Author : Khadija KMU Category : Love
abinda zuciyar shi takeyi don ba’a taba maida mashi martani irin yau ba
kuma cinkin mutane daga hannunshi yayi zuciyar shi banda tafarfasa ba abinda takeyi zai sauke a
fuskar shi Hurriya ganin marinta zaiyi da sauri ta cire dankwalin da tadaura yau cikin sa’a ta sanya
dankwalin ta rike hannunshi tana rikewa tayi sauri ta saki kamar ta kama kashi kowa kallonsu yake
itama tana kallon cikin idonshi tace Kana hauka ne ?sai tadan tsotsi bakinta kadan
Kumurci kam kallonta yake har baya kyaftawa tunda yake baitaba ganin mace mai kyaun ta ba don
lokacin da take mashi magana ya kura mata ido har gold din dake ratsin hakoranta biyu saida ya gani
saboda irin kallon da yake mata Hurriya kam lura da hakan yasa tayi shiru tana kallon tsakiyar
idanun shi Kumurci kallon dogon sumar gashinta yake don baitaba ganin wani da irin gashinta ba ko
subira da take take takama da kyau da gashi Hurriya ta fito don nata cike yake ga tsawo ga yawa
wannan yarinyar dole ya tafi da ita masarautar Qamar Hurriya daukar ledarta tayi tace wawa dan
akuya sannan ta kama hanyar kofaÂ
Kumurci kam daya saki baki yana kallon ta Sauran dogarawan kam kallom Kumurci sukeyi don ya
kasance Azzalumi kuma marar Imani Amman yau wata yar matsiyaciya yar talaka kuma karawu zata
zauna ta Gaya mashi maganaÂ
Laminde kam tsoro da fargaba ya cika mata ido tanason Hurriya bata kaunar wani abu ya sami
yarinyar dama bata zo ba saboda ta sani sarai bazasu barta lafiya ba.
Kattin dogarawan dake tsaye gefenta ne suka tare mata hanya a hankali ta dan ja baya jin saukar
wata azababbar dorina ya sanya ta juyowa wasu ta gani guda biyu dukan ta suka farayi ba ji ba gani
da wani irin rashin imani suke dukan ta laminde kam kuka take don duk bulala daya idan akayi mata
sai ji takeyi kamar ita ake duka mai unguwa saidai dauke kai yayiÂ
Hurriya kam tana durkushe don tun bulala daya da sukayi mata ta durkusa ta dukar da kanta ta hade
kafafunta da gwiwowinta dukanta suke ba ji ba gani duk wanda yaga Hurriya sai ya tausaya mata don
idonta sun kada sunyi jawur kukan zuci take wanda yafi ko wani kuka zafi da radadi fargaba da tsoro
duk ya cikata laminde matar Mai unguwa kuka takeyi kamar ita ake bugu kasa jurewa tayi ta rugo ta
wurin saitin masu bugun ta dan ture Hurriya aka zabga mata bulalar Ai laminde fitsari ne kawai bata
saki ba saboda azaba Hurriya dago jajayen idanunta tayi ta saukesu akan laminde kukan da Hurriya
zata iya cewa rabon da tayi shi har ta manta ne yazo mata laminde kallonta tayi ta girgiza mata kai ta
daina kukaÂ
Bulalar suka kara zuba ma laminde Hurriya zuwa tayi ta ture ta tana masu wani kallo Mai unguwa ne
ya kalli dogarawan sannan idonshi na taruwa da kwalla yace don Allah kuyi hakuri ku taimaka kuyi
hakuri ta gane kuskurenta yanzu Saminu ya kalli Kumurci wanda yake kallonsu yana kallon Hurriya
wadda tayi ligis Kumurci yace sharadi dayane zamu baku Mai unguwa yace ka fadi koma wani irin
sharadi ne zamu cikashi In Sha Allah murmushi yayi sannan yace ko matarka ta bimu masarautar
Qamar ko kuma wannan matsiyaciyar ya nuna Hurriya shiru Mai unguwa yayi Hurriya da idonta
sukayi jajir ta dago tana kallonshi wani murmushin mugunta yayi mata laminde tayi sauri tace ni
zanje wallahi ku kyale yar marainiyar yar nan ku taimaka don Allah Hurriya kallon laminde take
wadda banda kuka ba abinda take matar ta sota duk da hali na kin kulawa da take bata Amman bata
