Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kanwar MAZA 1&2 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   91 / 128

270K to 273K   out of 382K words

ba ?aramin burge iman yayi ba.

Sai da mai sunan baba ya fita, sannan iman ta samu ta tafi.

Rumaisa da yaya usy ta keSe, suna magana.

"Yaya yaushe za ka zo, akwai labari fa?"

Usman ya ce "Labarin me?".

"Ni dai kawai ka zo dan girman Allah"

Ya ce "Kar ki damu, zan zo in sha Allah".

Ana idar da sallar magariba, Adam ya zo tafiya da rumaisa, amma ta ce Alla kar ta ba in da za ta" sai da aka kai ruwa rana, sannan ta SanSaru daga gidan nan, suka tafi, sai dai ta sha kuka sosai da sosai, mama ta harhaWa mata ?an kayayyakin amfani da za ta tafi da shi.

Sam Adam bai kulata ba, har su ka je gida, dan haryanzu bai huce da abun da ta yi masa ba.

Ya ajiyeta a gida, tana jiran ta ga ya fito daga motar, ta ga ya juya ya tafi da sabir.
Hakan ba ?aramin haushi ya bata ba, hakan ya sanya ta shiga Wakinta, ta yi ta aikin kuka.

Da ya dawo daga mayar da sabir, bai nemi ruma ba, sai da safe, shi ma dan yana tsoron, kar ya kawar da kai a kan ta, ta yi wani rashin jin.

Sai dai ya tarar tana banWaki, ya ?arasa gaban gadon, ya kai hannu ya Wau littafin da yake buWe, da fensira a kai.

"Duk wanda ya duba littafin nan, ba da izinina ba, Allah ya isa!!!"

Tsaki yayi, ya buWe shafin gaba.

"Zan so ace ni marubuciya ce, da sai kun fi fahimtar abun da zan rubuta, amma gaskiya ba zan iya ba, ban sani ba ko ku gane me nake nufi, idan na zana abu mai muhimmanci da ya sameni a rayuwa, da wanda ya tsaya a zuciyata har in mutu ba zan manta ba, ina fatan ku ji irin abun da na ji, ko za a samu mafita".

Zane ne tiryan-tiryan, zane mai matu?ar kyau da Waukar hankali, daga fitarsu daga gida zuwa tasha, tare da ta?aitattaun bayanai, a gefe, na abun da ya faru". Nutsuwa ya nutsu yana bi, sai dai duk da haka ta cire wasu abubuwa masu muhimmanci.

Daga banWakin ta fito, tana kokowa da towel, sai dai ta yi turus da ganinsa, saboda ba ta san ma yana gidan ba.

Kallon-kallo aka shiga yi tsakaninsa da ita, kamar Sarawo da mai kaya.

"Meye wannan?" Yayi maganar yana nuna mata littafin.

"Waye ya ce ka Waukar mini littafi? Ba ka ga gargadin da na yi a farko ba?".

"Me wannan zanunnukan suke nufi, bayan kin ce mini, ke baki san komai ba? Meye ?arashen wannan zanunnukan, kuma a wace tashar motar ku ka hau mota?"

Tura baki ta yi ta kawar da kai, ya nufeta gadan-gadan, nan take ta ga idonsa ya fara wannan haya?in.

"Yi ha?uri, ka bani zan yi maka bayani"

Ya mi?a mata littafin, sai dai tana karSar littafin, ta ri?e towel Win ta, ta kasa da gudu ta bar Wakin.


Ayshercool.
08081012143




Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?


Bai yi wata-wata ba ya rufa mata baya, tuni ta yi downstairs, tana ri?e towel Win ta, ko da ya sauka ?asa ya neme ta ya rasa.

Ya kalli Asiya da take mopping a falon, ya ce "Ina ta shiga?"

Ta nuna masa kitchen, da sauri ya shiga kitchen Win, ya tarar da ita da barira, ta yi wu?i-wu?i da ido ta na kallon sa, sai dai ta Soye hannunta a bayanta.

"Ina yake ina littafin? Ina ki ka ajiye shi?"

Shiru ta yi masa ta na bin sa da kallo.

Takowa ya fara yi, yana cigaba da tambayarta, sai dai ta fara ja da baya, ganin idonsa ya cigaba da wannan haya?in.

