Author : Aysha Cool Category : Romance
je, na roƙa miki afuwa " Nana ta sake risunawa cikin girmamawa ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi"
Director ya ce "Tashi ki tafi" ta tashi jiki a sanyaye, hannunta riƙw da na Muhsin, da bakinsa yaƙi rufuwa yana ɗagawa babansa hannu.
Duk da ranta ba ya son faɗan da ake yi mata, yanzun ma ba ta ji daɗin faɗan ba, amma da tuna laifinta ne, haka nan ta haƙura, ta danne damuwarta ta shiga cikin ɗalibanta, tare da ƙoƙarin samarwa kanta nishaɗi da nutsuwa tare da yaran.
Amma sai ya zamana yaƙe kawai take yi, ƙasan zuciyarta tamkar ta fasa ihu, ga batun kaita gidan mai magani, duk da ba a kuma zancen ba, ga kuma maganar Saleh, ga malam Auwal ya juya mata baya baki ɗaya.
Da ta dawo daga makaranta, ta yi sa'a, ta tarar da wata guntuwar shinkafa, an ajiye mata, sai dai ko maggi babu, ta barbaɗa gishiri, ta ci ta tafi islamiyya.
Duk da ta san tayi sammako da yawa, hakan bai dame ta ba, saboda zaman gidan na su ne ba ta so, bata ƙaunar duk wani abu da zai ƙara dagula mata lissafi.
Kamar yadda ta saba, ta share duk wuraren da taga zata iya sharewa, ta shiga wurin ajiye tabarmi, ta hangi Auwal a cikin ofishin malamai, yana duba wasu litattafai. Ɗauke kanta ta yi, kamar ba ta ganshi ba, ta shiga ta ɗaukko tabarmar 'yan ajinsu, ta fito.
Ba ta sanya ran zai kula ta ba, dan sati guda kenan, ko gaishe shi ta yi, sama-sama yake amsawa.
"Nana" ya kira sunanta ba tare da tayi tsammanin haka ba, ta waiwaya tare da tunanin ko ba shi ba ne ya kirata. Amma ta ga yana kallonta, tabbacin shi ne yake kiranta. Sharewa tayi, ta fice ta tafi ajinsu.
Tana tsaka da shimfiɗar tabarmin ya shigo ajin, ya ce "Nana, ki na ji ina kiran ki ki ka yi share ni, Yaushe ki ka zama haka?" Ta miƙe sosai tana kallonsa, ta haɗiye wani abu mai ɗaci da ya tsaya mata a maƙogwaronta.
"Me yasa ba ka yi wa baba bayani ba, kuma ka hanani na yi masa; cewar kai malamina ne ba wanda yake so na da aure ba? Dama ka ce tausayina ka ke ji, ni kuma kasancewar wanda yake ruwa, ko takobi aka miƙa masa kamawa zai yi, na kawar da tunanin komai, na fara sonka ina tunanin ko yaya zan samu afuwa. Amma sai halayenka suka sha banban da abin da ka ke koya mana. Ina ma baka ce ana so na ba, na ci gaba da kallonka a matsayin malamina mai tausayina.
Jiki a sanyaye cike da borin kunya ya ce "Ki yi haƙuri Nana, na san ban kyauta miki ba, babu yadda zan yi ne, matsala aka samu, na rasa ta yadda zan yi miki bayani. Ina ta ƙoƙarin shawo kan matsalar ne, amma ban ce ina sonki dan na yaudareki ba, ko na yi wa mahaifinki wasa da hankali ba".
Shiru ta yi masa, ta ci gaba da gyara tabarmin, dan ba ta ma san meyakamata ta sake ce masa ba.
"Nana, ki ɗan bani lokaci kaɗan, ina daf da shawo kan matsalar"
"Tom" ta faɗa a taƙaice, ba tare da ta ko kalle shi ba. Bai taɓa zaton Nana tana fushi har haka ba.
Ya kalli yadda take ta jan tabarmin, ba tare da wani dalili ba, ya durƙusa a kusa da ita ya ce "Kalli ki ga" ta ɗaga kai ta kalle shi.
