KANWAR MAZA 1&2 BY Aisha Adam (Ayshercool)

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   76 / 128

225K to 228K   out of 382K words

ba a yankinmu take ba, wurin da take da tsaro"

Baba lawalli ya ce "A'a ba sai an kai ga sayar da gonarku ba, in sha Allah zamu iya, zamu fitar da rumaisa kunya"

Mama ta ce "Duk da haka, Wawainiyar aure, ba nan kusa bace ba, kuma da amincewar ?an uwanta za a sayar". Haka suka cigaba da tattaunawa, a kan yadda abubuwa zasu wakana.

Bayan sun watse, mama ta kira ammi a waya, ta yi godiya, sannan ta Wora da ?orafin kuWin nan sun yi yawa.

Ammi ta ce "Ni dai babu ruwana, babanta turaki ne ya bayar da kuWin, kin ga babu mai ikon cewa a rage yayi yawa, kuma duk abun da zamu baku, ai bai yi yawa ba, mutum guda fa zaku bamu, ina musu fatan alkhairi sannan ina sake yi muku godiya da karamci. Sanan dan Allah kar ku ce zaku takurawa kanku, babu abun da zai gagara, komai za ayi in sha Allah, rumaisa kawai za a kawo mana".

Mama ta ce "Babu abun da zai gagara ma in sha Allah, Allah Ya sanya alkhairi"

"Amin ya Allah, zuwa jibi in Allah ya kaimu ma zai shigo wurinta, idan da abun da take bu?ata na shirye-shirye sai su shirya"

Mama ta ce "To babu laifi, Allah ya saka da alkhairi" da haka suka yi sallama.

Mahmud kuwa, haka nan ya ji zaman garin duk ya ishe shi, Alla-Alla yake kawai ya koma, saboda haka ya haWa kayansa ya tattara ya koma.

Iman ma, haka nan ta fara ciwon kai a tsaitsaye, abu kamar wasa, sai dai ta sha magani ta basar, amma ko sauka baya yi, yau da aka kai kuWin auren nan tana murna, sai dai a gefe guda kuma tana fargabar abun da Samha zata iya aikatawa.

Da sallama ta shigo, hannunta ri?e da jarkar lemo, mama ta kalleta ta ce "Sannu, sai yanzu ki ka dawo? Haka muka yi da ke dama?"

"Dan Allah mama kiyi ha?uri, wasa muke yi ne"

"Wane irin wasa?"

"Wasan ?ar carafke, ?ar gala-gala sai kuma na koya Habiba yadda ake faten tsaki"

Mama ta ce "Ko kuma zuwa ki ka yi kina gaya mata zaki yi aure?"
Ware ido rumaisa ta yi ta ce "Wallahi ni ban gayawa kowa ba, kawai wasa muka yi"

Aliyu ne ya janyo hannunta yana cewa "Ke, kin kusa zama matar aure, dole ki daina wannan yawon,tun da an kawo kuWin auren nan"

Sororo ta kalleshi ta ce "Wai dama da gaske ne?"

"Au, da da wasa ne? Dubu Wari biyar aka kawo"

Ta buWe baki ta ce "Haba duka nawa ne? A sai mini keke a ciki, da akuya in din ga kiwonta"

Abdallah ya tunsture da dariya ya ce "Ke tafi can, gado za a saya miki ?ato, da wardrobe da kayan kitchen"

Ta Wan yi shiru sanan ta ce "To duk a gidan nan za a zuba su? Shikenan sai mu din ga kwana da ni da mama a kai"

Usman da yayi alwala zai fice masallaci ya ce "Gado bana mama bane ba, naki ne da mijinki, a gidan da zaki zauna za a saka miki"

Kamar adam yana wurin ta ce "TaS, ai wallahi ba zai hau mini kan gadona ba, ta yaya mace da namiji zasu din ga amfani da gado Waya"

Usman bai kuma cewa komai ba ya fice, gaba Waya suka watse suka bar tsakar gidan, jin zata fara rashin hankalin nata.

