Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DAFIN ZUCIYA Karyayyun Zukata By Fatima Binta Hussain

Author :  Fatima Binta Hussain Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 8

15K to 18K   out of 22.4K words

yace ai ta kare a cinya.



Malam yace ayimata ɗure. mai gyara yana yana kama ƙafa "Ladid taita ihu tana zage zage abin dariya abin kuka 'su "Ladidi harda fitsari tana zagin me gyara


Me gyara yana ma Malam bayani yace gaskiya ta bugu sosai zanada sati ɗaya zai dawo ya diba 'ya bata wasu magunguna.



Amira baƙaramin tashi hankalinmu yayi ba bamu san abinda yake faruwaba ? sai da naji umma, nace wa wai ai nafara bin maza naji maganan wani kala don bansan sanda na fara kukaba shima Amir kuka yakeyi'


Shima kanshi abbi baiji dadin maganan ba amma ya yarda da yaranshi dari bisa dari amma ba zai yarda da wanan iskancin na Umma ba abin yafara yawa' abbi yace ma Umma kada ki ƙaracema yarana masu bin maza.


Abbi ya juyu wajina yana taimbayata waye yaje inda nike sana'a jiya da yau ?nace walahi Abbi ban san shiba kuma ka tambaye wa'inda ke wajan ga Amir nan ma ka tambayeshi' ban ƙarasa magana ba Umma ta bugamin wani katako a kai nan na faɗi a sume' cikin tashin hankali Amir da Abbi sukayo kaina Abbi ya daukeni har yakai bakin ƙofa ya dawo yace walahi wani abu ya sameta abakin auren ke kuma ki tafi gida saina ne meki.




Hankalin Umma ya tashi don bata taɓa tunanin Abbi zai mata hakaba sai kuma ta kama dana sani


Ai dama dana sani keyace



Eshan an mai kiran gaggawa ya tafi port harcourt aiki kamar zaiyi hauka haka yatafi bayan ya isa yakira Abudul yace don Allah ka dinga kulamin dasu Amira kafin na dawo kana zuwa wajansu' bayan sun gama waya da Abudul yakira dan unguwan su Amira yaki tamabayan shi yasu Amira Abbas yace ai yanzu Abbi ya fito na ita daga gida kaman ba rai wata ƙara Eshan yayi



Please share and comment fisabilila


DAFIN ZUCIYA

✏️By Fatima Binta Hussain✏️

https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Assalamualaikum sister's Ykk Dan Allah ku yi haƙuri zan can za ma littafin suna saboda ku san mu biyar muke rubuta littafin kuma duka sunan book din iri d'aya hakan ya sa na mai da shi
DAFIN ZUCIYA na gode ku taya ni share



Kada mu taɓa tunanin don mun cuci wani muna jin dad'i ko kuma kayiwa mutum abu yace ma Allah ya isa kana da hankali kuwa duk abin da a kace Allah an gama komai dan Allah muyi koƙari mu sauke haƙin da ke kanmu


Bisimilahi Rahamanir Rahimin


Page 22



"Eshan hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba haka ya ƙara kiran Abdul ya faɗa mashi abin da yake faruwa yace dan Allah ya taimaka mai ya je unguwarmu ya taimbaya wani asibiti aka kaini sai yaje ya duba ni.






Shi ma Abudul hankalin shi ya tashi dan shima mun ba shi tausayi kuma bugu da ƙari ya kula da yarda Abokin shi kuma ɗan uwan shi yake son Amira.




"Ladidi Kam ƙafa nata samun sauki don yanzu kunburin ya sace.



Amma saboda rashin tawakali "Ladidi ta daura ma amarya laifi' wai ai itace ta ja mata.


Amarya' kam dariya abin ya bata don ta lura "Ladidi tana naɗe' tabarmar kunya da hauka ne.




Abbi kai tsaye asabiti nathenal hospital' ya wuce da "Amira in da Amir yake ta kuka Abbi abubuwa sun haɗe mai ga halin da nake ciki ga kukan Amir'


Abbi ji yayi kamar ya fasa kuka shima ko ya samu sauƙin abin da ke mai yawo a zuciya.