"Tabarmar ta shimfiɗu haka, ba ita ta yi miki laifin ba, ni ne amma ki yi haƙuri"
Ta kalle shi da idanunta, masu kama da za ta yi kuka, har za ta yi magana, sai kuma ta haɗiye ta fasa.
"Kin haƙura?" Yayi maganar yana tsareta da idanunsa shi ma.
Murmushi ta yi, ba tare da ta shiryawa hakan ba.
Shi ma murmushin yayi mata ya ce "Barakallahu fik, ki ci gaba da yi mana addu'a, in sha Allah komai zai daidaita amaryata".
Sunkuyar da kai ta yi, bakinta ya kasa rufuwa saboda murmushi.
"Ya jikinki, ina fatan ki na kula da duk adduo'in da nake baki"
Ta jinjina kai ta ce "Eh, ina yi"
"Yauwwa ki ci gaba da kula, Ubangiji Allah ya baki ingantacciyar lafiya"
"Amin na gode sosai" ya fice bar ajin.
A hankali ta ji zuciyarta ta yi sanyi, daga zunzurutun damuwar da take ciki.
Aka yi karatun Alqur'ani da ita lafiya ƙalau, sai da lokacin fita salla yayi, ta tashi abu ya gagara ta ji gaba ɗaya tamkar an saka sarƙoƙi, an nannaɗe mata ƙafafuwanta.
Duk wani ƙoƙari da za ta yi domin ta tashi abu ya gagara, kawai ta fashe da kuka.
Amira ta dubeta ta ce "Nana, menene ki tashi an tafi salla".
Cikin kuka ta ce "Amira na kasa tashi ƙafata ciwo take yi mini, kamar ana karya ni"
Ganin yadda Nana take kuka, sai jikin Amira yayi sanyi, a baya da yawa ana zaton Nana ƙarya take abubuwan da take yi, amma yanayin da take ciki yanzu dole mutum ya tausaya mata.
Amira ta fita ta kirawo malam Auwal, suka dawo tare, ko da suka dawo suka tarar ta mimmiƙe tamkar gawar da ta jima da rasuwa.
Cike da tausayawa shi ma ya tsuguna a kanta, ya kalli bakinta na ta fitar da kumfa, yatsunta daga na hannu har na ƙafa, sun lanƙwashe.
Ayoyin suratul jinn, ya fara karantawa yana tofa mata, ya idar ya koma ayoyi biyar ɗin farko na suratul baƙara, ya ɗan jima yana yi mata karatu kafin jikinta yayi saki, sai dai ba ta tashi ba.
Sosai tausayin Nana yake ratsa Auwal, Nana tana buƙatar kulawa ta musamman daga namiji mai addini, da haƙurin gaske, idan Allah ya taimake ta tayi aure, tasirin larurarta zai ragu idsn aka dagewa addu'a da kulawa sosai. Kwanakin nan jikinta ya tsananta, kusan kullum ba ta da lafiya.
Ganin ta yi bacci, ya sanya ya cewa Amira ta tafi wurin salla, su ƙyaleta ta huta.
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOTA(002
7
Wunin yau Nana, a ɗaki tayi shi, ta ɗauki azumi tana tawasalli da azumin da fatan Ubangiji Allah yaye mata larurar da take damunta ya ba ta lafiya.
Saboda ita kanta yanzu lamarin yana matuƙar ba ta tsoro.
A tsakar gida take ji yo radion mama, wani likita yana ta bayani, a kan cutar depression cutar damuwa, anxiety disorder cutar fargaba, shaye-shaye da farfaɗiya.
Shiru tayi, tana nazarin alamomin cututtukan baki ɗaya, cike da fatan ta gano wanne ne yake damun ta a ciki. Sai ta ji tana da wasu daga cikin alamomin anxiety disorder, wato cutar fargaba, sai kuma ta ga wasu alamomin na ciwon damuwa ne yake damunta. Tabbas akwai abubuwa da dama na ƙaluble daa suke binne a cikin zuciyarta, wanda galibi marasa daɗi ne. Ba ta tunanin akwai wani abu na farinciki da ya faru da ita, da za ta ce ba zata manta ba, gaba ɗaya rayuwarta a kan siraɗin ƙaddara take. Sai dai ta na godewa Ubangiji, da ya bar ta da imaninta.
