Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

JININ JIKINA Sirrin Tsakaninmu By Maman Noorul Hudah

Author :  Maman Noorul Hudah Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 13

9K to 12K   out of 36.1K words

haihuwan maryam haihuwa ya tsaya mata

Hakan yasa zinat ta fara ganin ita wata ce

Ta fara yiwa safiya gori wai ita ke da gida domin yaranta maza ne

(Mata muyi ta kiyaye abinda ke fita a bakin mu

So what in yaranki mazane?

Yawanci iyaye mata sun kashe zuciyoyi ya'yan su maza da maganar gado domin tun suna kanana suke ji ana fadin sune da gida

Hakan zai sa su taso babu zuciyar niman na Kansu domin suna ganin in mahaifinsu ya mutu suna da komai
Wanda kwata-kwata be kamata ba

Because babu komai a gado domin bata dadewa

Mu kiyaye please)

Safiya ko kulata batayi ba saima cusawa ya'yanta niman na Kansu

Alhaji sunusi mai dala asalin d'an Nigeria ne Adamawa to be pricise amma kasuwanci ya kaishi Cameroon

Allah ya jarabbeshi da son maryam domin duk ya'yanshi yafi sonta

Tunda aka haifeta duk wani kadara da tsiye sunanta ne akai

Hakan yasa zinat fara tsanata domin a ganinta ai ita keda yara maza daya kamata a mallaka musu komai shine dan cin fuska za a dinga saka sunan yar yariya da bata fi shekaro biyu ba

Ba tare da dogon tunani ba tasa wata kawarta hajiya dake shigowa Nigeria sace maryam

Tace"ki yi nisa da ita inda babu Wanda zai zargin tana wajen"

Hajiya binta tace"ai karki damu nasan inda zan kaita"

Nigeria hajiya binta ta kawota bayan zinat ta biya ta kudi masu yawa

A kofar orphanage din Maiduguri ta ajiyeta har worker suka sinceta

Kasancewar basu San sunanta ba kuma bata da wayau kir-kir yasa suka Samata suna saratu

Ba karamin kuka safiya tayi ba da b'ata maryam har ya haddasa mata hawan jini

Bayan wasu shekaru Allah ya tona asirin zinat ta sanadiyar fada da tayi da hajiya binta

Hajiya binta ta tona mata asiri domin tasan sirrinta

Harda na duk ya'yanta babu na alhaji sunusi ciki na samarinta ne

A station aka tursasa musu fadin inda suka kai maryam

binta ta fada sai dai ko da akaje maidugurin an tabbatar musu maryam ta rasu da ya'yanta

Ta sanadiyan rashin tsaro garin

Domin bayan barin ammi dasu samhat yan gari sun d'au kashesu akayi domin washe garin ranan ba karami kisa akayi ba

Sanadiyan abinda ya faru yasa alhaji sunusi tattaro iyalanshi bayan ya saki zinat suka dawo Nigeria a abuja suke zama

Nan ya bawa yaranshi mata biyu tarbiya da karatu mai zurfi

Inda hindatu ta zama Dr ita kuma rukkaya lecturer ce a university of abuja

Har yanzu sun kasa mantawa da mutuwar maryam domin abin yafi damun su da suka San tayi aure harda yara kuma duk sun rasu

Wanan shine kadan daga cikin tarihin ummi da Abba

Amar cikkeken likita ne da ake ji dashi a Nigeria ya bude asibiti a nan minna mai suna Amar specialist kuma yana dashi a abuja

Shikuma amir lawyer ne mai tashe da taimakon talakawa

Kwata-kwata BOBO da jb basu shiri domin BOBO ya taba wanka me mari a public

Saboda ya so yayi misbehave da ismat lokacin suna abuja

Hakan yasa jb rantsewa da inda har yana numfashi toh sai ya hana yan biyu zaman lafiya
Domin bayan mari da Amar yayi me Amir ya amsa case na yariyar da ya kashe kuma yasa ana bincike

Jb yarone da iyayenshi suka b'ata shi kuma babu Allah a zuciyarshi

Hmmm

Bobo dogo ne fari Sol kyakyawa ne ajin farko domin ya kai da a kiranshi da namiji ta kowani fanni

Miskili ne domin in baya gan dama ba sai ya wuni beyi magana ba

Shi babu Wanda ya isa yasa shi abu sai yayi niya kuma sai ummi kadai amma ko Abba baya sauraron shi

