Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kanwar MAZA 1&2 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   70 / 128

207K to 210K   out of 382K words

da nunawa juna soyayya kamar gidansu rumaisa.

A gigice mama ta tashi da suka shigo, ta ga jikin Aliyu duk ?asa, rumaisa kuma da fasashshen goshi, duk da ba ta zubar da jini da yawa ba.

"Mai sunan baba, maiyafaru?"

"Kar ki damu, ba abun da ya faru"

Mama ta ri?e Aliyu da yake huci ta ce "Ina fatan dai ba abun da ya sameka ko?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

Mama ta ce "Duk saboda wannan jairar yarinyar ne, da ba zata bari a zauna lafiya ba? Ina ke ina faWa da gagararren Wan daba saboda Worawa kai bala'i" Mama ta yi maganar tana ?o?arin kai mata duka, amma mai sunan baba ya tare ya ce "Ki ?yaleta please, baki ga ta ji rauni a goshi ba, ki yi ha?uri"

Mai sunan baba ya sakata a gaba, ya kai ta chemist, aka duba goshin, Allah ya taimaketa babu Winki, suka dawo gida.

Mama ta kai ?arshen ?ulewa da rumaisa yau, ta din ga yi wa ?an mazan faWa a kan biye mata wurin tare mata faWa.

Kasancewar ma?wabcin su rumaisa malam shamsu, yana cikin ?an kwamitin unguwa, shi ne mataimakin ?an ?ato da gora, yana dawowa aka sanar masa da abun da ya faru a unguwar, nan da ya ji ya samu damar rama wula?ancin da rumaisa da yayyenta suka yi masa, kai tsaye ya je ya sanar da ?an sanda abun da ya faru.

Mama har ta bar sallahun a rufe gida, ?an sanda suka yi sallama, suka ce sun zo tafiya da Aliyu.

Duk yadda aka so sasanta lamarin, abu ya gagara, ga Abubakar ya koma makaranta, Mai sunan baba da Usman suka bi bayansu, amma har wurin sha Wayan dare, ?an sanda suka ?i bayar da Aliyu, ?arshe ma suka sanar da su cewa sashin kula da manyan laifuka na bamfai zasu turasu, tun da Aliyu ya yi i?rarin kisan kai.

Haka mai sunan baba suka koma gida, jiki a sanyaye, mama ta rasa in da zata saka kanta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, tare da Wora zargin komai a kan rumaisa.

Adam kuwa bayan ya kammala cin abinci, ya tashi ya yi wa ammi sallama, ammi ta ce "Yauwwa, na ce ba" Adam ya Wan tsaya yana kallon ammi.

"Dan Allah gobe in Allah ya kaimu, tun da da wuri zaka fita, kuma ka ce zaka je gidan gona, dama unguwar su matarka ne, zan baka sa?o ka kai wa rumaisa"

Adam ya kalli Ammi ya ce "Matata kuma? Kuma ni zan kai ss?on?"

"Ban isa ba kenan?"

Ya ce "A'a tare da sunkuyar da kai"

"A yanzu kana da wata matar da ta wuce rumaisa ne? Zaka kai mata sa?o, kallonka kawai nake yi, har na je wurin turaki na dawo ba ka tambayi yaya muka yi ba, kuma ya zama dole ka din ga zuwa wurinta, saboda ta saki jiki da kai, kuma ka daina yi mata wannan muzuran"

Adam ya jinjina kai yana wasa da yastun hannunsa.

"Je ka, da safe in Allah ya kaimu kan ka wuce, ka biyo"

Bai ce komai ba ya fice.

Ayshercool.

Chat me on what's app, to subscribes yours
08081012143

*PAID BOOK NE, ? 500 NE VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA, 08081012143*



Gaba Waya ji yake duk wani girma da mutuncinsa sun zube, kamar shi ace wai zai je wurin wata ?ar yayyiyar yarinya yayi zance da ita, wai zai aureta, ko aurensa na fari aisha ta kammala deegree ya aureta, wannan shi ba ya tunanin ko primary ma ta gama.

