BUZU Book 1 Complete By Aysha Cool.docx

Author :  Aysha Cool Category :  Romance

Chapter   15 / 18

42K to 45K   out of 52.2K words

su 'yar ƙashi ɗaya, a tsumata zuwa jibi a sallame ta" Sai da Nana ta razana da abin da ta gani.

Bayan fitarsu ya kalli Nana ya ce "Idan ki ka kuma ƙaryata ni a gaban mutane, sai na je na ɗaure ki a cikin mahaukatan nan kema"

Nana ta ce "Amma ka ce ƙaisar ba zai kamu ba"

Ya ce "Zai kamu, ban yi niyyar kama shi bane"

Ta sake cewa "Amma ya ake ka ke wannan abubuwan haka? Ta ya ya ka ke sanin abin da baka nan aka yi?"

"'yan aike ne suke gaya mini "

"Aljnu kenan ko? Haramun ne fa hakan shirka kenan"

"Ba shirka ba ne, taimakon al'umma muke yi"

"Wallahi shirka ce, har fa tsafi ka ke yi "

Dariya ya yi ya ce "A ina na yi tsafin?"

"Ga shi nan ina gani kana yi, ya aka yi mage ya fito daga cikin mutum, kuma ya ake yi ka ke tura abubuwa da yawa a cikin 'yar ƙarama jakar nan?"

Sarki ya ce "Aljihuna ne da yawa a cikin jakar"

"To buɗe in gani" ya yi murmushi ya miƙa mata jakar ya ce "Buɗe da kanki" cike da ƙwarin gwiwa ta karɓi jakar, babu fargabar komai ta fara dubawa. Ya zuba mata ido yana dariya.

Sai dai ta zazzage jakar babu komai a ciki.

Ta kalle shi ta ce "Wallahi tsafi ne ina magen da ka saka a ciki ya tafi?" Ita kanta Nana tana mamakin yadda ta daina kewar gida gaba ɗaya, take jin kamar ta daɗe da sanin sarkin baka.

"Idan kin yadda ki bayar da magani, zan nuna miki yadda nake komai, ki koma gida ki taimaki mutane"

Ta girgiza kai ta ajiye masa jakarsa.

"Ki je ki huta, anjima tare za mu fita farauta da ke, ki je ki yi bacci yanzu"

Ta waro ido ta ce "Da wa za ayi farautar? Amma dai ba ni ba ko?"

"Eh ba ke ba" ya bata amsa

Ta juya da baya da baya, ta fita. Tana zuwa ɗakin da take, ta ga hayaƙi da wani irin ƙauri mara daɗi, cikin abin da bai fi mintuna uku ba, bacci ya kwashe ta.

Da Ƙaisar ta fara tozali, zaune a kan wani dutse a cikin wani rafi, ya miƙe ƙafafuwansa a cikin ruwan masu azabar tsayi kamar itacen dogon yaro.

Duk da ta riga ta saba da ganinsa, ba ta fiye razana dan ta gan shi ba, amma biyo bayan tuna mafarkin da ta yi da shi, a cikin sahara ya sanya ta zura da gudu tana neman hanyar guduwa.

Ta yi gudu mai nisan gaske, ta ga wani gida, kawai ta faɗa gidan, tana addu'a a zuciyarta amma ta kasa furta ta, a bakinta.

Sai dai bayan shigarta gidan, ta nemi hanyar fita ta rasa, kofofi kashi kashi a gidan, duk ƙofar da ta bi babu hanya sai dai ta sake dawowa guri ɗaya.

Ta dinga buɗe ƙofofin amma ta rasa hanya.

"Ina za ki ne?" Ya tambayeta bayan ya ajiye wata kwalba, jikinsa sanye da fararen kaya yana ɗigar da ruwa.

"Yau kuma tsoro na baki? Ko ba ki yi zaton ganina yanzu ba?"

Kuka Nana ta saka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, kar ka ƙona ni yau ma, dan Allah"

"Yaushe na ƙona ki?"