Haka kurum sai ta ɗan ji salama a ranta, ta fara saka ran larurarta ta asibiti ce, idan ta je za ta samu mafita.
Tayi ajiyar zuciya, ta lumshe idsnaunta, kawai ta ji an bushe da dariya.
Ta buɗe idonta da sauri, ta waiwaya ba ta ga kowa ba. A take ta tuna da ire-iren mafarke-mafareken da take yi, da yadda mutumin nan yake tilasta mata yarda da sharaɗinsa na sai ta bayar da magani. Ta tuna ire-iren gane-ganen da take yi, a zahiri kuma ba ta ji likitan ya yi bayanin makamantan wannan alamomin a cikin bayanin cututtukan da ya yi ba, a take ta karaya ciwon dai da ba ta son ace shi ne da ita ya tabbata shi ɗin ne dai, ko ta na so ko ba ta so aljanu ne suke damunta.
Ko ta yi yinƙurin kawar da tunanin, sai ta tuna yadda take ganin mutumin nan a mafarki, da irin maganganun da suke yi da shi.
Kawai ta fashe da kuka, babu wanda zai iya gane halin da take ciki, sai wanda ya tsinci kansa a halin da take ciki, dan wasu sun gaza yadda ciwo ne Allah ya jarrabe ta, kawai ta ɗorawa kanta ne, dan samun attention ɗin mutane wato hysteria a turance.
Ta tashi ta ɗaukko bagcon kayanta, ta din ga ciro magungunaa, kala-kala da ake ba ta, da sunan maganin aljanu, leda-leda ta din ga fito da su. Ta gama tattare su wuri guda, ta fita tsakar gida ta din ga tura su a murhu ɗaya bayan ɗaya. A take gidan ya kaure da ƙauri da hayaƙi mara daɗin shaƙa.
Mama ce ta fito tana faɗa "Ƙaurin meye haka mara daɗi kamar gidan 'yan bori?" Ta tarar da Nana a bakin murhun ta na ci gaba da ƙona kayan.
"Ke meye haka? Uban me ki ke tura mini a murhu?" Nana ta ɗago ta kalleta, ta yi shiru ta ci gaba da abin da take yi.
Tari mama ta hau yi, ta ce "Idan ma uwarki ce ta aiko miki da wata tsiyar ki ke babbaka mini, to baƙar aniyarku ta koma kanku, dan na fi ƙarfin ku daga ke har ita" gaba ɗaya hankalin Nana ba ya kan Mama, zancen zuci kawai take yi, tana kallon yadda kayan ke babbakewa a cikin murhu.
Ganin Nana ta mayar da ita mahaukaciyar ƙarfi da yaji, ya sanya ta koma gefe ta zauna, ta na cigaba da ƙananan maganganu.
Ko da Nana ta yi buɗa baki, kunun tsamiya kawai ta samu ta sha, hakan bai dame ta ba, ta mayar da hankali sosai wurin roƙon Allah samun lafiya, da miji na gari.
Yaro ne yayi sallama, ya ce ana kiran Nana a waje.
Jamila ce ta ce masa ya ce tana zuwa.
Nana ta fito ƙasan zuciyar ta cike da murnar, malam Auwal ya dawo, akwai yiwuwar ya fito ayi auren, tun da ya dawo.
Sai dai tayi turus, da hasken fitilar wutar lantarki ya haske mata fuskar Saleh, ƙanin mijin Ummi.
Wani takaici ne ya kama ta, amma ta dake ta ƙarasa fuskarta babu yabo babu fallasa.
"Hajiya Nana, barka da fitowa ya ki ke ya gida?"
"Lafiya ƙalau, ya su Anty Ummi?"
Saleh ya ce "Duk su na nan lafiya" ya ɗan yi shiru, sannan ya numfasa ya ce "Na san dai Ummi, ta yi miki bayanin komai ko?"
Nana ta kalle shi ta ce "Wane bayanin kenan?"
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ba ta kawo miki kaya ba, ta ce in ji ni?"