Har bayan sallar magariba, zancen yadda biki zai gudana suke yi, ita kuwa ?asan zuciyarta ta kasa manta, abun da take gani a game da Adam.

Tashi ta yi kamar mara gaskiya, ta je kusa da mai sunan baba ta zauna, ta yi ?asa da muryarta ta ce "Mai sunan baba, dan Allah ka ara mini wayarka zan yi waya, na duba ta mama babu kuWi a ciki"
Sai da ta fitar da rai zai yi magana, sannan ya mi?a mata wayar, ta saka hannu ta karSa, ta yi masa godiya, ta tashi ta je in da ta kwafi lambar iman ta kirata.

Duk da iman tana jin jiki, amma ta dake jin muryar rumaisa ta ce "Amaryar takawa, takawarki lafiya"

"Anty iman, baki da lafiya ne?"

"A'a lafiyata ?alau, ashe an kawo to Allah ya sanya alkhairi ya Kaimu lafiya"

Rumaisa ba ta amsa addu'ar ba ta ce "Ina rabin ran, dama kira na yi ki saka masa wayar a kunnensa na yi masa magana"

Iman ta yi murmushi ta ce "Bacci yake yi, amma idan ya farka kan ki yi barci zan kiraki in sha Allah, dan na san idan ya ji muryarki zai yi miki gwaranci"

Rumaisa ta yi dariya ta ce "Ke kuwa Muryar mamansa fa, ki gaishe mini da ammi, ba zan barci da wuri ba".

"To shikenan, yauwwa ki na ji na?"

Rumaisa ta ce "Eh"

"Dan Allah anty rumaisa ki dage da addu'a, akwai ?alubale a wannan auren naku, kin san duk wani abun alkhairi zai fuskanci suka, ki yi ta addu'a, wannan familyn da kike shirin shigowa, akwai tarin ?alubale da rikici, wanda su ke taka rawa wurin damuwowin da baban sabir yake ciki. Dan Allah idan kin aure shi ki din ga tausaya masa, maraya ne da ?alubalen rayuwa ya sanya zuciyarsa yin rauni, ki yi ta yi muku Addu'a mu ma zamu tayaku in sha Allah".

"Ni ma marainiyar ce ai, kuma shi ?ato ne, ni yarinya ce ni zai tausayawa, ya daina hantarata da hararata ai" tayi maganar iyakar gaskiyarta.

Iman ta yi dariya ta ce "Zai tausya miki in sha Allah, sai mun yi wayar, kar ki yi bacci da wuri, na san dole zai farka da wuri"

"To shikenan ina jira" sai da aka fara yi mata warning ta cinye masa kati, sannan ta mayar masa da wayar
Wayar da tsoron mai ita bai sa kowa ya raSeta, amma rumaisa ta je ta kwantar da kai ta karSa.

Gaba Waya batun auren nan baya kan rumaisa, ta ha?ura da rigimar ba ta so, tun da mai sunan baba ya sanya baki, sai dai tana tsoron kar ta je Adam aljani ne.

Mama da murnarta ta sanar da takawa, duk yadda su turaki suka yi a wurin kai kuWin auren, da yadda ya din ga yaba dattaku da kuma kimar dangin rumaisa da yadda aka karramasu cikin mutuntawa.

Ba dan Adam yana jin daWin hirar ba ya cewa ammi "To Allah ya yi mana jagora"

"Amin, ko kai fa, dan Allah ka saki ranka a kan auren nan, ba zan yi maka zaSen tumun dare ba, in sha Allah rumaisa alkhairi ce a gareka da yaronka"

Ya jinjina kai ya ce "Yauwwa, Allah ya sa"

"Amin ya Allah, yauwwa ka san dama wata Waya aka saka, bana son ku zauna a gidanka da kuka zauna? da aisha, bana son ka din ga wani abu da zai Sata mata rai, na san ba zan hanaka tunanin matarka ba da ka rasa, amma idan kana son samu cikakkiyar dama zama cikin kwanciyar hankali da iyalinka, ka yi iya ?o?arin ka, ka din ga danne tunanin aisha a gabanta, sabon gidan nan na jambulo, a sake yi masa fenti, tun da dama sabo ne sai ta zauna a ciki".

