Author : Hadiza D Auta Category : Romance
sai zai tafi ,kaya sosai ya kawo mana ni da ita. Matarsa da k'arfin guiwarta ta zo ganinmu har da turmin zanin goyo.
Haka iyalin Yaya Asad duk da basu zo ba amma kayan azriki mai yawa ya iso mana daga garesu.
An hakura an bar komai kamar yadda kaddara ta zabawa kowa rayuwarsa.
Zarya ta sami Sahal domin duk sati sai ya zo ganinmu.
Yaya Hamida babban galon din sanyi ta yi mini order tare da sauran kayan gyara na maijego ko ma na ce maijego package din gabadaya ta yi mini daga Bojuwa Herbals(08032773332) Kazar sababi ce sai na koma Kano zasu aiko mini. Ni da kaina nasan na hade na matse tamkar ban haihu ba.
Satinmu hudu muka tattara muka koma Kano, saboda hutun makaranta ya kare, ba dan haka ba sai na yi watanni biyu, tunda shi uban gayyar ba mai tsananine sosai ba.
A gugguje nake hakaito muku rayuwarmu ta baya iya wanda zan tuna da wanda yake da mahimmaci shi kawaii zan hakaito dan ku fahimci halin da na shiga ku yi mini alkalanci na gaskiya, dan haka ba zan hakaito wuraren da Basu da muhimmanci ko darasi ba.
Ranar da muka koma ya tisa ni da rawar jiki, ya dinga bare bare har sai da muka kebe sannan na samu saukin bibiyar da yake yi mini. Na zuba masa ido yana gefe yana barcin da ya zame masa ka'ida, matukar ya samu nutsuwa da ni to kuwa idan ya fara barci sai asuba sannan zai tashi ya yi wanka ya tafi masallaci.
Nazarinsa nake yi, na gamsu dari bisa dari baya mu'amala da matan banza. Domin shi gabadaya harkar bata zame masa irin do or die din nan ba. Yana iya sati ko sama da hakan bai yi ba, sai dai idan ya so kuma ba zai taba samun sukuni ba idan ba yi din ya yi ba.
Tsura masa idon da na yi kawai tunani nake yi, yadda bai taba hakaito cewar nima zan iya bukatarsa a wasu lokutan da shi na shi da bukatar. A wanccan lokacin da nake cikin shekarun kuruciya ba zan taba iya kada billena na nemi shi ko nuna masa ina da bukata ba, mussaman bisa al'ada an tafiyar da mu mijine yake da hakki akan wannan al'amarin. Kullum karatun da ake yi mana bita shine duk sadda miji ya bukace ki, to ki bar komai ki amshe shi if not ki fada cikin Allah da ma'aiki sannan ki kwana cikin tsinuwar mala'iku.
A fili na ce "To wai ita mace laifine idan ta bukaci mijinta ko kuma shi miji ba shi da wani laifi idan har sai yana da bukata za'a hadu, ko da ita mace tana da bukata?
Idona ya ciko da kwalla domin a kasar Hausa ba karamin abin kunya ba ne ka fito da maganar da shafi wannan lamarin bare har ka yi korafi.
Yanzun nan za'a yi maka mummunan zaton ka saba ma'amala da wasu mazan ne shiyasa ka raina kokarin mijinka daga yin aure shekara daya tak.
Na tuna sadda nake da watanni biyar da aure da na yiwa yaya Hamida korafi akan shaanin ban fahimce shi ba, ba karamin kunyata na yi ba.
A hakan na ba haka siddan na yi mata korafi ba. Maganin sanyi da na mata take ta aiko mini, na gamsu da kyaun kayan Bojuwa Herbals tunda tabbas daga Chad suke kawo wasu saiwowin. Mussaman na sanyi da na dahuwar kazar sababi. Akai Akai Yaya hamida take yin order duk sadda zata siya Kuma tare take siya mana, sai a kawo mini gidana ni sai na tura mata nata Kaduna tunda a can take aure.
A duk sadda na ci kazar sababi din nan yini nake yi cikin wani hali, idan kuma shi bashi da bukata sai dai na gama tsiyayata ni kadai.
Sa'a daya ma sanyi flusher da yake da tasiri nan da nan mai ciki bata sha.
08032773332 order ur sanyi flusher and kazar sababi now.
Dana gaji ranar da ta ce za'a kawo mini na ce mata "Yaya Hamida ni kam Kar a kawo mini, domin gaskiya ni ban wani gane kan abin ba, sannan ba kullum ne ake yi ba."
Salati ta dinga yi tana fadin "Bilkisu ashe baki da hakuri? Har yaushe aka yi auren da za'a ji wannan maganar a bakinki?
