Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kanwar MAZA 1&2 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   113 / 128

336K to 339K   out of 382K words

Mahaifin Jaheed duk da k wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab a rik ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.? Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K UDIRAR ALLAH& .

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaWantar da ku, da WaWan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA Win sa ya kasance daidai da na yaron da bai taSa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ?uruciya har girmansa, bai taSa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ?udurar Allah. Masu bu?ata kai tsaye za su iya tuntuSar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)





Dur?sawa takawa yayi, ya Wauki sabir yana juyi da shi, yana murmushi, ya ce "I so much miss you darling, how are you?" Yayi maganar yana sumbatar goshin sabir.

"Paapa, daddy kaga" yayi maganar yana nuna masa in da Mahmud yake tsaye.

Kallon in da Mahmud yake yayi, yana mamakin saurin wayon sabir, ya Waga kai yana dubawa ko zai ga su ammi, amma babu kowa sai Mahmud.

Ya kira laila a waya, ta sanar masa da cewa Mahmud ya zo Waukarsa, zai fara masifa, ta kashe wayarta.

Mahmud kuma yayi banza bai ce masa komai ba, bashi da wani zaSi, illa ya je ya saka akwatinsa a boot, sannan ya buWe bayan motar ya shiga.

Har suka fara tafiya, babu wanda ya tankawa wani, sabir ne dai daWi ya isheshi na ganin mahaifinsa, ya kasa zama wuri Waya, sai ya taka cinyar adam ya mi?e yana taSo Mahmud "Daddy ka ga papa"

Mahmud yayi murmushi,yana shafo kan sabir da hannu Waya.

Takawa ya ri?e hannun sabir ya ce "Ina mimi?"

"Mimi, iman, baba" ya din ga jero wa adam sunaye, adam yana ta murmushi, yana jin yadda yayi kewar Wan nasa.

Tun daga bakin gate, security suke yi wa adam barka da zuwa, aka Wauki akwatinsa zuwa cikin gida.

Cike da Woki da son ganin mimi ya ?arasa sashin ammi, ammi ce ta fara taro shi, ta rungume shi, ya dur?usa ?asa yana gaisheta.

Ammi ta yi masa alamar ya tashi, ta sake rungume shi tana faWin "Barka da sauka, ya hanya ya makaranta?"

"Alhamdilillah ammi, na same ku lafiya?"

"Lafiya ?alau Alhamdilillah"

Laila ta ce "?an makarantar bokoko, sannu da zuwa"

"Yauwwa big aunty" yaran laila safiya, anam da haidar, suma suka taho da gudu, suka rungume takawa suna faWin uncle.

Nusaiba da iman ma duk sannu da zuwan suke yi masa, fuskokinsu, Wauke da tsantsar farincikin ganin dawowar ta sa, sai dai ya gama rarraba idonsa bai ga mimi ba.

Ya kalli iman ya ce "Amarya ba kya laifi, ya shirye shirye? Kodayake dole a zo a sake wani shirin, tun da na dawo".

Dariya suka yi gaba Waya, yana ta son ya tambayi rumaisa, amma kunya yake ji, kuma dai ya san suna cikin hutun makaranta.

Nusaiba ta kai masa akwatinsa Wakinsa da yake sashin ammi, takawa ya ce "Nusiaba ina mimi ne?".

"Wallahi ban sani ba takawa, anty laila zaka tambaya" ya jinjina mata kai. Ya shiga yayi wanka, ya fito falo, an shirya masa abinci a dining, sai dai ammi kanta ta lura yadda yake ta le?e-le?e, ta san ba kowa yake nema ba sai rumaisa.

Laila kuma ta zauna ta saka shi a gaba da surutu, ya dubi laila ya ce "Yanzu a gidan nan a rasa wanda zai iya zuwa a cikinku ya taro ni?"

Laila ta ce "To yanzu a ?afa ka taho? Ba Waukkoka aka yi ba?".

"Amma shi ne yakamata ya je ya Waukko ni?"

"Wannan kuma matarka za ka tambaya, da ta shirya hakan".

Ya kalli in da ammi take, ya ga ba ta jiyo su, ya ce "Yauwwa, wai tana ina ne?"

