Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

JININ JIKINA Sirrin Tsakaninmu By Maman Noorul Hudah

Author :  Maman Noorul Hudah Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 13

15K to 18K   out of 36.1K words

yayi kara,yana dubawa ya gan Abbansu ne

Kashewa yayi gaba d'aya ya saka aljihu

Kiran ammi yayi amma bata d'aga ba

Kafin ya kira ismat ta kashe nata wayar

Ummi tace"ki tashe shi samhat"

D'an taba kafanshi tayi sai ya bude ido,wanda dama ba barci yayi ba duk abinda ya faru ya ji

Bude ido yayi ya kalli ummi.sai kawai tausayinta ya kamashi

Amir yace"ya jikin bro?"

Cikin karfin hali yace"da sauki"

Amir ne ya taimaka me yayi sallah magrib a zaune yayi

Shima yaje masallaci yayi nashi sallah

Ya dawo,a lokacin duk sun gama sallah suma"

Ummi tace"Amir ka kai hanifa gida kai ma kaje ka huta tunda yau ka dawo"

Yace"ke kije ummi ki huta ni zan kwana dashi"

Tace"no kaje kawai,ismat kema kije kawai sai gobe kin ji"

Samhat a ranta tace"ni fa banji ance in wuce ba"

Shima kallon samhat yakeyi domin yana jiran abinda zata ce, amma sai yaji tayi shiru

Amir yace"toh malama hanifa muje ko?"

Tace"eh muje"

Har ismat zata wuce,cikin dakiya samhat tace"ismat bari nima in zo ki saukeni a gida "

Amar a ranshi yace"da bakiyi magana ba da an canja miki suna"

Ummi tace"no daughter a nan zamu kwana banza iya zama ni kadai ba shiyasa na taho miki da kaya sai kiyi wanka a nan

Ranta beso ba amma babu inda ta iya tace"toh ummi"

Bangaren su hanifa ko suna fita a harabar hospital din

Direct inda ya paka mota suka je, ya bude mata ta shiga

Shima ya zaga ya shiga, kallonta yayi ya sakar mata murmushi

Kau da kai tayi

Yace"hani fushi kike dani dan jiya banzo zance ba"

Zaro ido tayi ta kalleshi tace"ni? "

Yace"yes kefa,ai na gan tun d'azu kike hararata"

Tace"ni dai ba ruwana ba haka bane"

Aza hanunshi yayi a saman nata yace"toh fad'a min yaya ne?"

Tace"please ka bari yaya zaiyi fushi kuma nasan yana can yana jirana"

Hade rai yayi yace"oh ni baki gudun b'acin raina ko?"

Zatayi magana ya katse ta da cewa"ba sai kin ce komai ba nasan dama ba sona kike ba nika dai ke wahala akanki"

Jan motan yayi,itako haka kawai taji bata son b'ata mashi rai

Sai kawai ta fashe da kuka

Basarwa yayi,sai dai yana jin kukan nata har cikin zuciyanta

Ganin bata da niyar yin shiru yasa shi parking a gefen titi.ya kalleta yace"me ya same ki?"

Cikin shashsheka tace"ba kaine kayi fushi ba"

Murmushin samun nasara yayi a ranshi yace"wanan akwai yaranta ba wayau"

A fili kuma sai yace"ai dole inyi fushi tunda kin nuna baki sona"

Tace"nifa bance ba"

Yace"toh kina sona ne?"ya gama magana da d'aga mata gira

Rufe fuska tayi tana murmushi,girgiza kai yayi ya ja mota

A kofar gidansu ya paka

Har zata fita ya jawota yace"toh ai bamu gama zancen ba"

Tace"toh"

Jawota yayi ta fadi jikinshi

Yace"fadamin me yaya naki yake fada miki?"

Turo baki tayi tace"ai cewa yayi shi zai aureni"kwashe komai tayi ta fada me

Yace"toh ke kina sonshine?"

Shiru tayi,tana turo baki

Yace"ina jinki"

Tace toh ni nasan miye so ne"

Cafke bakin yayi ya fara Sosa kamar sweet

Sanda ya gaji dan kanshi ya barta

Tace"babu kyaufa"

Ko magana ya kasa yi domin yana jin wani feeling ne a kanta

Da k'yar ya dai-daita natsuwan shi

Yace"na baki nan da sati d'aya zaki fahimci menene so"

Bude motan tayi ta fita,a kofa ta tarar da anwar

Yace"

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share

πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to MY FANS.

πŸ…Ώ5⃣5⃣&5⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace "ke zo nan"

Jiki na rawa ta karasa gabanshi

Yace"daga ina kike?"