Yana isa aka dauraata kan gadon mara lafiya a kawuce da ita in da za'a bata taimakon gaggawa.




Yusurah yauma zaune take kamar kullum tana abin da ta saba tunanin wanda bai ma san tana yi ba gashi kullum sai ta tura mai messages kusan sau uku a rana tun tana turawa ta ɓoye number har ta koma da nomal number ga shi bai mai do mata da amasa.



Ammie tana cin abinci taji gabanta ya faɗi ta dafa ƙirji tace "ya Allah me yake shirin faruwa da ni ne?


"Wannan wace kalar ƙaddarace kullum hankalinta a tashi' tana roƙon Allah ya bata ikon cinye ƙaddarar ta.




Umma ko mai ta tuna sai kawai tayi murmushi ta tashi ta haɗa kayanta tace ma Yaranta" idan sun ga dare Abbi Bai dawoba su rufe gidan da yake Yaran sun ɗan
girma dan ɗayan ya kusa Amir da" to" suka amsa mata suna kuka tace kar su damu za ta dawo.



Har Umma ta fara tafiya ta tuna kwana biyu basu haɗu da Ladidi ba ta koma ta tafi gidan su Ladidi ta na zuwa ta yi salama kamar ta Allah Amarya ta gani a waje tana shanya suka gaisa Nan ta tamabaye?





Ladidi Amarya tace "tana ɗaki ba ta da lafiya "subuhanal" in ji Umma tana shiga cikin ɗakin.




Asibiti.Likitoci sun samu numfashin Amira ya dawo amma wani tashin hankali' ta manta komai da kowa ta koma kamar jaririya hankalin likitoci a tashe suka fito suka faɗa ma Abbi shi kan shi sai da yayi kuka sosai Amir kam faɗuwa yayi ganin y'r uwarshi ba ta gane shi ba.




Wanine Dr Habib ya ɗau ke shi cike da tausaya
wa ya tafi office dinshi dashi.



Ladidi tana ganin Umma ta hau washi baki ta na cewa "yau ke ce a gidan nan sanu da zuwa" Turuss Umma tayi ganin Ladidi a zaune ƙafa duk bandeji




Abdul yana zuwa unguwar ya kira wanda yayi musu bincike yace ko yasan asibitin da Abbi ya kaini Abbas yace bari ya kira Abbi yakira Abbi ya faɗa masu sunan asibitin suka tafi suna zuwa Abbi yayi masu iso



Bayan sun shiga ɗakin Abdul ya kale ni cikie da tausayawa yace "Amira ya jikin? jin shuru yana kalona kafin yayi magana Abbi ya ce ta samu matsalan k'wakwalwa saboda rud'ewa sai da Abudul ya tashi tsaye.


Kuma a dai -dai nan kiran "Eshan ya shigo wayan shi



Please share and comment ❤️❤️❤️



DAFIN ZUCIYA


✏️By Fatima Binta Hussain✏️

https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8





*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Yan' uwa fatan anyi Jumma'a lafiya Allah ya maimaitamana kar a manata da salatin Annabi Allah ya amsa ibadunmu Amin




Bisimilahi Rahamanur Rahimin


Page 23




Umma ta ida shiga ɗakin Ladidi Umma tace me zan gani haka me ya faru?


Ladid tace ke dai zauna kisha labari Umma ta zauna Ladidi ta faɗa mata duk abinda ya faru


Umma tace kan bala'i kuma kika barta Ladidi tace to ai inanan zan dau fansa dan walahi bazan hakura ba



Ammie zuwa yanzu hankalin ta ya kasa kwanciya dan tabbas da abinda yake faruwa da yaranta dan hankalinta ya kasa kwanciya ta yanke shawaran kiran abbi taji lafiyar yaran ta?



Abudul ganin yarda hankalin shi yatashi kuma ga kira yana shigo wa wayan shi ya kasa ɗaga yasa likita ya kamshi ya zaunar da shi ga kiran Eshan yana ta shigowa ya kasa ɗagawa ganin kiran na yawa yasa ya kashi wayan.





Umma tace nima ina cikin yar damuwa bada yawaba amma zan kawo karshin Ladidi tace me ya faru Umma tace warcan shigiyar yarinyar ce Kalil yace ya ganta da wani wajin sana'a nan Umma tafaɗa ma Ladid abin da ya faru.