"Ita wa?"

"Meye haka ne, matata mana".

Laila tayi murmushi ta ce "Tana nan ?alau tana gaisheka"

Ya tsuke fuska ya ce "Wai meye haka ne? Dan Allah tana ina, ina son ganinta"

"Zaka ganta ne, kai dai ka kammala cin abincin ka huta"

Ya dire cokalin ya ce "ya haka ne? Watanni shida ba ma tare, na dawo kuma kin Soye ta".

"To wai me za ta yi maka ne? Sai mun gama jan aji tukuna".?

Yayi dariya ya ce "Jan aji, wane ajin kenan, ina fatan ba wata rigimar ki ka koya mata, in the name of jan aji ba?"

"You will see" tayi maganar tana dariya.

Mirsisi anty laila ta?i faWa wa takawa, in da rumaisa take, sai da ta kai ga ya cire kunya ya cewa ammi "Ammi wai ina maman sabir ne?"

Ammi ta ce "A'a bani zaka tambaya ba, ai dama da zaka tafi laila ka bawa ri?o, kuma da zaka dawo ta ce ba ruwana da abun ku, dan haka babu ruwana".

Wasa? har la'asar, tun yana tambayar har ya ha?ura, sai daf da magariba, laila ta ce masa jeka gida, zan kawota.

Da fari bai yadda ba, sai da ta rantse masa tukuna, sannan ya amince.

Da ya je ya tarar da gida ko ina tsaf, duk an sauya fasalin zaman furnitures Win, ko ranar da aka kai masa rumaisa, gidan bai haWu har haka ba.

Yana zaune a falo, yana kallon ?wallon dole, saboda ya ma rasa abun yi.
Ya ji maganganu ana hawowa sama, da sauri ya tashi tsaye, yana jiran isowarsu.

Laila ce da Iman, sai nusaiba, rumaisa ta du?un?une da mayafin lafayarta.

Murmushin sa ya faWaWa, suka matsa daga kusa da rumaisa, ta Waga kai ta kalleshi, ta sake rufe fuska tana murmushi, ?arasawa yayi gabanta ya rungumeta, yana murmushi.

Rumaisa ta rintse ido, saboda wata irin kunya da ta kamata, ganin yadda ya rungumeta a gaban su laila.

Nusaiba kuwa video take yi musu, tana cewa bari muyi ?ara'i tun da bamu yi a lokacin biki ba.

Ya Wagota yana son ?are mata kallo, amma ta hana shi damar hakan, sai cukuikuye jikinta take yi, mayafin gashi sai wani irin ?amshi ne kala? yake tashi daga jikinta.

Laila ta ce "Ku zo mu tafi, kar ya saka mini duka, saboda jan ran da na yi masa, ga ta nan ku cinye juna, ?arewar ?auna".

Adam ya ce "Eh Win, Allah ya bada lada, amma an wahalar da mu haba".

"Da ?afarka zaka zo nemana, zan rama ne" tayi maganar tana dariya, su iman suka bita suka tafi.

Suna tafiya, ya tsuguno dai-dai tsayinta, ya sake rungumota jikinsa, ya ce "I miss you little mimi"

Kasa magana tayi, kawai taji hawaye na zubo mata, jin tana sheshshe?ar kuka, ya sanya ya Wagota, ya ce "Yaya aka yi?" Kasa shiru tayi, ta cigaba da kukan.

Ya zauna da ita a jikinsa a kan kujera, ya ce "Gaya mini menene?".

"Ba kai ne ka daWe ba, kuma kwanakin suka ?i cika ba?"

Takawa yayi dariya ya ce "To ni na hana su cikar?. Allah sarki, duk murnar ganina ce har da kuka? I so much miss you dear"

Lafewa tayi a jikinsa, tana cigaba da kuka, cike da shagwaSa, ganin dawowar ta sa take yi, tamkar a mafarki.