Tace"asibiti ne muka je"

Yace"waye ya dawo dake?"

Tace"yaya Amir ne"ai sai taji saukan mari

Yace "Ashe bana hanaki kula wani ba?"

Zatayi magana ya katseta da cewa kina fadin ko kalma d'aya ne zan fasa bakin nan"

Fushi tayi ta shige gida yau for the first time da ta fara barin shi tsaye

Baki sake ya bita da kallon mamaki

Yace"ikon Allah"

Niko nace yo ba dole ba,ka fiya zuciya ga saurin fushi da duka

Bayan kwana uku

Sosai Amar ya samu sauki yana iya tafiya da kanshi

Ummi ne zaune a asibiti da samhat ta zauna a dadduma ta cika tayi pam domin ta gaji da kwanciyar asibiti

Shiko ya kwanta a gado yana satan kallonta time to time

Kallon Ummi yayi yace"Ummi kije gida kawai ki huta karkiyi zazzabi kin gan tun jiya kina fama"

Ummi tace"toh wa zai zauna da kai?"

Yace"ga SAM nan kuma ai incharge na nan"

Murmushi samhat tayi a ranta tace"for the first time tsoho yayi abin kirki"

Ummi tace"waye kuma SAM?"

Kallon samhat yayi,ummi tace"ok toh samhat ki zauna dashi"

Kallonshi tayi ya sakar mata wani kayatacce murmushi

Hararanshi tayi tace"ummi in zashi toilet wa zai kai shi?'

Kafin ummi tayi magana yace"ai incharge na nan"ya kare magana da yin murmushi kasa-kasa

A ranshi yace"tsohon nan dai da baki so kiyi jinya,yau aikin shi zakiyi"

Ummi tace"karki damu daughter usman na nan zai duba shi"

Ji tayi kamar ta kurma ihu,ji tayi kamar ta shake shi gashi yau akwai show

Ummi tace"inshaallah gobe zaki koma gida"

Tace"toh ummi"

Ummi tace"toh na tafi ismat zata kawo miki abinci da wani abin bukata"

Tace"toh"

Ummi na barin d'akin ta juya ta kalleshi

Tace"sannu da ka had'a wanan abin,me zan ma"

Yace"ba komai I just want to see you suffer"

Wani ihu tayi tace"Ashe yau akwai drama domin zan koya maka hankali tsoho ba wayau kawai,in ba iskanci ba ina matar da kanin ka zai aura zaka sani gaba Dan bakin ciki kamar ni na hana ka aure, shima munafuki Amar din ya tafi ya barni ko ganin sa ban tabayi ba"

Murmushi rainin wayau yayi mata domin yana jin sanda ismat kece mata Amar yaje abuja

Masifa takeyi ta inda take shiga ba nan take fita ba

Shidai shiru yana kallonta domin shi kadai yasan irin rashin mutunci daya tanadar mata

Misalin karfe 8:pm Amir ya shigo da basket din abinci

Ganinta yayi zaune a dadduma ta hada rai

Murmushi yayi yace"amarya lafiya kuwa?"

Ko kulashi batayi ba,ta cigaba da danna wayarta

Amar yayi murmushi yace"amaryar rikici take jin yi"

Ajiye basket yayi yace"ai gomma in tafi in barku karta hada dani"

Murmushi Amar yayi yace"da yafi maka because inda ta kumbure haka zata iya explosion kamar bomb"

Har Amir ya kai kofa zai fita tace"ka zo fa ka zauna da d'an uwanka dan bazan iya ba"

Zaiyi magana Amar yace"tafi abinka oh"

Yace"ai dama"

Yana fita wayarta yayi kara,mikewa tayi tasha rawa kafin ta d'aga

Shidai kallonta yake a ranshi yace"itadai komai ta iya yanzu ta gama karatu Al-qurani kamar yar SUDAIS"

Tace"ya dai Hafiz"

A can bangare Hafiz yace"kira nayi in fada miki akwai show ba 9:pm a youth centre"

Tace"ai zan zo ka bani nan da minti 30 su stars zasu zo?"