Ya Wan yi shiru sannan ya ce "Mhmm, bai yi mata girma ba?"

Ammi ta ce "To ai gidanka na tudun yola, ya fishi girma, kuma nan gaba iyali zaku tara, kuma tana matarka dole a yalwata mata mazauninta".

Ya ce "To" dan jin batun tara iyalin yayi wani banbarakwai, zuwa yaushe kenan, ta gama girman da zata tara iyali?.

"Sannan jibi in Allah ya kaimu, zaka je ku tattauna, idan da wani abu da take bu?ata, ko take son ka yi mata, a harkar auren. Ba ina nufin na manta da mutuwar aisha bane ba, saboda abu ne da ba zamu manta da shi ba, musamman a yadda ya zo mana, amma rumaisa yarinya ce, aure abu ne da ake fatan ya zo wa mace sau Waya a rayuwarta, bai kamata a tauye mata hakkinta ba, ayi aurenta kamar mara galihu ba"

Baya son yi wa ammi musu, amma gaba Waya ba jin daWin maganar yake yi ba, shiyasa kawai yake bin ta da to.

Sai da ammi ta gama magana, sannan ya tashi ya tafi, dan gaba Waya yau ba a gidan yake son kwana ba.

Yayi nafilfilinsa na dare, yana addu'a, ya idar zai mi?e aka kira shi a waya.

Sunan Bashir ne ya bayyana a kan screen Win wayar, ya Waga tare da faWin "Malam bashir"

"YallaSai, ya gida ya aiki?"

"Alhamdilillah, ya naka aikin"

"Lafiya ?alau, dama na kira ne na ji, ko zaka shigo Win?"

Adam ya Wan yamutsa fuska ya ce "Bana jin daWi ne, sai wani lokacin kawai"

Bashir ya ce "To shikenan, Allah ya ?ara afuwa, lambar nan da aka fara kiranka da ita, bayan sace madam, Sidi yayi bincike a kanta, ya turo mini bayanan wanda yayi register da layin".

Da sauri Adam ya gyara zama ya ce "Tom ina jinka, ya aka yi, kun gano shi?"

"Eh to, babu wata nasara dai, a gombe aka yi register da layin, na tura wakilai har wurin, abun da dai muka gano, mai wayar wani bafulatani ne, daga bisani ya bar gombe, irin fulanin nan ne na tashi, ya koma katsina, sai dai a katsinan ma da na je, na tarar an kai musu hari a rigarsu, an ?ona musu dabbobi, dan haka bana zaton shi mamallakin layin shi ne wanda yake da alhakin garkuwa da ita, akwai dai yadda aka yi".

Adam ya yi wata nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin jiki ya ce "To shikenan Bashir, na gode da ?o?arinka sosai"

Bashir ya ce "Adam, dan Allah kar ka damu ko ka karaya, ba zamu daina ba in sha Allah, sai mun ga abun da ya turewa buzu naWi, ni dai jikina ya gama bani garkuwa da Aisha plan ne kawai, amma zamu cigaba da addu'a da kuma bincike"

Adam ya ce "To Allah ya iya mana".

"Amin ya Allah, ina boy, da rigimammiyar babarsa?"

Sai a yanzu Adam ya tuna an saka masa rana da shi da rumaisa.

Haka nan ya tsinci kansa da cewa Bashir "Yana nan ?alau, an saka mana ranar aure ni da ita"

Waro ido bashir ya yi ya ce "Rumaisan?"

"Mmmm" ya amsa a ta?aice.

Wata dariya ce ta ?wacewa Bashir ya ce "What a perfect match, amma kamar ta yi ?arama da yawa fa"

"To ya zan yi, biyayya ne ga umarnin ammi".