Sai da ta dangana da jikin bango, ya zo ya tsaya a kanta.

"Wannan abu ne da ya shafi rayuwata, kacokan da iyalina, ba na wasa da duk wani abu da ya shafi aisha, zuwa yaushe zaki cigaba da wahalar da ni ne? Ki gaya mini abun da nake bu?ata, ki yi mini bayanin zane-zanen da ki ka yi?".

Kawar da kanta ta yi gefe, daga kallon fuskar sa, tare da bawa kanta ?warin gwiwar jure duk wani abu da zai yi mata.

"Am talking to you!" Yayi maganar cikin shouting.

"Ni ka ?yale ni, ai ba da iznina ka Wau littafin ba" ta ?arasa maganar tana ?o?arin jan jikinta ta wuce.

Dannata ya yi a jikin bango, ya zura hannunsa bayanta, ya ban?ara hannunta, ta zunduma wani uban ihu, sai dai babu littafin a hannunta.

Haya?in da kitchen Win yake yi ne, ya sanya shi Waga kai, kawai ya hango littafin ta tura a cikin gas, yake ?onewa.

'Innalillahi wa Innalillahi raji'un ' ya faWa a zuciyarsa, bai taSa ganin halitta mai azabar taurin kai da masifa, kamar wannan yarinyar ba'.

Baba uwani kuwa, magiya take yi masa a kan ya taimaka ya rabu da rumaisa, saboda yadda take kururwar zai karya mata hannu.

Da sauri ya nufi gas Win, barira ta ja da baya, saboda gaba Waya fuskarsa har ta fara sauyawa, saboda azabar Sacin rai da fushi. Sai dai kash tuni littafin ya babbake, ya zama toka.

Rumaisa kuwa zubewa ta yi a wurin, tana yarfa hannunta, saboda yadda take jin sa tamkar ba a jikinta ba.

A fusace ya waiwayo ya kalleta, ya zo ya sake dan?ar hannunta, ya ja ta daga kitchen Win.

Baba uwani ta bi shi tana yi masa magiyar ya rabu da rumaisa, amma ya shareta, rumaisa ta saka hannunta Waya, ta ri?e towel Win da yake barazanar faWuwa. Duk wannan masifar da ha?ilon, idon rumaisa mursisi, ba ta yi dana sanin abun da ta aikata ba.

?akinsa ya wuce da ita, ya rufe ?ofar gam, ya tankaWata kan gadonsa, ta zauna daSas, ita kokowarta kar towel Win ta ya faWi ?asa.

"Ki gaya mini me ki ka sani game da mutuwar aisha, da saceta?".

"Wai ya ka ke tamabyata kamar ni na sace ta? Ni ban san komai ba, ni ma fa sace ni aka yi".

"Amma kin san wani abu, akwai abun da ki ke Soye wa, atleast a bayaninki akwai wani abu da zai taimaka, na gane idan saceta haWin baki ne".

Ta ce "Oho, ni dai ban san komai ba, zanena kawai nake yi, idan kun ji haushi, tun da ku jami'an tsaro ne ku din ga aiki tsakani da Allah, ni ka daina yi mini masifa, ba abun da na sani".

Cikin matsananci fushi, ya ce "So ki ke na illataki ko? Idan ki ka bari na yi miki illa, na yi wa banza, ke zaki nakasa ba ruwana. Kin san muhimmancin aisha a wurina kuwa? She don't deserve, such kind of death, ki yi mini bayani kan na yi miki illa"

A karo na biyu ta sake kawar da kai, ta na zumSura masa baki.

"Kalleni"

"Ni ba zan kalleka ba, kai baka ganin abun da yake fitowa daga idonka?".

Ba ta yi tsammani ba, ta ji ya ri?e gashin kanta ya ja, sai da ta kusa shiWewa, ta mi?e tsaye tana ?o?arin ?wacewa.

Ga mamakinta, sai ta ga fuskarsa ma ta fara ba?i, duk ya yi wani iri.

A take mafarkin da ta taSa yi, ya fara ?o?arin zama gaskiya, dan faratansa ya fara karta mata a wuyanta, ya kuma sha?eta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ya na wani irin kakari.