Yace"eh"

Tace"ai irin haka be wuceni"

Yanke wayar tayi, tayi murmushi,agogo ta duba ta gan 8:40

Tace"good"tashi tayi tace"kai tsoho ga abinci in kaji yunwa zanje kallon show"

Mikewa yayi ba tare da yayi magana ba yaje ya kulle kofa ya zare key

Yace"toh sai kin dawo"

Zaro ido tayi tace"hello hy bye bye dama kana da lafiyar da zaka kulle kofa kasa ummi tasa inyi jinya ka,toh baka isa ba sai ka bude"

Yace"toh ina jira inji abinda zakiyi"

Tace"OK zamu gani domin yanzu zan danne ka in kwace"

Zuwa tayi amma kafin ta karasa ya saka key cikin wando yana dariya yace oya zo ki cire

Zama tayi ta fashe da kuka

Yace"wait har kin fara kukan ne tun dare beyi ba ai alkawari nayi baza kiyi barci yau ba "

Tace"mugu kawai"

Yace"yes nine"

Kwanciya yayi ya fara barci hankaki kwance

Itama gajiya tayi da kuka har barci ya d'auketa

Da misalin karfe 12:30am

Ku bari nima inyi barci da wuri saboda in farka in d'auko muku ruhoto yau aikin dare zanyi

Hello hy bye bye🀣

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to my fans

πŸ…Ώ5⃣7⃣&5⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Da misalin karfe 12:30am

Amar ya farka daga barci,tashi yayi ya zauna ya kalli samhat dake barci hankali kwance ta ma manta a asibiti take

Murmushin mugunta yayi yace"yau zaki gane shayi ruwa ne domin tsoho zai addabe ki"

Tashi yayi ya d'auko basket din abinci ya gan bata ci nata ba

Budewa yayi ya zauna a kushin din dake d'akin domin special word ne babu abinda babu"

Zama yayi ya cinye shi tas harda niman kari domin wani yunwa yake ji

Tashi yayi yaje toilet ya wanke hannu ya dawo,basket din ya kalla ya gan bobo a ciki wanda ummi ta bayar a bawa samhat

Domin d'an zaman da sukayi a asibiti ta lura cikin dare samhat sai ta sha bobo take barci

Murmushi yayi yace"WOW my bobo"

D'aukawa yayi ya bude ya fara sha d'aya bayan d'aya har ya shaye gora bakwai

Rufe goronan yayi kamar ba a taba ba

Sanan yaje gabanta yana kallon fuskarta

Ya dade yana kallonta kafin ya gyra mata suman daya rufe mata fuska

Kallon karamin bakinta yayi mai tsiwa har ya kai hannu zai shafa sai ta fara juye juye

Bude idon da zatayi sai idonsu ya had'u

Kashe mata ido yayi,itako a zabure ta mike da salati a baki tana gyra dogon riganta da ya d'an sauka ana d'an ganin kirjin

Tace"hello hy bye bye me kakeyi a nan?"

Yace"hy bye bye zuwa nayi in ci mutunci ki"ya kare magana yana kallon kirjinta"

Gyrawa ta farayi tace"ni fa ban son iskanci,wanan ai iskanci ne"

Yace"ai iskanci nan da ba ki so shi zamuyi yanzu"

Zaro ido tayi tace"toh wallahi baka isa ba in kai d'an iska ne ni ba yar iska bane.kai ko kunya Baka ji ina masayin budurwan kanin zaka nima kayi iskaci dani,toh wallahi gomma in bari ka keta min haddi gomma in rasa rayuwata"

Yace"ok zamu gani"

Yi yayi kamar zai fado mata tayi sauri kaucewa

Tace"kai mugu banza karka manta da JININ JIKINA kake rayuwa dan haka
Karka kawo min iskanci"

Yace"and so ai bani nace ki bani ba,iskanci ki ne yasa kika bani,anga handsome harda wani hade bakin mu da sunan bani numfashi tir da mai hali irin naki"

Haushi maganar shi ya bata ji tayi kamar da shake shi

Cikin jin haushi tace"Baka ma gode ba na had'a bakina da dogon bakin ka,kasan maza nawa ke mutuwar son wanan bakin nawa?amma ba gan laifin ka ba domin taimakon ka nayi da na barka ka mutu da yafi min "

Zuwa yayi dab da ita yace"bakin waye dogo"

Tace"naka mana"

Ba tare da yayi magana ba ya ja zuwa toilet

Dai-dai wajen madubi ya tsaya yace"ki kalli kanki da kyau zaki san kin fini muni domin nafi ki kyau nisa ba kusa ba"

Tace"ai ba sai na kalla ba ko makawo yasan nafi ka kyau"

Zatayi magana ya hade bakinsu,musu musu ta fara tana dukan kirjin shi

Amma yaki bari ya dade yana kissing dinta har ya fita hayyacin shi

Sanda ya gaji son ranshi ya barta

Kuka ta fashe dashi tace"oh ni na hadu da tsohon d'an iska"