Ladidi tace ai dama ta mutu kowa ya huta Umma tace ai ko w haka taji jiki.



Ladidi tace to yanzu tafiya zakiyi Umma tace zan tafi can garin mu wajan bokan ruwa can zanji aikin shi kamar yan kan wuƙa wajin shi zanji yayi min maganin kowa har shi kanshi Abbin zai gane.




Eshan hankalin shi ya kasa kwanciya don bai taɓa kiran Abudul yayi mai haka ba anya ba da abin da yake faruwa ba?


Yana cikin wanan tunani
Ahmad ya shago offic din shi yanata sallama bai jiba saida Ahmad ya taɓashi nan ya ɗago ya kale shi yace Abokina ina cikin damuwa bansan me ya same Amira ba?




Amira ya maimaita cike da mamaki yana kallon Abokin shin yace wacece Amira kuma nidai ban san ka da wata mace ba?




Eshan yace dama nace maka idan nadawo zan baka labari Abudul yace inajin ka nan Eshan ya kwashi komai ya faɗa mashi Ahmad ma yayi mamaki sosai kuma yaji tausayin Amira da Amir.




Amira Kam ta rasa gane wace ce ita? dan ko sunan ta bazata iya tunawa ba ita gani taki bata san kowa ba amma tana ƙoƙarin tuna wani abun sai ta kasa.



Mom tana ta murna saura kwana goma a gama azumi ko ta samu taje wajan dan tana jin haushi yarda yusurah ma bata damu da itaba da ta fara mata magana sai ta fara mata wa'azi gashi kuma tace ita yanzu bata son Eshan ita kuma Mom ta dage dole sai Yusurah ta aure shi ko zatayi yawo bakaya.



Nikam nace wahala bata ƙare maki ba



Amir bayan ya farka daga bacci Dr Habib yasa shi yaci abinci yashi magani.


Amir yace zai ji wajin Amira Dr Habib ya rakashi yana shiga ya ruga wajin Amira ta Kama kanta kamar zata yi magana.


Please share and comment.



*DAFIN ZUCIYA*


✏️By Fatima Binta Hussain ✏️



https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️






Ƴan uwa mu dinga yafiya



Bisimilahi Rahamanur Rahimin


Page 24

★★★


Umma sun rabu da Ladidi akan idanta ta samu sauƙi za taje wajen bokan Ladidin da kanta.

Daga nan Umman na fita daga gidan Ladidin kai tsaye inda zata hau motar garinsu ta nufa.





Abbi kam hankalin sa ya kasa kwanciya gashi ya rasa yanda zai yi ya faɗa ma Ammi shin idan ta sani wani hali zata shiga? wanne kallo kuma zata yi masa.?




Abudul kuwa dan ya kwantar ma da Eshan hankalinsa yasa shi ya ƙira shi yana ƙira ɗaya ya ɗaga. Yana ɗagawa ya fara tambayan shi ya Amira wani hali take ciki?


Abudul yace "kwantar da hankalin ka tana lafiya ta samu bacci"



Ajiyar zuciya Eshan yayi yace.
"To ya ƙarfin jiki?."




Wani ɗan numfashi Abudul yayi kafin yace "Alhamdulilahi taji sauƙi sosai So ka kwantar da hankalinka In Sha ALLAH babu abinda zai faru."




Aliyu Haydar yau dai haka nan yaji yana son yau ya maida ma me ƙiran amsa yana so yaji wacece wanan meyasa takiyi yi mai wanan message?.



Yusurah tana zaune taji shigowan saƙo tana dubawa taga number'n Aliyu Haidar ce. Dan haka gaban ta yana faɗuwa ta duba taga an rubuta wacece ke? Meye dalilin ki na ƙirana?...




Wani murmushi Yusurah ta saki tare da gyara kwanciyarta ta rubuta masa zaka sani ne amma ba yanzu ba.




Umma ta isa Garin Zamfara lafiya kai tsaye gidan su ta wuce.



Tana zuwa mahaifiyarta ta tmbayeta me yake faruwa ta ganta haka?


