Dingishin Kwado Part 1 By Hadiza D Auta.docx

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   6 / 15

15K to 18K   out of 44.6K words

muzurai da razana ni, amma fir ya ki, shiyasa na taso da matsanancin tsoronsa. Bama shiri ko kadan Kamar dai yadda Yaya Sulaiman ya tisa Abida a gaba Duk da Shi ba cin zalinta yake yi ba, kushe ya yake tare da gwasaleta.

Sadda muke firamare shine yake kaimu makaranta a mota idan ya zo hutu daga makarantar horar da y'an sanda ta Wudil.

Matukar Baba babba ya ga na bace masa a gidan to Yaya Asad na gari.

Wata rana na shiga wajensu, banbsan dodon ya zo ba, sai ganinsa na yi gurfane gaban Baban yana sanye da kakin yansanda wanda a lokacin bai fi wata da fara aikin ba.

Ina ganinsa na juya zan zura a guje. Yaya Faruku ya yi maza ya ruko ni ya ce "Ke ba abin da zai yi miki."

Yayin da shi kuma ya galla mini harara tare da ce wa "Nutsu ki zauna ko na d'ora miki duniya a kanki ".

Ai kuwa jikina ya hau tsuma domin kakinsa yasa na sake tsorata da shi, hakanan ni da Abida muna matukar tsoron ya d'ora mana duniya.

Wani abu ne da shi mulmulalle mai tsananin nauyi da yake dagawa na motsa jiki, idan ya so mana mugunta sai ya ce sai mun yi kama kama mun matsar da shi gefe wanda bama iyawa ko motsa shi, a haka zamu yi ta yi har sai mun gaji sannan zai ce mu bari.

Baba ya kalle shi ya ce "Ba dan ka yi mata tsufa ba da na baka aurenta na ga yadda zaka yi, ka takura sarauniyar shaiba da yawa Asad."

Yaya Faruku ya yi fit ya ce "Haba Baba a gabana zaka bawa tsoho auren amaryata, ai Bilkisu tawa ce".

Yaya Asad ya ce "ina da shekaru ashirin da bakwai kana da ashirin da biyar menene banbancin namu da zaka jingina mini tsufa?

Ni mai zan yi da wannan y'ar tastitsiyar yarinyar da har yau da ta ke cika shekaru goma bata bar cin tasono ba".

Sanin da na yi ya hana ni cin tasono ya sanya ina rawar murya na ce "Wallahi ban ci ba, ko rannan da Abida ta ga nasa hannuna a hanci na kai baki ba tasono ba ne, amma ta ce sai ta fad'a maka ".

Gabadaya suka saka dariya ban da ni da nake ta zufar fargaba.

Domin wahalar gaske yake ba ni wajen cewa sai na d'ora duniya a kaina.

Baba babba ya ce "Ke rabu da shi kin ji.

Daga shi har Faruku duk sun yi miki tsufa".

Da sauri na ce "A a Baba Yaya Faruku ne"

Suka sake yin dariya, yayin da Yaya Faruku ya yi ihun murna tamkar ba a gaban Baba yake ba. Da alfahari ya ce "ai tuni mun saito ta da Bilki komin tsufana ita ce amaryata".

Na numfasa daga hakaito kuruciyata da ban yi nufin budewa gabad'aya ba, na kalli yadda Abida take murnar gwale Yaya Faruku da na yi, tunda har yau da muka zama y'anmata yafi jana a jikinsa fiye da ita, ko gidansa muka je yafi haba haba da ni, lamarin da yasa matarsa ta washe ni ainun tun ban fahimci inda ta dosa ba har na gane, shiyasa da na yi wayo sai na daina zuwa, domin muddin muka je hutu to fa ba shi ba zama lafiya a gidansa har sai mun bar gidan. A garin Funtua yake zaune, shine kuma yake kula da shige da ficen kudi na Ladi farms, tunda Yaya Asad ya yi nisa yana Kebbi shekaru biyu kenan ya bar Asaba. A lokacin kuma yaransa biyu duk mata.