Basama shiri kasancewar ya tsane hallayen abban nashi ko kadan basa shiri

Kamarsu d'aya da Amir sai dai suna da babbanci ra'ayi

Amir Nada mata da ya guda matarshi kairat

Bata da hankali da tunani ga rashin tarbiya

Hakan yasa yake shirin kara aure a ra'ayin shi yafi son mace yar 18yrs

Amar shi mutum ne da baka gane meya keso ga shegen girman kai

Bari in barku a nan nasan yanzu kusan inda labarin ya dusa

Toh ga samhat ga BOBO ga jb ga kuma salmat yar minister

Ga kuma hanifa ga Amir da matarshi kairat da kuma anwar


Ga Abba ga senator bala da yayi sanadiyar kudinshi

Ga kuma samhat da jb keso

Shin samhat zata so BOBO koda bayan aurene in ta gane mahainshine yayiwa mahaifinta kazafi sata da kuma zancen mahaifiyar Abba Aisha ita ta kashe kakarsu halima?

Shin zata yafewa Abba in ta gane ummi yayar mahaifiyata ne zata hakura ta zauna da Amar?

Wani mataki jb zai d'auka in ya gane samhat yake so zata auri Amar makiyinshi?

Ya anwar zaiyi in hanifa ta nuna bata sonshi?

Ku biyoni dan jin ya zata karke

Nice maman
Noorul hudah


Sai na gan comment da zai girgiza group zan tsaki sauran labarin

Bana son sticker just comment da sharhi

In kinsan bazakiyi comment ba ki hakura kawai ki bawa masuyi wuri

Domin shine karfin guiwan mu

Real fans masu comment tanks alot

Muje zuwa
Let go thereπŸ˜€

Hello hy bye
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to my WONDERFUL MOM

πŸ…Ώ3⃣3⃣&3⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yanzu AMAR da Amir suna da shekara 35

Ismat kuma ashirin

Wanan kenan

Cigaban labari

Shiryawa ummi tayi Amir ya kaisu gidansu samhat tare da taimakon kwatancen ismat

A kofar gidan suka sauka yace"in sun gama su kirashi ya dawo ya d'auke su

Bayan su ummi sun shiga ciki ya juya kan motar shi dan komawa gida

Hanifa ne a hanya tana takowa da kayan makaranta duk yunwa ta dame ta domin yau takowa tayi anwar be je ya d'auketa ba domin aiki ya me yawa

Bata lura da motar dake fitowa daga lungun gidansu ba domin sauri take

Kawai sai taji anja birki mota kiiiiiiiiiiii

A tsorace ta kalli motar da sauran kiris ya kwasheta Wanda sab'an rudewa garin kwacewa ta fadi kasa

Jikinta sai rawa yake

Shiko Amir ganinta zube a kasa yasa shi fitowa karasawa yayi yace"ina fatan dai baki ci ciwo ba?"

Ba tare da tayi magana ba ta girgiza mishi kai alamun a'ah

Hanunta ya kama dan taimakata ta tashi

Jin hanunshi jikinta yasata d'agowa ta kalleshi

Idonsu na haduwa sukayi pause babu Wanda ya iya kwakwaran motsi

Sun dade a haka kafin ta fisge hanunta tace"na..
.go..de"

Yace" wow what a nice voice"yayi magana tare da mikar da ita

Murmushi tayi tace"thanks tana magana tana kokarin ratsashi

Yace"wait"

Cak ta tsaya

Yace"toh ya sunan ki?"

Cikn yaranta tace"ai yaya ya hanani kula maza yace shi zai aure ni"

Amir ya zaro ido yace"toh yaushe za ayi auren?"

Tace"ni dai yunwa nikeji na tafi gida"ta yi tafiyarta ta barshi tsaye

Binta yayi da kallo a ranshi yace"exactly my type"

Bangaren su ummi ko


Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to my GROUPS

πŸ…Ώ3⃣5⃣&3⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Bangaren su ummi ko tarba mai kyau Ammi tayi musu ba karamin dadi ummi taji ba da irin sakin fuska da karamci da suka samu a wurin ammi

Ummi tace"ni sunana hajiya hindatu na hadu da yar'ki a hanya shekaran jiya haka kawai naji ta shiga raina

Murmushi ammi tayi tace"Allah sarki ai itama yar'ki ne ai samhat akwai shiga rai"

Ummi tayi murmushi tace"ashe zaki bani ita d'an na ya aura kenan?"

Murmushi Ammi tayi ba tare da tayi magana ba

Ummi tace"nifa ba wasa nike ba"

Ammi tace"bari in kirata ai kunfi kusa"

Ummi tace"OK nasan ma baza ta ki ba"

Ismat ko dadi take ji yayarta zai auri samhat

Cikin jin dadi tace"ammi ina hanifa?"

