AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   76 / 77

225K to 228K   out of 230.9K words

ta daina kiransa, haka su Abbu ma sunyi tsittt kamar ruwa ya cinyesu a ɗakin. Fin minti biyu yana mata wannan kallon kafin ya sake ƙoƙarin jan idanun zai rufe Abbu ya kira sunansa shima..
       “Ajwaad!!”.
    Luuuu ya sake ƙoƙarin buɗe idanun ya saukesu akan Abbu. Murmushi yay masa, sai kuma ya nuna masa Maanal. “Kasan wannan?”.
      Idanun nasa ya juya a hankali ya sake maida su kan Maanal da Abbu ya nuna. Ɗan sake kafeta yay da kallon kafin ya maido idanun kan Abbu ya jinjina masa kansa alamar ya santa. Murmushi Abbu yay da jinjina kansa ya ce, “Alhamdullahi minene sunanta?”.
        Idanunsa ya ɗan rufe kamar yanda ɗabi'arsa take musamman a lokacin da bai son yin magana, kafin ya buɗe a karo na farko ya motsa pink lips ɗinsa da suka tattare waje ɗaya suka bushe kaɗan ya furta, “Besty”. Babu wanda yaji sautin muryar amma sun fahimci abinda ya faɗa daga motsin laɓɓansa. Cike da gamsuwa fuskar Abbu da murmushi ya nuna kansa shima ya ce, “Nifa?”. Nan ma lips ɗin ya motsa kawai ya ce, “Abbu!”. Nan ma Abbu ya jinjina kai ya juya ya nuna masa RK ya ce, “Wannan fa?”.
      A mamakinsu sai ya kauda kai yaƙi magana. Abbu ya sake maimaita masa, batare da ya juya ya kalla RK ɗin ba ya ɗan jujjuya kansa alamar bai sanshi ba. Kasa haƙuri RK yay ya fashe da dariya. Abbu ma dai murmushi yake sosai. Su dai sauran likitocin basu fahimci abinda ke faruwa ba sukam, amma sunyi mamaki da yace bai sanshi ba. Maanal da abin ya bama mamaki itama ta ce, “Rafeeq ɗin ne baka sani ba?”.
       Idanunsa ya ɗaga a hankali ya zuba mata, itama kallonsa take fuskanta da mamaki har yanzu. Cikin dariya RK yace, “Barsa daughter, zan fasa tariyar taki ne har sai randa ya fara ganeni ɗan rainin hankali”.
      Barin wajen Abbu yay yana dariya da girgiza kai, yayinda AA ya ɗan juya ido alamar don hararar RK yake son yi amma idanun sun masa nauyi, sai ya sake jimƙe hannun Maanal da ƙarfi har sai da ta saki ɗan ƙara dan dama a takure take dama, hannun ya mata tsami sosai. Karo na farko AA ɗin ya kalli abinda ke cikin hannun nashi, da mamaki ya zubama hannun nata mai zane da lalle raɗam idanunsa kumburarru. Fuskarsa na nuna mamaki ya juya ya kalleta, fuska ta ɓata sosai da tura baki gaba. Idanunsa kawai ya rufe, dan a karo na farko sai ya fara jin kamar mafarkin daya saba ne. (Wai ya akai ma ta kasance a kusa da shi, hannunta kuma cikin nashi? Ya rabba) Ya ayyana a zuciyarsa yana sake buɗe idon dai a kan hannayen nasu dan ya yarda kawai mafarki ne.
           Cike da shaƙiyanci RK ya duƙo saitin kunnensa ya raɗa masa, _“Kada ka wani firgita kanka yanzu kam HALAL ce. Besty ta zama mallakin Besty yarona”. Da sauri AA ya juya yana kallonsa. RK ya kashe masa ido ɗaya”. Harga ALLAH daburcewa AA yayi, sai numfashinsa ya nema fara wani irin fisga. Dai-dai nan Abbu da yaje yayma su Oum albishir ɗin farfaɗowar AA ɗin ya sake shigowa. Da sauri ya ƙaraso gaban gadon yana faɗin, “Subahannallahi mi kuma ya faru?”.
      Kallon da sauran doctors ɗin kema RK yasa Abbu kallonsa shima. “Miya faru Rafeeq?”.
        “Relax Abbu babu komai fa. Kawai na masa albishir ne”.
   Baki buɗe Abbu ya ce, “Amma kasan zaka iya maida shi cikin suma wane irin likita ne kai?”.
      Dariya RK yay. Ya ce, “Ai karka wani damu Abbu koya suma sai ya sake farfaɗowa. Ɗan rainin wayon bani yace bai sani ba”.
    Da sauri Abbu ya jawo abu alamar zai daki RK, aiko ya fita da gudu yana dariya.....