Daya ke Umman halin Mahaifiyar ta ta ɗauko bata ɓata loƙaci ba ta faɗa ma ta abinda ya faru.






Amma mai makon tayi mata nasiha sai ta ƙara zugata.



Amira tana so ta tuna wani abu amma ta ka sa.


Amir ce wa yake "Dan Allah ƴar Uwata karki ce kin man tani karkice baki san ni ba! Haka yake ta sambatu kamar wanda baya cikin haiyacin shi.





Ganin hakan yasa Dr. Habib yazo ya kama shi ya fita dashi yana bashi haƙuri.



Amira suna fita ta fashe da kuka tana tausayin kanta bata san me ya same ta ba amma ita tanajin ta manta wasu abubuwa masu mahimmanci ne a cikin rayuwarta.







Abbi Yana cikin tunanin ta yarda zai sanar ma Ammi dai-dai loƙacin ƙiran Ammin ke shigowa wayarsa. Wani kalan muguwar buga yaji zuciyarsa tayi yana kasa ɗaga ƙiran kai tsaye.



Ammi kam ganin bai ɗaga ƙiran ba yasa ta ƙara ɗaga hankalinta, hakan yana nuna mata cewar da abinda yake faruwa kenan lallai akwai abinda yake faruwa kenan?




Sai da tayi ƙira uku kafin Abbi ya ɗaga jiki a matuƙar sanyaye.




Ammi na ganin ya ɗaga ƙiran ta fesar da wani numfashi kafin a hankali tace "Ya yara na fatan suna lafiya dan haka kawai naji jikina na bani da abinda yake faruwa dasu ka faɗa min suna lafiya ko akasin hakan?



Ɗan sharce gumin daya feso masa Abbi yayi kafin yayi ƙarfin halin furta. "Haba Aisha babu ko gaisuwa sai a kama tambayan yara kuma?"




Sai loƙacin Ammin ta tuna da cewar basu gaisa ba. duk da Abbi Yana ɓoye damuwan shi sai da Ammi ta gane tace "Ina yarana?" Haka kawia Abbi ya samu kanshi da ce ma ta suna lafiya kai tsaye tace "Ka haɗani dasu to!" Kai tsaye yace da ita "Bana gida idan na koma zan haɗa ku"






Haka sukayi sallama ba don Ammi ta yarda da abinda Abbi ya faɗa mata ba.




Eshan wani mafarki yayi wanda ya tada mai hankali a firgice ya tashi bakinsa ɗauke da addu'a sai kawai ya tashi ya shiga bayi ya yi alwala ya dawo ya tada sallah, sai da yayi raka'a takwas sanan ya dakata kafin yayi addu'a sosai wanda wayan cin addu'ar akan Amira ce yayi ta.




Ladidi kuwa tana ta samun sauƙi a hankali gobe za a kwance ƙafar ma .





Amarya kam tana abinda ya dace dan ita tace batayi yi ma Ladidi abin da take mata ba idan tayi abinci tana bata.



Eshan bayan ya gama sallah ya koma ya kwanta amma bacci ya ka sa zuwa.



Please share and comment

*BY Fatima Binta Hussain ☑️*






DAFIN ZUCIYA



✏️By Fatima Binta Hussain✏️


https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




Page 25
✨✨✨




Eshan tunda safe ya ya shirya koma wa Abuja saboda ta taho saida yagama shirin shi.



Ogan shi ya kiyashi yace yayi hakuri da tafi akwai wani aiki mai mahimmanci babu yadda ya iya haka ya haƙura.






Ladidi yau an kwance ƙafa amma ance ta fara tafiya da sanda



Amma dan bala'i ganin babu kowa agidan Mijin su ya fita aiki ita kuma Amarya taje kunshi



Haka yasa Ladidi ta kama hanyar gidan boka tana cikin tafiya tayi nisa cikin tunani har batasan tana Tsakiyar titi ba



Sai dai taji anyi sama da ita




Abbi tunda sukayi waya da Ammi sai hankalinsa ya ƙara tashi shi da kanshi yasan be ma Ammi adalci ba




Abudul yana cikin damuwa dawowar Eshan dan harga Allah shi baya son yazo yaga halin da amira take ciki amma bai da yarda zaiyi




