Author : Maman Noorul Hudah Category : African Stories & Novels
d'akin nan ya d'auke sai yanzu aka kawu"
Da mamaki ismat ta kalleta tace"ai ba a d'auke wuta ba tun d'azu nike kallo"
Samhat tace "toh gaskiya daga yau na daina zuwa gidan Ku "
Ismat ta kalli goruna bobo da tasha
Tace"wa yasha wanan?"
Samhat tace"ai ina ganin shi miyau na ya tsinke toh shine na kasa hakuri na sha amma wallahi ni ba barauniya bace"
Dariya ta bawa ismat tace"toh wa yace miki barauniya?amma wallahi in yaya AMAR ya kamaki kin sha me bobo hmmm zaki fuskanci rashin mutunci"
Tace"waye shi AMAR din?"
Tace"ai YAYA na ne AMAR maye bobo ne sai yasha goran bobo 10 a take"
Samhat tace"wanan tsohon?shike shan bobo"
Ismat ta rike hanunta suka bar d'akin tace"wa yace miki tsoho ne?shekaranshi fa 35 "
Wani ihu samhat tayi tace"ai tsohon ne,35 hmmm amma yaranshi sunkai biyar ko?"
Ismat tace"no beyi aure ba d'an uwanshi ne Amir shine ke da mata da yara biyu"
Suna kaiwa falo samhat ta zauna dan dama suna tafiya ne suna magana
Samhat tace"nidai gaskiya bazan iya auren Wanda ya kai 35years ba ina laifin 25 nafi son saurayi"
Bobo dake kwance a kujera gyra kwanciya yayi
Ummi ne ta sauko daga stairs din tace"sannu daughter bari a kawu miki abinci"
Tace"dam nike ummina ai ina shiga dakin nan na bude fridge na gan bobo masu sanyi gaske shine na sha ki yi hakuri ban nimi izinin ki ba"
Ummi tace"babu komai"
Samhat tace"sai dai fa ummi akwai abinda ya faru ina ciki sai wuta ya d'auke kawai sai......"
Maganar be gama fitowa ba sakamakon
Tari mai sanani da bobo ya farayi kuma yaki d'ago fuska
Da sauri ummi ta karasa tace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πππππ
JININ JIKINA
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to MAMAN NOORUL HUDAH FANS PAGE.
π
Ώ2β£5β£&2β£6β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ummi tace"sannu BOBO tashi ka zauna abin zai lafa"
Girgiza mata kai yayi yace"iam ok"Wanda maganar ta fito kasa kasa ummi kawai taji
Tace"OK sorry my son"
Yace"thanks"
Tabe baki samhat tayi tace"ummi ni zan tafi gida kafin ammi ta fara nima na"
Tace"ok ga kaya can a leda naki ne"
Zaro ido samhat tayi tace"no ummi wallahi in na kai kayan nan gida ammina zata yi fada"
Tace"ai da kaina zan zo gidan in yi ma ammi magana mun zama d'aya musaman yanzu da nike son had'a ki da"sai kuma tayi shiru
Ismat tace"ai tare zamu in San gidanku amma bari muyi sallah yanzu 3:40pm sai muje"
Ta kare magana da Jan hanun samhat zuwa d'akinta
Suna shiga ummi ta kalleshi tace"BOBO ka tashi please ka kai daughter gida in kaje ka shiga ka gaida amminta"
Gyra kwanciya yayi ba tare da yayi magana ba can anjima ya mike
Ummi tace"yauwa son je kayi sallah ka shirya kafin su fito"
Bayan su samhat sun idar da sallah wani kwaliya ta sake yi
Tayi kyau ismat sai yaba kyaunta take
Tace"gaskiya zaki sa ayi ta hatsari a titi"
Dariya tayi tace"hmmm shiyasa nike so in auri under 25 saboda mu mori juna"
Ismat da ta rasa mai zata ce sai kwai tayi ajiyar zuciya tace"hmmmm"
Samhat tace"muje na shirya "
Suna fita suka tarar da ummi na sallah a falo jira sukayi ta idar
Babu inda ummi batayi ba akan samhat ta tafi da kayan amma taki
Ummi tace"kuje Ku jira son yanzu zai fito"
Ismat tace"toh"
A wajen motar shi suka tsaya samhat ta jingina da motar tana ta zuba surutu
Bayan minti goma taji an ja motar wanda yayi sanadiyar fadiwarta
Tace"hello hy bye bye kashe ni za a yi"
Ismat da dariya ya ci karfinta domin basu tab'a tunani yana ciki ba
Kuma yanayin fadiwar samhat ya bata dariya
Da k'yar samhat ta mike tace"waye ya min wanan muguntan?'