Mama kuwa kwana ta yi ba barci, sai addu'a kawai da take yi, ji take tamkar ta rufe rumaisan da duka, dan bayan gama ?an koke-kokenta tuntsirewa ta yi ta hau bacci.
Mama ta kalleta ta girgiza kai ta ce "Allah ya shiryeki, ya ganar da ke"

Da asubar fari, bayan rumaisa ta idar salla, ta tafi Wakin su mai sunan baba ta yi sallama, suka amsa mata.
Ta le?a ta ce "Yaya usy jiya kun dawo da yaya aliyun?"

Abdallah ya ce "Wuce ki bawa mutane wuri, duk ba ke ki ka janyo ba, karfa kawai"

Mai sunan baba ya kalli Abdallah ya ce "Kar ka kuma gaya mata haka, bai dawo ba a can ya kwana, duk saboda ke, gaba idan ki ka sake, ke zan kai musu in karSo shi, dan mun fi son sa a kan ki, mara kai kawai"

Sumi-sumi ta juyo za ta fito, ta fuskanci kowa haushinta yake ji yau.

Usman ya ce "Wallahi yau da na ga malam shamsun nan a masallacin asuba, ji na yi kamar na Waga shi na wurga shi cikin kwalbati, shi ne babban munafukin da ya je ya kai wa ?an sanda"

Mai sunan baba ya ce "Ba ruwanka da shi, ku bari mu kashe wannan case Win tukuna".

Abdallah ya ce "Ni malam lawan mai shago na kusa kifawa mari, ya biyo ni wai rumaisa ta yi masa asarar ?wai cret huWu, wai in zo in biya, na ce masa sai dai mu yi kokowa ya Wiba, gaba Waya mutane fuska biyu ce da su".

Rumaisa da take tsaye tana jin su da sauri ta ce "Wallahi ko kret Waya bai yi ba, bai fi guda shida ba fa"

"Au laSe ki ke yi mana ko?" Abdallah ya faWa yana nemo abun duka.

Da gudu ta shige Wakin mama, sai dai irin kallon da maman ta yi mata, ya sanya ta rasa in da zata saka ranta.

Haka ta tsuguna ta takure, da duku-dukun mama ta shiga kitchen, ta girka abinci, gari na yin haske, ta ce lallai mai sunan baba ya taso su tafi station Win.

Mai sunan baba ya ce "Mama, idan kin je wurin nan babu abun da zaki iya a kai, ki bari zan je ni da Usman"

Mama ta ce "Ni dai ka ?yaleni na je na ga a yaya ya kwana?"

"Lafiya ?alau ya kwana, kuma in sha Allah zamu dawo miki da shi, ki yi ha?uri" da ?yar mama ta yadda, ta basu abincin suka tafi.

Rumaisa ta ce ita ba zata tafi makaranta ba, sai yaya Aliyu ya dawo.

Mama ta ce "Aikuwa ba ki isa ba, sai kin shirya kin tafi, wata?ila kan ki dawo na huce, dan da na kalleki haushi nake ji, haka kurum saboda ke kin saka an kulle mini Wa, mara jin magana" shiru rumaisa ta yi tana kallon mama, kenan yanzu mama ta daina son ta?.

Jiki a sanyaye ta shirya, mama ta hanata kuWin makaranta, ba babban abun da ya sake ?ular da mama, irin yadda rumaisan ta zauna ta naWi abincinta, kamar abun bai dameta ba sosai.

Haka ta tafi makaranta, tana tunani kala-kala, amma har ga Allah abun ya dameta.

Kamar yadda ammi ta bu?ata, da safe Adam ya je gidan, a lokacin su iman duk sun tafi makaranta.

Ya Wau sabir yana yi masa wasa, sai dai ?ememe yaron nan ya?i dariya, sai bin sa da yake da kallo.

Ammi ta fito suka gaisa, ta ce "Yanzu wurin aikin zaka tafi?"

"Eh, na biyo na karSi sa?on ne".

Ammi ta ce "To, tun da baka tambayeni ba, ni bari na gaya maka yadda muka yi da turaki".

Ya sunkuyar da kai yana wasa da hannun sabir.

