Author : Hadiza D Auta Category : Romance
su haka ne?
Nima na zuba mata nawa idanuwan na ce "satowa na yi Abida" Na bata amsa a kufule domin na gaji da abubuwan da take yi mini, tunda aka ce sunana aka sawa jinjira. Bayan haka kuma, na fara ƙosawa da yadda take yawan haiƙe mini tamkar dai itace gaba da ni.
Ta jijjga kai ta ce "Na rantse zaki san kin mini gatse. Ai na riga na gane shima sonki yake yi, duk hirar da kuka yi rannan da daddare idona biyu bakam na yi, duk ɓare ɓaren da kika yi na girki, da yadda ya kaikaice yake faɗin abokinsa na sonki duk na ji, kin sani, nima na sani ba wanda ya aiko shi, kansa yake ƙwanƙwasawa ƙofa. Na rantse gari na wayewa zaku ga tsiya sai na tsarawa matarsa komai na ga yadda za'a yi ta cigaba da yarda da ke, shima kuma na ga ƙarshen juya mini baya. Muna komawa gida kuwa zan siyarwa Baba ƙarami da yaya Faruku wannan labarin domin shine shafin farko kuma mafi tsada a jaridata."
Jikina ya yi sanyi sosai. A raunane na ce "Kada ki yi mini haka Abida! Kin ga haka matar yaya Faruku ta tsane ni, ki taimake ni, mu bar garin nan lafiya, ina kuma roƙon ki kada ki saka baba ƙarami a maganar nan kinsan dai yarda zai yi, alhalin kuma na turawa baba babba wanda nake so."
Ta ja tsaki mai tsananin gaske ta yi kwanciyarta bayan ta juya mini baya. Hakan da ta yi mini tabbacin ne na ba zata sake yin magana ba, domin haka ka'idarta take matuƙar ta kwanta ta juya baya to ta gama.
Kan dole na kwanta nima. Amma na shafe awanni barci bai sure ni ba.
Washegari na dinga yi mata shisshigi da azarbabin ta kula ni, ita kuma tana yauki gami da cin magani tare da muzuran yau ƙwai zai fashe. Idan ta ce zata fasa ƙwai din nan sai na ji cikina ya yamutse.
Kai Abida ta mini iyashege iyaka. Ban da rashin wayona ai da na barta ta fasa ƙwan tunda dai da ɗan uwanta zai tashi, kuma ma ai bata da garantin son nawa yake yi. Amma gabaɗaya ta kiɗima ni. Ta firgita ni, ganin na matsu ta huce ya sanya ta ce sai dai na sayi gatsen da na yi mata.
Jiki na rawa na zaro dubu biyu na ajiye a gabanta. Ta dauka tana juya su.
Tsawon lokaci ina dakon mai zata ce, sai da gama ja mini rai sannan ta ce "saura wata dubun dan ba zai yiwu na sarayar da wannan labarin cin amanar a dubu biyu ba. Ki dinga soyayya da mijinta a cikin gidanta ita kuma ta dauki dukkan yarda ta zuba miki. Komai Bilki, Bilki dai, gara na taimake ta na faɗa mata yadda kuke son nukurkusa ta da baƙin ciki."
Ban ce komai ba, na sake zaro dari biyar biyu na ajiye mata. Ta haɗesu waje guda ta buɗe tsakiyar Mujallarta ta zubasu.
A tsume ta ce "Shike nan ba zan faɗa mata ba. Amma ki tabbatar idan kika janye biyayyar da kike yi mini zan faɗa ne kawai, ki cigaba da kawo mini abincina d'aki."
Dad'i ya ratsa ni na ce "To Abida ƙanwar Bilki na gode!
Daidai lokacin yaya Munirah ta fito daga banɗaki da yake cikin ɗakin.
Ta ja tsaki ta ce "Bilki ki rabu ita da mana sai wahalar da ke take ta yi, komai zata yi, ki barta ta yi ɗin ai dai ba za'a kashe ki ba, sai gana miki azaba take yi ke kuma kina ta bin kanta."