Ismat tace"wallahi yaya bobo ne, ya gaji da jiran mu shiga shine ya ja yayi tafiyar shi bari kawai insa driver ya kaimu"
Tace"na ratse da Allah sai na rama wanan abinda yayi min"
Driver ne ya kaisu har gida a lokacin har hankali Ammi ya gama tashi tasa anwar ya nimo ta
Ammi na ganin ta tace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πππππ
JININ JIKINA
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to MAMAN NOORUL HUDAH FANS GROUP.
π
Ώ2β£7β£&2β£8β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ammi tace"daga ina samhat?"
Samhat tace"ammi dan Allah ki yi hakuri naje wani gidane"
Hanifa tace"nima dai nace ammi ta kwantar da hankalin ta ai bazaki b'ata ba amma tabi tasawa kanta damuwa"
Anwar da shigowar shi kenan yace"ai ammi na abune kamar bata San halin samhat ba ita tasan inda ka aiki samhat ba nan take zuwa ba"
Kallonshi samhat tayi ta murguda me baki tace"hello by bye bye"
Buge bakin ammi tayi,da sauri ta rufe tace"yi hakuri ammi na daina kinji kiyi hakuri wallahi naje gidansu wanan ne"ta kare magana da nuna ismat dake ta kallon Anwar tunda ya shigo
Shiko ko kulata beyi ba
Har kasa ta sunguna ta gaida Ammi
Sanan ta gaida anwar dake ta wani basarwa
Sosai ammi tayiwa samhat fada akan karta kara zuwa ko ina ba tare da izininta
Ismat ma sai hakuri take bata
Kafin suka shigar da ita daki
Samhat ta d'auko musu shinkafa da mai da yaji
Suka ci hanifa ta kalli ismat tace"Ashe kina ci?"
Tace"me zai hana?"
Tace"naga Ku yan gayu ne masu kudi"
Murmushi tayi tace"babu abinda banci"
Ta dade a gidan kafin ta sallamesu
Da dare misalin sha d'ayan dare samhat ne kwance ta kasa barci sai juyi take
Tunanin abinda ya faru a gidansu ummi ke dawo mata
A ranta tace"toh wanene wanan ya zo ya rungumeni harda kiss?hmmm koma waye inaji a jikina ya hadu kuma yana da class.ga kamshin shi da dadi nidai ina son shi"
Wani zuciyar tace mata kinsan ko aljani ne?"
A fili tace"hmmm kuma fa abin yayi kama da hakan domin yana zuwa wutan ya d'auke kuma daya wuce wutan ya dawo kenan aljani ne,ya Allah karka d'auramin abinda yafi karfina"
Hanifa ta juyo tace"lafiya kina ta magana ke kadai?"
Tace"ai na hadu da dream man dina"
Tashi hanifa tayi ta zauna tace"a ina?"
Murmushi tayi tace"a gidansu ismat"
Hanifa tace"ya yake gista ni"
Tace"taya zan gista ki bayan ni kaina banga fuskarshi ba"
Tsaki hanifa tayi tace"taya kuka hadu?"
Samhat tace"zan gista ki amma ba yau ba,ya labarin wanan saurayin naki?"
Tsaki hanifa tayi tace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πππππ
JININ JIKINA
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to my fans
Na fa lura mutane kalikan keyin comment da sharhi sauran daga stickers sai txs in Baku so is beta in daina wahalal da kaina
Yan groups dina namarasa ya zanyi daku gaskiya zan fara shara
π
Ώ2β£9β£&3β£0β£
Bismillahir Rahmanir rahim
Hanifa tace"ai yaya ya koreshi kuma yace dana gama secondary school in cewa ammi zanyi aure,sai a mana aure in daina kula maza"
Samhat tace"toh ke kina sonshi ne?"
Hanifa tace"toh ni ina nasan manene so kawai dai zan aure shi"
Samhat tace"ai na dade da sanin yana sonki shiyasa komai hanifa ki so shi kawai hanifa dan shine abinda zamuyi dan nunawa ammi hallaci domin soyayarta a gare mu"
Tace"hakane ko bana sonshi zan danne"
Washe gari samhat ta tashi da Mura mai karfi har muryata be fita
Ammi tace"fadi gaskiya yar'nan ki sha abu mai sanyi ko?"
