Author : Hadiza D Auta Category : Romance
alherin da zaki tabbata kina sona. Fatan alheri mai yawa! Sai kuma kuka ya sake kwace mata.
Ina kuka sosai Yaya Faruk ya fita da ni. Domin bayan ii rabuwata da gida ba karamin raunana zuciyata ta yi da soyayyata da na gani a tare da Abida ba.
A motar baba babba C.R.V. muka tafi. Yaya Faruk ne mai tuki sai Baba babba da baba karami. Duk yadda su baba suka so Yaya Asad ya shigo a tafi da shi tunda ya riga ya dauki girma yana hurar da su dawainiya ya sanya suma suke jagorantar da shi akan sha'aninmu. Kansa a kasa ya ce "Allah ya kaiku lafiya Baba. Ga Faruku nan duk daya ne. Ya leko ya ce "Ki zama mai hakuri, ki sake ninka hakurinki. All the best maigado!
Daga haka ya matsa gefe. Cikin nutsuwa Yaya Faruk ya ja motar muka tafi.
Gidan Baba. Zaria aka kai ni. Baba babba ya rike hannuna ya damkawa wan mahaifin Sahal kuma waliyinsa amanata. Shi kuwa ya saka hannu ya rike hannuna gamgam.
Yana fadin "na karbi amaana in sha Allah y'arku tana amintaccen hannu."
Tarba ta karrmawa ya yi mana, iyalinsa kuma suka baibauemu da abinci da na sha, duk ni kaina kasa yake kuma a kunshe cikin mayafi . Basu wani jima ba suka tafi suka bar ni a gidan Baban Zaria. Zuciyata sai tsallen bad'ake take yi, yanzu shike nan na bar gidanmu gabadaya sai dai na je da bakunta? Iyayena da kansu suka dauko ni suka kawo ni wani gidan da nufin na zama cikin ahalinsu muddin rai. A raina na dinga jin lallai al'amarin aure ba karami bane a addini da rayuwa ba.
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.
*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*
*Lafazi writer's*
13
Message Amreesh spices & more on WhatsApp. https://wa.me/message/Y7KSRJ7PDQSCC1
*Fatan alheri ga*
*Haj Dr Safiya Saulawa*
*Haj Zahra Shehu*.
Sai da aka yi sallar isha sannan Baban zaria da matarsa da ake kira da Mama suka kai ni gidana da babu nisa tsakaninmu da su. Unguwar kusa ne kwarai da jamiaar.
A gidan muka tarar da shi tare da amininsa Lawal.
Addua sosai Baba ya yi mana tare da jaddawa Sahal girman hakkina da yake kansa.
Haka nima ya ta nanata mini na kulla abota da hakuri da kuma juriya, sanna na gane biyayyar da aka kallafa mini na yi masa umarnine daga Ubangiji. Dan haka duk abin da zan yi masa na hidima na yi min Allah dan kuwa shi ya shirya tsarin aure da kansa. Mama ta shigar da ni cikin dakina ta zaunar da ni akan gadona tana ta yi mini fatan Ubangiji yasa na zama tsohuwar gidan.
Basu wani jima ba suka tafi suka bar ni a sabon gidana da zan fara sabuwar rayuwa a cikinsa.
Jin ana kiran sallar magahariba ya sanya suka tafi, su Sahal suka rakasu wajen mota suna ta godiya da ban gajiya gasu Baba, sai da motarsu ta bace musu. Basu shigo ciki ba suka wuce masallaci dan sauke farali.
Bayan an idar suka shigo da ledoji da alamu sun siya tun dazu a mota suka barsu.
A guggurje ya yi barkwancinsa tare da ajiye mini bandir din yan 200 wai kudin siyen baki.
Ya yi mini sallama ya wuce, dan hanyar Katsina zai kama a daren nan.
Da kazangi ya dawo ya zauna daf da ni ya rungume ni yana shakar kamshina. Gabadaya na takura, bansan meyasa ban ji tsumin da na ji a lokacin da Yaya Faruk ya rungume ni ba a yanzu.
Tabbas jikina ya shiga bakon yanayi da bai saba ba, ban sani ba ko tsananin alhinin rabuwa da ahalina tare da fargabar yadda zan shiga cikin sabon ahali ne oho.
Cikin nutsuwa ya ware mayafin da na lulluba da shi. Ya mikar da ni ya ce "Zo mu je falo mu ci abinci. "
Tsire ne mai kyau sai yogurt da kuma ruwan roba masu sanyi.
Duk yadda nake jin yunwa ban iya cin naman ba, sai yogurt din na sha, shima ba wani mai yawa ba.
Bai wani sake ba, sai da ya dawo daga sallar isha.