Da azama na ce "a a yaya Munirah ai mun ma saito ta."
Yayin da Abida ta ja tsaki ta ce "To ta zuga ki kwabarki ta yi ruwa.".
Bojuwa herbs*
*Na ce kin taba shan sanyin flusher Dinmu?*
*Ko kinsan takanas ake kawo mini saiwowin da suke dagargaza dukkan sharrin sanyin da yake yiwa mara har ma da jijiya?*
*Ko kinsan sanyi flusher na kan gaba wajen garantin aikinsa a dukkan kayan da nake siyarwa?*
*Muna dafa ciccibin da yake ciki da mace, yake kyautata matuncin mace komin tsufanta*
*Kazalika muna sayar da saiwowin dahuwar idan ke kike so ki dafa da kanki*
*Muna dafa kazar sababi gangariya,mai saukar da niima da kuma hade mace*
*Akwia kuma saiwowin dahuwar idan zaki dafa da kanki*.
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida maijego*
*Bazawara package*
*Man ayun Chad da Marwa Wanda Babu algus, zumar silki kola*
*Hakkkn daka emergency na mussaman*
*Tightening set*
*Kudai ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin aminci da rahusa, bana siyar da abin da bashi da inganci*
*A Dade ana yi sai gaskiya*
*08032773332 what'sapp only*
✍️
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.
*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*
10
*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items*
*Egyptian abayas*
*Egyptian nighties*.
*Bags and jewelries*
*Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria*
*Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*.
# +201121544627
# +2349162662750
Ni dai na kame bakina dan nasan tana iya cewa ta fasa siyar mini da rikicin.
Dan haka kaffa kaffa na dinga yi da ita har muka fara shirin barin garin.
Ranar da zamu tafi Hafcy kuka har da bubburwar zata bini.
Su Khadijah ma duk sun yi lamo domin mun saba da su matuƙa gaya, direbansa ne ya tukomu a motarsa. Muka dawo gida lafiya dauke da tsaraba da kayayyaki masu yawa.
Murnar da iyayenmu suka yi da hidimar da yaya Asad ya yi damu ba kaɗan ba ce. Kwanaki biyu Baba Babba a cikin murna da kuzari yake yi. Motsi kaɗan zai ce "In sha Allah ko bama raye Abubakar zai jagoranci kula da dukkan alhalinmu . Barin idan Abida na rattaɓa masa irin kuttu da ta shaƙa a gidansa a dalilin fifita ni da yake a kansa. Sai ya sassauta murya ya ce "Hakan na sake alamtar da ni halin girma ne da shi, sannan zai cigaba da zama babba a tsakaninku muddin rai, ai itace ƙanwarsa ta tashin ƙiyama, kema yi maza ki ƙwace Sulaiman".
Ta kyaɓe baki haɗi da buɗe ƙofofin hancinta ta ce"Hmm Baba ke nan! Akwai something behind his caring to her! Definetly akwai wani abu a mind ɗinsa abun ya yi yawa. Bayan haka ni Yaya Sulaiman ina ruwana da shi bare yanzu da baya k'asar."
Jikina ya ɗauki tsuma tare da hirji.
Domin na tabbatar baba babba zai so ace wani cikin ƴaƴansa ya auri wata a cikinmu dan sake cure zuri'a ta zama dunkullaliya.
Sai dai ni kam ba qdai a kaina ba. Shiyasa na toshe dukkan ƙofar da za'a mini auren zumunci.
Tunda har yaya Faruku bai furta so ko wani yin motsi mai ƙarfi akan akan soyayyata da shi ba, ai kuwa sai dai a yi a bar ni, babu wanda zan so, in ba shi ba a cikinsu.