Yayin da Yaya Faruku yake da yaro namiji.

Na tausashe murya na ce "Har gobe ni ce amaryar Yaya Faruku"

Da yake shi mai haba haba ne yafi dukkan mazan gidanmu wayayyen kai, domin idan ya shiga cikin mata sai ka rantse shima mace ne, idan biki ake yi a gidanmu kuwa cikin su Yaya Salaha yake shiga a yi rawa da shi yana musu liki, gabadaya rayuwar Yaya Faruku abin sha'awa ce, baya da damuwa, ba shi da tsanani ga shi dan gaye na sosai kuma fari irin wanda nake so. Amma Yaya Asad ga bak'i, ga shi mummuna, duk da dai Abida ta ce nice nake ganin muninsa tunda na rufe zuciyata a kansa, ni kuwa bana yarda da maganarta duk da ban tab'a tsayawa na masa kallo sau biyu ba, amma nasan dogo ne mai murdadden jiki tunda ma'abocin motsa jiki ne ainun tun tasowarsa. Tabbas sifarsa ta dace da jami'in tsaro.

Ya yi tafi ya ce "Ni nasan duk yadda ake kushe ni nasan sarauniyar shaiba tawace".

Baba ya sake murmusawa, yayin da Abida ta yi gum alamun bata da tace wa.

Tamkar jifa sai gani muka yi mai gadi na bude tangamemen get din gidan.

Moto kirar pegoeat ta shigo, sai kuma wata irin ta y'ansanda mai dauke da logon y'ansandan k'asa reshen jihar Kebbi.

Motocin na tsayawa wani ya yi saurin fitowa ya bude k'ofar Yaya Asad ya fito da alamu shine jagorar tafiyar gabad'aya.

Yana fitowa suka fito da azama.

Shi kuwa ya durfafi Baba babba kai tsaye.

Yana zuwa gabansa ya cire hular kansa ya kame tare da sarawa Baban wanda hakan shine kololuwar gaisuwar girma a gidan jami'an tsaro.

Haka tawagar y'an sanda har su takwas suka yi layi suka yi Baba kwatankwacin yadda ogansu ya yi.

Shaukin gaisuwar ta debi ni, karon farko na ji sha'awa aikin damara ta shige ni.

Domin an yi ittikafin babu inda ake girmama wanda ya wuce ka mukami irin a aikin d'amara.

Abida sarkin kankanba ta yi maza ta matsa jikin baba tana ce wa "Baba pls na shiga rigar nima a mini wannan gaisuwar dan girman Allah."

Baba ya bibbigi bayanta tare da ce wa "Ho Abida!

Su kuwa da suka koma gefe sai suka sake matsowa suka jeru, suka cire hulunan suka yi mata tata gaisuwar tamkar ita ce momi.

Dad'i ya kamata ta dinga dariya tana fad'in thank you so much ".

Yaya Faruku ya matso gabana ya yi mini yadda ya ga sun yi, ya ce "Bilkina duk da ni farar hulane karbi tawa gaisuwar."

Na yi murmushi tare da ce wa "Na karba da godiya Yaya Faruku".

Ba zato kawai Yaya Asad ya yi mini yadda ya yiwa Baba babba. Kaina ya fasu na kasa boye kaduwar da na shiga a dalilin yadda ya girmama ni. Ba tare da bata lokaci ba yaransa ma suka ƙame mini.

Karon farko da Yaya Asad ya kambaba ni. Murya ba amo na ce "Na gode sosai Yaya!

Takaici ya shake Abida. Ta ce "Bilhillazi Bilki kin shiga uku, ni dai kam bansan me yasa aka had'amu sa'anni ba, haka kawai sai gana mini azaba kike yi. Ni sai da na roka aka k'ame mini, amma ke baki roka ba, har shugaban bataliyar ma ya rusuna miki, ga Yaya Faruku farar hula, haba haba gaskiya kina k'warata!