Nana ta ce"Ranar da ka zama tsoho ka koma raƙumi, ka yi haƙuri dan Allah"

Ya girgiza kai ya ce "Ba ni bane"

"Wallahi kai ne"

"Ni ban yi wannan tsufan ba ai, ba ni bane"

Cikin kuka ta ce "Kai na gani a sahara, ka zama raƙumi kana feso mini wuta"

Ya sake cewa "Ba ni bane ba, tawagar buzayen da ki ka gani ne lokacin da ku ka shiga gidan. Ni ban yi wannan tsufan ba dudu sheruna nawa ban fi ɗari biyar da goma ba, yaro ne ni"

Galala Nana ta saki baki tana kallonsa, shekara ɗari biyar da goman ne yaro. Tambayoyi ne fal a cikinta amma tana tsoron ta tambaye shi ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta.

Ya ce "Kalli can" ta kalli gurin da ya nuna mata.

Suwaiba ta gani tana ta ihu ana danneta, mama na kuka tana tofa mata addu'a, sai fizge-fizge take yi tana kiran sunan Nana.

Cikin damuwa Nana ta ce "wai me ya sa take kiran sunana, ba fa ni ba ce ba, ni me na yi mata?"

Ya watsa wani abu daga hannunsa a gurin da take ganin su Suwaiba, sai ga wannan bararojin, tana ta zuƙar jinin Suwaiba, sannan jikin Suwaiba na ci gaba da zubar da jini ta huda-hudar nan da jikinta ya yi da ta fesa turare.

Ɗif ta daina ganinsu, ta juyo gurin ƙaisar cikin damuwa, sai dai ba ta yi magana ba.

"Kin san dalilin da ya sa na ƙyale mutumin nan, da ki ke gidansa? Wasu dalilai ne, ki gaya masa har yanzu bai san ni ba, duk hatsabibancinsa akwai sararin da bai isa ya jefe ƙafarsa ba. Na zuba masa ido ne na ga iya gudun ruwansa, amma dole sai na nuna masa iyakarsa, kuma zan gani tsakanin ni da shi waye zai yi maganin wani, kuma wannan abubuwan da yake yi miki akwai wani abu a ransa za ki ce na gaya miki "

"Mene ne a ran nasa?"

"Za ki gani, ya ce yau zai tafi da ke farauta, zai ci gaba da nuna miki magunguna. Zan ga iya ƙarshen hatsabibancinsa"

Nana ta yi sororo tana kallonsa, duk da tana son tambayarsa, amma tana tsoron ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta.

Ya ce "Wuce ki tafi"

"Ai na rasa ƙofar fita"

"Bi waccan" ya yi maganar yana nuna mata hanya. Tana fita ta ganta a tsaye a ƙofar ɗakin da take tare da sarkin baka. Yana sanye da shigar hargi(irin shigar da maharba suke yi)

Bayansa rataye da kwari da baka.

Ba ta iya musa masa ba, ko jin tsoro ko makamancin haka ba, kawai ta saka kai ta bi shi. Daga shi sai ita yana gaba tana bin sa a baya hannunsa da fitila.

Wata ƙofa suka je, ya ɗaga asabarin ya shiga, Nana ma ta bi bayansa. Suna shiga ƙofar ta gansu a dokar daji.

Sai a lokacin jikin Nana ya hau rawa, tsoro ya kama ta, ta ja da baya ta domin koma amma ta ga babu ƙofar da suka shigo.

Ya kalle ta ya ce "Kar ki tsorata, babu abin da zan yi miki, bari na ɗaure dajin"

"Ina ne nan?" Tayi maganar cikin tsoro.

"Dajin igbele ne, na jihar delta"

Ta waro ido cikin kiɗima ta ce "Delta kuma? Daga Kanon mu ka zo delta?"

Sarki ya ce "Eh, wata kububuwa nake son kamawa zan yi magani da dafinta. Daji ne mai haɗari ana tsafi iri iri a dajin, amma da na kama Kububuwar za mu tafi" ya yi maganar yana haɗa wuta a gurin, ya zuba wani turare yana kewaye wutar. Ita dai Nana ta yi shiru tana kallonsa.

Sai da ya gama sannan ya yi gaba, ta bi bayansa.

