Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kanwar MAZA 1&2 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   58 / 128

171K to 174K   out of 382K words

ki damu zaki gane me nake nufi " ya kalli Adam ya ce "Takawa, Biliyaminu nan sun kawo sa?on 'ya ta, ba sai sun ganni ba, na ta ne a kai mini ita har gida, Allah ya yi miki albarka".

Rumaisa ta ce "To baba dan Allah ka saka baki ya bani Wana sabir, kaga na gaya maka anty aisha ta bar mini shi wallahi, amma ya ?wace mini shi, kar na kai shi kotu ne a ga kamar ban kyauta ba, kuma ina ganin girmanku kai da mamansa, amma da wallahi nima kotu zan kai shi wurin al?ali, wata a unguwarmu ta taSa bawa mama labari wai a kotu an ?wato mata Wan ta daga wurin mijinta an bata"

Turaki ya girgiza kai tare da murmushi ya ce "Subhanallah, ba za ayi haka ba, ai mu yanzu mun zama 'yan uwa, za a duba lamarin in sha Allah, sa?onki yana mota Allah ya tsare".

Rumaisa ta mi?e tsaye ta ce "To na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya maka bu?atunka na alkhairi Allah ya sa ka zama sarki, ka zama shugaban ?asa baba"
Sunkuyar da kai turaki yayi, yana rife fuskarsa da rawani, dan sha'anin na rumaisa ba ya ?arewa.

"Wuce mu tafi ina da wurin zuwa" Adam yayi maganar a kausashe.

"Ai ko ba ka ce ba zan tafi, ba sai ka kaWani kamar wata akuya ba" ta yi maganar tana ficewa waje.

Tun da ta fito usman ke cigaba da aika mata harara ko ta ina, amma ta yi kamar ba ta gani ba, haka suka fita suka hau motar takawa.

Suna tafe a hanya, babu wanda ya kula rumaisa a cikinsu, usman ya ce wa Adam "Ina ga idan muka ?arasa titi ka ajiyemu, sai mu samu abun hawa mu ?arasa gida".

Adam ya girgiza kai ya ce "A'a zan kai ku gida, akwai kaya ma, ba zai yiwu in ajiyeku a hanya ba" daga haka suka Wan shiga taSa hira suka cigaba da tafiya.

Tafiyar su takawa babu daWewa, Samha ta dawo, har ta shiga Wakinta ta canza kaya ta fito, ba ta ga gilmawar mama ba, dan haka ta bita Waki.
Ta iske mama na ta ?ananun maganu, da mita.

"Mama, wai baki san na dawo ba? Ke da waye ki ke ta mita haka ne?".

"Ba dole na yi mita ba, ubanku na nema ta ?arfin tuwo ya mayar da ni mahaukaciya".

"Ohh mama, kullum cikin case da Alhaji, yakamata ku daina zuwa yanzu".

"Ke dalla rufe mini baki, mai za a fasa? Ai yanzu aka fara ma ba ayi komai ba, na rasa abun da yake shiryawa da shi da adam, sai Soye-Soye suke yi, da rainin hankali wata shu'umar 'ya ya kawo masa, wai ita ta dawo Wan wurin aisha daga hannun 'yan bindiga"
Cikin rashin fahimta samha ta ce "Yan bindiga kuma, wasu 'yan bindigar kenan kuma? Ba a can in da take karatun aka ce ta haihu ba? To meya kawo ?an bindiga ban gane ba".

Hajiya Sauda ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ke, adam wani abun yake shiryawa, aisha ba wani a ?asar da taje karatu da ta mutu, a hannun'yan bindiga, da suka yi garkuwa da ita, ta haihu ta mutu a wula?ance ko gawarta ba wanda ya gani, waya sani ko shi ya cinyeta ko ya kashe ta yayi tsafi da gangar jikinta".

Cikin rashin fahimta samha ta ce "Mama kin yi wa kwanyata dabaibayi da zantukkanki, na gaza fuskantar ko da guda daga ciki, ki yi mini bayani gwari-gwari. ?an bindiga ne suka bi ta can suka sace ko kuwa?".

Nam mama ta fayyacewa samha komai, duk da gargaWin da turaki yayi mata a kan hakan.