"Mun tattauna da shi, ya ce mini in bari ya dawo daga umara, zai yi magana da su wambai, dan na san akwai ?alubale, tun da rumaisa ba jinin sarauta ba ce, ko ?ar wani sananne ba, dan haka zai yi muku Addu'a a can, da ya dawo aka daidaita kuWin aure za'a kai, bayan salla idan Allah ya kaimu za ayi"

"To, Allah ya wuce mana gaba".

"Amin, wai da ce mini yayi, Jamil ya ce ko za'a maye gurbin Fulani da samha, ni dai ban ce komai ba na shigar da maganar rumaisa, dan ita ta fi kwanta mini"

Adam har mamakin ?aunar da Ammi take yi wa rumaisa yake yi, tabbas da so samu ne, Samha ta maye gurbin aisha, dan ita ta isa mace da hankalinta da iliminta, kuma Samha ta daWe tana son shi, ya san hakan, amma ammi ta dage a kan wannan ?ar yayyiyar Yarinyar.

Ya numfasa ya ce "Allah ya kyauta"

Ammi ta mi?a masa leda ta ce "Gashi nan, sabuwar jakar makaranta ce, da litattafai da turare, ka kai mata ka ce ina gaisheta"

Adam ba yadda ya iya, ya karSa ya amsa da to.

Ya fita ri?e da ledar kayan a hannunsa, ya san zuwansa wurin Yarinyar nan, ba abun da zai ?ara masa sai raini.

A harabar gidan ya tarar da Mahmud, tun da ya dawo yana ganin shige da ficen motocinsa, amma basu ta Sa haWuwa ba sai yau, yana tsaye a wurin parking space Win Adam, kusa da in da zai Wau motarsa.

Adam bai kula shi ba, shi ma bai kula shi ba, ya je ya buWe motarsa ya kunna, ya Wan jima a ciki, amma ya ga Mahmud ba shi da niyyar matsawa, ya din ga danna horn, amma Mahmud ya yi burus, ba tare da wani Sata lokaci ba Adam ya bawa motar wuta, yayi reverse, ai kuwa ya buge Mahmud, ko kaWan Mahmud bai kawo Adam zai yi masa haka ba, kan ya ankara ya ga Adam yana ?o?arin bi ta kansa, ba shiri ya mirgina, Adam ya ja motar da gudu ya bar gidan.

Ma'aikatan gidan suka yo kan Mahmud suna yi masa sannu, suna ?o?arin Waga shi, sai dai ciki gwasalewa ya nuna musu shi zai iya tashi, sai dai abu kamar wasa, da ya mi?e Win ?afa ta?i takuwa.

***
Rumaisa tana hanya tana addu'a, Allah ya sanya yaya Aliyu ya dawo, Allah ya sa komai ya wuce, sai dai ko da ta iso gida, ta tarar da Usman da mai sunan baba amma babu Aliyu. Cikin damuwa ta ce "Yaya usy ina yaya Aliyun yake?"

"Ke, case Win nan fa ma?abcinmu malam shamsu, ya yi uwa yayi makarSiya yana ta kambama abun, gaba Waya ma sun ?i saurarmu a station Win, wai sai DPO ya zo, DPO na zaci wanda ku ka yi case Win nan ne kwanaki, ashe an canza wani, sun kafi wai sai an je state cid tun da aka yi i?rarin kisan kai".

Rumaisa ta ce "Na shiga uku, ba fa yaya Aliyu ne ya ce zai kashe shi ba, shi ne ya ce zai kashe shi".

"Koma menene ba ke ki ka janyo ba rumaisa, duk abun da mutum zai gaya miki sai dai ya shiga ta kunnen dama ya fita ta hagu, saboda wautarki kin jefa Wan uwanki a wahala"

Usman ya ce "Dan Allah mama ki daina faWar haka, ?addara ce"

A fisace mama ta ce "Rufe mini baki, ko na make ka, ai duk gidan nan babu mai koya mata rashin ji irin ka"

"Allah ya baki ha?uri, ba ri mu yi salla mu koma".

Adam kuwa ko kaWan bai ji babu daWi ba abun da ya yi wa Mahmud, dan a lokacin nan yadda ya hasala, da ya samu dama sai ya taka shi da mota uban kowa ya huta, ya sauke masa wannan girman kan da rashin mutuncin da yake ji da shi.
A haka yake wurin aiki, ya gama abun da yake yi ya fito, yana da niyyar zuwa gidan gona, sai dai dole ya je ya kai wannan sa?on kan mama ta Sata ranta.