To gyara ba dan mijinki ya gamsu zaki yi ba? Duk macen da zai taba nan gaba sai ya gane ke ta dabance. Ni din nan sai da na yi haihuwa uku sannan na gane kan lamarin ban kuma fasa gyara kaina ba.!
Na yi sakato ina sauraren yadda take kunfar baki.
Kunya ta kama ni. Haka na ajiye wayar ban iya cewa komai ba. Hakan da ta yi mini ya sake sakawa na kame bakina ban sake bude maganar ba.
Kan dole na tashi na yo wanka, na gyarawa Amrah kwanciya sannan na kwanta don nasan ba zata farka ba sai asuba.
Tare da shi muke rainonta, Indai yana gida yana bata lokaci wajen rike mini ita. Haka nan siye siye kayan ci da na wasa tun ba'a zo lokacin bukatarsu ba ya yara mata su masu yawa. Haka nima suturar da yake yi mini tamkar an yi masa gorin yana yi mini kwangensu, komai fa ban nema na rasa ba. Shi dai inda mace tafi bukatane hankalinsa baya kai ainun. Don kuwa tunda na haihu sai ya zama dalilin da rungume ni da yake yi idan zamu yi barci ya daina. A bisa hujjar ba za'a bar yarinya a gefe ita kadai ba.
Yarinyar ta shiga ransa ainun ga shi tana girma kammaninsa na sake bayyana a tare da ita. Bayan haka kullum cikin tsabta yake ganinta da kwalliya, ko da fara tumbidi bana gajiya da gyarata don gudun kada a ji karnin nono tare da ita.
Sosai muke zaune lafiya bani da matsalar danginsa ko rashin wani abu. Idan ya kaini makaranta ko idan ya samu sararin dauko ni da yawa mata kallon so da birgewa suke binsa da shi.
Domin kwarai da gaske mai kyau ne, duk da siririne sosai.
A hakan har Amrah ta shekara tana kuma tafiya.
Bani da kawa sai Basma kusan a Kano ma bansan kowa ba sai ita. Shiyasa muka kulle muke aminci tamkar jinine ya hadamu.
Mun kammala karatunmu na fara bautar kasa a cikin Kano bayan an yi cuku cuku an maido ni domin da jihar Bayelsa aka tura ni.
Amma ban je can ba a dalilin an mini marriage certificate. Da taimakon baban Zaria aka bar ni a Kano.
Basma ce aka tura ta jihar jigawa. Satinmu biyu da fitowa daga camp aka bikinta, sosai muka yi hidima ni da Abida, min halarci bikin har Katsina inda aka kaita muka je kai Amarya.
Lafiya lau muke rayuwa har zuwa lokacin da muka shafe shekarun biyu har da watanni ba zance ga babbar matsala a aurena ba.
Na farko Sahal ba shi da takura, ma'ana baya mini kullen nan, shi dai kafin na fita ma sanar masa, ko daga makaranta ne na so wucewa wani wuri ba shi da matsala da hakan matukar zan kira shi na Sanar masa. Haka nan akai akai zai kwashemu mu je restaurant mu yi dinner mu dan zaga malls ya mana siyayya.
Bana rasa kudi a hannuna don baya mini shamaki da kudinsa.
Kawai inda matsalar take sha'awarsa akan mace ne ta yi mini kadan. Dan muna nisa abin na sake yawa, a farkon zamanmu baya wuce sati bai nemi ni ba, amma a yanzu sai mu kwashe kwanaki goma har a d'ora.
Idan aka dauke wannan matsalar bansan matsala a aurena ba. Wasu dararen haka zan yi ta hawaye marar sauti, har barci ya sure ni. Ba Wanda nake son na tattauna wannan matsalar sai Abida aman babu dama dan kuwa ta rufe dukkan amincin da zai sa na kai mata korafin aurena.
A lokacin kuma tuni Yaya Munira ta yi aure amma ba'a kasar take ba, tana Paris, tana ta zurfafa iliminta na lauyanci.
Yayin da Abida na daf da kammala karatun likitanci.
Har kuma lokacin bata bada kofar da zata yi saurayi bare a yi mata maganar aure.
Kwanci tashi asarar mai rai Amrah ta yi watanni goma sha bakwai a lokacin kuma mamanta Abida ta zo daga Zaria ta dauketa suka tafi Funtua zata yayata. Tun watanni biyu na so yayeta domin komai ci take yi sannan kuma ta jima tana yawo ma'ana ta jima da yin kafafuwa, ga ta doguwa tamkar Babanta.
Abida ce ta ki amincewa bisa hujjar Indai itace uwarta, itace zata yaye ta to sai ta samu dogon hutu. Sosai Amrah ta saba da ita. Dan haka bata yi mata kuka ko rikicin yaye ba.
