayi tadan fara wasa da ruwan saida ta dauki mintina kafin tayi applying showe gel dinta mai
sanyi dadi ta wanke jikinta tass sannan ta fito
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: Masarautar Qamar 
By Khadija (KMU)
Page 13&14
A hankali ta fito daga toilet din tana fitar da wani kamshi har tazo tsakiyar dakin da angyara shi tass
kamar ba’a taba kwanciya ba vanity table ta zauna tana kallon kanta olive skin dinta sai glowing
takeyi ringing din wayarta ne yayi kara wanda tasan ba kowa bace face kilan mahaifiyarta a hankali ta
tashi kamar wadda batasan taka kasa saidai ba kasa bace batason takawa tsantsar sarautar dake
yawo a jikinta ne   bata fuska tayi ganin Mai kiranta kin dauka tayi har ta tsinke karar wayarta ne ta
karayin kara dauka tayi ta kanga a kunnenta muryar mai dadi da sautin amo tana ratsa dakin don da
tsiwa take maganarta liya wai lapia kike kirana kamar wadda ta ci maki bashi daga dayan Bangaren
liya wadda tagama shiryawa tace I just missed my twin sister i decided to check on her ko nayi laifi ne
Neela takirata da karfi tace liya da bacin rai a muryarta dariya liya tayi tace wallahi kiyi sauri ki fito ko
In kira basai na fada ba kindai san sauran su idan na kirashi Neela tayi sauri ta dafe zuciyarta tace
bansan kalar wasannan dariya liya tayi tace Don’t forget to wear green palazzo and white shirt 
Tun jiya na sanya akawo maki kayan so kiyi sauri kinsan mu suke jira tunda Mai Martaba da kanshi
yace Aikinmu ne Neela da take saurarenta cike da taikaici tace I know I know go to hell Liya I hate you
liya dariya tayi tace I love you Neela kashe wayarta tayi . Twin sister dinta kenan she always gets on
her Nerves shiryawa tayi cikin kayan da  Liya tace akawo mata tun jiya wandon palazzo ne na prada
da wata rigar gucci da takalma da scarf 

Inner wears ta sanya sannan ta fesa turaruka masu tsananin tsada ta shirya cikin kayan wadanda
elegance dinsu sun fito ko ta ina kayan ba karamin kyau sukayi mata ba don dan karamin scarf ta
daura kusan duka rabin gashinta ya zuba a baya sai kamshin mai masu dadi takeyi Kallon kanta tayi
A madubi sannan taga yadda tayi kyau murmushi tayi wanda ya fito mata da dimples dinta she’s
proud of her beauty don masarautar tasu sai kana da kyau za’a san da existance dinka shiyasa subira
tayi masu fintinkau saboda tsanin kyau da mulkinta Tunawa kawai da tayi da ita taji zuciyar ta na
tashi bloddy Hell tace saboda tasan ta kusa dawowa ba dadewa Neela tace koda yake da da yanzu ba
dayaba ,ba zata iya daukar iskancin subira ba zuciyarta ce tace kullum sai kince da da yanzu ba daya
ba Amman kullum dayane saboda ba abinda kuke iyawa a gaban yarinya mai jin kan tsiya.