Salati samha ta yi, tare da tafa hannuwa cike da tsananin mamakin sar?a?iya da ruWanin lamarin, a fili ta ce "Oho musu, ko ma dai yaya ne, a wannan karon nasan babu abun da zai hanani mallakar takawa".

She?e?e mama ta kalleta ta ce "Wai ke samha wace irin mara zuciya ce ne?, Au ke yanzu duk abun da ya faru da ke a baya, da irin cin kashin da yayi miki baki ha?ura da batunsa ba?"

"Dan Allah mama karki ce komai, wallahi ina son sa haryanzu kuma abun da ya faru, ya riga ya wuce, dan Allah kiyi ha?uri ki bani goyon baya a wannan karon na auri adam dan Allah"

"Kin ga tashi ki je, ina da abun yi yanzu".

Samha ta haWa hannayenta biyu cikin magiya ta ce "Please mama".

"Na ji, amma jeki yanzu, ki bari na yi tunanina" Samha ta tashi ta bar Wakin mama, tana ta nazari da zancen zuci a kan abun da maman ta gaya mata.

Nusaiba ce ke ta bawa iman labarin rumaisa, da abun da ya faru Wazu da suka zo, zasu je gidan turaki.
Iman ta ce "Allah sarki, na ji ina son ta tun ban ganta ba, ai mu duk mai son waninmu muna son shi".

Nusaiba ta ce "Ke kin ganta, wallahi yarinya ce sosai, dan ba ta kaimu ba ma ko kaWan, na yi mamakin yadda ta iya tsira da sabir".

Iman ta ce "Ai babu mamaki a cikin lamarin Ubangiji, babu abun da bau iya ba".

"Gaskiya ne, amma wai ya maganar uncle J ne, kun kuma magana da shi?"

Haushi ne ya kama iman ta ce "Dan Allah ki rabu da ni da wani uncle J"

"Dole na yi miki maganarsa, ke ma kin san rasuwar nan ce ta hanashi cigaba da bibiyarki, ina son nema miki mafita ne, idan ya je ya biyo ta saman fa kamar yadda ya gaya miki?"

Iman ta Wan yi jimmm sannan ta ce "Bak???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?omai, Allah ya fishi, mu bar maganar nan sai wani lokacin*.

Lura da yanayin yadda iman ba ta son zancen, ya sanya Nusaiba jan bakin ta ta tsuke.

Rumaisa kuwa bayan kayan takaicin da ta turawa su usman, suna tafe a mota tana yi musu wa?e-wa?e, tayi wannan wa?ar ta saki ta kama wata, gashi galibin wa?o?in na indiya take yi, sam ba ta san ma me suke faWa ba, kawai dai tana yi ne, kuma cikin ikon Allah daga usman har takawa ba wanda ya tanka mata har suka ?arasa gidan rumaisa.

Usman ya kalli Adam ya ce "Mun gode ?warai da gaske Allah ya saka da alkhairi".

Adam ya ce "Bakomai, ni ne da godiya ai".

"Hmm ai Yakamata in ?ara ma da baka ha?uri, a kan abun da rumaisa ta yi, ka yi ha?uri dan Allah" Adam yayi Murmushin gefen baki ya ce "Kar ka damu, akwai sa?onta a mota amma, bari na buWe booth Win"

Ruma buWe motar tayi, ta ruga da gudu cikin gida tana kwaWa sallama.

Kaya ne fal a booth Win Adam, da wanda ammi ta bawa rumaisa da wanda turaki ya bayar a bata.

Usman ya Wauka ya yi wa Adam godiya suka yi sallama ya ce a gaida mama.

Ko da ya shiga gidan, rumaisan ya tarar har ta tuSe kayanta tayi Wai-Wai wai ta gaji.

"Dan ubanki ni bawanki ne? Da zaki bar ni da kwaso miki kaya dan baki da kunya?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ganin irin kallon da yake yi wa rumaisa ya sanya sanin cewa akwai abun da rumaisa ta yi.

"Usman, ya aka yi ne? Kun je Win?"

"Eh mun je, amma ba ta sauya zani ba, ta yi iya shegen na ta da ta saba"

Mama ta kalli rumaisa ta sake kallon usman ta ce "me ta yi?"