Yana cikin tunanin sai ga kiran Eshan bayan ya ɗaga suka gaisa Eshan yake mai bayani game da aikin da ya hanashi dawowa




Ladidi wani me adai dai ta sahu ne ya bigita kuma shi bada sani yayi ba yanata mata hon amma bata jiba




Kuma birkin shi yaki yai aiki ganin ya bige wata mata yasa shi fitowa cikin tashin hankali


Yana taimabayan ta bataji cewo ba tace eh


Yace ta hau ya kaita inda zata tace takusa zuwa ya barshi



Ladidi har ga Allah tana jin zafi Bama kamar ƙafarta da aka gyara amma baza ta iya fasa zuwa wajin boka ba





Amira tana cikin kuka Abudul ya shigo tana ganin shi ta kama kanta sai tayi kamar zata tuna wani abun sai ta ka sa



Likitan da yake kula da ita ganin haka yace idan tana wanan abun insha Allah zata iya dawo wa dai-dai a kowani lukaci




Abbi bai san abinda yake faruwa ba dan yaji ya duba Umma da yaran ta ta tafi ko ta barsu



Yana zuwa gidan yaga a kule amma da alamar mutum a ciki gidan hakan yasa bugawa



Ladidi tana tafiya tana hutawa har ta isa gidan boka


Tana shiga yaita binta da wani mayen kallo


Bayan sun gaisa yace nasan me yake tafe dake amma ki sani wanan lukacin bani zan yi aiki da keba Aljani tugudidi ne zaiyi amfani dake kuma ta baya zai ne meki

Ladidi tayi shuru tana tunanin yanzu da Aljani zata kwanta anya zata iya kuwa





Abin yana tsaye yaji anacewa waye yace shine jin Muryar shi yasa yaran suka ɓude kofan ya shiga




Abbi ya tambaye yaran ina Umma cikin rashin tarbiya babban yace baka koritaba kuma zakazo kana tambayan mu




Akam Abbi ya Kama yaron da duka sai da yayi mai dukan tsiya sanan ya barshi




Cikin ƙunar zuciya abbi ya fara magana ba zan dau rashin tarbiyar da uwar ku take koya makuba saina gyara maku zama



Hankali Ammi fa ya kasa kwanciya ta yanke shawarar tafiya Abuja bada sanin kowaba



Please share and comment


BY FATIMA BINTU HUSSEIN✨✨✨

















https://chat.whatsapp.com/Gvh8Kfitxaw0Qwme0hezcZ


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page 26



Bisimilahi Rahamanur Rahimin

"Ladidi ganin tana so burinta ya cika ya sa ta amincema Boka.



Abinda bata ba Al'jani ne zai sadu da itaba Boka ne zai' sadu da ita.





Amira Kam ta ƙara zama abin tausayi dan yanzuma ko abinci bata ci aita fama da ita bata iya yin komai sai kuka.





Hakan ya ƙarasa Abbi da Amir cikin matsananciyar damuwa.




Umma tunda suke tafiya cikin dajin basuga kowa ba sunyi tafiya sosai kafin suka isa wata buka da ke saman wani tsauni.






Shi kuma wanan Bokan ƙa'idar shi shene a shiga da tsalan kwadi.




Suna shiga wani kalan ɗoyi ya bugi hancin su da sauri Umma ta tushi hancin ta sabuda wanan warin.



Wata gigitarciyar tsawa aka daka masu ana cewa


"ku la ananu ku suwaye da zaku shigo Fadar Ƙanin Sheɗan kuna tushi hanci to ku koma inda kuka fito kun ɓatama Sarki rai.





Eshan koda suka gama waya da Abudul.


Mame ya kira ya "faɗa mata bazai samu zuwa gida sallah ba wani aiki ya riƙe shi Mame tayi mashi addu'a sosai daga nan sukayi sallama.




Ya kira Abba shima suka gaisa shima ya faɗa mashi abinda ya riƙe shi.



Yau har Farha sai da ya kira suka gaisa take tambayan shi Yaya yashi zaka dawo ce sai bayan sallah zai dawo yana da aiki ne shiyasa.





Yana jin dadi a duk lukacin da yake cikin family nashi ko sukayi

6 / 8