Tsoki tayi ta fito katon parlon ta wanda yake cike da abubuwan more Rayuwa tunda ga floor din
parlon da chandeliers din da suke à sama wanda suke bama ko ina wani irin haske wall bracket din
kuma masu wani irin designs na royalty masu bala’in kyau fitilu ne ko ta ina haske kam har zai iyayi
ma mutum illa saboda parlon baida wani hayaniya sosai don American parlor ne ko royal chairs babu
kujerun l-shape designs masu kyau 
Tana fitowa kuyangin Dukansu suka dukar da kai kujerar dining daya daga cikin su ta ja mata ta
zauna sai kuma daya daga cikinsu tazo da sauri ta zuba mata Irish da liver sauce sai coffee cewa tayi
su ta zataci abinci don duk sunyi mata tsaye da sauri kuyangin suka fita waje suna jiranta tagama cin
abinci ta take hankalin kwance saidai wayarta na hannunta tana duba wani abu a Instagram kara taji
wadda karar ta kusa firgitata,Neela da tasan ba wanda zaiyi hakan sai liya don waye ya isa bama
wanda ya isa liya janye plate din Neela tayi ta faracin chips din tace shey you’re here enjoying your
breakfast nikuma banci komai ba haba Neela tana maganar tana dafe zuciyarta sannan tace Baki da
kirki kallo daya zakayi Neela kasan ta gaji da halin yar Uwarta wadda kammanin su daya don idan
zaka tsaya kana kallon su baka isa ka gane daya acikinsu ba,saboda kamanninsu. liya cin cips din take
harda mugunta while Neela kallonta kawai takeyi har ta cinye sannan ta dauki coffee din dake
gefenta ta shanye dariya tayi tace yanzu naji Daidai tashi mu tafi Neela hararta tayi tace liya daga yau
kada ki kara shigo mani chamber dafe zuciyarta tayi sai ta bata fuska tace haba my twin kin sanya an
raba mana chamber yanzu kuma so kike in daina shigowa chamber kwata kwata tana dafata tsoki
Neela tayi ta ture ta dariya liya tayi tace muje 
Tare suka jero suna tafiya Dukansu kuyangin a bayansu wasu kuma a gabansu olive skin dinsu sai
shining yake with the help of the sun don Duk bala’inka baka isa kace ga Neela ba ,ko liya saboda
tsananin kammannisu moto ci aka bude ma kowace a cikinsu sannan suka shiga baya Daidai inda su
Bintu da sauran mutanen da suka zo dasu suka tsaya Bintu da sun kusa awa uku suna jira Dukansu
sun gaji ga yunwar da sukeji kamar mi saidai hankalin ta baki daya yana wurin Hurriya da har yanzu
bata ganta a wurin ba.
Kallon princesses guda biyu masu kama daya sukeyi su Dukansu kamar kauyawa maza da matan
duka kallonsu sukeyi kyau, siga, gayu ,sa’ar rayuwa da mulki kawai suke gani lahaula wala kuwatta
illah Billah kawai Bintu take cewa kamar rana haka suka fito don sun haske ko ina don kowa su yake
kallo 
Kuyangin a gaba da bayansu sukuma a tsakiya Har sukazo inda aka tanadar masu su kadai don su
zauna kujerun kansu abin kallone 
Su Bintu natsuwa sukai wurin ya dauki wani irin shiru liya da Neela kallon kowa sukeyi da isa kuma
da sarauta da idanunsu masu kaifi 
Kuyangin kuma duk sun dukar da kansu a tsaye magana liya tayi da kuyangar dake kusa da ita 
Ita kuma ta isar da abinda tace ga uban kuyangu da bayi.

Hurriya tun dazu ta tashi lokacin da ta tashi sai taga ba kowa a dakin don haka ta fito ganin kuyangu
tayi duk suna ta hidimar su kowa da abinda yakeyi wanka takeson tayi don jikinta duk yayi tsami bata
matsa daga inda take ba tsaye saiga Kumurci yazo da ledar kayanta da mamaki yake kallonta Saboda
yaga sauran yan uwanta wurin da suke jiran Gimbiya Batatuma da Gimbiya shawata cike da mamaki
yace ya akayi Bakije ba banza tayi dashi,Hurriya kamar bada ita yake magana saida ta jima sannan
cikin muryar ta Mai tsanani dadi tace bani kayana ta ida maganar tana tsotsar bakinta kadan 
Kumurci kallonta yake yana kara tasbihi aranshi yarinyar Allah yayi mata tsananin kyau ga wani uban
kwarjini da take dashi ita kam da tasan yadda daurewar fuska keyi mata kyau data rage daurewa
tana dariya kilan mazan masarautar hankalin su bazai dauku da kyawunta ba 