Ya sake janmu sallar nafila ya yi mana adduar zaman lafiya da albarkar rayuwaa.
Da rawar Jiki ya mannu da ni ya ce "Yau ranace ta mussaman a tarihin rayuwarmu gabadaya. Ina fatan Ubangiji ya sanya albarka a dukkan zaman da zamu yi."
Murya babu amo na ce ",ameen".
Duk yadda nake jin bakunta ta kewaye ni sai da ya hilace ni ya dangana ni da lafiyayyen gadonmu da ya sha shimfida ta alfarma.
Cikin gaggawa yake yin komai, gabadaya ya dinga sarrafa ni, ya jima yana shafata tare da kissing dina. Bai samu nutsuwa ba sai da ya tabbatar ya isa inda ya dade yana fatan ya isa. Bai wani jima ainun ba. Yayin da ni ban wani gane komai ba sai radadi.
Na kalle shi yana ta numfarfashi, daga haka barci ya yi awon gaba da shi. Na jima ina ta sake saken zuci ban kuma isa na hakaito mai nake sake sake a akansa ba.
Na duba wayata na ga shadayan dare. Na mike na shiga bayi dan yin wanka. Domin Mami ta ce mini kada na bari na dinga barci da janaba in ba dole ko lalura ba.
Na gasa kaina sannan na yi wanka. Har na kammala na shirya bai motsa ba. Na lallaba na kwanta a gefensa.
A haka nima barci ya yi awon gaba da ni.
Bamu makara sallar asuba ba, sai dai da muka koma din sai wajen goma muka farka a dalilin dukkanmu mun tara gajiya, na fito daga wanka ina shiryawa cikin nutsuwa, shi kuma yana daga kwance yana kallona cikin murmushi.
Daidai lokacin kuma ya fita ya karbo abin karin kumallo da aka aiko mana daga gidansu.
Funkaso ne da kunun gyada. An zuba cikin kyawawan kwanuka.
Kaitsaye dakin ya shigo da kwandon. Ya zuba mini ido ina sanye cikin guda daga cikin kyawawan material din Malaysia, mai kalar siminti da yarfin kwanduwar kwai.
*Contact umm Nihla for all your *Malaysian fabrics.
*Malaysian Batik and more*
*All are unique and classy*
*Available wholesale and retail*
.......
Ya ce "Billy kin kara kyau sosai
Na murmusa cikin kunya na ce "Na gode ".
Ya wuce bayi yana ce wa "bari nima na yi wanka kada tazarar da kika yi mini a kyau ya sake tsananta."
Na murmusa ba tare da na ce kanzil ba.
Bai wani jima ba,¹0 pop-up ya fito daure da tawul na yi maza na dauke kaina. Bai ce komai ba ya fice zuwa daya dakin da yake a matsayin nasa.
Na hanzarta canja zanin gadon da duk ya baci da jinin budurci na canja wani. Na shiga bandaki na kama duk inda ya baci na wanke, na yarfe sannan na ninke na baza shi akan kyauren bandakin.
Ya shigo sanye cikin yadi mai taushi shudi kalar sararin Subhana(sky blue).
Sosai ya yi kyau zuciyata ta doka da tsananin gaske, take raunin da soyayyarsa ta yi a dalilin Yaya Faruk ya kau, mai kyaune irin wanda nake so duk da dai siriri ne irin sosai din nan, na tabbatar sirintarsa tana karawa tsayinsa kaimi. Sabuwar soyayyarsa ta sake yun mmkuro mini tana sake bin dukkan sassan jikina tana mamaya da k'arfin gaske.
Idona ya kada kwallar shauki ta cikasu taf.
Da hanzari ya iso inda nake. Ya ce "sannu da aikin lada Bily. Allah ya yi miki albarka! Mu je mu karya yunwa nake ji sosai."
Gabadayanmu kamshi muke yi. A plate daya ya zuba mana abincin. Ya turo mini kofin shayi gabana tare da ce wa "zuba sugar da su madara yadda zasu yi miki".
Ban ce komai ba, domin kaina a kasa yake, kunya da bakunta ke dawainiya da ni gabadaya.
Cikin nutsuwa da walwala muka karya duk da ni kunya ta yi mini dabaibayi.
Bai fita ba sai da aka yi sallar azahar. Ya yi tafi masallaci ya ce zai shige gida ya gaidasu Baba.
Na idar da tawa sallar. Na dauko wayata da take kashe tun daren jiya.
Na kunna, na jinkirta ta daidiata.
Mami na fara kira, ta amsa da walwalar da take alamta mini ta yi kewata sosai.