Gabadaya wajen aka dauki dariya domin kowa yasan zata mayar da gaisuwar da aka mata wani abin alfahari ne.

Sai gashi nima an mini fiye da tata.

Daidai lokacin Yaya Sulaiman ya shigo harabar gidan a lokacin kuma yana ta shirin tafiya k'asar Germany dan yin karatun likitanci.

Duk da basa shiri ko kadan ya ce "Abida yau d'aya bari na miki alherin da kike ta fadin ba ni da shi".

Ta galla masa harara tare da ce wa "Ba an mana iyaka ni da kai ba? Na rantse sai na fadawa Baba k'arami".

Ya k'ame mata tare da sara mata ya ce A yafi Malam Sule Abidan Baba".

Ta wani dauke kai ta ce "Na karbi tubanka, ban sani ba ko ba zaka dawo ka tarar da ni ba, ko kuma kai ba zaka dawo ba".

Jikin kowa ya yi sanyi amma Yaya Sulaiman ya ce "Yauwa Abida Allah ya yafe mu gabadaya ba sauran fada in sha Allah a tsakaninmu. Sannan in sha Allah zamu tsufa kafin mu mutu".

Daga haka ya koma wajen Yaya Asad da jama'arsa yana marabtarsu.

Wannan karamcin da Yaya Asad ya yi mini ya sanya na saci kallonsa na k'are masa kallo. Tabbas ba shi da muni ko kad'an, sannan kuma ba zai shiga sahun masu kyawun fuska ba, mussaman idan da su Yaya Faruku, da kuma saurayin da na kasa mancewa da shi S.S.Mashi. Amma kuma duk ya keresu haiba da ginannen jiki.

Abida ta ce "To ga shi Allah ya kawo Yaya Asad sai ka bashi motar ya kai mu Baba".

Yaya Faruku ma ya ce "Ai kuwa dai, ga shi".

Nan da nan Baba ya canja fuska ya ce daga zuwansa ko ciki bai je ya gaisa da iyayensa ba, bare su sha ruwa sai ya hau kai ku makaranta?"

Abida da take son a kaimu a motar dan darajarta ta k'ara d'aguwa ta mairairaice ta ce "Ina Funtua ina Bakori Baba babba? Balle a wajen jami'in tsaro irin Yaya Asad ba sai ya arce da k'afafunsa ba ma, bare a mota".

Gabadaya y'ansandan suka sake yin k'asa da kansu suna dariya tare da fad'in "drama girl".

*Contact me 08032773332 what'sapp only*

*For all your kayan mata gangariya*

*Bridal package*

*Maijego package*

*Uwargida package*

*Bazawara package*

*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*

*Ciccibin garari*

*Tsumin saiwowi*

*Hakkkn daka emergency*

*Gumbar ridi*

*Gumbar saiwowi*

*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.

[8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*

*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*

*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*

# 08032773332#

# 09069067488#

*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO*

*BY*

*SURAYYA DEE*

06

*Bojuwa herbs*

*Oder your kayan mata for women of class*

*Our products are healthy and original*.

*Tested and trusted*.

*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.

*Dan Allah Ki zo mi saka order din ciccibin garari ko kazar sababi Ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.

*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*

*Just DM for your order @08033773332*.

Yaya Asad ya ce "Ni ne zan kai ku? Shekara da shekaru wa yake kai ku?"

Ni dai da ba wani sakewa da shi na yi ba, ban ce kanzil ba. Yaya Faruku ya ce "Baba ne ya ce "Ba zai ba ni motarsa na tuka ba, wacce kuma aka yi nufin kaisu a ciki ta k'i tashi.

Shine ya ce kai kad'ai zai iya bawa motarsa. Sai kuma Allah ya kawo ka babu zato ba sai ka kai su ba ".

Nan da nan ya ce hakkun ya aki Umar. To marabci wadannan da na zo da su."