A kai a kai Sahal yake zuwa zance. Duk ranar da zai zo bana cikin sukuni, girki kwalliya duk na musamman ne. Abida kuwa bata sake cewa komai akan lamarinsa ba. Da gaske ta runtse idanuwanta daga lamarinmu. Sai dai akai akai take yi mini habaicin na ƙi ƴan-uwana ko karar zumunci ban iya ba.
Ranar da ƴan kirkin suke kusa ta leƙa su gaisa, ranar da take a botsare ko tunkararta bana yi. Yaya Munirah dai duk sadda ya zo sai ta je sun zanta akan shirye shiryensu na tafiya call to bar a jihar Kano.
Wata ranar juma'a da yamma muna tare da Sahal na ci kwalliya ta burge wa. Sai jifan juna muke yi da wani irin murmushi da yake fitowa daga ƙasan zuciya. Ina samun nutsuwar zuciya idan ina tare da shi. Ina jin farin ciki mai daɗin gaske. Domin tunda ga ƙasa zuciyar nake jin farin ciki da zumudi.
Muna haka yaya Faruku ya shigo harabar gidan.
Kai tsaye ya iso inda muke ya mikawa Sahal hannu suka gaisa. Cikin barkwanci ya ce "Dama na matsu na ganka na ga mai ka taka ne daga zuwanka ka rushe gwamnatina a wajen Bilkisu tashi guda?".
Kunya ta kama shi ya ce "Yayanmu ba rushe ka na yi ba, girma ka ci ka matsa mini kaɗan".
Yaya Faruku ya faɗaɗa murmushinsa ya ce " Tunda kasan ba ƙarfina kafi ba shike nan, na zama surukinka, ka riƙe mini ita amana domin ita ɗin mai haƙuri ce kuma mai nutsuwa ce."
Cikin kunya Sahal ya ce "Da ikon Allah zan rike ta da kyautatawa".
Daga haka ya kalle ni, Ni kuma cikin nauyi na ce "Yaya Faruku barka da yini."
Ya amsa yana faɗin ai na ɗauka kin zama kurma". Ya wuce cikin gida.
Ya numfasa ya ce "Yaya Faruku mutumin kirki ne Bilkisu".
Na ce "Sosai fa"
Muka cigaba da hira cikin shauki domin ban ƙi mu tabbata muna hira cikin wannan yanayin mai dadi da walwala ba.
A wannan dogon hutun mun sake shaƙuwa domin tsallaken kwana ɗaya kacal yake yi. Wani zubin ma kullum ne sai ya zo ko tsoron titi ba ya yi.
Ranar wata Laraba da ba na mantawa da yammaci lis muna hirarmu a inda muka saba zama wato harabar gate dinmu daga gefe, domin mu a gidanmu ba'a yarda da hirar falo. Sai dai a filin Allah ƙarkashin bishiyoyi da furannai.
Ba zato yaya Asad ya bayyana shi kaɗai babu ƴan rakiya daga dukkan alamu a jirgi ya iso Kaduna. Sai kuma ya iso Funtua tunda haka yake yi matukar zai zo ganin gida.
Ya hango ni, ya dunfaromu cikin saurinsa domin shi mutum ne mai hanzari ga shi ƙarfaffa na gaske. Zuciyata ta buga, bansan me ya sanya nake matuƙar nutsuwa idan na ganshi ba, hakanan a duk sadda idanuwana suka hango shi ko da ban ji kalaman bakinsa ba sai zuciyata ta harba da tsananin gaske. Na kan rasa wannan kasafi sai dai na fi tunanin tsoronsa da ya gina a zuciyata tun ina mitsitsiyata. Duk da a yanzu kirki yake yi mini tare da tarairayata fiye da ƴar ɗakinsa sarkin rikici Abida.
Yana isowa na mike tsaye murya a dashe na ce "Baban Bilkisu sannu da zuwa. Ya su Nana da Anti?"
Maimakon ya amsa da baki sai ya cire hularsa tare da ƙamewa ya kuma sara mini tamkar dai yadda ya taɓa yi mana ni da Baba babba shekarun baya.
