Author : Aysha Cool Category : Romance
lafiya, ni kuma ba ni da isasshen lokaci, na shiga wani meeting ne, shi yasa na daɗe ban zo ɗaukarsa ba, ki yi haƙuri na ɓata miki lokaci". Jinjina kai kawai ta yi ta tashi, ya ce "Mu je sai mu sauke ki a hanya" sai dai haryanzu ba ta yi magana ba, ta bi shi su ka tafi.
Jamila na zaune, tana ta zaman kashe wando a gidan maman khairat, kamar yadda ta mayar da hakan ibada, tana tayata aiki su na hira.
"Ni kuwa jiya kin ci abincin jiya Jamcy?"
Jamila ta ce "Lallai ma Anty Safiyya, me zai hana ni ci, na yi abincin kuma na kasa ci?"
"Wallahi ni gaba ɗaya kasa cin abincin na yi, na ce da na sani, na ce ki tafi da shi duka"
Jamila ta ce "Subhnallah, ko dai Khairat za a yi wa ƙani"
Tayi murmushi ta ce "Rufa mini asiri, wallahi sai da ki ka tafi na ga kamar abincin ba zai ishe ku ba, kuma har su Nana duk sun samu sun ci?"
Sai da Jamila ta yi mamakin tambayar, amma ta ce "Eh mana, Nana ce ma babu lafiya, ba wani ci ta yi ba, kin san 'yar ƙi faɗi ce, sai na je da abu sau shurin masaƙi amma babu lallai ta ci"
"Eyya, to ai ba komai, mun riga mun zama ɗaya Allah ya ba ta lafiya, ta sha lemon ma?"
"Eh amma ba da yawa ba"
Safiyya ta jinjina kai ta ce "Dan Allah ki yi mata sannu"
Jamila ta ɗan taɓe baki ta ce "To, za ta ji, kin san ita kullum cikin ciwo take ne, abin nata ba na ƙare bane ba"
Suka ci gaba da hira, ƙasan zuciyar Safiyya, cike da farin ciki
*****
Ƙarfe huɗu da rabi na yammaci, sannu a hankali yake ƙarewa garin kallo, duk ya kwana biyu baya garin, amma ba wani abu ne ya canza ba, amma har cikin zuciyarsa yake jin kewar Kanon dabon.
Tun daga can babban titi ya sauka, ya saɓo hanya, domin ya samu isashshiyar damar ƙarewa garin kallo, yadda yake so.
Dandazon mutane ya hango a wani wuri, mutane na ta surutu da hayaniya.
Har ya yi gaba, kawai ya dawo da baya domin ganewa idanunsa abin da ya tara wannan cincirindon al'ummar.
Ya din ga kutsawa, yana ture mutane.
Kawai ya tarar da wata matashiyar budurwa a kwance a wurin, sai dai ta juyar da fuskarta ba a iya ganin fuskarta.
Ya taɓa wani mutum ya ce "Malam lafiya, me ya faru don Allah?"
Mutumin ya ce "Wallahi tun azahar, muka ganta a kwance a wurin nan, an zata ma ko ba ta da hankali, ko kuma ba ta da lafiya, amma jikinta fes babu datti ba alamar hauka a tare da ita. An yi anyi ta tashi ko motsi ba ta yi, kuma tana da rai. An duba jakarta babu waya sai maka da kuɗi, yanzu ma dai an kirawo 'yan sanda".
Bai ce uffan ba, cikin azama ya nufi kanta, mutane na ƙoƙarin hana shi, amma bai saurari kowa ya je kanta ya ɗago ta.
Idanunta a rufe, sai dai hawaye da yake ta fita ta gefen idonta, ga jikinta zafi tamkar wuta.
A sanyaye ya ce "Nana" shiru ba ta amsa ba.
Miƙewa yayi yana ƙoƙarin ɗaukarta, wani ya ce "Malam lafiya, ina zaka kaita?"
"Ƙanwata ce" ya faɗa a taƙaice, ya fita ya taro adaidaita sahu. Bai sake tsayawa yi wa kowa bayani ba, ya saɓa Nana ya shiga adaidaita sahu, ya tafi da ita.