Cikin girmamawa ya karbi mukkullin mota a hannun Baba babba. Shi da Yaya Faruku suka kwashe kayanmu suka dawo da shi motar da za'a yi tafiyar da ita bayan ya dakatar da tawagarsa da suka yi nufin kwashewa tare da ce wa "Wannan hidimar ta mahaifina ne dan haka ni yafi cancantar na yi da kaina".

Ni na shiga gaban motar a dalilin yadda nasan Abida owners coner ne wajen zamanta tana matukar son ta zauna a wannan gefen ana janta, ita kuma ta hakimce bayan ta sanya glass ta hau duba mujallar Tambari ta ado da kwalliya ko littafin Hausa.

Ni mamakin yadda take daukar ta d'aya nake yi. Domin yana wahalar gaske ka ga Abida ta yi karatun da ya shafi na boko, matukar zaka ganta a nutse tana karatun cikin nutsuwa to kuwa littafan Hausa ne ko mujallar ado da kwalliya ko kuma na girke girke.

Amma karatun boko a gajarce take yinsa. Daga k'arshe sai na gano tana cikin jerin dalibai da ake kira student with high I.Q. Tana da tsanin hazakar da ta kerewa dukkan y'aya' matan gidanmu. A maza kuwa da Yaya Asad da Ansar k'anina zasu fafata.

Ni kam average ce, ba ni da hazaka sai naci, nacin ma na dole ne, domin hidima iri d'aya ake yi mana, amma kullum ta kawo sakamako mafi daraja wato 1st position, ni kuma na dinga kawo babu yabo, babu fallasa. Kishin haka ya saka nake nacin karatu tare da bita har na samu nake kawo sakamako mai kyau domin bana wuce tsakanin 5-9.

A duk sadda zamu tafi a hanya sosai muke hira da Yaya Faruku ya yi ta zolayarmu tare da sakamu dariya ta hanyayoyi da dama har ya ribacemu mu manta fargabar komawa makaranta.

Amma a wannan tafiyar tsit kake ji hatta Abida da ba wani shayinsa take ji ba, baka jin bakinta, a karshe ma sai ta ciro da littafin Tsuntsu duka Tsuntsune na marigayi Malam Abubakar Imam ta hau nazarinsa, domin ta ce ba karatu take yi kawai a littafin ba, har da nazarin yadda zata samu azanci.

Mun fara nisa amma gabadaya a takure nake zaune. Wani irin abu ya mamaye ni na rashin sabo da zullumi, na dinga jin tamkar na ce ya dakata na koma baya.

Na dinga mutsu mutsun rashin sukuni.

Ya kalle ni ta madubi ya ce "Ina fatan yadda kika zama tsaleliyar budurwa no more cin tasono".

Na yi k'asa da kaina cikin jin kunya k'warai da gaske.

Abida ta yi gajeriyar dariya ta ce "Ta daina cinsa amma kasan farce take ci duk girman nan nata ".

Ya ce ",Wonderful! From Shan majina, to cin tasono, to cin farce, sannu mai sabbin update". Abida ta fashe da dariyar iyashege tare da ce wa "Bak'in ciki kamar na sume idan muna tafe tana fama cusa yatsu a baki, gabad'aya sola ya danne zahirin sunanta. Ya murmusa ya ce "Wai ke autar Momi waye babba a tsakaninku ne? Na ga fa kin rainata da yawa".

Ta ce "Ai ita ce gabad'aya wata iri ce, ba wadanda yasan wacece Bilki sai Allah sai ni".

Ya share Abida ya juyo gare ni tare da ce wa "To ki bude kunnen ki da kyau. Ba hadisi ba ne, amma maganar masu Ilimin rayuwa da hikima ne, ta yadda idan suka yi magana ko hasashe sau tari yana zama wajabat. Cin farce mafi yawa ance yana dauwamar da mai yinsa cikin kunci da talauci. Kina son daga gidan arziki ki fad'a na talauci ne?"