Kafin ammi tayi magana hanifa ta shigo da sallama

Ummi da tun shigowar hanifa take kallonta

Gaishesu hanifa tayi ummi ta amsa

Hanifa tace"Ammi yunwa nikeji yau yaya be zo ya d'aukeni ba"

Ammi tace"je kicin abincin ki na nan"

Tace"yau ammi har wani dishi dishi nike gani"

Ammi tace"mutum sai shegen cin tsiya"

Hanifa da ke kai loma d'an wake tace"ai gomma in ci shiyasa nafi yar'ki karfi mai shan BOBO"

Ummi ta karbe zancen da cewa"ai da gaskiyarki ya'ta ai bobo ba abinci bane"

Ammi tace"tarun dangin za ayiwa ya'ta"

Ummi tace"aini dukan su biyu zan kwace"

Jagora Ammi tayi musu zuwa d'akin su samhat

Kwance take tana jin jiki zazzabi ya rufeta sai nishi take sama sama

Ganin halin da take yasa ummi karasawa tace"subhanaallah daughter meya same ki haka "

Ammi tace"ai sanyi da ta sha a gidan Ku shi ya haifar da haka"

Ummi tace"iam so sorry ai bansan nimonia petient bane dana hanata sha"

Ammi tace "ai samhat bata jin magana"

Ammi tace"wani magani ta sha?"

Samhat cikin maganar marasa lafiya tace"yanzu nayiwa kaina allura inshaah zai lafa"

Ummi tace"OK"

Kallon ammi tayi tace"ki fada min inda za aje niman auren samhat saboda in tura magabatan Amar"

Gaban samhat ne ya fadi tace"Amar kuma waye shi? Kuma ai banda niyar aure yanzu"

Ammi ko da ta d'au wasa ummi keyi d'azun da tace a bata samhat d'anta ya aura da mamaki ta kalli ummi

Tace"aure kuma?"

Tace"yes ai bana son abin ya wuce nan da sati biyu"

Ammi tace"shi d'an naki yana son samhat ne?"

Ammi tace"karki damu ai samhat bazata wahala ba amma muje waje muyi magana"

Fita sukayi a d'akin zuwa sakar gida

Ummi ta kalli ammi ta

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Wanan na kane MU'AZ

πŸ…Ώ3⃣7⃣&3⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Suna fitowa ummi ta kama hanun Ammi tace"yar'uwa na zo ne ki taimakeni ki bani auren samhat d'an na ya aura ki rufamin asiri kema sai Allah ya rufa miki domin na yaba da hankali samhat shiyasa bana son d'an na ya rasata"

Ammi zatayi magana ummi tace"dan Allah karki ce a'ah"tana magana tana kokarin durkusawa ammi

Ammi ta rukota kafin ta kai kasa tace"miye haka hajiya"

Ummi tace"please ki amince"

Cikin sanyin jiki ammi tace"ni bani da tacewa sai abinda samhat ta yanke in tana so ai zan amince kasancewar bani da wata buri da ya wuce in gansu cikin farin ciki domin marayu ne nine na zame musu uwa da yan uwa"

Ummi tace"kina nufin ba ke kika haifesu ba?"

Ammi tace"eh bani na haifesu ba hasalima bani da dangi dasu amma munyi zaman mutunci da iyayensu wanda mahaifinta ba karamin taimakon mu yayi a baya"labarin komai ammi ta bata sosai ta tausaya musu wanda ta karajin soyyaya yaran a zuciyarta har take jin da anyi auren su samhat da BOBO zata nimawa Amir auren hanifa

Bangaren su samhat ko su ammi na fita ta d'ago da k'yar ta kalli ismat tace"waye Amar kuma ya yake da shekarunshi"

Ismat da ta fuskanci samhat bata gane BOBO shine Amar ba

Tace"kanin su yaya BOBO ne ni ke binshi shekaran shi 25" domin samhat ta fada mata bata son wanda yafi 25years

Samhat tace"yi min kwatancen shi da aikinshi"

Ismat tayi murmushi tace"fari ne yana da tsayi ga farfadan kirji"kwantata mata yaya BOBO tayi ta kare da cewa"Dr ne"

Samhat tace"wow,amma yace yana sona ne?"

Ismat tace"eh mana shi ya takura mu wai ashe ya ganki randa kika zo lokacin da zaki kai BOBO d'akin"

Samhat tayi shiru tana tunani a ranta tace"kenan shine ya biyoni yayi min kiss ko dai d'an iska ne?"

Ismat tace"ya naji kinyi shiru?"