Sannu a hankali rayuwa take tafiya. Ban jima da gama makaranta ba na fara sana'ar kayan fulawa(snacks) tare da abincin yara. Kamar na fada muku na karanci nutrition and dietetics. Muna yawan zuwa kauyuka da asibitoci muna wayarwa jama'a hankali akan abin da ya kamata su dinga bawa yaransu da su kansu saboda lalurar tamowa tana yawaita a kan yaran karkara.
Bincike kuma ya nuna na rashin isesshen ().
Dan haka sai nake yawan rubuce rubuce cikin harshen Hausa da na Ingilishi a kasar sadarwa ya Facebook a lokacin ita kadaice kafar sadarwa da zaka dinga yada manufofinka.
Dan haka na tara mabiya sosai, cikin hikima sai nake tallata hajata na bakery da nake yi. Cikin kankani lokaci na samu karbuwa domin a Kano kusan duk manyan bukukuwan da za'a yi ni nake aikin kayan snack da drinks da za'a sha a bukukuwan.
Sosai Ubangiji ya sanya mini albarka. A hakan Kuma Sahal bai taba kin yi mini hidima dan yana ganin ina samun kudi ba.
A shekarar da Abida ta kammala karatunta ta zama likita ta fito a matsayin physician.
Na haifi namiji. Domin walimar da su baba suka shirya mata na je da tsohon ciki, na dawo Kano da kwanaki uku na haifo yaro lafiyayye fari tas. Sai dai wannan kama yake yi da ahalina, ma'ana dangina ya kwaso.
Cikin kyautatawa Baban Amrah ya bani dama na zabi sunan da za'a sakawa yaro. Kaitsaye na ce masa "Yaya Faruk nake so na yiwa takwara".
Ba ja in ja, take ya yiwa yaro huduba da sunan Umar Faruk. Tare da fatan ya samu albarkar da yake cikin sunan, ya kuma gaji kirki da fara faran din mai sunan nasa.
Na fahimci har zuciyar Sahal na ganin k'imar Yaya Faruk yayin da ko ambaton Yaya Asad ba ya son a yi a gabansa balle a je ga jallin yin hirarsa.
Cikin nutsuwa nake jegon yaya Faruk domin har mun lankaya masa inkiyar, amma da Yaya Faruk ya zo ganinsa ya bada umarnin a kira shi da Faruk dinsa indai shi aka yiwa mai suna to a kira shi da sunansa kamar yadda shari'a tafi so.
Shike nan ake ce masa Faruk yayin da ni sai na hada da Yaya Faruk ko ma na ce yayana kawai.
Wannan karon umma da zo mini zaman jego sati uku kawai ta yi mini ta tafi nisa hujjar mijinta ba ya jin dadi, abokiyar zamanta. Dan haka saddiqa autar Mami da a lokacin tana aji hudu na sakandire sai aka turo mini ita tunda basu jima da yin hutu ba. Amrah kuwa dama tana Funtua wajen Mamanta duk da Abidan Mami ta barwa ita domin tana yin Housemanship a generall hospital Katsina.
Ban jima da yin arbain ba aka yi auren Anisa kanwata da take bin Ansar.
Hatta baba babba bai so aka yi auren Anisa ita kadai ba, ya so ne a hadasu da Abida amma ta kafe akan ita bata sami miji ba. Dan dan haka ayi auren Anisa tunda ita ta samu miji.
Akan dole aka yi bikin Anisa Wanda a lokacin tana shekarar karshe a nursing school ta Kaduna.
An rasa gane inda Abida ta saka gaba akan aure. Gabadaya ta ki daukarsa da muhimmanci, ta ki bawa kowa fuskar da zai tunkare ta. Wani malaminsu a nan jamiar Ahamadu Bello ba irin nacin da bai yi mata ba. Sadda zata zo Kano da na haifi Yaya, zata kwana daya, sai ta dauki Amrah su wuce Funtua, yana jin ta zo Kano ya biyo ta daga Zarian, falonmu aka sauke shi.
Aka kai masa samosa da meat pie tare da lemo da ruwa.
Bai wani jima ba ya tafi. Na kuma tabbatar sallamarsa ta yi, ta hanyar gabatar masa da tana da uzzirin da zata yi a lokacin.
Cikin kwantar da murya na ce "Autar momi wannan kam ya yi ba shi da kyau sosai, sannan cikakken jikine da shi, ga shi d'an boko ne irinki."