Kallon kayan jikinta yayi tun na jiya ne wanda yaganta dasu ba hijab ko dankwali babu don duka
gashin yayi baya ya sauka a bayanta tsaki Hurriya tayi tace malam ka samu Tv ne?kumurci da yadan
daburce cike da borin kunya yace ga kayanki Hurriya kallon kayan tayi sannan tace ka ajiye zan dauka
da mamaki yake kallonta don ba’a taba yi mashi irin haka ba Hurriya kam ta rungume hannunta tana
kallonshi ido cikin ido kwarjin tayi mashi sosai don haka ya janye idonshi akwai abinda yakeson gaya
mata Amman bai iyawa saboda yadda bakinshi yayi mashi nauyi juyawa yayi ya tafi ita kuma Hurriya
tayi tsoki ta kalli wata kuyanga sannan tace ina zata tayi wanki Kuyangar sakin baki tayi tana kallonta
don sauran kadan ta ruga saboda kyauwunta da gashinta kallonta kuyangar kawai takeyi Hurriya da
ranta ya fara baci don ta tsani kallo itama cike da rainin wayau tace wai Tv na Zamar maki ne hajajju
Aa baiwar Allah kinada kyau ina jiye maki tsoro ne ga kuma kina da gashi kuma naga shigar kamar
bata musulma ba tsoki Hurriya tayi tace akwai wata doka ta sanya kayane? Girgiza mata kai kuyangar
Tayi tace ina guje maki karnunkan masarautar nan ne maza da mata 
Hurriya tace kinsan fundamental Human right?girgiza kai tayi Hurriya akwai Right of choice yanzu
idan naga dama zanyi yawo yadda nakeso kuma ba wanda ya isa yayi depriving right dina so shiga
zanyi wadda nikeso hakajju iyakar ki kallo 
Kuyangar tace iyakata kallo kuwa shiga kuma duk wadda kika ga dama kiyi zaki basu labari ne a
masarautar Qamar Hurriya dage rigarta tayi ta daureta daga gefe shafafen cikin ta wanda sai daukar
ido yake sai kuma wata yar sarka ta gold da take like a cibinta ta fito kallon matar tayi tace kafin In 
fara bada labari ke ya kamata ki fara basu labari tace  munafuka  magulmaciya kuyangar mutuwar
tsaye tayi tana kallon shafaffen cikin Hurriya ko kyaftawa batayi Hurriya tsoki tayi ta saki rigarta tace
sakara munafuka ta barta baki sake don kam taji kunya kuyangar sosai Hurriya tayi gaba abinta tabar
ta tsaye tambayar wata tayi aiko ba bata lokaci ta rakata har inda suke wanki bata da sabulu don
haka ta kalli wadanda suke wanki a wurin wanda suma suke ta kallonta
Tsoki tayi ta kalli wata da take kallonta kamar zata lasheta sabulu ta gani da ruwa a gefenta don haka
Hurriya ta zuba ruwa cikin bokitin dake gefen yarinyar ta dauki kayan da tasan zata sanya yau saboda
idan tace zata wanke duka zai dauketa lokaci don haka kala daya da zata sanya yanzu ta sanya
wandone palazzo da yar top ta duka ta fara wankewa 
Hurriya tanajin ana kallonta a jikinta amman tanason ta gama wanki da takeyi saida ta gama wanke
kayanta tass ta juyowa tayi ta kalli yarinyar dake mata wani irin kallo Hurriya ruwan kumfa ta diba ta
watsa mata nan take ta juya tana soshe kanta Hurriya ruwan dauraya ta zuba taje ta shanya kayanta
inda taga ana shanya ta ajiye mata bokitin yarinyar tace mata ki kawo sauran kayan ki in wanke maki
naga ke bakuwace Hurriya banza tayi da ita ta jawo wayarta ta sanya waka ta samu wuri ta zauna
tana bin wakar tanajin idanu sosai akanta amman ko a jikinta kallon kafarta tayi har dan kumburi tayi
ita ba ma’abociya sanya safa bace amman ya zatayi tsaki tayi 
Alamun bushewar kayanta da ta ganin ya sanya ta dauki abunta ta tafi. wanka take Bukatar yi don
jikinta duk ya dameta tanayin wanka fin sau biyu a rana jikinta har yanzu bai saki ba don tanajin
radadi har yanzu a fatarta a waje ta hadu da Habiba 
Amman bata ganeta ba Hurriya sarai taganeta zuwa tayi inda Habibar take tace ki samo man ruwan
zafi inyi wanka kallonta Habiba kawai takeyi Hurriya shiru tayi tana mamakin yan masarautar basu da
aikin yi ne sai kallon mutane tsoki tayi wanda ya sanya Habiba cewa to bari in samo maki a kitchen
mi zakiyi dashi? Shiru Hurriya tayi tana kallon Habiba tanason karantar ta saida tagama kare mata

kallo sannan tace Bath shiru Habiba tayi alamar bata gane ba tace mata wanka da sauri habiba tabar