Shiko a ranshi yace"nayi fuck up meyasa bana iya controlling kaina in ina gaban yariyar nan yanzu ai sai ta raina ni ta d'auka sonta nike"

Hade rai yayi yace"ke miye haka kikewa mutane kuka?karki gan Dan nayi miki karamin abin nan ki d'auka sonki nike, ni bana sonki ko kadan"

Cikin kuka tace"Allah ya isa sakani na da kai mugu kawai,toh in dai wanan karamin abune a gun ka that means kanayin wanda yafi wanan"wani kuka ta kara fashewa dashi sai cewa take hello hy bye bye

Buge mata baki yayi yace"daga yau karki karamin Allah ya isa in ba haka ba zaki sha mamaki"

Kuka ta fashe dashi domin taji zafin buge mata baki da yayi

Shiko fitowa yayi ya kwanta ya barta a toilet

Bayan minti goma sai gata ta fito tana rike ciki alamun yunwa take ji

Direct gaban kula taje ta bude ga mamakinta ta gan wayam

Kallon gefenshi tayi,sai ya kau da kai

Murmushi tayi data gan goruna bobo tace"shiyasa nike sonki ummina"
Da farin ciki ta d'auka sai taji shi ba nauyi

Budewa tayi ta gan babu cikin tashi hankali ta fara bude marfin goran d'aya bayan d'aya amma empty ne

Kallon gefen shi tayi tace"kan uba yau akwai hy bye bye a dakin nan"

A fusace ta tashi ta karasa inda yake kwance ta rike kugu

Tace"

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share

πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to my niece peace

πŸ…Ώ5⃣9⃣&6⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Tace"sannu tsohon mugu abinci ka cinye dan mugunta baka tsaya a haka ba ka ka shanye min bobo,toh yau zaka gan rashin mutunci domin wallahi kowa a gidan mu yasan gomma a shanye min bobo gomma an sace min waya"

Kallonta yayi daga sama zuwa kasa yace"please let me sleep in peace domin na koshi dayawa ina bukatan hutu"

Wani ihu tayi tace"kan uba na ratse da Allah sai ka biyani bobo na dan wallahi ba yarda zanyi kuji min rainin hankali kai ka cinye abinci ka kafin kayi bacci shine dan mugunta zaka cinye min nawa,dan mugunta gaskiya ni bazan yarda ba ta kare magana tana karkada kafa

Yace"toh yanzu ya kike so inyi domin ni na d'au kin koshine shiyasa na cinye ashe zaki ci,kuma ai kema kin taba data min bobo a d'aki"

Tace"Ku ji min mugu azalumi mara imani in bada mungunta ai kai kanka kasan ina bukatar in ci abinci saboda JININ JIKINA"

Yace"toh yanzu ya kike son ayi?"

Tace"biya na zakayi ko ka amayo Wanda kaci"

Yace"toh in banji aman fa?"

Tace"wallahi sai ka amayo shi dan bazai yiwu ka ci ka koshi ka kwanta hankalin ka kwance ba,is not possible ni kuma in kwana da yunwa ba"

Yace"toh ki yi abinda zakiyi dan nidai bacci nikeji"

Yayi magana yana kokarin kwantawa

Ai jawoshi tayi har wuyan T-shirt din rigar jikin shi ya barke

Tace"na ratse mutun yayi abinda zai b'atamin rai yanzu ko zai gan ba dai-dai ba ehee nidai na fadi tun yanzu kan ran mutum ya b'ace"

Yace"toh wallahi in baki bari nayi barci ba ranki zaiyi mumunan b'aci"

Tace"wallahi sai dai ranmu amma banawa kadai ba kujimin rainin wayau "

Yace"wa ke raina miki wayau?ni sa'anki ne?"

Tace"ai wanan babu wani maganar sa'a mugunta ne kamin kuma sai na rama tsohon banza wanda baya iya sauke hakkin iyalin shi"itafa bata San ma'ana sauke hakkin iyali ba ji tayi anyi fada a mokatansu mata da miji matar tace"tsohon banza baka sauke hakki iyali shine itama yau ta fadi"

Zaro ido yayi yace"wani irin hakki kenan kike nufi"

Tace"ai kafini sani mugu kawai d'an duniya"

Yace"toh nagode amma kiyi hakuri in an mana aure zan sauke hakkin"

Tace"aure da kai dawa?ai sai dai kanin ka danni bazan aure tsoho ba"

Yace"na nawa kuma ke da kika zo har gida kika nimi aurena wajen ummina,kuma ni dai bason ki nike ba"

Tace"dama wake sonka ai cewa akayi Amar zan aura"

Yace"fool ai nine Amar"

Wani ihu tayi tace"wallahi sai dai a fasa in kaine Amar ni me zanyi da tsoho Allah kadai yasan matan da kayi ta kissing wama yasan ko kawuce gurin"

Murmushi yayi yace"wani wuri kenan?yimin bayani"

Tace"banda lokacin d'an iska irin ka"

Murmushi yayi yace"toh bari in kwanta tunda baki da lokacina"

Kwanciya zaiyi amma samhat tayi tsale ta..