taba gajiyawa da ita ba laminde ta kalli maiunguwa da idon shi sukai ja tace ga Hurriya nan don Allah
ka kula da ita Maiunguwa cewa yayi laminde tare zamu tafi mubar Hurriya a garin nan ni zan biki
murmushi tayi tace idan mun tafi kuma mubar ma wa ita? Hurriya da zuciyarta tagama karewa ta
bude baki kamar tana tsoron magana tace I will go with them cewa tayi banji Mai kikace ba Hurriya
tace zan bisu Kumurci wani murmushi ya saki yace da kin taimaki tsohuwar da take tsugune tana
rokona Don wannan matar idan har ta bimu sai na sanya ta Zama baiwa mafi kaskanci a masarautar
Qamar kuma sai na tabbatar da ko wani kaskantar bawa ya kusanceta yayi dariya Hurriya kam
idonta kadai inda ka kalla zakasan tana cikin zallar bacin rai ga galabaitar da duk tayi laminde girgiza
kai kawai take tace ba inda zaki ni zan tafi tana kuka tana girgiza kai Hurriya kam abinda bata tabayi
ba shi tayi lallashi don bata iya ba ma kwata kwata Amman daga jin yanayin muryarta zakasan kokari
ne take tana magana zan dawo zan kira shine abinda tace Kumurci kam kokarin turata ya farayi
juyawa tayi ta kalleshi tace kada ka sake ka taba ni da kazamin hannunka a irin yanayin da tayi
maganar zaka san ba abinda bazata iya ba idan har ya kara Kumurci kallonta yayi yaga yadda idonta
ba wani abu wai shi tsoro shiru yayi sannan yace yarinya zaki gane kurenki a masarautar Qamar don
karnukan suna da yawa ya fada a zuciyar shi.
Hurriya jikinta duk ya mutu saboda dukan da akayi mata laminde kuka kawai takeyi don abun yafi
karfin ta Jikinta sai kyarma yake ledar dake yashe ta kayanta ta daukaÂ
Kumurci ya kalli mutanen da dogarawan yace su fito su tafi kamarshi ake jira aka tasa kyayar
samarin suna turasu kamar jakunaÂ
Hurriya gashinta duk yayi budu budu saboda bata maida dankwalin da ta cire ba lokacin da zata rike
hannun Kumurci shikam Kumurci da ya juyo ya kalli yadda take struggling yakejin gabanshi na
faduwa saboda yadda yakejin zuciyar shi ya kosa su isa masarautar su Mai cike da zallar zalincin he
can’t wait to have her in his bedÂ
Cikin hiace din emirates din ake ta tura maza saida aka cika mota guda uku Hurriya dai tana tsaye
bata matsa ba saboda duk duniya ta tsani taji jikin wani kusa da ita gashi duka marmatse suke saidai
fa ko zata mutu a wurin bata shiga motar nan don waye ma baisan Hurriya Faisait hamood ba duk
wanda yayi gigin tabata da hannunshi saidai yaji saukar mariÂ
Daya daga cikin dogaren ne yazo ya zuba mata bulala ke yar matsiyaciya shiga banza tayi dashi donÂ
wani bansan kallo tayi mashi bata ko daga baki ba ballantana yayi tunanin zata bashi amsa kara mata
wata bulala yayi har tana durkushewa kasa da kayanta shegiya matsiyaciya ki wuce ki shiga Dukanta
ya fara kamar Allah ya Aiko shi yana zagin Hurriya da ta shiga motar Amman shiru tayi saidai fa ba
hawaye amman idonta sunyi ja saboda radadi da azabar da take ciki Kumurci ne ya buga mashi
tsawa yace shaho ya isa hakanan shaho badan ya gaji ba ya daina dukan ta ya lura wata isa gareta
alhalin ita din ba kowa bace face kaskantarciya Kumurci ne yazo saitin da take yace Mai kike jira da
bazaki shiga ba banza tayi dashi kamar batasan da ita yake magana ba kara tambayar ta yayi banza
Hurriya tayi dashi har cewa yayi zai kira shaho ya kara mata still bata ko motsa ba Hurriya kam taki
ko matsawa kowa mamakin Kumurci yake da aka ga yana lallabata saboda waye baisan Kumurci ba
saida Hurriya ta mula sannan tace ban iya zama kusa da kowa cikin motar I want to seat alone kallon