"Mimi, meye sirrin ne? Kin ga yadda ku ka yi kyau kuwa, kalli skin Winki, duk da dare ne, kin yi fresh ga wani ?amshi mai daWi da ki ke yi, i like it baby"

"Baby kuma, kamar wata mijin anty laila, gursumemen dattijo wai baby, ni in dai zaka ce mini baby, sai ka sayo mini feeder, da kayan wasa"

"Ai na sani, ko shekara Wari za ayi, ba zaki canza halinki ba mimi"

Hira suka sha sosai, rumaisa ta din ga bashi labarin wasu daga abubuwan da suka faru, sai dai tafi karkata ga laabrai masu daWi da suka faru.

Haka shima ya din ga bata labarin makaranta, sai da suka raba dare a falon, ya ce suje Wakinsa su kwana, amma ta kada baki ta ce Ba zata kwana a gado Waya da shi ba, sai ka ce Anty laila.

"Au kina nufin laila ce mara kunya ko, sai na gaya mata. Kuma banda gulma ba sau biyu kina kwana tare da ni ba?"

"To ai wannan tsautsayi ne, Anty laila dai kama rayuwar turai ta ratsata, take gaya mini ita Waki Waya take kwana da mijinta, wai tare a kan gado ya rungumeta, ni dai wannan karatun nata ba Wauka nake yi ba. Dan ba iyawa zan yi ba"

Yayi murmushi tare da shafar sumar kansa, ya ce "Shikenan a sauka lafiya, tsarabarki sai Allah ya kaimu da safe"

Babu kunyar komai, ta wuce Wakinta.

Sai dai da ta tafi Wakin, ta kasa manta rungumar da yayi mata, haka ta shirya ta kwanta bacci, tana sake ganinsu a tare a cikin idonta, yana magana yana yi mata dariya.
Rungume pillown tayi, ta furta "papa a hankali"

Washegari da wuri ta tashi ta hau aikace-aikace, ta gyara ko ina duk da babu datti.
Ta shiga kitchen ta haWa abincin karin kumallo, ta le?a Wakin Adam.

Ya lulluSe jikinsa da bargo, saura fuskarsa kawai a ya bari a waje, baccinsa yake yi hankali a kwance, kai da gani ka san a gajiye yake.

Ta kalli agogon Wakin, tara da rabi na safe, a hankali ta ce 'Papa baka jin yunwa ne?'

Sai kuma ta tuna lecture malamarsu da ta laila, wai yadda ake tashin miji daga bacci.

Ta rife bakinta da hannunta ta ce "Ni, haka kurum in je in wani kama shafa shi, ina cewa ya tashi, kamar wani mage, ko Wan jariri, ai gara in daki ?ofa da ?arfi irin yadda mama take yi wataran a gida, idan haka ne abun, meyass a gida ba a haka ake tashin su Yaya usy ba? Kai anty laila bata da kunya, zaman turai duk ya canza ta'.

Ta gama soki burutsunta, ta koma kitchen tayi wanke-wanke.

Daga nan ta tafi Wakinta, yin wanka.

Sai dai ko da ta fito daga wankan, bisa mamakinta adam har ya tashi, dan ya ma biyota Wakin.

"Wai daga zuwana nayi wanke -wanke har ka tashi?" Tayi maganar a Wan tsorace tana rufe jikinta.

Maimakon ya amsa, kawai ya hau dariya, ta tsaya cak ta ce "Menene?".

Purple Win brezia da ta bari a kan gado, ta shiga banWaki, ya Waga mata ya ce "Meye wannan?"

Kame-kame ta fara tana son faWar abun da zata kare kanta da shi.

Ya ce "Inyeee mutuniyar, ai kamata yayi a nuna mini, ni dama tun da nayu hugging Winki jiya, i feel it but i thought na scam you wanta scam me, ashe na gaske ne, come let me see inyeee".

Shan kunu tayi ta ce "Papa bana so"

"Meye ba kya so kuma? Ganin kawai"

?arasowa tayi zata karSi breziar, amma ya ri?eta yana dariya, ta saka hannu ta ri?e towel Win ta gam, tana ihu.

"Ni wallahi da baka nan, nafi sakewa"

"Abun har da sharri, kamar ba jiya ki ka gama kuka ba, saboda kin ganni. Anyway, shirya ki zo mu yi breakfast, zamu yi magana"

Sai da ya bar Wakin sannan hankalinta ya kwanta, ta shirya, ta fito tana wani haWe rai.