Tace"a'ah babu komai toh ina wanan BOBO naku wallahi ko na aure kanin shi sai nayi me rashin mutunci"

Ismat tace"yana nan amma be kamata ki rike yayan mijin ki a zuciya ba"

Tace"hello hy bye bye sai dai in fasa auren mijin amma sai na rama"

Ismat a ranta tace"hmmm tirkashi"

Su ammi ne suka shigo

Ummi tace"dear ya jikin?"

Samhat tace"da sauki"

Ummi ta zauna kusa da ita ta rike hanunta tace"ina niman alfarma a gunki daughter"

Samhat tace"ki bani umurni kawai ummina inshaallah zan zama me miki biyyaya"

Cikin jin dadin maganarta ummi tace"toh nagode ina so ki auri d'ana Amar"

Samhat zatayi magana ummi tace"umurni ne nasan na is a dake ne"

Shiru tayi ta dukar da kai tana wasa da yatsan hannayenta

Ummi tace"nagode ya'ta domin shirun ki ya tabbatatmin kin d'aukeni a matsayin uwa a gareki"

Ummi tace"ammi ki yiwa makocin naku magana gobe zan turo tunda kin ce shi ke musu komai kuma yasa ayi bincike"

Ammi da abin mamaki yake bata tace"toh amma a kara mana lokaci"

Ummi tace"karki damu kudi ba matsala bane"

Babu inda ta iya tayi shiru

Sun dade a gidan wanda ummi ta saki jiki dasu har d'an waken ta ci

Hakan yasa Ammi ta kara sakin jiki da ita

Kafin ta kira Amir ya zo ya d'auke su

A kofar gida ya tsaya ya kirasu

Ummi tace"hanifa ba za ayi mana raki'a bane?"

Hanifa tace"bari insa hijab

Ammi zata musu rakiya ummi tayi saurin cewa"a'ah yi zaman ki kar a barmin daughter ita kadai"

Ammi tace"toh a gaida gida"

Tace"zasu ji"

A zaune a saman mota suka tarar da Amir

Ummi na ganin shi ta washe baki tace"Amir sannu da zuwa"

Amir da yayi nisa wajen kallon hanifa ko keftawa bayayi yace"yauwa ummi"yayi magana ba tare da ya kalleta ba

Dadi taji a zuciyarta kar dai Amir son hanifa yake?

Ummi tace"hanifa je Ku gaisa da yayan ki"

Hanifa da duk kunya ya lullubeta tayi murmushin karfin hali tare da cewa "ina yini yaya"

Shima murmushi yayi yace...

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Wanan nakane 80k

πŸ…Ώ3⃣9⃣&4⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"lafiya lau yar kanwata"

Murmushi tayi ummi tace"hanifa yaushe zaki zo gidanmu?"

Tace"zanzo inshaallah in mu gama waec next week"

Kafin ummi tayi magana Amir yace"zan zo in kaiki"

Tace"ah'a yaya zai kawoni"

Wani haushi ya dibeshi yace"ah'a ni zanzo in kaiki ai besan wuri ba"

Kafin tayi magana Anwar ya dawo a mashin

Wani fadiwar gaba yaji ganin hanifa nayiwa Amir murmushi

Gashi yalura da irin kallon da yake jefa mata

Idansu na haduwa ya harareta da gudu ta shige ciki ta bar Amir tsaye

Ismat ne ta washe baki ta kalleshi tace"sannu da dawowa yaya anwar"

Fuska ba walwala yace"yauwa"ya shige gida

Tabe baki Amir yayi a ranshi yace"karya kakeyi"

Ummi dake zaune a mota da dadewa tace"toh Ku shigo mu tafi mana"

Shiga sukayi Amir yaja mota

A mota sai hira suke wanda rabi tsara bikin su samhat ne

Ummi tace"kayiwa d'an uwanka magana ya kwantar da hankalin shi ayi bikin nan kafin mahaifinku ya dawo ya b'ata mana komai"

Ummi tace"nafi son ayi kafin wanan kakan tamu ta samu labari"

Ummi tace"inshaallah baza a samu matsala ba"

Amir yace"ai in naje zan zaunar dashi muyi maganar fahimta"

Ummi tace"da dai yafi ai gata ake mashi"

Suna kaiwa gida kowa yayi part dinshi

Da misalin karfe 8:30 Amir ne zaune da Amar suna hira

Amir yace"bro wallahi kayi sa'a mata daga gidan karamci da tarbiya"

Tsaki yayi yace"nifa ba auren ne bana so ba, nifa bana son auren karamar yariya ce kuma naji ance she is just 20 haka kawai ta zo tana min yaranta kuma nasan bazata iya d'aukan lalurata ba"