yadda take magana yake fuskar ta a daure kuma kamar tana bashi order abun ma dariya yaso ya
bashi Amman da yake Kumurci ne yayi saurin murtuke fuska ya kalli motar da duk maza ne a ciki
sannan ya fitoda mutum biyu yace ta shiga da kyar take tafiya Hurriya saboda dukan da tasha ,har ta
kawo wurin cikin motar kayanta gam a hannunta kamar daman sune rayuwarta kusan duka mazan
saida suka juyowa suna kallonta saboda kyaunta ga gashin dake yawo a bayanta tsawa Kumurci ya
buga masu dukansu suka shiga taitayinsu Hurriya bayan ta zauna ta fara sauke ajiyar zuciya tunani
take yanzu to ina rayuwa zata kaita lokacin da bata tsammani haka ya faru da ita saidai duk inda zata
tana fatar Allah ya bata ikon jurewa don ga dukkan alama sun nuna ba wurin jin dadi bane a hankali
ta duka ta nemo safa cikin kayanta ta sanya dukar da kanta tayi yadda ba wanda zai iya ganinta ta
cire sarkar dake wuyanta da kuma dayar sarkar ta sanya su cikin safarta harda kudinta duka ta sanya
su wayarta ce kadai ta bari a aljihunta tafiya ne suka fara Sosai don tunda ma aka fara tafiyar Hurriya
wani bacci ya dauketa tafiya sukayi sosai don kusan tafiyar awa biyar sukai don lokacin har amfara
kiran sallah la’asar shine suka tsaya domin yin sallah Â
Hurriya jin hayaniya ya sanya ta bude idonta a hankali nan taga sun tsaya masu gyada nata tallah
masu rake panke awara duk da sauransu cikin rashin kuzari ta sauko Amman jikinta yayi mata
mugun tsami don da kyar take tafiya wasu panke manya guda biyu ta siya aka bata canjin ta sannan
ta koma chan gefe ta zauna ta fara cin abunta
A hankali take ci ba don dadi ba sai don yunwa Hurriya taji ankira ta da mamaki ta dago kanta sai
taga Bintu.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: í ¼í¼šMasarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 9&10
Mika ma Bintu fanke daya tayi kato cikin jin dadi ta amsa tace nagode Hurriya ,shiru Hurriya tayi tana
kallon yadda Bintu ke cin panke a hankali ta kara kiran mai fanken cikin muryarta Mai dadi kara mika
mashi kudin tayi tace ya bata na dari guda biyu ya kara bata mika ma Bintu tayi amsa tayi tace inason
ki Hurriya sannan ta rinka cin fanken kamar bata taba cin abinci duniya ba Girgiza kai Hurriya tayi
Bintu ce tace ma Hurriya kalli abinda dogarawa can keyi Hurriya mun bani Hurriya kallon saitin da
dogarawan suke tayi taga sun sanya sun jera layi layin maza daban na mata daban Hurriya batasan
ma cewar akwai mata ba sai yanzu da tagansu jere a layi kallon Bintu tayi tace tare dawa kukazo
Bintu da har ta fara kuka ta kalli Hurriya tace da wadancan azzaluman dogarawan daga kai Hurriya
tayi tace ya akayi kika biyosu kuka Bintu ta fara tace muna zaune a tsakar gida saiga kawar Larai
nusaiba ta shigo daki suka shi itafa Larai nusaiba tace ga yan masarautar Qamar nan sunzo zasu
dauki ma’aikata da bayi. Shine tace kawai ta tura ni aiki ba bauta ba suna biyan kudi Sosai kuma ita
za’a rinka bama kudin ina labe inajin su har nusaiba ta fito kallona tayi tace kuma naji ance sun fison
mata kyawawa kuma kinga Bintu ba daga baya ba sai Larai tayi dariya tace kedai bari ba karamin
taimakona kikayi ba nusaiba zan yadda kwallan mangwaro In huta da kuda gshi kuma Abun riba biyu
dariya kawai nusaiba tayi tace ai kin yanman albashin nata ko?? Larai tayi dariya tace abinda yafi
albashi ma don bakaramin taimakona kikayi ba suka kalli Bintu Larai ai nasan ubanta baida matsala
nusaiba kenan ya bani matsala ma yaga ikon AllahÂ