Mama na tsakar gida tana tankaɗen tuwo, sai ganinsa tayi a tsakiyar tsakar gida.
Suwaiba da take jan ruwa ya kalla ya ce, "Shimfiɗa mini tabarma a tsakar gida"
Ta ajiye gugan, ta ɗaukko tabarma, ya kwantar da Nana a kai.
Ya ɗebo ruwa a kofi, ya zo ya zauna a kusa da ita, yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta rame sosai da sosai.
Cirko-cirko mutanen gidan suka yi, su na bin sa da kallo, kowa da magana a bakinsa, amma babu damar furtawa.
Ya tofa ayatul kursiyyu, da falaqi da nasi, kowacce da bismillah, ya shafa mata ruwan a fuskarta, da tafukan hannayenta. A hankali yake bin jikint da kallo, yana mamakin shaidar duka ce, ko ta ƙonuwa a jikinta.
"Nana" ya kira sunanta. Cikin sa'a sai ta buɗe idonta a hankali, ta sauke a kan fuskarsa.
Shiru ta yi tana kallon sa, kamar ba ta taɓa ganin sa ba, zuciyarta na raya mata kawai tarkacen mafarkin da take yi ne. Ta yi shiru, ta tuna ta shiga motar baban Muhsin, su na tafe a hanya, a kunnenta ta ji ana ce mata, ga Auwal can a marrraba, nan da mintuna goma tirela za ta taka shi.
Babu shiri ta tsayar da baban Muhsin, bai gama parking ba, ta buɗe motar ta fita daga nan kuma, sai ta ɗimauce ta rasa gane gaba da baya.
Mayar da idanunta tayi ta sake lunshewa.
"Ma'u" ya kuma kiranta yana matsa hannunta.
Ta sake kallonsa a hankali ta ce "Wai da gaske kai ne?"
"To da waye? Dama haryanzu ba ki warke ba, ki na wannan ciwon Nana? Kuma uban waye ya dake ki duk jikin ki ya tashi haka?" Ta yinƙura ta tashi zaune, kawai ta fashe da kuka.
"To kukan uban me ki ke yi kuma? Na ce uban wa ya dake ki?"
"Ba dukana aka yi ba" ta bashi amsa tana share hawayenta.
"To me ya kai ki yin bacci a titi, maza sun baibaye ki, kamar ƙudaje sun ga mangwaron Binta suga"
Ba ta bashi amsa ba, ta ci gaba da kuka.
Ya tsuke fuska ya ce "Dalla yi mini shiru, ina yi miki magana ki na wani kukan banza"
"Me yasa ka tafi ka bar ni?" Ta yi magana cikin kuka.
Guntun tsaki yayi, ya ce "To dai ba ga ni na dawo ba? Uban me ake tsinana mini a gidan idan na zauna, yanzun ma tunaninki ne ya addabe ni, nake ta mafarkinki shiyasa na taho, kuma ina zuwa na tarar da dandazon mutane, ina dubawa na ga ke ce. Allah dai ya tsinewa wannan matsiyatan aljanun naki banzaye marasa imani"
Za ta yi magana, Baba yayi sallama suka amsa, sai dai ya ja tunga ya tsaya, ganin wanda bai taɓa zato ba a gidan.
"Kai imrana, uban me ka ke yi mini a gida? Me ya kawo ka gidana?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Kamar yaya? Ya ka ke magana kamar wani shege ba kai ka haife ni ba? Gidan ubana na zo, kuma wurin 'yar uwata na zo"
"Ban yi maka iyaka da gidana ba? Ki na me ki ka bari ya shigo mini gida?" Yayi maganar yana kallon mama.
A ƙufule ta ce "Au to kokawa ka ke so na yi da shi? Ko saɓa shi zan yi na jefa waje, tun da kai ka dawo sai ka fita da shi ai"
Ya sake kallon imrana ya ce "Ba magana nake yi maka ba? Ban hanaka zuwar mini gida ba?"