Da fari su barira sun biyo bayan baba uwani, baba Uwani ta kasa kunne a jikin ?ofar, ta na jiyo abun da suke cewa, sai dai tun da rumaisa ta yi ?ara suka ji shiru.

Jiki na rawa barira ta ce "Baba uwani, ko mu kira masu gadi, a ceto ta, kar ya yi mata illa".

Baba uwani ta ce "Ke ina ruwan ki? Dalla ku wuce ku je ku cigaba da aikinku"

Rumaisa kuwa bayan ya yi mata wannan sha?ar, sai da? ta suma, ya saketa ta faWi ?asa, sannan ya yanke jiki ya faWi a gefenta, cikin yanayi mai kama da bacci.

Asiya kasa nustuwa ta yi, ta ce "Barira, tsoro nake ji fa, kar ya kasheta, ko police station aka kaimu bayar da shaida an cucemu".

"Bari kawai, wallahi nima a tsorace nake, ga matar nan ta hana a nemo taimako".

Asiya ta ce "Bar ?ar rainin hankali mana".

"Ita ma dai, ta na da azabar taurin kan tsiya, ni ina girki kawai na ga ta shigo da gudu, ta tura abu a wuta, zan yi magana ta ce in yi shiru, sai ga shi ya biyo ta, amma na ji yana magana a kan Aisha, wata?ila abu ne mai muhimmanci da ya shafe ta".

"To waya sani, ni dai fatana kar ya illata kawai".

Bayan sa'oi uku, Adam ne ya fara yin juyi, dan ji yake kamar barci yake yi, kawai ya ga rumaisa a kwance a ?asa, ita daban towel Win ta daban, da ga ita, sai gajeren wando.

Tashi ya yi zaune yana ?o?arin tuna abun da ya faru, kawai dai ya iya tuna yadda ya janyota har Wakinsa, amma daga nan komai ya goge a kansa.

Tsura mata ido ya Wan yi, yana tunanin ko barcci take yi ne? Amma sai ya ga yanayinta bai yi kama da haka ba.

'Ko wani abun na yi mata?' ya tambayi kansa.

Matsawa ya yi kusa da ita, ya Wagota, ya ga jikinta a sake.

A gigice ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, i lose my sense again?" Rabon da ya fita completely daga hankalinsa haka, an kai shekaru goma, ko ya yi loosing control, ya na iya tuna abun da ya faru, amma completely yau ya kasa tunawa.

Wuyanta ya kalla, duk shedar an karceta da farce.

Ya Wan girgiza ta ya na kiran sunanta.

"Rumaisa!" Amma shiru ba ta motsa ba, ya taSa hannunta, ya ji zuciyarta na bugawa, numfashi da take yi a hankali.

Ya kwantar da ita ya shiga banWaki, ya Webo ruwa a hannunsa, ya dawo ya shafa mata a fuskarta, ya ?ure gudun Ac da na fanka.

Bai Waura mata towel Win ba ya ?yaleta, ya lulluSe ta da shi, ya tsura mata ido yana fatan Allah ya sa ta farka, dan kuwa idan ya Wauketa ya kai ta asibiti, asirinsa zai iya tonuwa, dan babu lallai ta yi shiru, kuma dole a tambayi mai ya sameta, ya cigaba da addu'a Allah ya sa ta tashi.

Babu tsammani, kawai ya ga ta tashi zaune, tana ganinsa ta ja da baya, ta kare jikinta da hannunta.

Sai a lokacin ya yi ajiyar zuciya "Ki Waura towel Win mana" ya faWa a sanyaye.

"Dole ka ce na Waura mana, bayan ka yi mini tsirara, za ka kasheni, wallahi gida zan gudu, ba zaka kasheni ba? A hakan zan gaya maka abun da na sani Win? Dama ban san komai ba ma, wallahi ba zaka kasheni a banza ba, ka sha?eni kamar wata Sarauniya".

A hankali ya ce "Ya ilahi, i attempt to kill her?'

Ta saka hannu ta ja towel Win, ta rufe jikinta, ta yin?ura ta tashi, ta fice daga Wakin.