"Ohh na tuna, na gode sosai da sosai"
Yayi murmushi ya ce "Ai ba wani abu, ta ce Baba ya ce ba sai na wahalar da kaina ba ma, na yi miki kayan ɗaki kawai ba sai an yi lefe ba. Kin ga faɗuwa ta zo daidai da zama, sai mu tafi can lagos tare wurin sana'ata, akwai ɗakin da nake haya komai akwai a ciki na buƙata"
Nana ta sake kallonsa ta ce "Baban bai gaya maka ba ni da cikakkiyar lafiya ba?"
Ya gyara tsayuwarsa ya matsa kusa da ita ya ce "Ai duk wannan ba wani abu ba ne ba, muddin za a samu fahimtar juna da ni da ke. Wallahi a matse nake ne Nana, ni ko wannan juma'ar ta jibi, a ɗaura ki tare a gidanmu kan na gama shirin tafiyarmu ikko" yayi maganar cikin numfarfashin rashin gaskiya, yana ƙoƙarin ya kai hannunsa jikinta.
Ja da baya ta yi, cike da takaici sai dai kafin ta yi magana, ta hango Auwal a tsaye, hannunsa riƙe da leda ya tsaya sak yana kallonsu.
Ta kalli Saleh da yake ƙoƙarin kuma matsowa, ta kalli in da Auwal yake, kawai ta juya ta shiga gida, gabanta yana faɗuwa, ba ta san ma me yakamata ta yi ba.
Kawai ta shiga ɗaki ta kwanta. A waje kuwa Gaddafi ne ya tarar da Saleh, suka gaisa Gaddafi ya ce "Mutumina yau kai ne a gidan namu?"
Saleh ya ce "Wallahi kuwa, na zo wurin Nana, kuma mu na cikin magana ta shige gida, ba ta ce mini komai ba"
"Ita Nanan?"
"Eh wallahi, ina so mu fahimci juna da ni da ita, ayi a wuce wurin kawai"
"Ka kwantar da hankalinka, kamar ka aureta ka gama ne, har wani zaɓi take da shi, kai da zaka taimaka mata. Ka manta da ita kawai ka turo a kawo kuɗi"
Saleh ya washe baki ya ce "Allah mutumina"
"To me za a jira, kawai ayi abin da ya dace" Nan ya tsaya suka ci gaba da hira, saboda Gaddafi ma a Lagos yake neman kuɗi, kuma su na haɗuwa da Saleh sosai.
Sai da suka gama hirar, sannan suka yi sallama, Gaddafi ya shiga cikin gidan, ya dira wa Nana bala'i da cin mutunci a tsakar gida. " 'yar gidan uban waye ke, da za ki hurawa mutane hanci, ke da da za a taimakawa, mahaukaciyar banza da ta wofi. Ki na yawo a kwararo ki na wannan tamɓelen ki hana jama'a bacci, kowa ya san mahaukaciya ce ke a unguwar nan, kin samu ana sonki, amma ki bujire. To wallahi ba ki isa ba dole ki auri Saleh, ki fita ki bar gidan nan ƙila ma rashin aure ne ya sanya ki ke wannan haukan "
Nana ta toshe kunnneta, saboda zafi da tururin da zuciyarta take yi, ji take tamkar ta ɗura masa ashariya, ta rama cin mutuncin da yake yi mata, amma ta din ga maimaita Innalillahi wa innalillahi raji'un.
Baba ne yayi sallama, ya tarar da Gaddafi yana bala'i, da ya tambaye shi ba'asi, ya ji da Nana yake, sai ya karɓa ya ɗora shi ma.
Nana ta rasa wannan jaraba, babu wanda aka tsangwama yayi aure a gidan sai ita, saboda su ga babarsu a gidan, ita kuma ga rashin uwa, ga larura ga shi duk wata hanya da za ta samu mahaifiyarta ko a waya, Baba ya datseta, har yana nema ya yi mat baki.
'meye na damuwa ma, matar da ko in da ku ke ba ta zuwa, ta ga halin da ku ke ciki, balle ki gaya mata halin da ki ke ciki, ta saka ki a addu'a, ko kuma t nema miki magani' wata zuciyar tayi mata tunin, abin da ba ta so, domin in dai tana ire-iren waɗannan tunanin, ta na jin zafin mahaifiyarta a ranta.