Cikin rashin ɗa'a Imaran ya ce "Sai ka ce wani gidan kirki, to ka mayar da ni in da na fito, cikin uwata ta mayar maka da ni"
Nana ta ce "Imarana Baba ne fa"
"Shi ɗin, shekaru uku ba ka ga ɗanka ba, da haka yakamata ya karɓe ni komai girman laifin da na yi masa? Ba azabtarwa da ake yi mana ne ya tilasta mini barin gidan nan ba"
Gaddafi ne ya shigo, bayan dawowarsa ya jiyo hayaniya daga cikin gidan ya shigo, domin duba abin da yake faruwa.
Shi kansa mamaki ne ya kama shi, ganin Imran a gidan.
Baba kamar ya fashe da kuka ya ce "Imrana ni ka ke gaya wa haka? Ka tashi ka fita ka bar mini gida na ce maka"
"Idan na bar gidan shege nake, wallahi sai na gama kwanakin da zan yi. Ke Nana ga jakata nan zan je na dawo.
Nana ta tashi ta ɗauki jakar, ta nufi ɗakinsu da ita, Baba ya daka mata tsawa ya ce "Bashi jakarsa ya bar mini gida"
Cikin kuka Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah Baba ka yi haƙuri, tun da ya ce idan ya gama kwanakinsa tafiya zai yi. Shekara uku ban ganshi ba, dan Allah ka yi haƙuri"
"Au Nana kin fi son ɗan uwanki da ni ko? Amma yana sane da mu, ya kama gabansa ya tafi gantalinsa har shekaru uku, yana gararamba bai waiwayo gida ba, sai yanzu saboda ya mayar da ni ɗan iska zai dawo mini gida?"
Imaran ya nufi Nana, ya karɓi jakarsa, ya kaita wani ɗan lungu ya ajiye, ya fice ya bar gidan. Shi kansa Gaddafi kasa magana ya yi, saboda tsagwaron zunzurutun tsageranci kawai yake iya ganowa a cikin idon Imran ɗin.
*****
"Hajiya Sa'a aiki ya lalace fa"
"Ban gane ba, kamar yaya?"
"Akwai wani hatsabibin shaiɗani a tattare da yarinyar nan, ya lalata mana aiki gaba ɗaya. Ba a samu adadin jinin da ake buƙata a jikinta ba"
Dafe kai Hajiya Sa'a tayi, ta ce "Yanzu mene ne abin yi, ka ce akwai sa'a a tattare da yarinyar yanzu babu wata dabarar kuma? Yarinyar ce wata irin majanuniya, har kaya na bayar a kai mata, babu yadda ban yi a sake kawo mini ita gidan yarinyat Safiyya ba, dama a can na ganta wai ta ƙi yarda. Ni kuma na abin na je gidansu ba, ba na son zargi da saka ido"
"Aikuwa neman mafita ya ganki, domin wani baƙin sheɗani ne a tattare da ita, babu lallai ya bari wani ya raɓe ta, saboda wasu dalilansa, 'yar aiken tamu ma ya ƙona ta. Yanzu dole ki san yadda za ki yi, a sake ba ta maganin zamu sake tura wani ɗan aiken"
Hajiya Sa'a ta jinjina kai ta ce "Amma, ba yadda za ayi a samo jininta nata, dole sai an bata wani abin ta ci?"
"Eh dole ne, idan ba haka ba babu ta yadda za a samu jininta, ba zai bari a tunkare ta ba. Kuma ko ba haka ba, idan ba ta hanyar abincin da za a bata ba, ba kowane aljani zai iya raɓarta ba, saboda tana zama da alwala, kuma tana adduo'i shi kansa aljanin jikin nata, ba ƙaramar azaba yake sha ba. Dan haka yanzu ko dai a samu jininta ta wannan hanyar ko kuma ki janyo ta ƙungiya"
Hajiya sa'a ta ce "Ba abu ne mai sauƙi ba hakan, muguwar miskila ce, ba kamar 'yar uwatta ba, da ɗayar ce ko nan ka ce na kawo maka ita, zan kawo ta, amma babu komai zan san abin yi, dole haƙata ta cimma ruwa"
"Babu laifi"
****
A hankali jikin Nana ya ci gaba da yi mata raɗaɗi, tamkar ana kunna mata wuta, ta daure ta din ga nanata suratul jinn, tun daga farko har ƙarshe a zuciyarta.