A hankali ya lumshe idanunsa, ya bawa hawayen da suka taru a idonsa damar zuba, ba zai so ammi ma ta ji wannan maganar ba, iya rayuwarta a hanyar nema masa magani take, ana murna abu ya Wan yi sau?i sai abun da ba a rasa ba, kwatsam yau abu ya dawo kamar da.

Sai ya ji tashin ciwon nan nasa, ya shafe abun da rumaisan ta aikata masa.

"Mahaukaci ne ni? Ko kuma maye? Ko kuma namiji mai mutanen Soye, wato aljanu?" Tambayar da tun da ya shekara takwas a duniya, yake yi wa kansa da ya gaza samun amsarta.

Ba shi da tabbacin rumaisa ta rufa masa asiri, haka zalika bai san ta ina zai fara yi mata bayani, ta fahimce shi ba, sai a lokacin yake ganin rashin kyautawar da aka yi, na rashin yi musu bayanin larurarsa.

Madigar kuwa ta na zuwa Wakin ta, gado ta hau ta cigaba da bacci.


Baba uwani kuwa, ta fita ta zagaya, jikinta na tsuma, ta kira lambar Mummy.
Aka yi sa'a mummy na kusa, ta Wag wayar, gulma na cin ta ta ce "Allah ya taimake ki"

"Ina jin ki".

"Akwai abun da ya faru".

"Je ki kai tsaye".

Baba uwani ta waiwaya sannan ta ce "Ranki ya daWe, muna cikin aiki muka ga ya biyota afujajan, a kan wani littafi, sai dai kan ya cimmata ta tura shi a wuta, na ji yana magana cewa, abun da ya shafi aisha ne, baki ga sha?ar da yayi mata ba, ?arshe dai ya shiga da ita Wakinsa, ya rufe su, sai yanzun nan ta fito".

Mummy ta ce "Good, kin fuskanci ya yi mata wani abu ne?"

"Ban san me yayi mata ba da ya rufe su, amma na ga ta fito tana kamar magagin bacci".

"Kin sanar da samha ne?"

"A'a Allah ya baki nasara".

"Kar ki sanar da ita komai, sai abun da na umarce ki".

"In Allah ya yarda".

"Ki koma, ki cigaba da sanya mini ido a kan duk wani motsinsu".

Baba uwani ta ce "An gama uwar Wakina". Ta katse wayar ta koma.


Adam kuwa ya yi sallar azahar, ya jingina da jikin gado, ya yi shiru yana tuna abubuwan da suka shuWe, gaba Waya jikinsa ya yi sanyi.

Kiraye-kirayen, sallar azahar ne ya tashi rumaisa, ta je ta yi alwala, ta saka kaya, ta tsaya a gaban mudubi, ta na kallon wuyanta, da ya shata yake mata zafi.

Shiru ta yi tana tunanin tabbas ta taSa ganin wannan abun a mafarki, ko kuma ya taSa faruwa.

"Wallahi sai na gaya wa mama, tun da kasheni zai yi, sai na gudu na bar gidan nan"

Can kuma sai wata zuciyar ta tunatar da ita, muddin mama ta ji a kan meye, ya yi mata abun da yayi mata, ba zata goya mata baya ba, faWa za su yi, a bata rashin gaskiya, kuma a kirsheta ace sai ta faWi abun da ta sani, bayan ta riga ta ce ita ba ta san komai ba.

'Subhanallah, na fasa faWa, bari na yafe masa, wataran ya na da kirki, amma wallahi ko zai kasheni ba zan faWa masa komai ba, sai lokacin da na ga dama, bari na lallaSa na san yanzu ji yake kamar ya kashe ni' sai kuma ta Wan yi shiru ta ce "To da ya sha?e ni kuma sai na yi bacci, oho dai? Ta gama abun da Allah ya nufe ta da yi, ta yi salla ta fito dan yunwa take ji.

Adam ya tashi ya nufi Wakinta, domin ya duba ko ta na lafiya ta gama wartsakewa, sai dai ya jiyo motsi a kitchen.

Ya le?a kitchen Win, ya hango ta taka kujera, tana saka Wan wake, kamar babu abun da ya sameta.
Abun har mamaki ya bashi, kamar ya yi mata magana, sai kuma ya fasa ya fita.

Baba Uwani na ganin fitar Adam, ta lallaSo ta hawo benen.