Bintu ta kalli Hurriya dake kallonta shine fa suka sanya na biyo dogarawan Hurriya daga mata kai
kawai tayi ta juya saitin dogarawan tana kallon tsantsar zalincin da sukeyi Maza da matan dake jere a
layi ake cajewa duk abinda aka ganka dashi sai a amshe har cikin riga suke lalubar matan cikin
tsantsar zalinci abun gwanin ban takaici Hurriya a hankali ta zaro sauran kudinta dake cikin aljihu ta
sanya su cikin safarta gyara safar tayi yadda ba wanda zaiga abinda ke a cikin kafarta cikin sa’a kuma
ba wanda ya kula da lokacin da ta dauke kudin Shaho ne da yake kusa da Kumurci suna zaune suna
kallon duk abinda ake don kamar sune manya kaga wata yarinya Mai kyau kamar ita tayi kanta nifa
bantaba ganin mai kyau irinta ba dogon gashinta ya bani mamaki nace anya bahaushiya ce kuwa ko
yanayin shigarta kadai zata nuna maka haka saidai fa kaga yadda take kallonmu girgiza kanshi yayi
Kumurci nifa idanuwanta tsoro suke bani Kumurci yarinyar can fa na cikin hadari saboda karnukanÂ
dake masarautar mu fa sunada yawa gashi ba babba ba yaro don ko nifa sai na lasa yana karasawa
da lashe baki Kumurci wani kallon banza yayi mishi wanda ke hade da gargadi shiru shaho yayi cikin
ranshi yace wallahi sai na lasa ai kaima nasan manufar ka munafukiÂ
Wani dogari ne ya kalli saitin dasu Hurriya suke kai tsinanu yan gidan matsiyata kuzo nan Hurriya ko
motsi batayi ba Bintu tace mata Hurriya ki taso don Allah mu tafi kadasu dake mu banza Hurriya tayi
da ita don maganar duniya taki ta tashi su Kumurci da shaho duka suna kallon abinda ke faruwa
Bintu zuwa tayi ta shiga layi kwalla na zubo mata dogarin kau cikin hasala yazo saitin Hurriya kallon
shi tayi cikin ido shine ke sanya hannunshi acikin rigar mata tashi tayi tsaye tace da uwarka da
ubanka sune manyan matsiyata da har suka haifo wanda baisan dajar halitar mata ba kaskantarce
kuma duka halayenka ke defining kaskanci Bullock wata muguwar ashariya shaho ya saki yace kaga
wannan yarinyar Kumurci shuru yayi kowa ma shiru yayi yana jira yaga abinda zai faru Azuciye
dogarin ya daga bulalar ya zuba mata a baya,mata da mazan wurin duka tsigar jikinsu tashi tayi suka
juya itakam Hurriya kwalla ce ta zubo mata abinda ta dade batayi ba a rayuwarta wato kuka ta
kasance a kullum rayuwarta ita Mai kukan zuci ce har tana jin dama zata iya irin kukan da Bintu keyi
kilan ta samu sanyi ko yayane a ranta bulalar da yayi mata har cikin kanta taji azaba matuka wanda
ta durkusa kasa hawaye na zubowa Daga hannunshi yayi da niyyar kara dukanta Kumurci ya rike
hannun yace ya isa haka Garba ajiye hannunshi yayi ba don yaso ba sannan Kumurci ya yace tayi
shiru sannan yace ki iya bakin ki idan ba haka ba to kina hanyar da bazata bullar dake ba don
masarautar Qamar sai yayi murmushin mugunta Hurriya tana durkushe a hankali ta shafo hawayen
don ta tabbatar da idan nagaske ne kallon hawayen tayi fa dagaske sune tasan ba lallai ta kara
maimaita irin wannan kukan ba saboda yau sau biyu tayi kuka sannan ta kasance zuciyar ta Mai
rauni ce saidai idan kaganta zakayi mamakin minene ya sauyata har haka da ba abinda yake girgiza
ta ko ya bata mamaki kuma fa rashin ganin mutumcin kowa duk girman ka Daidai take da kowa don
ko yaro yajefeta da magana sai ta maida mashi martani da wadda tafi tashi zafi shine kawai abinda
ke sanya ta magana ko sai kuma idan tana tare da Bintu don Bintu zata iya awa tana mata magana
baifi ta bata amsa daya ba saboda miskilancin ta Bintu har ta saba.