Imaran ne ya dawo bayan sallar isha'i, hannunsa riƙe da ledoji.
"Nanawo, sannu ya jikin?" Yayi maganar bayan ya ja kujera ya zauna.
"Jiki Alhamdilillah"
"Kai Nasiru ɗaukko faranti" yayi maganar yana kallon Nasir.
Ya je ya ɗaukko faranti, ya zazzage musu gurasa da nama fal a kai.
Ya kalli Nana ya ce "Ina Jamila ne? Tun da na dawo Suwaiba kawai na gani, ko an yi mata aure ne?"
Nana ta ce "A'a tana maƙwabta"
Ya tsuke fuska ya ce "Har bayan sallar isha'i, kamar gidan ubanta?" Yana rufe baki ta yi sallama.
Sai dai ta tsaya da ta ga Imaran, ta ce "Imran dan Allah kai ne ko gizo idona yake yi mini?"
"Ban sani ba, tun la'asar ba kya gida kina can kina gantali a gidajen mutane"
"Haba ai ka bari mu gaisa, ina ka tafi shekara uku ba wanda ya san inda ka ke?"
"In da ki ka aike ni. ware ki wanko hannu ku zo mu ci abinci"
Ta ce "Yanzu ma kuwa"
Cikinsu ya shiga, suka rufarwa gurasar, yana kallon Nana, da ƙyar take ci. A haka Gaddafi ya shigo ɗaukar abincin dare ya tarar da su.
Imran ya kalli Nana ya ce "Wai ba za ki ci ba ne?"
"Imrana ba a ɗebarwa Baba ba, Mama ba a bata ba"
Haushi ne ya kama shi ya ce "Wallahi ba zai ci ba, da na zo ko ruwan gidansa ya bani, ba kora ta ma ya yi ba? Kar Allah ya sa ki mayar da hankali ki ci"
Abinka da 'yan uwa, haka suka kewaye Imran.
Jamila ta ce "Wai dan Allah tsawon wannan lokacin, ina ka tafi?"
"Duniya na shiga mana, tun da an kore ni an ce ba a buƙata ta a gidan"
Baba yayi sallama, suka amsa masa gaba ɗaya.
"Imarana ban ce ka bar mini gida ba wai?"
"Wallahi Baba ba zan bar gidan nan ba, sai na gama abin da nake yi"
A fusace Gaddafi ya ce "Wai kai baban ka ke yi wa magana a haka?"
Imran ya kalle shi ya ce "Kai kuma ina ruwanka da ni? Kai a yaya ne baka yi masa magana, ya taɓa korarka ne? Ka ga tun da na zo ban kula ba kar ka shiga harkata ehee"
A fusace Gaddafi ya yo kan Imran, Imaran ya miƙe tsaye ya ce "Wallahi yanzu ba da ba ce, wallahi ka taɓa ni sai na soka maka ƙarfe".
Baba ya tare Gaddafi ya ce "Rabu da shi, kar ya yi maka rauni, alamu sun nuna haryanzu yana shaye-shaye"
"Wallahi Baba ko uban me yake sha, dai-dai nake da shi, ka bari na sauke masa tsagerancin da yake kansa"
"A'a gara dai ya riƙeka, dan wallahi ka taɓa ni sai na buga ka da ƙasa ba abin da ya dame ni" ya kaɗe rigarsa ya fice.
Nana ta dafe kanta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, tun tsaowar su Baba ba sa shiri da Imran ko kaɗan, tabbas a baya babu wanda suke tsoro sama da Gaddafi sun daku a hannunsa, saboda ya ce babar su ce ta yi sanadin da aka saki babarsa, kuma har ta mutu Baba bai dawo da ita ba.
Ta yi alwala ta yi sallar isha'i ta kwanta, ba dan tana jin bacci ba.
Kwanciyarta ke da wuya, ta lumshe idanaunta, ta lula duniyar tunani, ta buɗe idonta domin juyi ta gyara kwanciyarta, kawai ta ganta a bakin wani ruwa a zaune.