wurin da niyyar nemo ma Hurriya Ruwan wanka bata wani bata lokaci ba sai gata da ruwan zafi 
lokacin har tana wurin Hurriya ta cire safarta habiba na dawowa ta mika mata kayan data wanke  da
safar alamar ta rike mata jiki na rawa habiba ta amsa sannan Hurriya ta shiga inda take tunanin toilet
ne da kyar Hurriya take wanka a wurin saboda shegiyar kazantar dake ciki bata wani jima ba don
watsa ruwan tayi ko sabulu babu ta maida kayan jikinta ta fito 
 A inda tabar Habiba ta amshi kayanta sannan ta shiga katon dakin har inda suka kwana itada Bintu
kallon katifar tayi taga an gyara tsaff tsaki tayi jin rashin brush din da batayi ba a hankali ta dauki
madubi ta bude bakinta tana kallon hakoranta da suke farare jere yan kanana kallon abinda yake
gefe da gefen hakoranta tayi golden wanda sai salki yake kurama abun ido tayi tana kallo sai kuma ta
rufe bakinta tare da yin tsoki abubuwa da yawa sun dameta ba abinda tazo dashi na yau da kullum
na rayuwa da ace bata siye kayan nanba da batasan yazatayi ba tunawa tayi da sauran kudinta aiko
ta bude ledar kallon kayan tayi don tana gani tasan anyi mata bincike bata wani damu ba itadai
damuwar ta kawai sarkokinta wadanda suke taimaka mata wurin cigaba da rayuwa a hankali
tajawosu taga sai sparkling sukeyi zame rigarta tayi ta kalli tatoo din dake zane a jikinta sannan ta
kalli zanen sarkar da akayi design da irin tattoo din jikinta a gefe, sai Stone din dake tsakiyar sarkar
dake rubuce da H baro baro kallon dayar sarkar tayi zuciyarta na kuna so take tayi kuka amman
tasan ba lallai ta iya kukan ba wani wando ta zaro yana da aljihu can kasa kuma daga ciki sannan ta
sanya abinta tare da addu’ar kada a dauke mata kara kallon tatoo dinta tayi wanda yake a gefen
bayanta jin motsi mutum ya sanya tayi saurin sakin rigar tareda sauke ajiyar zuciya habiba kallonta
tayi tana kallon rabin jikinta da ya fito saboda rigar daman buttones gareta to da ta bude rigar kusan
har cleavage dinta ana gani kuma bata maida buttons din ba lumshe ido Hurriya tayi Habiba kam
tsaye tayi tana kallon jikinta wanda bata taba ganin fata mai sheki da kyalli irin tata ba tana tunanin
ko twins albarka.
Hurriya tanajin idonta a jikinta saidai batada energy na magana don duniyar tunanin takeson fadawa
abinda ta tsana kenan rayuwarta don tunanin rayuwarta ta baya pure darkness ne wanda bata fatar
wani ya tsinci Kanshi a ciki ,ta iya shutting kuma ta iya controlling emotions dinta abinda tasani shine
idan har kaine kake da kanka to zaka iya controlling abubuwa da yawa saidai akwai abinda baka iya
controlling saboda we’re human beings kuma Humans are weak.
Please comment share and like
Love you all
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar 
By Khadija (KMU)
Page 15&16
Bude idanunta masu kyau tayi sannan ta sauke su à habiba da take binta da wani irin lustful look
Hurriya zuba mata idonta masu kaifi da kwarjini tayi da sauri Habiba ta gyara tsayuwarta sannan tace
kina bukatar wani Abu a hankali Hurriya tace comb da sauri Habiba ta kawo mata comb kallon dogon
gashinta takeyi wanda kwata kwata bai kama dana yan Nigeria shiryawa tayi cikin wani brown
palazzo sai red riga gashinta sakwa sakwa ta daureshi Habiba na kallonta kamar zata cinye ta so take
ta taba gashin taji idan nata ne Amman tsoro ya hanata takalminta ta sanya ta fita batasan inda
wurin yake ba saida ta tambayi wani ya nuna mata hanyar da zata bi duk inda ta wuce kallonta akeyi
tanaji a jikinta kuma tasan ana kallonta saidai ta saba ko a garinsu haka akeyi mata irin wannan
kallon tafiyar ma taki karewa saboda nisan tafiyar wurin.

Uban bayi ya kirga su Amman ba mutum daya acikin mata kuma ance masu su talatin ne mamaki
sosai ya kamashi don haka ya nufi inda twins suke Allah ya taimaki shawata Allah ya kara maki
nasara Babu mutum Daya a cikin mata kuma su talatin ne liya da mamaki take kallonshi don ba’a
taba samun

5 / 13