Kumurci kallonta yake saboda yasan akwai matsala a masarautar nan idan har Hurriya ta shige ta
don ya lura bazata taba saukar da kanta kasa ba don haka yake tunanin hanya daya zai bi don
tasamu barin masarautar batare da ansamu matsala ba shine yace baiwa ya samota kuma yaroki
alfarmar ta zama Baiwa hakimi shine kawai mafita anma ta cigaba da haka baisan a hannun wazata
mutu ba don princes da princesses din masarautar nan basu da imani ga kuma dayar matsalar don
Kumurci yayi nadamar tahowa da Hurriya don yasan ba karamar wuya zatasha ba don ko yaran sarki
kadai sun isheta don sun tsani wani yafisu kyau duk da daman masarautar kyawawa akafi kaiwa
saidai ba wanda san dalili to zai iya rantsewa tunda ake kai kyawawan mata a masarautar baitaba
ganin Mai kyaun wannan yarinyar ba don su kansu yaran mai martaba sai sun raina kansu.
Kallo daya zakayi mata kasan ta jigata ba karamar jigatuwa ba ma don wandon dake jikinta duk yayi
datti fuskar ta kuma duk ta kumbura ga babu annuri kwata kwata saida fa annurin kyanta nan don
sai salki takeyi Kumurci yace ki tashi ki shiga mota mu tafi yanzu bada hargagi yayi mata maganar ba
don zuciyar shi ta dan karye kadan Kallonshi tayi da idanunta masu kyau da wani kaifi Kumurci ya
daga mata kai tare da fatar kada tayi kafiya irin wadda tayi dazu.
A hankali take takawa amman zaka iya hango zallar mulki dake cikin tafiyar tata har ta shiga motar a
hankali Kumurci girgiza kai yayi don ya hango kurar dake tafe da ita saidai Allah ya kyauta don aikin
gama ya riga ya gama.
Bintu kam lokacin da ta koma layi cikin sa’a ba ba wanda ya lalubeta saboda hankalin kowa da ya
koma kan Hurriya tanajin su karime dake gabanta cikin layi suna dariya suna cewa Allah ya kara
sa’ade ce tace kinsan dadin da nikeji yadda ake bugun Hurriya karime tayi murmushi tace naki kika
sani ni yarinya ta dade tana bani haushi shegiya ga isa ga iko sai kace wata shegiya sa’ade tace bata
da mutunci Hurriya kinga cin mutunci da tayi ma mahaifina kuwa harda watsa mashi man awara
akafa bayan tagama zazzageshi cikin mutane karime yo naji maganar tana yawo agari ki bari idan
munje mu hade kai mu ci ubanta don ni ta dade tana bani haushi don kiga duk anguwar mu ace
mazan ita kadai suke kallo to yanzu lokacin mune idan munje muyi maganin karuwa Mai ma maza
jiki.
Bintu duk tanajinsu don harda kukan ta wurin da suka ce mata karuwa don tasan karya sukeyi Allah
ya saka maki Hurriya inji Bintu ta fada cikin ranta.
Hurriya da ta koma wurin zamanta ta jinginar da kanta jikin window tana rufe idonta saidai kyarma
kawai takeyi tana harhade hakoranta ga sanyi da ya isheta dankwalin da ta daura ta rufe gashinta
dashi ta koma ta kwanta saidai sanyi ya matsa mata don bata daina jinshi ba ledar kayanta dake
gabanta ta jawo saboda Asabe hada kyautar doguwar hijab tayi mata don lokacin har ta kawo zaure
Asabe ta kwala mata kira a hankali asabe ta mika sabuwar hijab doguwa maroon tace Hurriya ko
bazaki sanya ki fito ba ai nasan kina sallah to ki rinka sallah da ita inda so samu ne ki rinka fita da ita
sai kuma ta tabe baki tace nasan yaudarar kaina nike ba inda zaki da ita tace Hurriya ki godema Allah
don wallahi inasonki duk wanda yaji nayi kyauta sai ya kusa suma saboda mamaki kindai sanni da
san kudin tsiya Hurriya batace mata komai ba har tagama maganar ta sai Hurriya ta mika mata ledar
alamun ta sanya Asabe kam sauri ta dauko ta sanya Hurriya ta tafi ba godiya bare sallama.
Hijabin ta lalubo ta sanya ta dunkune kanta ciki a hankali bacci ya dauketa.
Sosai suka sha tafiya har suka iso Babbar masarautar Qamar bata sani ba don kowa ya fita a motar
ya barta Kumurci ne ya kula da babu ita don har anfara kada kyayoyinsu Kumurci ya bude motar
yazo inda take bacci da yake