Daɗi ya ratsa ni har zuciyata domin gaisuwa ce mai ƙololuwar daraja bare kuma ace mai ɗamara ne ya yiwa farar hula irina da ba ni da wani muƙamin komai sai dan girmamawa kawai.
Murmushi ya subuce mini, na ce "Baban Bilkisu na gode da karamcinka".
Ya taya ni murmushi fararen haƙoransa suka haska baƙar fuskarsa.
Ya ce "So nake Bilki ta manta batun duniyar yaya Asad ta yi ta ganinsa a cikin mutanen da suke sonta tare da kambaba dukkan lamarinta."
Na ƙayalkyale da dariya na ce "Ai tunda ka mini takwara na yafe maka, na manta komai na gane na sha gaban Abida. Amma fa ni gaskiya har gobe yaya Faruku ne best"
Ya yi waiwaye ya ce "Idan autar momi ta ji wannan maganar ai kin kunyata ni Maigado".
Na sake yin dariya na ce "Ai gaskiya na furta".
Daidai lokacin Sahla ya gaishe shi cikin nutsuwa domin ya lura ma tamkar bai lura da shi ba, ko kuma mun manta da shi gaba-daya.
Ya amsa gaisuwar babu yabo babu fallasa sai dai ko kadan babu raha ko karramawa. Ya wuce cikin gida ya barmu.
Hirar da bata yiwu ba ke nan. Domin mintina biyar ya ƙara ya mike tare da faɗin "Zan wuce ina son na isa Zaria da wuri. Baba ya ce zan raka shi dubiya bayan maghriba".
Ban kawo komai a raina ba na ce "To"
Muka yi sallama ya tafi a sanyaye.
Na shiga falon Momi na tarar da shi tare da su Baba suna taya shi rarrashin Abida domin tunda ta gaishe shi bata sake kula shi ba, duk yadda take tatsarsa a dalilin bai mata takwara ba, sai ni ya yiwa, bai sa ta huce da shi ba har lokacin.
Na zauna na ce "Wato Allah ya so ni da ba zamu yi kishi ba Abida."
Ta galla mini harara tare da ce wa "Yo ai ke tsare mini gaban da kika yi ko kishiya sai haka. Kowa Bilkisu, kowa Maigado, duk wanda suke jama'atane a da kin kwace mini su a yanzu. Abin kaicon kuma naki mutanen kin riƙe su gam tsabar haɗama."
Gaba-daya aka kwashe da dariya, yayin da ta gintse tata dariyar da take neman ƙwace mata.
Baba ya ce "Abida ƙanwar Bilki kina sanya ni nishadi, idan kuna makaranta sai na ta jina tamkar wanda ya rasa wani abu. Domin kullum kuna ɗebe mini kewa na yi ta tuno da ƙuruciyarku."
Yaya Asad ya ce "Yaran nan kun samu duniya, Allah yasa lahirarku ta zarce hakan."
Wannan karon Abida ce ta yi dariya tare da ce wa "Kai Yaya!
Ya murmusa ya ce "To me zan ce? Gaba-daya kun tattare soyayyar ya'yan fari da ya'yan karshe ku kaɗai. Fatan Allah yasa kuna ibada tuƙuru yadda lahirarku ma zata yi muku daɗi fiye da nan"
Ya nisa ya ce "Wai ina Muni ban ji ɗuriyarta ba".
Baba ya ce "jiya ta je Katsina yayarsu bata jin daɗi shine ta je ta ɗan kula mata da yara kafin tafiyarsu Kano ta taso".
A ladabce ya ce "Allah ya bata lafiya, amma mun yi waya bata faɗa mini bata da lafiya ba".
Baba ya ce "ka manta zurfin cikinta ne? Kasan kuma ce wa zata yi, kana nesa ba zata tayar maka da hankali ba tunda ba kashirban take ba '".