Har na ji dadin yadda ta mu'amalance ni. Ta dinga fadin nasan kina da hakuri da shanye damuwa, ki yi kokarin ninka hakurinki Bilki, hakurin nan dai shine aure, shine ma rayuwa gabadaya. Murya babu amo na ce "To Mami na gode Allah ya kara miki lafiya da hakuri. Ta amsa da fadin "ameen, amma ai ni bana hakurin da zan cutu, a sha'anin aure ne kawai nake dukkan hakuri domin zawarci bashi da dadi Bilkisu!
Ko a gaban uwarka da ubanka zaka yi shi kuwa bare ni marainiya ce, tun ba'a aurar da ni ba na rasa uwarta, mahaifina kuwa ban yi haihuwar fari ba na rasa shi. Ga shi ni din an jarrabe da wata irin nannauyar jarabawa.mai matukar nauyi. Y'anuwana suna cikin magautana."
Na nisa na ce "Mami sunnar rayuwace ai, ba ke kadai bace kike da k'alubale da y'anuwanki ba, mutane da yawa ne, kawai ke dan kina yawan furzarwar ne, ba kya iya barin al'amarinsu a ranki ko dan a samu saukin gaba da b'acin rai. Manyan bayin Allah sun fuskanci kiyayya a wajen danginsu, haka Annabawan Allah. Idan kuma Allah ya rufa maka asiri Mami ba wani mahalukin da zai tona maka. Sai dai ya tonawa kansa.
Na numfasa na ce "Allah ya jiqan magabatanki, Allah ya saukaka miki dukkan kasafinki Mami ".
Ta amsa da"ameen ameen a sanyaye."
Karon farko da na yi mata jirwayen hakuri akan shaaninta da danginta bai zame mini sanadin bacin rai ba.
Na kashe wayar na kira su baba daya bayan daya.
Su kam dukkansu albarka da addua suke yi mini. Suna sake jaddada mini basa jin dar a kaina ba zan kunyatasu ba.
Abida na kira daga karshe, muka sha hira, tana ta tsokana tana cewa "Na ajiye mata kazar amarci a fridge tunda satin sama zata dawo makaranta.
Cikin nutsuwa da tattali muke rayuwarmu. Babu damuwar komai, sai dai ni duk yadda Ake fadin ango na gajiyar da amarya ta hanyar kusantarta a kai kai da sunan doki ban ga hakan ba.
Don kuwa ina amarya ma ba wani sosai ba, sai mu debi kwanaki bai yi ba, illah iyaka idan zamu kwanta zai rungume ni mu yi barcinmu. Hakanan da rana yana dan rungamata da sumba idan zai fita ko idan ya dawo shima ba wai dole ba.
Tuni muka koma makaranta.
Abida ga dawo tana hostel, duk yadda na so ta dawo mu zauna a gidana ki ta yi tare da gabatar mini da hujjar ba zata taba munafuntar iyayenmu ba . Don kuwa ba zasu yadda ta dawo ta tare mini a gida ba. Dan haka ba zata yi kuma a boye ba.
Ko weekend Ina son ta dinga yi mini amma yar ra'ayin rukau din bata gamsu ba. Asalima sau biyu tak ta zo mini gidan.
Duk da na shafe watanni da auren.
Zuwa lokacin kuma na riga na gane Sahal na cikin jerin maza da basu damu da harkar auratayya sosai ba.
Sai dai kuma yana kokarin ya ga ya gamsar da ni idan har an hadun.
Watanni biyar da aure ya samu aiki da Nigerian airways na lokacin. Sun dauke shi cikin jerin lauyoyin da zasu yiwa kanfanin aiki.
Dan haka ya wadata ni da komai na more rayuwa tun daga kan abinci har tufafi duk da yana ganin na lefe da yawa ban waiwaiyesu ba.
Duk satin duniya zai bar Kano ya taho Zaria.
Ranar jumaa da yamma zai zo sai ya yi sammako ya tafi litinin da asuba.
Duk wannan jelen da yake yi, sau daya tak zai neme ni, ma'ana idan ya zo jumaar nan aka hadu to fa sai wata jumaar. A kasan raina ina son ace had'uwar tafi hakan yawa ko da sau biyu ne sai dai kunya da nauyi sun hana ni magantuwa ko nuna wata alamar ina bukatarsa sama da yadda yake.
Mamakin da nake yi, idan har yana gida to kuwaa kusa da ni daf yake zama koma nace a jikin juna, haka idan ina kicin ina aiki to yana gefe yana taya ni tare kuma da kai hannunsa duk inda yake son tabawa baya damuwa ko ya zama sanadin da zai ja ni dakin, yayin da ni kuma nake tsintar kaina na jike jagab.
Sadda muka kammala aji biyu zamu shiga na uku muka koma Kano da zama, baban Zaria ya yi cukun cukun da na koma jamiar Bayero na shiga aji ukun na cigaba da karatuna a can.