    _____________★

         Sai muce Alhamdullah, zuwa bayan sallar la'asar AA da aka saka barcin awoyi dan brain ɗinsa da zuciyarsa su zama fresh ya sake farkawa. Zuwa yanzu dai kam anata shiga duba shi, dan har an canja masa ɗaki ma. Maanal dai tun da ya fara barci suka wuce gida ran Oum fes, dan anayin azhar aka fara gudanar da walima. Bayan an idar da la'asar akai buɗar kai, a kuma lokacin ne AA ya farka acan asibiti su Abah zagaye da shi. Dan duk mazan ne dai yanzu matan duk suna gida wajen walima. Duk da dai hankalin Oum da Maanal duk yana asibitin amma suna daurewa ne kawai na dole. Hakama Mamy da gaba ɗaya take a jagule dan ko wajan walimar bata zauna ba, sai ma ƙirƙirar barin gidan da sukayi ana fara walimar zuwa can gidan babbar yayarsu. Acan suka samu damar baje zantukan bakinsu yanda ya kamata. Da tsare-tsaren yanda zasu cimma Maanal da Oum, dan yanzu kam dai yaƙin ya zame musu biyu. Sai batun Nuratu da suke tunanin Darma Family ɗin da zasu iya cewa bazai yiwu a wannan satin ba saboda halin da AA ɗin ke ciki. Dan haka hankalinsu a tashe yake tannan ɓangaren shiyyasa suketa faman tausar Mamyn akan son birkicewar da take neman yi....
         Shida na yamma aka kammala komai da komai, aka shirya amare domin musu rakkiya. Nuwaira gidan Abbu za'a kaita ɓangaren RK daya sha gyara, sai daga baya zai ɗauka abarsa su wuce Abuja tunda can rayuwarsa take shi. Sai Raihana haɗaɗɗen gidan Uncle Najeeb dake kusa dana Baban Yola shima dai, hakama su Modibbo duk kusa da kusa suke. Wannan kusan aƙidar Darma family ce, da wahala kaga yaransu sunyi nesa da su.. Maanal dai tana nan gidan Baba Sardauna su sai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce Abuja. Danginta dai da ƙawayenta da suka zo wajen walima duk a ranar suka tattare a can gidan da suka sauka. Suma dai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce Kaduna. Su Didi wayo sukaima Maanal akan zasu dawo gobe suka gudu, dan haka ta sakankance da hakan. Ga kuma Najma na ɗebe mata kewa ga Oum. Dan yanzu tana a ɗakin Oum ɗinne. Zuwa bayan isha'i gidan Baba Sardauna ya rage mutane sosai, dan wasu zasu kwana a gidan Baban Yola da gidan Abbu ne da sauran gidajen ƴan uwa. Zuwa safiya kowa ya kama gabansa, dama dai danginsu ne na Yola sukafi yawa. Sai dangin mahaifin su Nuwaira da ƴan kura dangin Abbu.
        Kusan takwas da rabi Oum ta saka Maanal shiryawa dan zasuje asibiti sake duba AA, duk da Fawzan ya kira Oum yana sanar mata Autan nata ya saka bore shi sai an sallamesa sai da Abah yay masa jan ido da Abbu sannan. Amma yace shi gobe babu wani asibiti da zai wuce gida zaije, tunda an sanar masa gobe zasu wuce Abuja. Ji Maanal tai kamar ta langare tace bata da lafiya. Dan dama ɗazun allurar da akai masa ce ga ceceta suka gudo. Amma babu yanda ta iya dole ta shirya ɗin suka wuce. Sauƙin ma basu kaɗai bane. Harda Umma, Hajiya Majdiya, Mamy, da wasu sauran dangi da suka rage manya. Sai ita sai Najma a yara da su Saheeba. Sun iso asibitin abin mamaki suka sami ƴan uwan Mamy harda Nuratu da basu san sanda ta zo Kanon ba. Dan tunda aka fara bikin nan babu ita. Tunda Mamy taga Nuratu take ta faman murmushi, yayinda Nuratun babu kunya ta wani rungume Mamy. Su Mamanta kuma suna gaisuwa da su Oum.