Shi kuma ya ?ureta da ido, har ta zauna.

Ta?i kula shi, tayi serving Win sa, ta ja nata ta fara ci, duk yadda ya so ya maze kasawa yayi, dan yana jin daWin tsokanar rumaisa yaga ta haWe rai.

"Papa dan Allah ka daina kallona kana dariya, Allah zan tashi".

"Allah da iko yake, abun ne da mamaki, six months back, a ?wailarki na tafi na barki, amma in just six months ace lamari ya kankama haka, kuma kin ?i yarda na tabattar kar in je acuci ake yi mini.
Abunki ras da ke, ai ni yanzu kuma na daina takara da ke, na yarda yafi nawa nesa ba kusa ba, wane ni ma? Ai ni yanzu babu suaran jayayya, zaki iya rainon baby yanzu sosai, kai congratulations mimi, kamata yayi fa mu yi party, tare da celebration, mimi is no more ?waila, she's now a big girl, she can bear a baby, she even wore brezia size nawa ne ma ki ke sakawa, mu je mu sayo dozens of it" ?arshen ?uluwa rumaisa ta ?ule, ta jefa masa guntun ?ashin da yake hannunta, ta tashi za ta tafi. Ba dan ya iya shanye dariyarsa ba, ya ri?e ta yana cigaba da ?ya?yatawa.

Duk da tsiyatakun da yake tayi mata, ta kasa fushi da zuciya, watannin nan da yayi, ba ?aramin missing Win sa tayi ba, amma dawowarsa ya sakata a gaba da tsokana kamar tayi kuka.

Ta tafi kitchen yin wanke-wanke ya bita, ba abun da yake tayata, ya sakata a gaba da tsokana.
Ruma ta kalleshi, kamar ba shi ne idan ya kamile ya tsuke fuska, ko fara'ar kirki ba ya yi ba, yayi ta muzurai, mussman idan yana cikin shigarsa ta sarauta, amma yadda ya sakata a gaba sai ka ce yaya usy saboda tsokana.

Ya ?araci dariyarsa ya koma falo, ya cigaba da kallo, lokacin sallar azahar yayi, ya tashi ya fita masallaci.

Sai dai da ya dawo, har ta kammala girki, ta yi salla ta canza kaya, amma ta kima uban hijjabi, tana so ta ganshi sosai, amma tsiyar da yake mata duk ya takurata.

Ya Waga kai ya kalleta ya ce "Budurwar, meye haka kuma?".

"A ina?".

"Meye na wani saka hijjabi ana zaune ?alau, wannan abu na farinciki da ya same mu, gaskiya ban yadda ba".

"Allah papa zan tafi Waki na daina fitowa"

Ya ce "Sorry, ke kin san yadda na yi kewarku kuwa, tsokanar da na daWe ban yi miki ba nake fanshewa. Ya ?arasa wurinta ya cire hijjabin, tana ri?ewa amma ya cire shi.

Kasancewar ba a dining za su ci ba, suka zauna a ?asan carfet.

Ta janyo kwanukan abinci, da plate biyu, ya ce mata "an daina raba plate, a Waya zamu ci" ta tuna anty laila ta ce mata cin abinci kwano Waya da miji, yana ?ara soyayya, amma ita ba wannan ya dameta ba, sai tambayarta da tayi, to ba zai yi mini kishiya ba, laila ta ce sai kin kula da abubuwan da na koya miki tukuna.

Ta zuba abinci ta ajiye masa spoon, ya kalleta ya ce "Ke ni fa tun farko a baki ake bani abinci, ba zaki ajiye mini cokali ki maza ba".

"Ni zan baka abinci a bakin?".

"Eh mana"

Ta ce "TaS papa, ko jajjage baka yi mini ba da ina girki, ko sannu sai ma tsokanata da ka yi tayi, na gama abincin kuma sai na baka a baki, in bawa sabir abinci a baki, in bawa babansa saboda jin daWi".