Na yi kewar Abida sosai. Duk ba wani zuwa gidana take yi ba. Amma kullum sai na yi mana girki na tafi mana da shi makaranta.
Ban wani sha wahala a B.U.K ba saboda Basma Maska anan take, k'awancenmu ya sake zama sabo mai cike da aminci da nutsuwa.
A lokacin kuma ina a dauke da ciki na watanni biyar.
Ban nemi komai na rasa ba, komai daidai gwargwadon iyawarsa yana yi mini. Haka na yi goyon ciki, cikin kulawa da tarairaiya don kuwa duk abin da nuna sha'awarsa ya dinga siyowa har sai ya gundure ni.
Cikin marka markan ruwa irin na watan Augusta na haifo kyakkyawar yarinya mai kama da Babanta sak. Murna kamar me domin ina son abu maikyau a rayuwata.
Daga shi har danginsa sun nuna mana gata da kulawa domin kaya har rasa inda zan ajiye su na yi.
Haka nawa dangin suka dinga zarya tsakanin Funtua zuwa Kano.
An kawo mini yayar Mami da suke 'yay'an mata zar wacce jininsu ya jitu. Zata zauna da ni idan an yi suna sai mu koma Funtua tare tunda na yi sa'a cikin hutu haihuwar ta zo.
Ya dade da fada mini idan mace na haifa to sunan maman Zaria(Hajiya Rabi) zai saka domin kuwa ta yi masa alakairai daban daban da ba kowacce mace zata yiwa d'an k'anin mijinta haka ba.
Dan haka tuni an yiwa yarinya huduba da Rabi'a
Na lank'aya mata Amrah wanda Abida ce ta zabo inkiyar.
Ranar da ta zo ganin baby ta kula da yadda nake yawan kallon jinjirar ga shi ko ya ya ta yi kuka zan mika hannu na karbe ta.
Tana ganin inna ta shiga bayi ta ce "Wato Maigado kina da zurfafa soyayya. Soyayyar Babanta ce ta shafe ta kike kasa kawaici, ko kuwa kina cikin iyaye masu tsananta soyayyar 'ya'yansu ta yadda basa iya boyewa a gaban kowa?"
Na yi k'asa da kaina domin kuwa na sani Abida ta na fahimtata tamkar yadda ta fahimci kanta.
Ta numfasa ta ce "ki sassauta, ki danne, na sani dole ki so ta, amma dinga yin kawaici a gaban manya, sannan fa ki sani wannan ba taki ba ce tawa ce, domin dai ni ce zan haifo miki ta ki"
Na murmusa na ce "Abida to yaushe za ki mayar da ni uwa tunda har yanzu k'in ki kula kowa bare ki yi aure na saka ran zaki haifo mini tawa".
Ta murmusa ta ce "lokaci ne ai Bilkisu! Idan Allah ya kawo lokacin sai ki ga an yi ko da ban so ba".
Na tabe baki tabbacin ban gamsu ba. Dan dai ban isa yin musu da ta mai yawa bane yanzun nan zata murde mini.
Tunda na yi aure bata yarda ta kwana a gidana ba sai sanadin haihuwar. Daga Zaria ta taho kai tsaye har aka yi suna tana nan. Bayan suna da kwanaki uku ya kaimu Funtua da kansa tare da uban kayayyakinmu.
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://chat.whatsapp.com/KK6YX9u8tej7fpnQUEtvGS?mode=ac_t
*Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.
*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*
14
Duk yadda Abida bata son yara, haka duk yadda bata bada fuskar da iyayen yara zasu hada ta da hidimarsu bare ta yi musu raino. Amma ta zage da dukkan k'arfinta tana rainon Amrah. Bata son goyo a rayuwarta. Amma kullum Amrah a bayanta take yini bata ko gajiya, kowa tu'ajjibi yake yi, ita kuwa fadi take yi, tunda ita aka haifawa dole ta yi rainonta dan ta ji kanta idan ta tsufa, ko kuma ta yi mata addu'a idan mutuwa ta sure ta.
Ranar da ta fada hakan jikin kowa ya yi sanyi, aka dinga fadin haba autar momi ai ba zaki mutu ba, sai kin haifawa Bilkisu tata diyar da kika bata tun shekarun baya.
Ta murmusa ba ta ce komai ba.
Na yi matukar jin dadin zaman jego a gidanmu domin bana aikin komai tsananin na yi wanka na bawa baby nono sai ko barci. Komai yi mini Ake yi tun daga kan iyayenmu har kan yayyen da kaina. Amrah ta sha gata sosai.
Yaya Faruk kullum ya shigo sai ya saka Abida ta kunto masa ita ba zai bata ba,