BUZU Book 1 Complete By Aysha Cool.docx

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   18 / 18

51K to 52.2K   out of 52.2K words

salaryana ka taimaka ka bani na last month"

"Ba za a bayar ba, shi ma last month ɗin wani zuwan kirki ki ka yi, kullum ba ki da lafiya"

Nana ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah ko rabi ne, ka taimake ni"

"Ba zan bayar ba, asarar da ki ka janyo mana, na wahalar neman wata malamar a kuɗinki" Nana ta ji zafin korar da aka yi mata, duk da ta san laifinta ne, amma dai yakamata a bata hakkinta.

Ko sallama ba ta yi da sauran malaman ba, dama ba cikinsu take shiga ba, saboda yadda suke yi mata kallon Nanny kawai.

Dama da ƙafa ta zo makarantar, dan haka yanzu ma ba ta da kuɗin abin hawa, da ƙafarta ta miƙi hanya.

Horn ɗin da aka ishe ta da shi ne, ya sanya ta tsaya, ta waiwaya. Motar baban Muhsin ta gani. Ya ƙaraso gurin da take ya ce "Anty kwana biyu lafiya kuwa? Muhsin na ta rikici ba kya zuwa makaranta shi ba zai zo school ba"

"Wallahi na ɗan yi rashin lafiya ne"

Cikin tausayawa ya ce "Eyya Allah ya sauwwaƙe, mun yi magana da director ya ce sallamarki zai yi, ba yadda ban yi ba, amma ya ƙi yarda ya haƙura" Nana ta yi guntun murmushi da iyakarsa laɓɓanta ta ce "Ba wani abu, rabona ne ya ƙare a gurin kawai".

"Eyya babu daɗi, to hawo na sauke ki a gida"

Ta girgiza kai ta ce "a'a ba komai na kusa ƙarasawa ai"

"A'a da saura ai na sani, hau dan Allah" ya yi maganar yana buɗe mata ƙofar gaban motar" ta yi bismillah ta hau.

"Wallahi ban ji daɗin sallamar ki da director ya yi ba, ki na da ƙoƙari matuƙa gaya." A wannan karon ma murmushin dai ta yi tana wasa da yatsun hannunta.

"Ki bani takardun ki, na nema miki admission a school of legal studies, ko koma makaranta mana"

Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode sosai"

"Me yasa? Karatun ne ba kya so? Nana ba zan cutar da ke ba. Ba na wasa da duk abin da ya shafi yarana, yanzu haka Muhsin ne ƙarami, amma duk lokacin da nake gari ni nake kai shi makaranta, saboda yana son hakan. Da ɗa da dukiya ba ayi musu mugunta ba ka san wa zai amfane su ba. Amma ki yi tunani idan kin amince zan samar miki admission ba, ko ba duka ba zan ɗauki ɗawainiyar karatun naki."

Cikin girmamawa ta ce "Ka na cikin mutanen da ba zan manta da su ba a rayuwata, ba zan so ka ɓata kuɗin ka ba, ina ga nan da wani ɗan lokaci za a ɗaura mini aure, kuma garin zan bari gaba ɗaya"

"Allah sarki, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Bani wayar ki na saka miki lambata, idan lokacin bikin ya yi ki sanar da ni, zan halarci ɗaurin aure in sha Allah"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ni da waya ai, ka yi mini addu'a na gode sosai da sosai. Sannan a cewa Muhsin ya yi karatu da kyau, Allah ya yi masa albarka" jiki a sanyaye yake kallon Nana, haka kurum take ba shi tausayi gaba ɗaya yanayinta ya nuna akwai labari mai ban tausayi a tattare da ita.

Ya yi parking daidai gurin da take sauka, tana kiciniyar buɗe ƙofar motar, ya miƙa mata kuɗi, ya ce "Ga wannan ba yawa, Allah ya baki wani abin yin." Za ta yi magana ya girgiza mata kai. Ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai"  ya daɗe yana kallon yadda take tafiya da ƙyar ta shige cikin layuka.