Yayi dariya ya ce "To ki bari in baki, ai ni a wurina da ke da sabir, duk Waya, baku da wani banbanci dan abun da yake na shiririta kema yi ki ke" kan tayi magana ya Worata a cinyarsa, ya Webo abinci a cokali ya kai bakinta.

Rufe fuska tayi ta ce "Ayi haka? Kunya nake ji fa"

Sauke hannunta yayi, ya tura mata cokalin a baki, tun tana no?ewa ta saki jiki tana karSa, ta ce "Da na san haka bawa mutum abinci yake a baki da daWi, ai da na daina ci da kaina, idan na dafa sai ka bani a baki".

"Ni zaki saka aiki, yanzu ki ka gama cewa saboda jin daWi zaki bani abinci a baki, amma yanzu kina gaya mini, in din ga baki abinci a baki. Mara kunya kawai baby mimi an zama lady mimi"

"Wallahi idan ka ce babyn nan kunya ka ke bani, ga abinci a baki ga baby, idan aka ga na koma yin rarrafe kai ne ka ja"

Dariya Adam yake yi, rumaisa ba za ta taSa girma tayi hankali ba.

"Mimi, kin shiga kin fita kin hana auren jabir da iman, ki ka haWa da yayanki, kin saka jabir gaba da ni, Jamil ma har na je na dawo bai yi mini magana ba, gaba Waya fushi suke yi da ni, duk saboda ke mimi"

"A'a nifa ban hana aurensu ba, kuma can suka ?ulla soyayyar su da mai sunan baba, ban sani ba ina gefe ni ?arfafawa kawai nayi. Kuma papa kawai fa ban gaya maka bane ba, kar na zama munafuka kai baka san me jabir yayi wa ammi ba, wai saboda ba yi auren sa da iman ba, ka ja maganganun da ya din ga gaya mata? Wallahi sai da Mahmoud ya mare shi".

"Wane Mahmud Win?"

"Daddy" ta bashi amsa. Yayi shiru yana mamaki, ya san rumaisa ba za ta yi masa ?arya ba, yanzu har jabir zai iya kallon ammi ya ci mutuncin ta, matar da duk da abubuwan da mahaifiyar sa take yi mata, bai hana ta Wauke shi tamkar Wa ba.

"Papa ni fa wasu lokutan ba haka kawai nake tsanar mutum ba, da jabir sonka yake tsakani da Allah, kome ammi za ta yi masa, ba zai wula?anta ta ba. Shi kuma jamil sake bina yayi, wai sai na gaya masa yadda aka yi anty aisha ta Sata, da kuma in gaya masa abun da na sani a kan ta, na ce masa ban san komai ba, sai filin da gwamanti ta karSa a hannun turaki, ake bashi percentage ya sanya anty aisha a matsayin magajiyarsa, shi ne hankalinsa ya kuma tashi, ya ce kaine ka gaya mini"

Adam ya saka hannu ya juyo da fuskar rumaisa tana fuskantar sa, ya ce "Rumaisa, meyasa ba zaki daina yi mini yawo da hankali ba? Yanzu magana ake ta shekara guda da watanni, da Satan aisha, ba zaki tausaya mini haka ba, ki daina yi mini Soye-Soye? Kin bani zane ya Waga mini hankali, kuma ban gane komai a ciki ba Please rumaisa" Yayi maganar jikinsa a sanyaye.

"Papa ba laifina bane, laifinka ne haryanzu, ka wuce duk wasu matakai da yakamata, kuma ina iya ?o?arina na tallafa maka, Waya ya rage haryanzu, nima ba son raina bane in ta wahalar da mijina ba, baban Wa na"

"Wani mataki ne mimi?".

"Sauran ma ka tsallake su, ba tare da ka sani ba, wannan ma dan kan ka nake son ka yi surrender ka tsallake shi. Kullum ina yi maka Addu'a, duk wanda na yi wa abu yaji daWi, sai in ce ya saka ka a addu'a, komai zai zo ?arshe fa"

Jiki a sanyaye ya ce "Shikenan mimi, Allah ya yi mana jagora"

Ta Webo abincin ta kai bakinsa, amma ya girgiza

113 / 128