Tace"wallahi ammi bobo 8 ne kawai nasha mai sanyi a gidansu ismat"
Ammi tace"ai kin kyauta kin san fa jikin ki be so abu mai sanyi shine zaki sha ko?"
Tace"yi hakuri"
Ammi tace"toh sai ki fadi sunan maganin da za a siyo miki kisha"
Zatayi magana wayarta tayi kara tana dubawa ta gan ismat ce
D'agawa tayi tace"ya dai "tayi magana cikin sigan marasa lafiya"
Ismat tace"ya dai?naji muryar ki wani iri"
Tace"eh wallahi banjin dadi ne"
Ismat tace"dama ummine tace"in kira ki ko zaki zo taji kewar ki,ga ta kuyi magana"
Ummi tace"daughter ya kike"
Samhat taja majina tace"lafiya ummina"
Tace"ya haka"
Tace"wallahi zazzabi ke damuna"
Ummi tace"aiko gani nan zuwa in gan daughter na "
Murmushi samhat tayi tace"sai kin zo"
Yanke wayar tayi tare da kallon BOBO da kanshi ke saman cinyarta tace"kaji wai daughter ba lafiya"
Lumshe ido yayi ba tare da yayi magana ba
Amir yace"ummi wai wacece wanan daughter ne"
Murmushi tayi tace"eh mata na samo ma BOBO"
Ai mikewa yayi yace"what?"
Tace"yes ita zaka aura"
Ismat tace"yaya Amir baka ganta bane she is very beautiful but she talks alot sha,but bata karya"
Murmushi Amir yayi yace"wow perfect match kin gan tunda BoBo mun baya magana ai zata koya me"
Ismat zatayi magana ya daka mata sawa da cewa"my friend will you keep quiet?"
Shiru tayi ya kalli ummi yace"ummi please stop it before it get worst "
Tace"wallahi in kana son ganin farin cikina toh ka so samhat domin tana da tarbiya ina ganin ta nasan she is the one for you Amar bazan bari a lalata ma rayuwa ba kamar inda akayiwa d'an uwanka Amir"
Amir yace"ni kadai nasan abinda nike going through da wacce akuyar da Abba ya aura min wai mata"
Yace"ai ni bazan yarda a min auren dole ba I will get married when iam ready but not now"ya kare magana dasa takalmin shi ya bar falo
Ummi tace"zamu gani ko ni na haifeka ko kuma kai ka haifeni"
Amir yace"ummi mu bishi a hankali ni bansan meyasa kwata kwata baya son maganan aure ba"
Cikin b'acin rai ummi tace"wallahi this time around bazaiyi escaping ba cause na gaji shi ba yaro bane,kwata kwata twins brother ka beda tunanin"
Nace"twins kuma?sai yanzu na lura da kamaninsu gaskiya ummi na kokari wajen gane su"
Ummi tace"tashi muje gidansu zanyiwa amminta magana ina so ayi bikin nan da kankanin lokaci kafi abbanku ya dawo ina son ya dawo ya tarar dashi da matarshi dan bazan yarda ya aura me wanan yar'iskan yariya ba salma"
Amir yace"hakan yafi domin babu alkhairi tattare da ita gashi nima ina fama da wanan kairat din"
Ismat tace"ni har ban son Abba ya dawo"
Ummi tace"muje amir ka ji"
Wanene BOBO?