Bamu tashi ba sai da aka fara kiran sallar magarib. Ni da Abida muka yi sashinmu dan bawa baba babba damar ganawa da baban Bilkisu sosai. Tunda ya mini takwara na koma ce kishi hakan a gabansa ko ba'a gabansa ba. Na kuma fahimci yana son sunan domin da karsaahi haɗi da kazangi yake amsawa.
Daren ranar shiru Sahal bai ƙira ni ba, tunda tara da rabi ta yi na shiga tunanin ko lafiya domin da zarar tara ta yi idan muka fara waya muna kaiwa goman dare ko fiye da haka tamkar da akan iska muke magana ba kuɗi ba.
Da goma ta yi sai na kasa haƙuri na buga masa, amma har ta katse bai ɗauka ba, kuma bai katse dan ya biyo baya ba. Ban shiga mamaki ba sai da aka shafe mintina talatin bai bugo ya gabatar da uzzirin baya kusa ko yana tare da iyayensa ba. Gabadaya na daburce, na sake ƙira a karo na uku sai na ji an kashe wayar ma bakiɗaya. Da yake fashin sallah nake yi, sai na takure a kan gado gaba daya na rasa jin daɗin zuciyata. Yayin da tuni Abida ta yi barcinta cikin nutsuwa. Idan akwai abin da yake burge ni da Abida to rashin sanyawa kai damuwar duniya ne. Samsam bata yarda ta yi sabo da abin da zai dame ta. Kusan kullum sai ta ce mini soyayya lalura ce kabiran. Kafin ta yi barci ma da ta lura da yanayina sai da ta ja tsaki ta ce "Ya miki sabo da kalaman da kaso saba'in cikin ɗari na daɗin baki ne ba na gaskiya ba. Da zarar an haɗaku zaman aure hirar mintina goma ma sai an wayi gari ba zai iya ware wa cikin lokacinsa ya yi da ke ba, a yanzu kuma ya yi miki sabo da doguwar hirar da idan baki ji daga gare shi ba zaki kidime ki kasa sukuni. Me za'a yi da soyayya irin taki ne Bilki?"
Da nasan gaskiya ta faɗa sai na kasa amsa mata domin ba ni da bakin yi mata musu ko raddi dan idan ta kaikaice ta fara cashe mini sai ta sanya ni kuka na gaske. Sannan zata juya ta yi kwanciyarta, cikin nutsuwa zan ga tana sauke numfashi tabbacin barci mai cike da nutsuwa take yi.
Da ƙyar na yi barci ina ta saƙesaƙe ko jinya ce ta kwantar da shi tunda a kullum sai ya ce mini ba zai iya barci bai ji muryata ba. Shiyasa ma baya ƙirana sai ya yi sallar Isha domin da zarar mun gama waya barci yake yi muryatace abu na ƙarshe da yake ji a ko wanne dare.
Ina idar da sallar asuba na sake ƙiran layinsa amma shiru kake ji a kashe take.
Na shiga damuwa duk yadda nake son komawa barci ranar ban samu sukunin komawa ba.
Sai da muka karya muka yi sashen Momi hannuna ɗauke da ledar alawa da biskit masu tsada cikin wanda Sahal yake kawo mini na ɗiba na zuba a leda da yawa da mufin na bawa baban Bilkisu ya kaiwa Hafcy. Muka tarar shi kadai yana karyawa kuma ya yi haramar komawa. Muka gaishe shi ya amsa tare da faɗin "Na shiga gaida Mami da Baba ƙarami baku tashi ba".
Abida ce ta amsa da ce wa "ki ce ban tashi ba kawai, amma ita bakam ta yi bata cikin hayyacinta saurayinta ya yi mata fushi tun daren jiya ta rasa walwala da kuzari ".
Ga mamakina sai na ga ya ɓata rai, bacin ran da ya bayyana har a fuskarsa. Da farko tamkar zai share sai kuma ya kasa