Mahmud kuwa ?arshe, sai ka shi sashin Mummy aka yi, a rikice take tambayarsu maiya same shi, suka gaya mata Adam ne ya buge shi da mota.
Nan da nan ta hau ta fara bala'i "Wannan wane irin wula?anci ne, anya Adam bai fara shaye-shaye ba? Ko dai haryanzu haukar ce a kansa, tayaya zai taka ka da mota? Wallahi ba zan lamunta ba sai na Wau mataki"

Mahmud ya Wan cije lips Win sa ya ce "Ki rabu da shi zan rama ne, yanzu ni dai ?afata zafi take yi ki yi wani abu a kai"

"Wallahi ba zan ?yale ba, Fauziyya Wauko key mu tafi asibiti kawai, Allah ya sa ba wani abun ne ya samu ?afar ba"

"Mummy, dan Allah ki rabu da shi, am just testing his anger, ashe yana nan a yadda yake bai canza ba" yayi maganar cikin zolayar Mummy.

Cikin fushi ta ce "Ka rufe mini baki, this is an serious issue, ba zan bari ba" ganin yadda ta Wau zafi ya sanya shi yin shiru yana kallon ?afarsa.

A ?ofar gidan su rumaisa, Adam ne a tsaye, yake kiran wayar Aliyu, amma shiru bai Wauka ba,???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? wayarma a rufe take, ya kira har ya gaji, ya aika yaro ya ce ace ana sallama.

Usman ne ya fito, domin duba waye, ya tarar da Adam a tsaye, ya ?arasa yana wani basarwa, suka gaisa sama-sama.

Adam ya ce "Aliyu nake nema, na kira wayarsa ba ta shiga"

Usman ya kalleshi, ya lura ta su ta zo Waya da Aliyu sosai.

Ya ce "Ya Wan haWu da tsautsayi ne" ya bashi amsa a ta?aice.

"Wane irin tsautsayi kuma?"

"Eh waccan yarinyar ce ta tsokano Wan daba, ya je tare mata, kuma dama ta yi rigima da ma?wabta, shi ne mai gidan ya saka aka kama su, tun jiya muke zuwa police station, an ?i sakinsa, yanzu ma komawa zamu yi"

Mamaki ne ya sha kan Adam, duk rumaisan ita kaWai ta janyo wannan tarzomar.

Cikin mamaki ya ce "Wai duk ita wannan Yarinyar ce ta yi faWa da Wan daban?"

Usman yayi wani irin murmushi ya ce "Wannan ta wuce tunaninka, ka san ?anwar maza ce, bamu raineta da tsoro ba"

Adam har cikin ransa ya ji babu daWi kama Aliyu da aka yi, ya ji da rumaisan aka kama ita da ta janyo abun.

Ya ce "Ko zan iya magana da maman?"

Usman ya ce "Ok, bari na yi mata magana".

Bayan an yi wa Adam iso ya shiga gidan, ya tarar da rumaisa a takure a falon mama, sai rarraba ido take yi, suka gaisa da mama ya sanar mata da Usman ya gaya masa abun da ya faru"

Mama ta ce "To, yakamata ka sake tunani a kan auren nan naku, ku gidan sarauta ba kwa son shirme, rumaisa kuma Allahn da yayi ta ba ta ji ko kaWan, faWa da ma?wabta faWa wai har da Wan daba, yaron da har kisan kai yake yi"

Adam ya kalli in da rumaisa take, ta haWe rai saboda yadda mama ke kwance mata zani a kasuwa, ya ce "Me ya haWaki da ?an daba, har aka kama Aliyu?"

Shiru ta yi tana wul?ita ido, mama ta ce "Zaki yi bayani ko sai na mareki?"

?asa-?asa da murya ta faWi abun da ya faru, ta wani fannin tana da gaskiya, a kan me zai aiketa sayen sigari.

Adam ya ce "Ba damuwa mama, bari mu je a fito da shi, ba wani state CID, wani station Win ne?"