Gurin wani dutse suka nufa, daidai jikin dutsen akwai wani kogo, ya ajiye fitilarsa ya watsa wani abu a bakin kogon. Ya ciro wata raga a cikin sanhonsa ya kafa a gurin. Nana tana tsaye tana kallon ikon Allah.

Ya gama ya ce "Mu je wani dajin na nuna miki wasu abubuwan"

Al'ajabi ya hana Nana magana, suna tafe yana nuna mata wasu tsirran yana gaya mata amfaninsu.

"Kin ga idan ki ka samu kashin giwa, da hauren toronta, wato namijin giwa, da kashin ungulu, ki ka haɗa su da kaucin kuka, da tazargade da garin ganyen kuka, da ganyen magarya arba'in ki haɗa jan miski, a haɗe su guri guda. Idan aka yi hayaƙin su, duk wani ƙaramin shaiɗani sai ya gudu, ke babban ma sai ya sha wahala wallahi, kuma aljani sai dai ya ganki ya bar ki"

Nana ta dube shi ta ce "To ta yaya mutum zai samu wannan abun, duk sai mutum ya yi wannan wahalar? Najasar dabbobi ce za ta hana aljanu shafarsa? Bayan ga azkar da Alqur'ani"

Sarkin baka ya yi murmushi, yana son ƙi faɗin Nana ƙwarin gwiwar ta na burge shi ya ce "Hala ke da Ƙaisar yake tare da ke, ba kya azkar da karatun Alqur'ani"

Cikin damuwa ta ce "Ina yi mana, amma wasu lokutan idan ban yi ba na fi zama lafiya ma, na fara tsorata kar hakan ya sanya imanina ya yi rauni".

Ya yi murmushi ya ce "Magani fa ba ƙarya ba ne ba, kin yarda bature ya baki maganin ciwon kai ki sha ki warke, wannan ba shirka ba ce ko, wannan technology ku ke wa ko?" Sai kuma ta ɗan yi shiru.

Ja ya yi ya tsaya, ita ma ta tsaya, hasken wuta ta hango daga nesa, a hankali suka ƙarasa daf da gurin, suka tsaya, amma su na iya hango komai.

Mutane ne tsirara sai ɗaurin ƙyalle ja a ƙugunsu, maza da mata su na kewaye wuta kowa da ɗan ƙoƙo a hannunsa.

Wani mutum a tsakiya yana ta karanta wasu abubuwa, gefe wata mata a kwance ba ta ko motsi da tsohon ciki a jikinta. Ta ga mutumin nan ya nufi kan matar da wata wuƙa a hannunsa yana karanto wasu abubuwan.

Razana ta yi, za ta ƙwala ihu sai kuma ta daina ganinsu, ta ga sun koma dajin da sarkin baka ya yi wa kububuwa tarko.

"Idan muka tsaya, ki ka ci gaba da gani,  za ki iya rasa hankalinki"

Jikin Nana na tsuma ta ce "Su suka kashe matar?"

Ya jinjina kai ya ce "Eh, jaririn cikinta za su cire, jininsa za su sha, ƴan ƙungiyar asiri ne. Nan da ki ka gansu manyan mutane ne, da suka sadaukar da lahirar su domin duniya. Akwai 'yan kasuwa a cikin su, da 'yan siyasa"

Jikin Nana sai tsuma yake yi, ba ta taɓa tunanin da gaske akwai ƙungiyar asiri ba, ta zata shaci faɗi ne  kawai ake faɗa.

"Bari mu koma ki kwanta, da asuba zan dawo na kama macijiyar nan, naga duk a tsorace ki ke . Sai dai ina son mu yi wata magana da ke".

Jiki a sanyaye ta ce "Wace irin magana ce?"

"Ina son ki sadaukar mini da uban duƙusa wato ƙaisar, na din ga aiki da shi!"

Littafin nan 1k ne a telegram ta wannan account ɗin

0069685771

Aisha Adam

Stanbic ibtc

Sai shaidar biya ta

Ayshercool

08081012143

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807

BUZU

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

YOTA/002

P14

Cikin hanzari Nana ta ce "Na yarda na amince, na bar maka shi"

"Ai ba da baki kawai za ki faɗa ba, akwai buƙatar yin wani aiki, idan kin amince za ki sadaukar mini da shi, za ku rabu har abada"

"Eh na amince"

Sarkin baka ya ce "Za mu ƙarasa maganar da safe"

Kawai ta gansu a ƙofar ɗakinta, suka yi sallama ta shiga ta kwanta. Sai dai jikinta na ta tsuma da tunanin wace matar aka kashe, kuma ake ƙoƙarin cin zarafin gawarta haka.