Fuska ba walwala ta ce ",Ko kusa da yi bai yi ba, Bilkisu. Kinsan har yanzu bai tunkare ni kaitsaye ba sai dai hannunka mai sanda tare da gifts din da bazasu rude ni ba. Mafi muni ma rainon yaransu zan yi masa. Matarsa ce ta rasu 7months ago. Ta bar masa yara biyu duk maza. Shine yake neman wacce zai aura ya mai mata lalurar yaransa idan kuma ka ce ba zaka yi ba society ma ba zai maka adalci ba, idan kuma ka karba yaran kana musu hidima su yi ta azabtar da kai, kuma ubansu ma ba yaba maka zai yi ba.!
Ta muskuta ta ce "Kin ga na yi kama da wacce za'a aura dan ta yi rainon yara? Ko kin ga na matsu da yin auren ne bare har a yi madadi da ni?"
Da azama na ce "Ina kuwa maman Amrah!
Saboda yadda ta daure fuska ainun nasan idan na kawo mata misalin da yake nufin ba lallai al'amarin ya zo a yadda ta fahimce shi ba, ta janye sassaucin da ta yi mini har take yi mini bayanin da zan gamsu da ra'ayinta cikin lumana. Kuma Gaskiyar magana shakkarta nake yi har yanzu da muka girma. Abida no nonsense ce sannan bata taba karban abin da bai yi mata ba, kunya ko kawaici basa tasiri a inda zata cutu.
Ta sake ce wa",An dame ni da ina korar samari. Na auren ne bai zo ba, ai ni bana son wannan wahallaliyar soyayyar Maigado. Sannan duk da namijin da ba zai iya tunkarata kaitsaye da nufin yana sona ba, to kuwa ba zan taba sauraronsa ba domin ba shi da confidence ni kuwa jarumi nake so na gaske."
Na numfasa na ce "Allah ka turo jarumin nan da wuri."
Bata motsa ba, bare kuma ta amsa. Na tsura mata ido na ce ,"Amma kinsan dai na matsu ki haifo mini tawa yar ko Abida?"
Ta murmusa ta ce "Aure ai ba shine tabbacin idan an yi za'a haihu nan da nan ba. Ke dai ki yi fatan Ubangiji ya kawo masu albarka, ba ga Yaya Faruk nan a hannunki ba, ai shi naki ne".
Na rike hannunta murya na rawa na ce "A a ba haka muka yi ba autar momi. Kada ki canja magana".
Ta yi murmushin da take yi idan zata yi maganar da take nufi har zuciyarta.
Ta ce "Bana magana biyu kin sa ni. Sai dai dole ki jira lokaci. Aure, haihuwa da mutuwa duk saurin mai sauri sai ya jira lokacinsu, idan kuma lokacin ya yi zasu zo ne tamkar habo ko da baka shirya ba. Kika sa ni ma ko ni ba ni da rabon auren a nan duniyar!
✍️
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://chat.whatsapp.com/KK6YX9u8tej7fpnQUEtvGS?mode=ac_t
*Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.
*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*
15
*Contact me 08032773332 what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*
*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.
*Littafi na d'aya ya kammala*
*Masu son cigaban labarin ku biya kudin karatu a kai ku paida group zamu fara kashi na biyu gobe litinin idan Ubangiji ya so*.
*Idan mun fara kuma babu fashi daga ranakun litinin Har juma'a za'a dinga samun update*
*Babu posting a ranakun asabar da lahadi*.
*Ina mik'a Godiya ga wadanda suka siya littafin nan mussaman wadanda suka fara biya tun kafin na fara sakin shafukan kyauta.*
*Na gode sosai Allah ya bar kauna, ya saka muku da alheri*.
*A madadin Ummiel foods*
*Ina tallata muku kulikuli tamkar kilishi*
*Ba ordinary kulikuli bane.*
*Classic kulikuli da ba'a yaro mai k'iwa, ina wadanda aka Hana iyayensu cun nama kuna suke fama da kwadayin?*
*Maza ku garzaya ku siya musu wannan kulikulin da Idan ana cinsa tamkar kilishi ne*.
*An yi Shi cikin tsabta da ta samu nasarar tantanceqa data Nafdac*.
*Ana siyan daya ana bada sari*.
*Akwai a Abuja*
*Akwai a Kano*
*Akwia a Lagos*
*Sannan nation wide delivery ne*.
*Ana samunsa a wasu daga branches din Rufaida Drinks na cikin birnin Kano*.
*Don saka order a tuntubi Ummiel foods a 08036355535*.
"Gabadaya sai nake ganin tamkar kwanakina sun kusa karewa, kawai Baba babba nake ji, if not Indai zan gama lafiya, ai ba ni da wani zullumi domin mutuwa tilas ne komin dadewar da zaka yi a doron kasa kuwa".
Hawaye ya kece mini, na kasa furta kalma ko guda
Bata yi yunkurin hana ni ba, sai dana daina dan kaina sannan ta numfasa ta kaurara murya ta ce "this will be the last time da zan zo gidanki, ki tisa ni gaba kina