Na girgiza kai da sauri.

Ya ce "To ki daina cire farce da baki."

Da hanzari na ce "Tom".

Abida ta ce "Allah yasa dan ya riga ya zame mata addiction".

Yaya Asad ya ce "Zata daina mana Abida".

Yadda ya yi maganar sai na ga kamar ba azababben nan da yake kidima ni ba.

Na saci kallonsa na ga still yana nan a mai siffar k'arfi, bai yarda ya tara teb'a ba. Ko a yanzu yafi matarsa kuruciya, haka nan sai ka dauka bai yi aure ba, duk da shekarar da muke shiga sakandire ya yi auren ga shi yanzu idan mun dawo mun kammala.

Ya waiwayo ya ce "Wai ke kallon me kike ta bina da shine haka? Tun dazu nake jin kallon ki a jikina, kada ki bari fa na juya na d'ora miki duniya".

Abida ta kyalkyale da dariya mai yawa.

Yayin da na yi muk'us a dalilin babu sakewa a tsakaninmu.

Sai da ta yi dariyar da ta ishe ta sannan ta ce"Kasan kullum idan muka je sashen samari bata yarda ta wuce ta kusa da duniyar, kuma bata gajiya da fad'in duniyar Yaya Asad bana son ki".

Shima ya yi dariya amma ba mai yawa ba sannan ya guntse fuska ya ce "Oh ba kya son duniyata? To ki tabbatar idan ba ki daina cire farce da baki ba, kina tare da ita. Kun cike jamb ne?"

Murya babu amo na ce"Eh".

"Wanne course kika cike?"

A hankali na ce "Computer science "

Ya ce"da kyau".

Ya mayar da hankali kan tukinsa ba tare da ya sake fad'in komai ba.

Abida ta ce "Yanzu kai ma babban Yaya haka zaka mini? Ai dai ni ce y'ar dakinka, amma ka tambaye ta akan karatunta ni baka tambaye ni ba, alhalin haka Yaya Faruku yake nuna mana banbanci, na yi ta cika bakin dan nawa yayan ya yi nisa ne, shine daga zuwanka zata k'wace mini kai?"

Ya bugi sitiyari bayan ya yi murmushi mai sauti ya ce "Wa zai shiga tsakaninmu, ai nasan ke guru ce, na kuma dad'e da sanin burinki, ki zama likita, ashe kuwa ba sai na tambaye ki ba, ita kuma na tambaya ne dan ta d'an saki jiki da ni, ba ki ga yadda ta takure ba ne?"

Ta numfasa ta ce "Na fahimta yanzu, amma da na ji haushi domin na kai kololuwar gajiya da yadda ake k'unsa mini takaici akan Bilki, da yadda ake yabon ta fini nutsuwa."

Ya yi dariya tare da ce wa "Autar Momi ke ma ki zama marar hayaniya irin ta mana, kinsan nutsuwa a wajen mace adone na mussaman da yake kawata ta fiye da adon da ake yiwa fuska".

Ta yi fit ta ce "A a Yaya bar ni na dinga k'watar kaina a wajen jama'a ita ma shiru shirun nata na nunkufurci ne, ni tunda muka je Katsina ta nemi rikicewa akan wani solalayi mai zubin makirai na tsorata da ita na fahimci ta wuce tunanina."

Da mamaki ya ce "Maigado wannan kike nufi?"

Da kazangi ta ce "Bilkin da take gefenka dai."

Ya numfasa ya rasa abin fad'i. Can ya sake numfasawa ya ce "Wonder shall never end! To kuma ta fasa da Faruku ne?"

Abida ta ce "Ai tunda ya yi aure ta ce "Ta fasa fas dama kuruciya ce".

Ya kallo ni kad'an ya mayar da fuskarsa a kallon gabansa.

Ya ce "Maigado wai kin fasa da Faruku da gaske?"

Da yake ni ban iya karya ba, ko zagaye zagaye

6 / 15