*****

Malamin Hajiya Sa'a yana zaune, ya duba wurin da yake gabansa, ya kalle ta ya ce "Hajiya a wannan karon ma babu sa'a fa, 'yan aikenmu sun makara, domin fafur sarkin baka ya hana yarinyar nan, ƙarshe ma ya mayar da ita gida, ya ce mu je can mu ɗauke ta, yanzu haka tana can"

"Kai wannan wace irin masifa ce? Ni an taɓa bani aiki mai wahalar wannan ma kuwa?"

Ya yi dariya ya ce "Ai na gaya miki hatsabibin aljani ne a tare da ita, kuma mutane irinmu, mu na burin mallakar aljani irinsa, domin kaf jinsin babu aljani mai tsananin juriya da kasada kamar sa, tun da sarkin baka ya mayar da ita ba tare da ya mallaki aljanin ba, na san akwai matsala. Yanzu ki bar wannan mu jingine ta zuwa wani lokaci kaɗan. Yanzu ga wani aiki mai ɗan sauƙi, 'yar aikenmu na kan waccan yarinyar da ta yi amfani da turare kuma ta warke ma. Ki duba dangi wanda yake jininki ki samo yaro da bai wuce shekara biyar ba, a sadaukar mata da shi, domin ta ƙara samun kuzari zan sanya ta yi miki wani aiki"

Hajiya sa'a ta ɗan yi shiru ta ce "Akwai ɗan wa na, ba zai gagara ba"

"To shikkenan, tashi ki je, Sa'a na tare da ke Hajiya Sa'a tun da ki na bibiya ga duk abin da aka saka ki. Ki je za a sanar da ke lokacin da ake buƙata" tashi ta yi tana jin daɗin yabon da ya yi mata.

*****

Nana da ta koma gida, ta tarar an kai Suwaiba asibiti, daga gurin masu magani, wai jikinta babu jini an riƙe ta a asibiti.

Sam Nana ba ta yi gigin bin su ba, ta dai yi wa Suwaiba Addu'a. Ta duba kuɗin da baban Muhsin ya bata dubu goma cif. Addu'a ta din ga kwarara masa da shi da zuriyarsa, saboda ta ji daɗin kuɗin nesa ba kusa ba.

Da yamma Ummi ta zo gidan, ta tarar da Nana a gida.

"Nana ke ba ki je asibiti duba Suwaiba ba?"

"Hmm kin san da yadda ta yarda nake zaune a gidan nan ne ma? Su na cewa ina ƙoƙarin kashe Suwaiba, wai ina sha mata jini.. sauran maganar ya kakare mata saboda kukan da ya kufce mata mai taɓa zuciya.

Jiki a sanyaye Ummi ta ce "Yanzun ma da na je, su na ta maganganu amma dan Allah ki manta da su. Ke dai Allah ya baki lafiya. Na zo ne a kan batun shirin bikinki, Baba ya ce ba za ayi taro ba. Amma ko ba za ayi taro ba ai kya fara gyaran jiki dai ko?"

"Me zan gyara? Ni dan Allah ki rabu da ni"

Ummi ta ce "Kamar yaya na rabu da ke? Aure fa za ki yi."

"Auren jeka na yi ka ba? Ai kun san ba so nake yi ba, amma babu yadda na iya ne, shi ne sauran mafitar da ya rage mini"

"Au Nana ba za ki daina maganar ba kya so ɗin nan ba ko? Ke ba kya tausayin kanki da wannan wahalar da ki ke ciki ko? Ki je ki ki yi ta yi, sai mutum ya tausaya miki, idan ki ka tafka wani rashin mutuncin zai gane ke ba abar tausayi ba ce. Ki je ki yi abin da ki ka ga dama, ni na cire hannuna a kan ki"

"Allah yana tare da ni, na san shi ba zai cire hannu daga kaina ba" Nana ta yi maganar hawaye na gangarowa daga idanunta.

Ayshercool

08081012143

Alhamdilillah free pages sun kammala, masu buƙatar ci gaba su na iya tuntuɓata a kan lambar wayata.

1k ne a telegram

Via 0069685771

Aisha Adam stanbic ibtc sai shaidar biya ta 08081012143

18 / 18