"Hmmm za ki sadaukar wa wani ni ko? Har kin yi sabo da shi haka kin yarda shi?" Ta ji maganar ƙaisar a tsakanin zuciyarta da ƙwaƙwalwarta.

"Eh zan sadaukar da kai, muddin hakan zai sama mini lafiya da nutsuwa" ta yi maganar a fili. Dariyarsa kawai ta din ga ji, gidan baki ɗaya yana amsa kuwwa.

Bayan ta yi sallar asuba, ta zauna tana azkar bayan ta idar, ta yi shiru tana tunani, addu'a ta din ga yi Allah ya rabata da ƙaisar, muddin abin da sarkin baka zai sakata bai saɓa wa Allah ba, za ta yi domin ta rabu da ƙaisar.

Da kanta take zuwa gurin Sarkin baka yanzu, duk ta san hanyoyi a gidan.

Kuma ganin ta samu sassauci daga takurar ƙaisar, da sanya mata cututtuka da sauran damuwowi ga abinci tana samu babu mai takura mata da damuwa, ga kuma sukulle da kyautatawar da sarkin baka yake yi mata, sai ta fara sakin jiki da mantawa da damuwar da take ciki.

Abin mamaki, yau da Alqur'ani ta tarar da sarkin baka, bugun warshi yana karantawa, sai da ya idar sannan suka gaisa suka fita.

Sai da suka fara zuwa gurin da ake harhaɗa masa magunguna, har da injin niƙa a gurin, shi ma ma'aikatan gurin daban, ga tarin saiwoyi da tsirrai.

Gaggaisawa ya yi da masu aikin gurin, ya ce "An kawo saiwoyin nan kuwa?" Ya yi maganar yana kallon Salamatu.

Salamatu ta ce "A'a sarki, ta rafi ake jira, ba ta kawo ba"

"Aljanar nan akwai sheɗainiya, idan ta bari na nemo wani ya ɗebo mini, wallahi sai ta ɗanɗan kuɗarta" Nana ta kalle shi ta ce "Aljana kuma?"

"Eh, wasu saiwoyin ai sai dai aljani ya ɗebo, ba dai mutum ba. Akwai abubuwan da a cikin ruwa muke ɗebo su, kuma akwai dai-dai lokacin da muke ɗibar su, idan ba aljani ba sai dai ka nemi masunta, su kuma idan ba su ga dama ba, ba za su baka ainihin abin mai kyau ba" Yana gama yi wa Nana bayani, ya ci gaba da maganar sa.

"Akwai masu shanyewar ɓarin jiki, mutum biyu Salamatu a je a duba, idan na aljanu ne, a jira ni ki ba su taimakon gaggawa. Idan kuma na larura ne maza a haɗa musu magani, a ɗauki ɓawon kwakwa, da sassaƙen zogale, da zoɓo da ɓawon abarba, a dafa su sosai, a ƙara ruwa, a din ga basu kofi ɗaya sau uku rana. Ba cin man gyaɗa, ba cin gishiri ba cin kanwa, uzairu ya yi musu ƙaho zan zo na ga jikin nasu" cikin girmamawa ta ce "To sarki"

Tun Nana tana mamakin al'amuran sarkin baka, har ta zuba wa sarautar Allah ido kawai

Amma duk da haka, Nana ta kan kasa jurewa sai ta tambayi wasu abubuwan, yanzun ma ɗan gyaran murya ta yi ta ce "Sarki, su wannan magungunan da ka ke bayarwa haka da ka, ba ka tunanin ya yi wa mara lafiya illa, a asibiti akwai maganin da idan mutum yana da wani ciwon fa ba a ba shi, ku kuma nan ba tantancewa ku ke yi ba, kuma ba auna maganin ku ke yi ba"