Nan ya gaya mata iskancin da ta din ga yi, mama ta girgiza kai ta ce "Wai rumaisa me bawan Allah nan yayi miki da ki ke yi masa wannan rashin mutuncin? Duk jan kunnen da na yi miki ba ki ji ba kenan?"

"Mama na faWa komai fa"

Usman ya ce "To amma meye na cewa sai mun fita, a matsayin sa na mijinta yafi kowa bu?atar sanin meyafaru da ita".

Mama ta ce "Meyasa baka kama mini ita ka zaneta ba".

Ya Wan Wage kafaWa ya ce "Ai kin san wasu lokutan sa'a ce da ita, daga zuwanmu ta dinga zuba tana yi wa dattijon shishshigi tana ce masa baba,? aikuwa ya dinga biye mata, saboda sakarci har da ci masa abinci a gabansa"

Huzaifa da yake banWaki yana jin hirarsu, yana fitowa ya ce "Sai ka ce mayya daga zuwa ba?unta ki hau cin abinci"

Aikuwa ta ce "To zigazigi wutar ma?era, mai zuwa lahira da ?o?on dambu waya kasa da kai gwanin na iya".

"Kin rufe mini baki ko sai na taushe shegen bakin naki"

"Wallahi mama ni ban ci abinci ba, wannan abun na kayan gara mai kamar kashin nan da suga shi kawai na ci".

A fusace mama ta ce "Ni rufe mini baki, bera kawai" haka ta koma ta tura baki tare da jin haushin yadda kowa yake caccakarta.

Adam sai da ya fara biyawa yayi sallar la'asar, yana komawa mota ya tarar da missed calls Win Bashir.

Bin kiran yayi, bayan bashir ya Waga sun gaisa ya ce masa akwai issue, su haWu a wani wurin cin abinci bayan sallar isha'i.
Adam ya amsa masa, ya yanke shawarar fara zuwa gida, kan lokacin sallar isha'i sai su haWu da Bashir.

Ko da ya je gida, Ammi ta din ga tambayarsa yaya suka yi, da fari basarwa yayi, da ammi ta matsa ya gaya mata cewar rumaisa ba ta yi magana a gabansa ba sai da ya fita.

Ammi ta yi shiru ta ce "Wai ni anya Adam babu wani abu a tsakaninka sa yarinyar nan ?ar tsamar da ku ke ta yi yawa, ta rainaka da yawa".

Ya girgiza kai ya ce "Ni ban santa ba sai a dalilin abun nan da ya faru, dan haka ni babu komai a tsakanina da ita"

"To, amma ina kyautata zaton akwai wani abu mai muhimmanci a bakinta, tun da ta?i faWa a gabanka".

"Haka nake tunani nima, amma zan koma wurin turaki, sai mu yi magana".

"To shikenan, Allah ya yi jagora"

Ya amsa da amin.

Kamar yadda suka shirya, suka haWu da Bashir a wurin cin abinci, ya tambayi adam mai za a kawo masa ya ce ba ya jin yunwa.
Bashir ya ce "A'a ba zai yiwu ba, sai ka ci abinci ko na koma da labarin da na zo da shi".

Da ?yar adam ya yarda a kawo masa chips, bashir ya din ga yi masa hira, tare da gaya masa ya kusa komawa abuja wurin aiki.
Adam dai bai iya tankawa ba, jira yake kawai ya ji me Bashir zai ce masa.

"Wai ni kuwa ya ake ciki da maganar binciken da ka ke yi ne, na mutanen nan mutane hukuma fa suke jira, su ji sakamakon binciken ku, gashi wa'adin da kwamitin da gwamnati ta kafa ya cika ya wuce, amma ba su ce komai ba, kaima kuma kun yi shiru.

Adam yayi ajiyar zuciya ya ce "Bashir, sawun giwa ya take na ra?umi ai, ?asar da ba ta damu da halin da al'ummarta suke ciki ba, tayaya zan cigaba da wahalar da kaina, a hukumar tamu ma kana gani sun rabu biyu, wasu suna goyan bayanmu wasu ba sa yi, a ?asa kuwa talakawa ne kawai suke supporting Winmu. Ni yanzu hankalina yafi karkata ga binciko wanda suke da hannu wurin sace matata, dan a jikina nake jin na jikina ne".