Ta ɗaga kai ta waiwaya, ba kowa a wurin, sai dogwayen bashiyu koraye shar, ruwan gabanta kuma sai tambal-tambal yake yi tamkar zai yi ambaliya.
Ta kalli jikinta, ta ga babu kaya a jikinta, sai wani ɗan mayafi da aka rufe mata ƙirjinta, zuwa al'aurarta.
Jikinta duk ya ɗuri ruwa, ya kwaile saboda ƙuna.
Ta yinƙura za ta ja ƙafafuwanta, ta tashi ta gansu ɗaure a jikin sarƙa.
Free pages na daf da ƙarewa. Contact me to subscribe yours.
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
YOTA/002
AYSHERCOOL
P10
Ta waiwaya jin maganganun su Suwaiba, a kusa da ita, har su na faɗa a kan charger, amma ba ta ganinsu sai ita ƙwal a wurin.
Ta rintse idanunta, tana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah"
Ji ta yi an taɓa ta, ta buɗe idonta tana tsammanin ganinta a ɗakinsu, amma ta ganta dai a wurin a zaune.
Ya durƙusa ya kwance sarƙar ƙafarta, sannan ya kalleta, ba ta iya kallonsa, duk da a suffar mutum ya bayyanar mata, duk da dogwayen yatsunsa masu ɗauke da zaƙo zaƙon farata sun fallasa bambancin da yake da shi da bil adama.
"Kalli jikin ki, kalli irin raunukan da suke jikin ki, saboda azabar taurin kan ki da dan halin ki zan bi, da sai dai ciwon nan yayi ajalinki"
Nana ta ɗan kalle shi, ta kawar da kanta ta ce "kai ne fa ka yi mini raunin, da tartsatsin wutar da ya din ga fitowa daga bakinka"
Ya dube ta ya ce "Ba zan yi miki irin wannan illar ina sane ba, kafofin da za a din ga zuƙar jininki ake so. Ina sake jaddada miki ki karɓi abin da ƙaddara ta zana miki. Ni hadiminki ne zan zama mai biyayya a gare ki, idan kuma ki ci gaba da bujirewa zan ci gaba da azabtar da ke, dan rayuwata ba za ta salwanta a banza a kan ƙoƙarin kare ki da baiwarki ba, ba wannan aikin na karɓi yi daga wurin kakaninki ba".
Ta ɗan ɗago ta ce "Wani irin aiki ka karɓa a kaina, kuma meyasa ka dage lallai ni zan yi harkar bori? Kai ba ka ga ilimin addini ya yawaita ba yanzu? Su ma na yi imani da Allah, rashin ilimi ne ya sanya su ka yi wannan harkar. Kuma duk sauran mutanen dangin babu wanda za ka matsawa ya yi harkar shirka sai ni?"
"Ba ni da lokacin da zan tsaya yi miki wani dogon bayani, amma ina mai tabbatar miki tashin hankali da masifun rayuwa yanzu a ka fara, ko ƙafa ba ki saka ba domin ba ayi komai ba".
Nana ta ce "Abin da Allah ya ƙaddara ya zai same ni ne kawai zai faru da ni, na zan taɓa yadda da duk wata tatsuniya da za ka karanta mini ba"
"Shikenan, ba na buƙatar dama ki yarda, zan cire hannuna na ja da baya na zura miki ido, da kan ki za ki neme ni".
"Da ni da kai duk bayin Allah ne, dan haka babu yadda za ayi na nemi taimakon ka. Ko da ka tare mini wani abu, Allah ne ya tare mini kai sila kawai za ka zama" Ta yi maganar cike da ƙwarin gwiwa.
Yayi mata shiru, ya juya ya kalli ruwan nan, ya fara fito da wata baƙar iska daga bakinsa yana hurawa ruwan. A take iskar ta dinga tafasa ruwan har da tururi. Ya kwantar da Nana, ita kuwa ta zuba wa sarautar Allah ido.
Ya ce "Maganin da matar nan ta baki ki ka sha, ta samu damar tsinka wata jijiya a mararki, shi ne ki ke wannan fitsarin jinin kuma sun samu sun tara, duk da bai ishe su ba.
Wannan ciwon na jikinki, ba ƙonuwa ba ce