"Sannu ?ar nan, ina fatan bai yi miki komai ba?"

Rumaisa ta waiwayo ta kalli baba uwani ta ce "Yayi mini me?".

"Ai ganin yadda ya janyo ki Win nan, abun ya tsoratani, ke ma da ko me yake bu?ata kin bashi kin wuce wurin, idan ransa ya Saci hankalinsa gushewa yake wasu lokutan, zai iya yi miki illa. Ko dai hakkinsa ki ka hana shi ne?"

Rumaisa ta juyo gaba Waya ta kalli baba uwani ta ce "Wane irin ha??i kuma?".

"A'a ha??in aure mana".

"Meye ha??in aure kuma?"

Baba uwani ta ce "Ahh shikenan, bari maganar kawai".

Har baba uwani za ta fita ta ce "Kenan papa da gaske maye ne?"

A razane baba uwani ta waiwayo ta ce "Me ki ka ce?"

"Kin ji me na ce ai".

"Ke waye ya gaya miki?"

Rumaisa ta ce "Ke ce ki ka gaya mini yanzu"

Baba uwani ta ce "Ke, yaushe na gaya miki? Ki ji tsoron Allah"

"Ke ki ka faWa, wannan ne karo na biyu ki na gaya mini, zan kuma tambaye shi".

"Dan girman Allah ki rufa mini asiri, da wasa nake yi ma fa, dan Allah kar ki gaya masa"

Rumaisa ta juya ta cigaba da saka Wan wakenta, baba uwani kuwa ta toshe baki ta na fatan, Allah ya sa kar garin neman gulma, ta janyo kwaSarta ta yi ruwa, domin kuwa ta lura bayan ?uriciya, har da wauta ke damun rumaisa.


***
"Hajiya Lubabatu, ki na free gobe in Allah ya kaimu". Mummy ta yi maganar da waya a kunneta.

"Ya aka yi ne?".

Mummy ta ce "wurin malam na gidan dutse, zaki rakani, akwai case ne".

Hajiya Lubabatu ta ce "Wane irin case kuma?".

"?an maje ne ya turo mini sa?o, wai ya ji mai martaba zai wakilta turaki, zuwa taron bun?asa al'adu da harsunan afrika, rainon burtaniya, wai ya Wauki mutum biyu a matasan yaran nan ya tafi da su, kuma da alama za a samu cigaba, wai ya ji turaki ya ce har da Adam za ayi tafiyar".

Hajiya Lubabatu ta ce "To ba sai su yi ta yi ba"

"Ina ba fa zai yiwu ba, wai ke meyasa ki ke Waukar al'amuran nan da sau?i, komai sai dai shi, duk wannan miyagun fentin da suke tare da shi, komai sai dai a saka shi, ke me zai hana a tafi da Jabir, ga mahmud, ga Jamil nan, ina su yarima jikokin mai marataba, duk ba a Wau kowa ba sai shi? A dalilin me?".

"Kuma fa da gaskiyarki Jamila"

"Dan Allah ki shirya, na ga da yadda zai tafi ai".

"Ke dole ma, zan shigo da wuri ma yi maganar, ni Jabir ne yadda ki ka san an yi masa asiri,gaba Waya hankalinsa ba ya kan harkar sarautar nan, mussman idan abu da adam a ciki, sai ka ce ya yi masa asiri".

"Ni ma na fuskanci kamar aikin da ake yi wa Mahmud ba kamar da ba, zamu haWu kawai".

***
Ko da Adam ya dawo da yamma, ya iske ruma, tana kwance a doguwar kujera, tana kallon cartoon.

Ya kalleta ya na jiran ya ji ko za ta ce wani abu, suna haWa ido ta galla masa harara, bai dai tanka mata ba, ya wuce Wakinsa.

Adam dai hatta abincin sa bai iya ci ba, yadda aka kawo su, haka ruma ta Wauka ta mayar musu.
bacci sai Sarawo, kwana ya yi ya na juyi, kuma yau sai ya kasa tashi ya yi sallar dare kamar yadda ya saba, tasbihi ma sai ya kasa saSanin da, sai ajiyar zuciya da istigfari, ji yake komai ya yi masa zafi, ba

91 / 128