         Sai da aka gama gaishe-gaishen sannan suka shiga, dan suma su Nuratun isowarsu kenan ashe. Oum dake riƙe da hannun Maanal ce a gaba, sai Umma sannan Mamy da Hajiya Majdiya dake a jere. Bayansu su Nuratun ne da su Shaheeda. Zaune yake kam yanzu an ɗan ɗago gadon ta saitin kansa sosai sama sai ya zam ya jingina. RK na tsaye a gefensa yana cire masa drip, babban yaya a kujera, Fawzan a gadon kusa da ƙafafunsa da kofi a hannu, sai Uncle Mahmud da Uncle Hussain nata ɗayan gefen zaune a kujeru suma. Yanda fuskokinsu ke wasai zai baka tabbacin hira suke cike da nishaɗi. Yayinda AA ke ɓata fuska yana kallon kofin shayin hannun Yaya Fawzan da alamu suka nuna shi zai ba mawa. Sannu da zuwa gwarazen mazajen kema iyayen nasu, suka kuma shiga tashi domin basu kujerun. Yayinda AA ya zubama Maanal idanunsa shanyayyu har yanzu. Ita ko tunda dai masa kallo ɗaya ta janye abinta kanta ma a ƙasa take gaida su babban Yaya. Cike da neman magana Ya Fawzan ya ce, “Kai Alhmdllh gara ma dai da kuka zo. Lilly zo kiji da mijinki dama daru yake ma mutane yaƙi cin abinci”.
       Ji Maanal tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige. Ta sake riƙe hannun Oum sosai cikin nata tana matsawa jikinta. Murmushi Oum tayi da faɗin, “Kace kana nan kana takura min shi da takurarka”.
         “Oh Oum hakama zakice. Shikenan wlhy Lilly zauna ku ƙarata tunda babarsa ma maimakon ta gode min kinji mitake faɗa.”
     “Eh anji ɗin”.
Cewar Oum tana zaunar da Maanal a inda Fawzan ɗin ya tashi kusa da AA kenan a gadon jiyyarsa. Ta kuma amshi tea ɗin ta miƙa mata. Kuka kawai ya rage Maanal ta saki dan kunya. Dan yanda ta kalla Oum kamar zata fasa ihu. Amma sai Oum ɗin tayi kamar bata gani ba ta damƙa mata kofin a hannu. Dariya su Umma daketa tsokanar Maanal irin wasan kaka da jika tun jiya take musu. Ta zauna a kujerar da Babban yaya ya tashi yana gyara mata tana faɗin, “Ɗan nema, ni zaka kalla ba ita ba ai, kasan dai da tsohuwar zuma ake magani”.
       Dariya su Oum sukayi, AA daya shagala a kallon Maanal tun ɗazun ya janye idanunsa a hankali yana ɗan murmushi saboda zancen Umma. Dama shi bai iya maida wasa sai Fawzan da Babban Yaya. Kosu kakanni sukai masa iyakarsa murmushi ne. Umma ta riga ta san hali dan haka bata damu ba ta maida kallonta akan Maanal da tunda Oum ta damƙa mata kofin shayi ta kasa motsi. “Maanal matsa ki bashi kada ya huce kinji, idan ma dan nice bazanyi kishi ba, zan daure na haɗiye ko iya na yau ne tunda amarya kike. Amarya kuma ance kota buzuzu ce daɗin suna ne da ita”.
     Dariya su Fawzan suka sanya. Hakama su Oum.........✍️