Usman ya ce "Dama yanzu zamu koma da mai sunan baba sai mu tafi gaba Waya " wani mugun kallo da mai sunan baba ya yi wa Usman ya sanya yayi shiru, Sarai Adam ya ganshi, dan haka ya ce "Bari mu je da wuri, kuma dole ita ma a tafi da ita".

Mama ta ce "Idan ma sun ?i yarda, ku basu ita ku dawo mini da Aliyu" sanin ba ta da gaskiya ya sanya ta sunkuyar da kai ta yi shiru.

Mama ta so bin su, amma kasancewar yanzu magana ake ta siriki, mama ba zata iya shiga motar Adam ba.

Bayan tafiyarsu mai sunan baba ya ce "Amma ba kya ganin yawan shigarsu cikin al'amuranmu da yi mana alfarama, ba zai saka nan gaba su cigaba da kawo bu?atunsu ba, kuma ba yadda muka iya sai mun bi ba?"
Mama ta ce "Babana ka san na fi kowa taka tsantsan da gudun duniya, bana jin hakan, shi ya sanya na amince"

Ya Wan rausayar da kai ya ce "Shikenan, bari na bi su a napep"

Suna tafe Adam yana kallon rumaisa ta mudubi, sai wani gyatsine baki take yi, tana harare-harare kamar mai shirin iskokai.

Cikin station Win suka shiga, aka yi musu iso wurin DPO, cikin sa'a suka tarar da malam shamsu a station Win yana ta cigaba da zigar kai su Aliyu CID.

Adam ya ce "Case Win ?anina na zo mu yi magana a kai, na san shi ba mai laifi ba ne"

Malam shamsu ya ce "Ta ina, yana mana i?irarin kisan kai a cikin unguwa"

Usman ya ce "Wai kai malam shamsu meye yake damunka, meye ribarka idan an rufe Aliyu ne?"

Mai sunan baba ne yayi sallama ya shiga, suka amsa masa ya nemi wuri ya zauna.

Adam bai ko kalleshi ba ya cigaba da magana ya ce "Da ku ka caje Aliyu kun same shi da makami?" DPO ya ce "A'a"

"Good, Wayan fa, abokin rigimar ta sa"

"Eh, mun kama shi da wu?a?e da tabar wiwi"

Suna cikin maganar aka shigo da su Aliyu.

DPO ya kalli rumaisa ya ce"Ni mamakina ma da wai duk a kan wannan Yarinyar ce ta haWa faWan, ke meye ya haWaku?"

Ta cunkusa baki ta ce "Cewa yayi na sayo masa sigari, kuma ni ba ?ar iska ba ce ba da zan taSa sigari ina ?a ma ce mai mutunci "

Adam a ransa ya ce "Ko wa ya tambayi jinsinta kuma oho'

Malam shamsu ya kada baki ya ce "?ar iska kum ta nawa, zance da ya cika unguwa"

Zabura rumaisa ta yi ta ce "Yaya usy ka ji ko? Yanzu idan na yi magana ace ba na jin magana, da kunnenka ka ji yana ce mini ?ar iska, ni fa bar ?ar iska ba ce ba, bana wasan banza da maza, meyasa ake ce mini ?ar iska?" Ta yi maganar hawaye ya wanke mata fuska.

Malam shamsu ya ce "Ke da aka ce an yi garkuwa da ke, ki ka dawo da Wa, ai ba abun mamaki bane ba, tun da kowa ya san a unguwar nan ba ji ki ke yi b.... Mai sunan baba ya daki tebur da ?arfi ya ce "Ya isheka malam"

DPO ya ce "A gaban nawa, da rashin mutunci da rashin sanin darajar doka".

Malam shamsu ya ce "Tuba muke YallaSai".

Usman yayi ?asa da muryarsa ya ce "Uban waye ya saka ki yi kuka a gabnsa, salon ya rainaki, idan ya kuma gaya miki ki ce kin yi Win"

Adam ya numfasa ya ciro ID card Win sa ya bawa DPO ya ce "Ina son a bi tsarin doka, a bani Aliyu sannan a tura mai laifi gaba"

Ware ido DPO yayi ya ce "Ranka ya daWe dama kai ne? Ai da ko waya ka yi ya wadatar ba wani abu in sha Allah, case ya mutu

70 / 128