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls sha re
πππππ
JININ JIKINA
πππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to my fans groups
π
Ώ3β£1β£&3β£2β£
Mai karatu natsu ka karanta wanan page din domin shine labarin
Bismillahir Rahmanir Rahim
Dr Hassan shamsudeen Yusuf shine asalin sunan shi su uku iyayensu suka Haifa maza biyu mace d'aya
Su yan biyu ne shida husaininshi Amma anfi kiransu da Amir da Amar
Sai dai kuma a gida anfi kiranshi da BoBo
Bayan haihuwarsu sanda ummi tayi shekara 15 kafin ta haifi ismat
Shamsudeen Yusufu shine mahaifinsu da mahaifiyarsu hajiya hindatu
Alhaji shamsudeen d'an ne ga alhaji Yusuf mai rago
Alhaji Yusuf ya kasance yana da mata biyu Aisha da halima
Halima itace uwargida ta dade bata samu haihuwa ba hakan yasa ya kara aure ya auro Aisha
Aisha na zuwa ko shekara batayi ba ta haiho d'an namiji
Ba karamin farin ciki yayi ba da haihuwar da akayi me sai dai haka besa ya wulakanta halima ba kuma baya bari Aisha ta wulakantata
Hakan beyiwa Aisha dadi ba domin taso ne tayi ta kuntatawa halima sai dai kash bata gan fuska ba
Ranar suna yaro yaci shamsudeen
Halima na matukar son shamsudeen sai dai Aisha bata bari halima ta d'aukeshi
Hakan yasa halima kama kanta
Ga gorin safe daban na rana daban
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Aisha tayi haihuwa uku maza biyu mace d'aya
Sosai duniya tayiwa halima zafi domin zaman gidan na niman gagaranta
Domin da Yusuf yasa kafa ya fita kasuwa wajen sana'an dabbobin shi toh Aisha zata fara yiwa halima gorin haihuwa
Sai dai ta shiga daki ta ci kuka
Cikin ikon Allah da addu'oi kwasam sai ga ciki ya bayyana a jikin halima a lokacin shamsudeen nada shekara goma
Babu inda Aisha bata shiga ba dan a zubar da cikin halima amma hakan ta gagara
Cikin so da kulawa yusuf ke kula da halima
Domin yana bala'in ji da cikin nan
Bayan wata tara ta haihu d'anta namiji ya ci suna Mohammed
Yusuf na bala'in son Mohammed domin kap ya'yan shi yafi son shi
Hakan da yake nunawa shi ya haddasawa Aisha bakin ciki da mugun kudiri da kuma haddasa babu abinda take burin kamar ta gan wani abu ya same Mohammed
Sai kawai ta shiga biye-biye bokaye da b'atawa ya'yanta tarbiya domin kwata-kwata basu da tarbiya
Babu kamar shamsu da ta Riga ta cusa me kiyayya d'an uwanshi kwata-kwata ya tsane Mohammed ko kadan bata son ganin shi cikin walwala
Mohammed Nada shekara goma jinya mai sanani ya kama halima ta dade kwance kafin rai yayi halinshi
Wanda dasa hanun Aisha
Sosai mutuwar halima ya girgiza Yusuf da mutanan garin domin macece mai hakuri da juriya
Bayan rasuwar halima gidan ya zamewa Mohammed wuta domin dashi da almajiri ko ince bawa babu banbaci domin Aisha ta mallake Yusuf kome tayiwa Mohammed baya magana
Harta tukan tuwo,dibo ruwa wanki da wani aiki duk shi keyi sai dai in baya nan zainab yar Aisha ta taya shi a boye domin tana tausayin shi
Sosai rayuwa ta yi me zafi
Domin wani lokaci sai yayi kwana uku baici abinci ba
Sai dai makota su bashi
Haka fa rayuwa ta cigaba da tafiya inda duk yaran gidan na boko amma shi baya zuwa
Mohammed Nada shekara ashirin ya fara buge buge niman hallak babu aikin da bayayi
Kasuwa yake zuwa yana kwasan kaya a Biro a biyashi amma daya dawo zata kwace kudin
Yana da shekara ashirin da biyu Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa
Wanda mutuwan ya girgiza Mohammed domin shi kadai yake gani ya ji dadi
Shamsu ko har ya gama jami'a a Nigeria yayi karatu sai dai shi ya taso da mugun zuciya da kuma son abin duniya Wanda zai iyayin komai dan cikan burin shi
Sosai Mohammed ke wahala yana kaiwa Aisha kudin
Yana da shekara 23
Wata rana yana kwace a zauren gidan domim nan ne d'akin shi yaji jama'a sun shigo gidan
Sai cewa"ina munafukin yaron b'arawo"
Kafin ya mike an rufeshi da duka cikin rashin sanin abinda yayi yace"me nayi muku?"