"Kenan kana nufin zaka fito ka cewa duniya sace matarka aka yi, bayan an gama jita-jitar a ?asar waje ta zo haihuwa ta mutu?"

"Bashir dole hakan zan yi mana, ba zan bar mutuwar aisha ta tafi a banza ba, ko da haka yana nufin zubewar kimata ne a idon duniya".

Bashir ya jinjina kai, ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ya Wan daddana sannan ya mi?awa adam.

Adam ya karSa ya fara dubawa, shafin wata jarida mai suna ciki da gaskiya ya buWe masa.
Yana shiga ya ci karo da hotonsa, tittle Win labarin aka rubuta dara ta ci gida.
Shahararren jami'in tsaron nan na farin kaya, mai jagorantar wata tawaga da ta zama babbar barazana ga manya Sarayin ?asarmu, ko kuma dai ace, shugabannin da yake yi wa sharrin sata, wato Adam Sharif Galadima. Kwanaki kaWan bayan kamala zaman makokin mutuwar mai Wakinsa, An bankaWo wani babban al'amari game da shi, in da lamarin mutuwar matarsa ya sha ban-ban da abun da aka sanar game da rasuwar ta ta, ashe ?an bindiga ne suka yi garkuwa da mai Wakinsa, har ta haihu a hannunsu, daga ?arshe ta rasa ranta.
A wata majiyar kuma, aka ce da sanya hannunsa a yin garkuwa da matar ta sa in da ya kasheta yayi tsafi da gangar jikinta, kwatsam wata yarinya ta zo da jariri a zuwan Wan matarsa ne, duk dan a Satar da hankalin mutane, da tunaninsu daga kan zargin shi wannan za?a?urin bawa da yake jin cewa ya fi kowa gaskiya da adalci, masu bibiyarmu ko menene ra'ayinku game da wannan labari?!

Hannun adam har rawa yake yi a lokacin da ya kammala karanta labarin, wani irin wahalallen gumi ya din ga tsatstsafo masa, ya aka yi maganar nan ta fita? Waye ya yi masa wannan yankan bayan?.
Jiki na rawa ya ajiye wayar, ya mi?e tsaye, jin kansa ya fara sarawa, yana neman rasa nustuwarsa, bashir ya tashi zai yi masa magana, amma tuni adam ya sulale ya bar wurin.

Kafin ya cimmasa, ya hau motarsa yayu mata key, ya fice daga restaurant Win da gudu.




08081012143

*Paid book ne ? 500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*



Gudu yake sosai a kan titi, Bashir ya hau motarsa ya bi bayansa, amma ya kasa cimmasa.
Ko da Adam ya ?arasa gida, wani irin horn ya din ga yi kamar tashin hankali. A gigice masu tsaron ?ofar suka buWe masa gate ya shiga da motar, ko da ya fito ko rufeta bai yi ba ya wuce sashin Ammi.

A can cikin gidan kuwa, bayan sallar isha'i, wata hadima ta shiga ta sanar da ammi cewar mummy na son ganinta.
Mamaki ne ya cika ammi, meya kawo mummy a wannan lokacin? Ba tare da wani Sata lokaci ba, ta tashi ta fita falonta, ta tarar da mummyn tare da autarta ru?ayya.

Ta kalli ammi ta yi murmushi ta ce "Barka da warhaka giwar mata".

"Barkanki dai, kuna lafiya?"

"Alhamdilillah, ya kuma mu ka ji da wannan lamari da ya faru?"

Ammi ta amsa da "Alhamdilillah"

"To Allah ya ji?anta da rahama"

"Amin ya rabb"

Mummy ta gyara zamanta ta ce "To, ni dai giwa idan wani abun na yi miki dan Allah ki yafe mini, ban san me na yi miki haka ba, ai ko ban samu shigowa ba, ya kyautu a ce kin aika mini jaririn na gani, nima jiakana ne, amma har su Fauziyya suka zo aka hanasu jaririn, yaran nan ko muna so ko ba ma so tsatsonsu Waya fa, wannan abun babu in da zai kaimu, ni dai ki yafe mini, amma a bani yaron na ganshi"

Ammi ta Wan dubi mummy, kamar ba a wurin zaman makoki suka din ga yi da ita a gabanta suna yasar mata da maganganu ba, ta basar ta ce "Bari a kawo shi ki ganshi" tayi maganar ba tare da ta tanka wancan maganganun da ta yi da fari ba.