"Kuma in sha Allah ba zaka taSe ba, ni nayi maka murnar hakan wallahi, zamanku wuri guda zai sanya idan da wani abu da zai taimakawa bincikenmu da ta sani ta gaya maka"

Adam kawai ya girgiza kai, dan ya san azabar taurin kai irin na rumaisa kan a kai ga faruwar hakan, aiki ne ja.

"Na gode bashir, bari na Wan kwanta"

"To shikenan ango, Allah ya tashemu lafiya" Adam ya ajiye wayar, ya lumshe idanunsa, abubuwa daban daban, suka cigaba da karakaina a cikin kansa.

Mai sunan baba kuwa wanka yayo, ya zo ya yi shirin kwanciya, lokacin ?arfe goma da mintuna ashirin, har ya kwnata wayarsa ta fara haske, alamar ana kiransa.
Ya kalli wayar babu suna, dan haka ya gyara kwanciyarsa, sai dai har kusan sau uku ana kiran wayar. Ya saka hannu ya Wau wayar, ya kara a kunnensa.

?ar siriryar muryarta, mai cike da shagwaSa ya ji ta ce "Anty rumaisa, Allah ya sa baki yi bacci ba, gashi ya tashi"
Zirrrr ya ji wani abu ya tsirga masa, tun daga kansa har ?afafuwansa, yayi shiru bai ce komai ba.

"Anty rumaisa, ko kin yi bacci ne? Ki yi magana mana".

"Ta yi barci" ya faWa a ta?aice.

Babu tsammani ta ji muryar ta sa, a rikice ta ce "Innalillahi, yi ha?uri" ta kashe wayar ?irjinta yana bugawa da sauri-sauri.
Ajiye wayar yayi yana jan guntun tsaki, ya juya bayansa yana mamakin, yadda take sha?e muryarta a iya wuyanta tana magana, wata ?ar murya kamar ?ar tsanar roba.

Da asubar fari, rumaisa ta tashi ta fito, zata shiga banWaki ta tarar da mutum a ciki, ta zuba ruwa a buta, ta zauna a gefe tana hamma.
Gajiya ta yi da zama, ta ce "Wai dan Allah waye a banWakin nan, zan yi a tsakar gida fa".
Shiru aka yi ba a bata amsa ba, waWanda suka yi alwala suka fara tafiya masallaci.
Usman ne ya buWe ?ofar ya fito, yana hararta.

"Yaya usy wai dama kai ne a ciki? Wai dan Allah kai kullum sai ka yi wanka da asuba? Wankan me ka ke yi, ka yi da asuba, ka yi da safe zaka tafi makaranta, idan ka dawo da yamma ko da daddare sai ka yi, wanka da asuba ko sanyi baka...."

BuWe baki yayi ya ce "Zan ci ubanki, saka mini ido ki ke yi ina ruwanki da ni".

Aliyu ne ya fito yana dariya, ya ce "Malam ka yi mata bayanin wankan uwar me kake yi da asuba?"

Tsuke fuska Usman ya yi ya ce "Ba na so"

"Meye ba ka so, tun da ba zai gaya miki ba, in anjima idan ya zo Wakin mama ki tambayeta, wankan me yake yi da asuba?"

"Ai ba sai ta tambaya ba, ita da zata yi aure kwanan nan, za ta yi ita ma".

"Aliyu ya ce "Kai fa ba ka da hankali".

"Allah ya kiyaye, wallahi ba zan wanka da asuba ba, sau Waya zan din ga yi a rana, lokacin sanyi ma wataran ba zan yi ba"

Usman "ke dalla tashi ki bar wurin nan, munafuka cctv Camera, wuce ki je ki yi abun da zaki yi ko na karya miki wuya" tashi ta yi ta ja butar ta sum-sum ta tafi banWaki.

Yau asabar ce, dan haka bayan sallar asuba, mai sunan baba ya dawo ya kwanta barci, sai dai wajen ?arfe takwas na safe, wayarsa ta ishe shi da vibration a ?asan pillow.

Cikin bacci ya Wau wayar, ya saka a kunne yana lumshe ido.