Sai suka ce mun samu labari kai kake zuwa gonakin mutane kana sata
Yace"wallahi bani bane"
Suka ce"yi shiru munafuki da ne muke tausayama amma ba yanzu ba"
Duka suka me sosai wanda sunki su saurare shi kuma sahun b'arawo ya taka domin shamsu ne yayi satar bayan ya dawo shine Aisha ta tura shi ta hanyar sanan ta kira wani ya je ya gan shi
Shine suka biyo shi
Sosai Aisha ta ji dadi domin babu Wanda zaiyi zarginsu ne kuma ganin Mohammed a bakin ciki yana sata nishadi
Shiko an had'a me jini da majina
Ya shiga cikin gida ya ji tana cewa"ai kaga gomma da mukayi me sharri yanzu masu tausaya me suna ganin muna kuntata me zasu daina"
Hawaye ne ya gangaro me ya d'anga labulen ya shiga yace"tabbas burin ki ya cika amma daga yau na bar miki gidan Ku kuma bazan taba yafe muku kazafin da kuka min ba kuma inshaallahu zaku gan sakkaya"
Shamsu ne ya tureshi ya fadi har kasa
Mikewa yayi ya bar gidan
Zuwa yayi ya kwashi ajiyar da yakeyi a boye da abinda zai bukata ya bar gidan
Motan dake shigo da raguna Nigeria ya biyo inda suka sauka a Maiduguri
Sosai Mohammed ke niman na kanshi babu aikin da beyi ba kama daga shoe shiner wanki da guga da tura Biro
Wanda kirkin shi da rikon amana shi ya hadashi da wani hamshakin mai kudi
Ya fara zama me a shagon turaruka ya zama yaron aikin shi yana biyarshi duk wata dubu 15 Wanda Mohammed ya tara kudi
Bayan wasu shekaru yayiwa alhaji sani magana akan shima yana son bude nashi shagon na kanshi
Ba karamin dadi ya ji ba yace"nawa kake dashi?"
Yace"dubu dari"
Yace"toh zan kara maka"
Godiya yayi me alhaji sani yace"karka damu halinka ya jawo hakan wallahi da ina da ya'mace dana baka"
Yayi murmushi yace"wanan ma nagode"
Sosai abubuwa suka fara canzawa domin ya bude shago kuma ba laifi yana samun kasuwa
Bangaren shamsu ko bayan Mohammed ya bar gari ya tattari inashi inashi ya bar gari ya dawo Nigeria
Shima ya fara niman aiki har Allah ya bashi under kamfanin wani minister alhaji bala
Sosai shamsu ke yiwa bala duk wani dirty work
Hakan yasa alhaji bala ke sonshi
A cikin kankanin lokaci yayi kudi har ya auri wata hindatu Wanda ba wani halinshi ta sani ba kawai ta amince domin ya zo mata mutumim kirki
Haihuwar farko shine ta haiho Amir da Amar
Sai ismat
Shiko Mohammed bayan ya kafa kanshi yasan zai iya tsayawa da kafafun shi ya fara niman mata
Amma dayawan mutane basa son bashi domin ba asan asalin shi ba
A gidan marayun da yake kai musu taimako ya hadu da saratu har ya aureta yar shekara 17 wanda gidan marayu sinta ta akayi tun tana da shekara biyu sunyi cigiya gidan radio da tv station amma babu Wanda ya zo yayi claiming nata harta girma
Haihuwar farko itama yan biyu ne sai kanne su mata biyu
Sosai shamsu ya zama mai kudi sai dai baya kaunar talaka komai nashi ya dawo Nigeria
Allah yayiwa kanin shi rasuwa basiru shi da kanwar shi sakina suka rage wanda tafi ta harkanshi kuma tana aure a nijar
Mahaifiyarshi ne keme shige shige dan niman tsari
Building company yake dashi yana amsar kwangila a gomnanti domin in ba an fada ba ba a sanin shi ba d'an Nigeria bane
Zai iya yin komai dan ya samu kwangila shiyasa ya had'a Amir aure da kairat yar senator ya so a had'a bikin dana Amar (Bobo)da wata yar minister salma amma Amar yaki kasancewar yasan halin Amar yasa shi bawa minister hakuri akan a kara me lokaci domin salma tace"sai Amar in bata aurashi ba zata kashe kanta"
Salma bata da tarbiya ko kadan tana da wani saurayi musician jibrin amma anfi sanin shi da jb shima d'an minister ne baya jin magana ko kadan
Kwanaki yayiwa wata yariya fyde ya kasheta
Wanda yanzu case din na hanun barrister hussaini shamsudeen Yusuf (Amir)
Ummi ta fara gajiya da halin mijin nata domin ya fara using yaran for his own selfish games na niman contract
Shiyasa ma ta baro abuja zuwa minna da zama domin kwata kwata ba jin dadin zama da shi tana dai jurewa ne dan darajar ya'yan dake tsakanisu
Hajiya hindatu (ummi) ya'ce ga alhaji sanusi mai dala baban ta Sana'a canji kudi yake
Watoh bureau de change
Mata biyu yake dashi safiya da zinat
Safiya nada ya'ya uku duk mata kuma ita ce uwargida
Hindatu da rukkaya sai maryam
Ita kuma zinat yara biyar duk maza itace amarya
Kasancewar ita safiya tun bayar