"Ke Nana, zo ga waya Atine za ta yi magana dake" maganar Baba ta dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula.
Gabanta ne ya faɗi, wata sabuwa in ji 'yan caca, ba ta ƙaunar duk abin da zai haɗata da matar nan a rayuwarta.
Ba tare da ta amsa ba, ta tashi ta fita.
Baba ya miƙa mata waya, ta karɓa hannunta na rawa ta saka a kunneta, ta yi shiru.
"Ke ma'u ki na ji na?"
"Eh" ta amsa a cunkushe.
"Dan ubanki sai ki yi mini shiru, ko gaishe ni ba za ki yi ba, har kya yi wa mutane ƙaryar iskancin aljanu, mu da a ka yi gadon bori a gidanmu.
Nana ta yi shiru, tana mamkin yadda jahilci, ya sanya yaya Atine alfahari da harkar shirka, da shi ne musababbin gadar mata da bala'i, kamar yadda mutumin da take mafarki da shi, yake iƙrari.
"Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, ranar asabar ki yi kuɗin mota, ki taho gidana, akwai gidan wani mai magani da zan kai ki. A baki maganin aljanu da na farin jini, aure dole ki yi shi babu fashi, ko shi wanda ba kya so ɗin ko wani daban. Ke wannan baƙin jinin kamar an jiƙa hatimin jaɓa an baki, daga nonon babarki ki ka shawo shi. Mu zuriyarmu farin jini ne da su wallahi, babu mai nauyin jini"
"Yaya atine, idan ni a nonon uwata na sha, su suwaiba a naki nonon suka sha? Tun da Uwar tawa ba ta nan, menene na sakota a zancen ki, koma wani bala'in ne ya same ni, ba duk a dalilin shirka da iyayenku suka yi ba ne, da har ki ke alfahari da ita" ita kanta Nana ba ta san yaya aka yi, suke fita daga bakinta ba, saboda yadda ranta ya ɓaci zuciyarta take tafasa fiye da kima.
"Ma'u ni ki ke gaya wa haka?"
Gaddafi ne ya yi kan Nana, amma Baba ya tare shi, ya ce "Rabu da ita, ka na taɓa ta babu lallai, mu yi bacci mai daɗi a gidan nan, wataƙila ma ba ita ba ce ba, ƙyale ta"
Ta ajiye wa Baba wayarsa, ta koma ɗaki.
****
Cike da damuwa Auwwal ya koma gida, 'yar tsarabar da ya yi wa Nana, ya bawa ƙannensa, wani irin kishi ya addabi zuciyarsa, sai dai kuma yanayin kallon da ya ga tana yi wa wanda suke tsayen ne, bai gama gane kansa ba.
"Auwwalu" Umma da ta gama kasa gurasa da naman gabanta.
Ya kalleta ya amsa da "Na'am Umma"
"Magana nake son mu yi da kai ta fahimtar juna. A matsayina na mahaifiyarka".
Ya tattara mata hankalinsa baki ɗaya cike da ladabi.
"Ka zo mini da maganar aure, na ce maka ka dakata, ba yanzu ba tukuna. Karo na farko abin da ba ka taɓa yi mini ba, ka kai ƙarata wurin kawunka ƙanin mahaifinku. Ya zo har gidan nan baka nan, mun yi magana ta fahimta da shi sosai na kuma fahimce shi, har ya gaya mini ka gaya masa sunan yarinyar da gidan mahaifinta. Na ce masa to ya ɗan saurare ni. Na zo da kaina na saka ayi mini bincike, shi ma kawun naka na saka yayi ta nasa ɓangaren. To magana ta domin Allah ba zan yadda ka auri wannan yarinyar ba, ashe ita ce wadda ka ke bani labari mara lafiyar nan. 'yan unguwarsu sun tabattar da ba ta da wata matsala sai wannan iskokai, kuma ana kyautata zaton kakaninta 'yan bori ne, ni kuma gaskiya ba zan yadda a ɓatawa tsatsonmu suna ba, a sa a gada wa zuriya masifa ba.