"Anty rumaisa, barka da safiya jiya ki ka yi bacci na kira kin yi barci".

"Ke! Ba wayarta bace kar ki sake kirana wayata ce ba tata ba" a wannan karon ma ba ?aramar razana ta yi ba, cikin rawar murya ta ce "Yi ha?uri, na zata wayar mama ce".

"To ta umar ce, ki ka sake kirana ni da ke ne, an hana mutane barci tun jiya, ki yi ta wani yenyen, ba zaki buWe baki ki yi magana ba" ya ?arasa mitar yana kashe wayar.

Nusaiba da take gefenta ta ce "Wannan wane bala'e'en ne haka?" Iman ta girgiza kai ta ce "Ba kowa, ga Sabir nan bari na je na kwanta"
Nusaiba ta karSi Sabir, ita kuma ta tashi ta tafi Wakinta tana tunanin yadda mai sunan baba ya faWa haka take magana.

Sunansa da ya faWa umar ta sake maimaitawa, dole yayi masifa, ta faWa a ranta.

Tana shiga Wakinta ta ji tamkar an sha?eta, kuma ta kasa gaba ta kasa baya, hannu ta saka tana ri?e wuyan nata, amma ta ji numfashinta yana neman Waukewa. Cikin fita hayyaci ta sulale Jikinta ta faWi ?asa.

Can katsina kuwa, Gwaggo har da taka rawa saboda murna, tana faWin Allah ya dubi ?ar marainiyarta, za ta yi a gidan daraja, gidan sarauta gidan masu abun hannu.
Nan da nan ta ce ba zama, azo a kama wasu daga cikin dabbobinta a sayar, ta fara saye-sayen kayan da za a kai wa rumaisa.

Iman kuwa ba a tashi sanin halin da take ciki ba, sai bayan wasu awanni, da nusaiba ta ji ta shiru, ta shiga Wakin ta tarar da ita a ?asa a sume.

A kiWime ta je ta sanar da ammi halin da ake ciki, ranga-ranga aka Wauki Iman zuwa asibiti, ba tare da ta san waye a kanta ba ma.

***
Gidansu ruma kuwa, mama ma ta fara shirin tafiya kasuwa, domin fara saye-sayen da za a bu?ata, dan ba ta taSa kawo wa rumaisa aure yanzu ba, amma cikin ikon Allah, sai gashi ba tare da wani shiri ba, dan ko ?an kwanuka ba ta fara saya ba.

Rumaisa na uwar Wakan mama, tana ta zane-zanenta, mama sai mita take ba ta son zane-zanen nan, wata?ila ma zanen ne yake sanyata firgita cikin dare.
Rumaisa ta yi dariya ta ce "Haba mama, zanen ne zai tsortani, kin ganni nan kin san bana tsoron kowa sai Allah, balle wani zane".

"Kya ji da shi dai" ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yi maganar tana fita falo.

Yaya Abubakar ya yi sallama a falon mama, mama ta amsa masa ta ce "Garbatina ya aka yi ne?"

"Fita zaki yi ne?"

Mama ta ce "Eh, kasuwa zan shiga na fara saye-saye".

"To da magana nake son mu yi, amma idan kin dawo ma yi"

"A'a, zauna ka gaya mini sai na fita"

Suka zauna, Abubakar ya kalli mama ya ce "Mama, kamar yadda muka yi da ke, na je na Wan zazzaga unguwar ina tambayar ya yanayin gidansu yake, da kuma shi kansa mu'amalarsa da mutane, to sai dai sakamakon baki ya rabu biyu. Wasu suk ce mutumin kirki ne, mai yawan kyauta, da girmama mutane kuma miskili ne, wasu kuma sun ce ba shi da kirki, yana da faWa da zafin rai wai kwanan nan ya taka ?aninsa da mota, ba wannan ne ya fi Waga mini hankali ba, wai ana kyautata zaton maye ne, kuma yana da taSin hankali!!!

Ayshercool
08081012143

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar

76 / 128