09032345899


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*





*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖1️⃣0️⃣2️⃣


______________





........Babu yanda Maanal ta iya ganin hankalin su Oum ya koma a gaishe-gaishe da su Uncle Mahmud dole ta matsa kaɗan zuciyarta na wani irin bugawa, jikinta na gogar ƙafafunsa musamman ta wajen gwiwa zuwa cinyiyinsa kaɗan saboda yanayin zaman nasa. Batare data kallesa ba ta miƙa kofin shayin kusa da bakinsa.
        Idanu ya ɗan zubama kofin kafin a hankali ta yanda ita sai wanda ke kusa da su gab suka ji ya furta, “Idan da zafi kuma fa, baki sha kinji ba sai ya ƙona ni?”.
     Idanunta da suke ɗan tara ruwa na kunya ta ɗago ta ɗan kallesa, sai ya wani sake narke nasa dake kallonta ƙasa-ƙasa yaɗan matse fuska. Da sauri taja numfashi tare da jan hannunta baya, kamar zatai kuka ta ce, “Babu fa wani zafi”.
       “Ban yarda ba kisha na gani ”.
   Ya faɗa kamar mai raɗa. Kaɗan ta hararesa sannan takai kofin kusa da bakinta a kunyace ta ɗan sha. Shi ko ya wani zuba mata ido kamar ya manta da basu kaɗai bane ba fa. Sai da ta sake maido kofin kusa da bakin nasa tana ɗan tura baki sannan ya janye idanun lips ɗinsa suka motsa kaɗan kamar zai yi murmushi. Maimakon ya amsa a haka sai ya ɗaura hannunsa a hankali saman nata dake riƙe da kofin a haka ya kai bakin nasa. Lumshe idanunta tayi tsigar jikinta na tashi....
      Duk da wannan abu dake faruwa akan idon Mamy da Nuratu, Nibras, Saheeba da Mamansu da yayar Mamy ne. Dan su amaimakon gaisuwa da hirar da akeyi a ɗakin hankalinsu na kan AA da Maanal ne. Suko su Oum hirarsu suke cike da dattako sun basar kamar basa ganin komai. Yayinda Hajiya Majdiya ke karance yanayin su Mamy ɗin tsaf tanama RK nuni da idanu. Shi dai murmushi kawai yayi dan abun nasu Mamy ma dariya ya bashi. Dan duk da Mamy ɗin na ƙawata fuskarta da murmushin dannewa mai hankalin daya saka mata ido zai fahimci ranta a dagule yake. Nibras kam tuni ƙwalla sun cika mata ido, dama kwana biyun nan hankalinta a tashe yake, ko bikin bata so zuwa ba amma ta rasa ta hanyar da zata zame tunda tasan Mamanta bazata barta ba, ace ana bikin gidansu da family ɗin mijinta gaba ɗaya babu ita zai zama abin magana. Wata kalar tsanar Maanal take ji mai tsannanin gaske. Hakama Nuratu ta kumbura tayi fam kamar ta shaƙe Maanal take ji. Dan har ƴar zabura tayi kamar zataje kansu Mamy ta damƙe mata hannu a kaikaice. Saheeba kam nata faman taɓe baki.
      Oho su masoyan ma basu san anai ba. Musamman Maanal ma data juya musu baya. AA kam ta shan shayinsa yake ko gaishe shi da sukai kowa bai kallaba a cikinsu dan baima san waye da waye ba, babu wani daɗewa sai gashi ya shanye tas, a take zufa ta shiga tsatstsafo masa a goshi. Aiko sai Fawzan da RK suka samu na tasashi a gaba da tsokana. Wai gulmamme ashe yana jin yunwar yaketa basu wahala tun ɗazun da yake su ya raina su. Yanzu da yake Bestyn sa ce ta bashi gashi ya shanye babu ko gargada. Harararsu kawai yay ya ɗauke kansa, sai Oum ce ke tare masa su Umma da su Uncle Mahmud na dariya. Mamy dai ta ɗauke kai ita adole bata san anai ba. Tsabar neman magana irin na Hajiya Majdiya sai ta ciri tissue dake a bed side drawer ta miƙama Maanal tana faɗin, “Daughter share masa wannan gumin goshin kinji. Son ko zaka ƙara da wani abun? Kaga farfesu nan Oum ɗin ka ta maka da kanta yanama ina?”