Amir yayi dariya yace"toh tsoho tuzuru masu lalura amma a ganina auren yariya mai yaranta yafi sai tayi ta zuba ma yaranta kai kuma kana kwasan gara kana fresh"

Basarwa yayi kamar beji ba

Amir yace"nasan ka jini but let be serious ya kamata kaje ka gaida amminta da ita ka mata sannu da jiki"

Yace"babu inda zani"

Amir yace"toh bari in kira ummi ka fada mata domin umurninta ne"

Yace "toh naji zani amma sai jibi"

Murmushi amir yayi yace"ai tare zamu domin nima inada mission"

BOBO be sake magana ba har Amir ya gaji da surutu ya bar me part dinshi

Bayan kwana biyu sosai samhat ta samu sauki amma da sauran zazzabin kadan

Yau take shirin zuwa wani show da dare na mawaka

Da misalin karfe 8:pm ta saci hanya ta bar gidan

Tana fita su AMAR suka zo gidan

Domin Ummi tame rashin mutunci,shiyasa ya zo

Har kasa suka sunguna suka gaida Ammi

Taburma ta shimfida musu

Gaisuwa suka mata da kyau tare da tambayar ya mai jiki tace"da sauki"

Ruwa ta kawo musu shiko Amir sai raba ido yake ya gan inda hanifa zata bullo

Shiko Amar ya sunne kai kasa

Ammi ko rasa rasa me zata ce musu tayi domin samhat bata gida

Can dai Amir yace"ina mara lafiya?"

Ammi tace"wallahi tayi barci sai dai in kunzo gobe sai Ku gaisa"

Amir yace"babu komai Ammi"

Shiko Amar a ranshi yace "kenan bata gida kenan?"

Amir yana so ya tambayi hanifa amma kunya ta hana

Can dai sai gata ta fito a d'akin Anwar domin nan suke kallo

Yana ganinta ya sakar mata murmushi

Sai ga anwar ya biyota

Hada rai Amir yayi

Amar ko ya sallami ammi

Shiko anwar wani murmushi ya sakarwa amir dake ji kamar zuciyarshi zata tawartse

Bayan sun bar gidan

Amar ne ke tuki dai-dai inda zasu fita lungu gidan sai ga samhat tsaye da wani daya rakota

Amar ne ya hangosu har ya haska musu wuta

Tsaki samhat tayi tace"hello hy bye bye kuji sabon iskanci haka kawai za wani haskawa mutum wuta"

Rai b'ace ya ja Motan da gudun bala'i

Wanda har suka kai gida babu wanda yayi magana

Washe gari sun kara zuwa da dare amma still ta fita duk da fada da ammi ta mata

Bayan kwana biyu

Yau ta kasance Monday samhat
ta shirya zuwa asibiti domin
Incharge din asibiti ne ya kira samhat wai ta zo yau oga zaiyi resuming

Shiryawa tayi ta sallami ammi

Takawa takeyi domin babu abin hawa

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
JININ JIKINA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to NANA KHADIJA KANO

Gaskiya naji dadin comment dinku ya sani nishadi harda su bobiya🀣🀣🀣🀣a cigaba da gashi suya sai ran sallah.I LUV U FANS kuyi hakuri da rashin reply kunyi yawa ne amma ina jin dadin shi
πŸ…Ώ4⃣1⃣&4⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Tafiya takeyi a gefen titi kasancewar babu abin hawa,duk keken da ta tare a cike yake da yan makaranta

Bangaren AMAR ko da safe ya shirya zuwa asibiti yana sauko falo ya tarar da ummi zaune a dining tana breakfast

Tana ganinshi tayi murmushi tace"my son zo kayi breakfast"

Murmushi yayi yace"good morning mum"

Tace"morning my son how was your nite?"

Yace"fantastic"

Tace"zauna mana"

Yace"no sauri Nike cause na makara kuma Amir yace in biya chanchaga in amsa mishi files"

Tace"shi Amir din ina yake"

Yace"ya tafi Abuja tun da asuba"

Tace"shine ba sallama?toh Allah ya kiyaye hanya"

Amar yace" zai kira ki a waya,mum ni dai na wuce sai na dawo"

Tace"take care"

Yace"I will mum"

Da kanshi yaja mota har ya bar gida

A chanchaga ya karbi sako a hanyar komawa shi office ne

Ya samu wani mugun hatsari dai-dai city gate domin wani motar tanka ne ya sha gabanshi kafin yace"zaiyi wani abu it

4 / 13