Iman ce ta Wauko sabir, ta kawo wa mummy shi, ta sanya hannu ta karSe shi, tana wani irin murmushi ta ce "Tubarkallah masha Allah, wannan yayi wayo sosai, sai dai ni kasa gane ma da wa yake kama a tsakanin aishar da takawa"

Ammi kawai ta kalleta ba ta ce komai ba.

"To wane sunan aka saka masa?"

"Mahmud, ana kiransa sabir".

Da sauri Mummy ta kalli Ammi ta ce "Mahmud kuma? Sunan Mahmud ya ci kenan?"

Ammi ta ce "Eh, sunansa ya mayar masa"

Mummy za ta yi magana, Adam ya faWo Wakin kamar wanda ya ?wato a hannun miyagu.

Tun a falon ya fara Salle rigarsa, saboda wani irin gumi da yake yi, ?afafuwansa kamar ba zasu iya Waukarsa ba.

A gigice ammi ta tashi ta bi shi tana kiran sunansa, sai dai bai iya tsayawa ba, Mummy ma tashin ta yi ta bi bayansu, tana tambayar ko lafiya.

Kan gadon ammi ya haye, jikinsa ya fara wannan mazarin, kamar wanda ake bugawa gangi.

A gigice ammi ta ce "Iman, Wauko maganinsa maza"

Da hanzari iman ta fita ta bar Wakin, ammi Cikin damuwa ta ce "Takawa meyafaru ne? Meyake damunka?" Bai amsa mata ba, sai runtse idanuwansa da ya yi.

Iman ta dawo da jarkar maganin da ake shafa masa, ta buWe ta tsiyayo, ta fara ?o?arin shafa masa, amma ya juya kansa ya ce "Kar ki shafa mini, a hayyacina nake, jikina zai daina rawar ne, ku lulluSeni" duk yadda ammi ta so shafa masa ?in yarda ya yi, sai lulluSe shi da aka yi.

Bin maganin da kallo Mummy ta din ga yi, sannan ta ce "Wai giwa harzuwa wani lokacin zaki bar yaron nan ya cigaba da rayuwa da wannan larurar ba tare da kin nema masa magani ba?"

"Ina iya ?o?arina, Allah ne bai kawo ?arshen abun ba"

"To kina zaune Allah za kawo ?arshen lamarin, shi meye wannan Win da ake shafa masa?" Ganin ammi ba ta bata amsa ba ya sanya iman cewa "Magani ne"

"Mi?o mini na gani" ta yi maganar tana tsare iman da ido, iman ta Wauka ta mi?a mata, ta karSi jarkar ta din ga jujjuyata, tana nazartar meye a ciki, amma ta kasa ganewa, ta ajiye robar ta ce "Shikenan, ga wannan yaron, amma akwai bu?atar ki mi?e tsaye fiye da da, ko kuma ya dauwwama cikin nakasa" kamar dai Wazu, a yanzun ma ba ta samu amsa daga ammin ba.

Bashir kuwa tun da ya ga Adam ya Sace masa, ya ha?ura ya koma, dan bashi da tabbacin in da zai nufa ya bi adam Win, kuma ya kira shi bai Waga wayarsa ba.

***
Rumaisa kuwa zazzage kayanta ta yi da aka bata, na wurin Ammi da na turaki. Turmi biyar ammi ta bata na atamfar tare da turare mai ?amshin gaske.
Turaki kuma ya sanya an cika mata ledoji da kayan dubulan, da uban kilishi fal da soyayyen naman kaza, sai kuma turaruka, ga kuma nono mai kyau kusan galan guda da man shanu. Ruma ta din ga yashe baki tana murna.

Mama ta ce "Eh dole ki yi murna mana, a dalilinsa kin samu iyayensa sun yi miki sha tara ta arziki ke kuma kina yi wa Wan su rashin mutunci"

Ruma a ranta ta ce "Hmm mama ba zaki gane bane ba, baki san girman laifin da mutumin nan yayi mini ba, sai na

58 / 128