. Ta shiga waige-waige. Miƙo mata Najma dake kusa da Yaya Fawzan tayi, dan itama fa a bikin nan ita da Yaya Fawzan wani al'amari ne mai girma ke neman shiga. A mamakin kowa babu musu AA yace zai ci. Aiko Maanal ta tura baki gaba tana kai tissue ɗin da Hajiya Majdiya ɗin ta bata saman goshin nasa. Yanzu ma hannun nata ya riƙe a haka aka goge gumin tana jin kamar ta fasa ihu dan kunya.
     Tsaf Hajiya Majdiya ta zuba farfesun a ƙyaƙyƙyawan glass bowl ƙarami ta miƙama Maanal. Cikin marairaicewa Maanal ta ce, “Ummy zaifa iya ci da kansa”.
    Daƙuwa Hajiya Majdiya ta mata da faɗin, “Ungo nan, ashe inada sauran tsalle sai na zauna na sake miki sabon karatu kuwa, dan in kinji ana uwar zamani nice nan, maza bashi bawan ALLAH yaci daga ciyarwarki ya godema ALLAH wannan ramar duk ta ɓace yayi angwancinsa kamar sauran baby muke so da wuri in sha ALLAHU nan da wata goma muna nan a Kano kamar haka taron sunan ƴaƴa da jikoki”.
      Abu Oum ta ɗauka ta kaima Hajiya Majdiya kamar zata daketa ta ce, “Kedai Majdiya anyi uwar banza wlhy”. Da sauri ta kauce tana dariya. Hakama su Umma da su Babban Yaya kai kawai suka kauda gefe suna dariya. Yayinda takaici ya turniƙe su Mamy har wuya. Maanal kam jitai kamar ta zura da gudu daga Kano har Kaduna a ƙafa. Da yatsa AA da kansa ke a ƙasa yana wani munafukin ɓoyayyen murmushi ya ɗan takali hannun Maanal cike da tsokana. Ƙin kulashi tayi, sai da taga ya cigaba ta ɗan kalla gefe da gefe da ido taga kamar babu mai kallonsu takai hannu ta mintsini hannun nashi...
       “Ouch!! Oum kingata ko”. Ya faɗa a hankali yana ɓata fuska.
   Juyowa Oum tayi, yayinda Maanal ta daburce mamakin AA ɗin na neman halakata. Ganin yanda Maanal ɗin tai tsuru-tsuru da ƙyar ya danne dariyar dake neman suɓuce masa, cikin wayancewa ya ce, “Yunwa nake ji Oum ki amsa ni to bani tunda ita bazata ban ba”.
        Cike da lallashi Oum ta ce, “Kwantar da hankalinka zata baka. Babyna kinga bashi kada ya huce. Kinga magani zai sha.”
      Kai Manaal ta iya jinjina ma Oum kawai, ta ɗiba naman takai bakinsa, ido ɗaya ya kashe mata tare da ɗan dallo halshensa kaɗan alamar gwalo. Itama cike da haushi da shagwaɓa ta ce, “Oum kinga yana mun gwalo”.   
          Da sauri AA ya waro idanu waje yana nuna kansa. Yayinda Oum ta kai masa ɗan rankwashi tana faɗin, “Auta ka kiyayen ALLAH bar ganin baka da lafiya. Dama ka samu take baka”.
      Duk wanda yasan rayuwarsu yasan wannan ba komai bane. Dan haka Fawzan karaf yace, “Aifa yanzu munga takanmu. O'e tsokanar faɗa, o'e kai ƙara”.
       “Kai kuma sa ido ba”.
   Cewar AA yana hararrasa.
Babban Yaya ya ce, “Sana'ar banza kuwa nan yafi afki”.
     “Oh haɗin kan zai dawo kenan?, ALLAH yaso nima yanzu ina da magoya baya. Ga Naufal, Anum, Saheeba ga Nibras”. Fawzan ya faɗa yana kallonsu a ɗage.
       Sosai abun ya bama su Umma dariya ya kuma birgesu. RK ya ce, “Nima kuwa ina bayanka Son. Suje suyita haɗin kan mana ganinsu a rana ba wuya zai yi ba”.
     “Aniyarka ta bika, ai dama halinka ya kwaso kwabo da kwabo”. AA ya faɗa yana jifan RK da spoon ɗin cikin farfesun hannun Maanal. Cafe cokalin RK yayi, ya ce, “Eh lallai ai

76 / 77