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to hajiya Hamamatu

πŸ…Ώ6⃣1⃣&6⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Tsalle tayi ta haye bayan shi tace"sai mu gan ta inda zakayi barci"

Yace"oh my goodness zaki sauka ko sai na yarda ke"

Kara rike shi a wuya tayi, ta matse sanda ya tsaki kara

Tace"oh ka d'au kai kadai ka iya mugunta?"

Yace"sauka ko in baki mamaki"

Tace"babu inda zani wallahi yau bakai ba barci"

Yace"kiyi wa Allah ki bari in huta in samu barci wallahi kai na ya fara bugawa"

Tace"Allah yasa ya fashe dan rainin sense"

Mikewa yayi ya fara zagaye d'akin da ita a baya har ga Allah kanshi na ciwo

Cikin dauriya yace"SAM please kiyi hakuri wallahi iam seriously felling headache kin ji bari in kwanta you know my condition ko?"

Tace"your condition is not my problem just make me sleep"

Yace"ok "

Zagayawa ya farayi da ita,yana jin jiri

Itako wani dadi taji a bayan shi,a hankali barci ya d'auketa

Jin shiru kuma nauyinta ya karu shiyasa ya gane tayi barci

Yace"SAM!SAM!!SAM!!!

Can kasan makoshi ta amsa da uhrmmm

Ajiyar zuciya ya sauke yace"thanks goodness she is asleep "

Karasawa yayi gado ya kwantar da ita shima ya kwanta ya azata a kirjin shi ya rugunme

Kiran sallah farko ya tasar da ita daga barcinta mai dadi

A hankali ta bude idonta,jin an rungumeta yasa ta kalleshi

Barci yake hankali kwance

Tsayawa tayi tana kallon fuskarshi tace"hmmm he is handsome and cute"

Shafa sumar kanshi tayi ta lumshe ido tace"matsala guda daya ne shine shekarun shi"

Har zata taba lips dinshi ya bude ido yana murmushi

Da sauri tayi yinkurin sauka,ya jawota

Yace"repeat what you just said"

Tace"bance komai ba"

Yace"dama dai ina son in fada miki ne,dont fall for me domin ina da Wanda nike so"

Murguda baki tayi tace" hello hy bye bye go to hell kuma ina son ka sani I always do the direct opposite of what people don't want so is possible I may fall for you and if that happens you have no choice than to love me back fiye da wanda nikeyi maka"

Yace"hmnm"domin yama rasa abinda zaice dan da tasan zuciyarshi da bazata fadi hakan ba

Toilet taje ta d'auro alwala ta tada sallah

Tana idarwa ta mike ta jawo waya ta kira Hafiz abokinta

Yana d'agawa tace"ya dai Hafiz ya show din jiya?"

Hafiz yace"hmmm ai bari an sha dake ai jiya anyi bidiri,amma meya hanaki zuwa?"

Tsaki tayi tace"kadai bari wani tsoho na tsaya jinya amma yau ka kirani zan zo"

Shiko kallonta yake yana murmushin mugunta

tana
gama waya ta ajiye wayar a tebur ta mike tana wakar JININ JIKINA

Kallon wayar yayi murmushi yace"perfect"mikewa yayi ya d'auki wayar dama akwai wani ruwa a roba da cleaners sukayi using basu fitar ba

Yace"SAM kalli"
Juyowa tayi ta kalleshi

D'agawa wayar ya ya saka ruwa yana murmushi

Da gudu ta zo tace"hello hy bye bye wallahi sai ka biyani na ratse kasan ya akayi bakin mugu ya siyamin wayar ne da k'yar ammi ta tursasa shi,shine dan mugunta ka saka a ruwa wallahi sai na rama"

Wayarshi me tsada ta saka a ruwa tana huci amma still haushi take ji

Yace"toh miye na haushi ba kin rama ba?"

Tace" ai ka cuce ni ko"wayar ta samo a ruwa ta fara kokarin budewa tace"hello hy bye bye Allah yasa noban star dina na cikin sim"

A ranshi yace"oh number ya dameta yanzu zanyi maganinta"

Kwace wayar yayi ya cire sim ya karya

6 / 13