Ya gyara zaman sanhonsa ya ce "Ban da sharri irin naki, da kuma abu irin naku na 'yan boko aƙida, da ku ke cewa maganin hausa ba shi da awo, ba yanzu a kunnen ki na faɗi gwargwadon abin da za a ba su ba? Wanda ya sani fa ya sani Asma'u, wanda bai sani ba bai sani ba, galibi gurin masu neman na Abinci kawai ake zuwa, wani koya ya yi amma ba a koya masa maganin yadda yake ba, dan ba kowa ne yake yarda ya bayar da sirrin sa ba. Ni na gada kuma na koya. Bature ya yi nasa ban raina masa ba, kuma nima na yi nawa ba wanda ya isa ya raina mini. Ke shaida ce duk abin da ba ni da maganinsa ina gaya wa mutane. Kuma ni ba dan neman kuɗi nake bayar da magani ba. Ki din ga tambayata abin da ba ki gane ba zan yi miki bayani, amma muddin na ji kushen abin da nake yi, ba zan ba ki amsa ba, kuma kin yi wa kanki, dan ba ki san a ina abubuwan da ki ka koya a gurina, za su iya amfanar ki ba, ko su amfani wani ba" jin sa kawai Nana take yi, tana ganin me za ta amfani wani da wannan abubuwan da babu scientific proof ko research a kan su.

Bayan sun gama da nan suka tafi ɓangaren da ba ta taɓa zuwa ba a gidan.

Shi kuma garke garke ne na dabbobin dawa da na gida, wani abin ma ba ta taɓa ganinsa ba.

Ya din ga nuna mata dabbobin, da magungunan da ake yi da wasu sassa na jikinsu.

Yana cikin yi mata bayani, ta ga ya yi shiru ya daina magana, ta leƙa fuskarsa za ta yi magana kawai ta ga ƙwayar idonsa ta koma baƙa gaba ɗaya, jikinsa ya hau tsuma.

Cikin sanhonsa ya zira hannu, sai ga shi ya fito da wani shirgegen zaka, ya gaji da riƙa cerarsa jawur da ita.

Jiki na tsuma Sarkin baka ya saka hannu ya raba kan zakaran da gangar jikinsa.

Ya ɗaga gangar jikin, ya tsiyaye jinin a bakinsa, ya gama ya hau cin gangar jikin zakaran a ɗanyensa da gashinsa da komai yana zazzaro ido.

Ihu Nana ta saka tana karkarwa, ta juya za ta kasa da gudu, kawai ta ganta a jikin Salamatu tana shafa mata wani abu.

Nana ta juya ta ga ba ta ga Sarkin baka ba, sai ita da Salamatu a ɗakin.

Salamatu ta ce "Nana zamanki a gidan nan, ya ci ace kin daina tsorata a mafarki, ki koyi dakiya garin tsoron nan wataran za ki iya zaucewa fa. Shi ya sa Sarki yake nuna miki wasu abubuwan domin ki saba ki rage tsoro"

Ajiyar zuciya kawai Nana take yi, cike da tsoron abin da ta gani da ta kasa tuna mafarki ne ko kuma gaske.

***

Gaddafi na zaune a rumfar mai shayi, yana jiran a dafa masa noodles da ƙwai ya ci.

Babu tsammani sai ga jami'an tsaro sun dira a gurin, tare da Imran.

Imran ya nuna Gaddafi aka kama shi, cikin mamaki Gaddafi yake tambayar ba'asin abin da ya faru, amma ba su gaya masa ba suka tafi da shi.

Sai da su ka je charge office, sannan aka ce Imran ya faɗi abin da ya kawo ƙarar Gaddafi a kai.

Imran ya ce "Yallaɓai, ƙanwata ya ɗauka suka haɗa kai da yayar babanmu, aka kai ta wani guri wai neman magani. Kusan sati guda kenan na yi na yi, su gaya mini ina suka kai ta sun ƙi, kuma ita kaɗai aka baro a gurin babu ɗan jinya".

Cikin mamaki da takaici Gaddafi ya ce "Amma ka cika mara mutunci, me ya hana ka saka a kama da Baban, sai ni zaka saka a kama, bayan tare muka kai ta".

Imran ya ce "Eh wannan ai ubana

15 / 18