Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
canja daga hakan.. ƙiri-ƙiri da zai shiga gida yace tazo suje taƙi. Dole babu yanda ya iya ya barta wajen Alhaji kamar yanda ya roƙa.
Yini guda Maanal na tare da Alhaji Aliyu Darma, Tare da yaransa uku da tuni ta saki jiki da su. Musamman Ajwaad da tunda ya fito da kayan wasansa ta naniƙe masa. Lokacin da rana tayi sai ga Shahidah da kula cike da alala an kawo musu. Sosai Alhaji Aliyu ya nuna jin daɗinsa tamkar ya ari baki dan godiya. Anan ma Shahidah tayi-tayi Maanal ta bita suje gida amma taƙi. Dole ta barta itama ta tafi. Sai da akai la'asar sazu tafi sanan su Fawzan suka rakata har gida da ledan kayan ciye-ciye da kulan da aka kawo musu alala sukai godiya. Yayinda ita kuma ta shiga kuka saita bisu, sai da Baabu ya mata tsawa sannan ta nutsu. Dan a duniya Maanal na tsoron hargagi musamman na Baabu..
Wannan rana itace sanadin tarayyar waɗan nan ahali guda biyu. Dan kuwa washe gari sai ga itama mahaifiyar su yaran ta biyosu domin yin godiya. Anan ne kuma ta tarar da Ammie nama wata amarya gyaran jiki, itama tace ai sai ai mata kuwa.. tunda tazo Maanal na manne da ita. Kasancewar yaranta ita duk maza ne tana masifar son ƴar budurwar yarinya, shiyyasa tana ganin Maanal da jiya tasha labarinta a wajen ƴaƴanta yarinyar ta shiga ranta. Ga wayonta da surutunta na sakata nishaɗi. Yau ɗin ma dai da ƙyar aka raba Maanal da su, musamman Ajwaad da wasansu na yau yafi na jiya armashi. Dan yau ya saki jikinsa ba kamar jiyan ba. Haka yake bashi da saurin sabo sam, akanyi baƙi a gidansu kwana da kwanaki babu ruwansa da su, dan shi yarone mai irin shegen tsantsenin nan, ga zuciyar tsiya da ƙulafucin iyaye. Ammafa idan ya soka to yaso ka kenan. Idan kuwa baka masa ba to babu abinda zakai masa ka birgesa ko kaja ra'ayinsa da shi. Shiyyasa a yau ɗin ma mamakinsa ya kasa barin Oum ganin yanda ya saki jiki a gidan tamkar a gidansu. Dan duk inda kaga Ajwaad yaje yaci maka abinci kansa tsaye to lallai yanayi da masu gidan....
★★★
Kafin Alhaji Aliyu ya kwaso iyalansa su tare a sabon gidan nasu daya haɗu matuƙa gaya shaƙuwa da zuminci mai ƙarfi ya shiga tsakaninsa da iyalan Baabu ta yanda har suna kallon kansu tamar wasu ƴan uwa na jini. Oum ba itace kawai matarsa ba, ashe tana da amarya ma, sai da suka tare su Ammie suka sani. Bayan tarewar tasu kuma sai al'amarin ya ƙara ƙarfi fiye da tunanin mai hasashe. Ba shaƙuwar ahalin biyu ne kawai abin mamaki ba. Wadda ke a tsakanin Ajwaad da Maanal tafi zama abin kallo ga kowa. Dan takai a yanzu ako ina ɗaya yake ɗaya na wajen, shiyyasa idan baka sani ba baka taɓa gane ainahin gidan kowannensu. Dan takai yanzu ma Maanal taƙi zama a makarantar da take yi da yan uwanta. Da safe anta dagama kenan tace ita Ajwaad zata bi tasu makarantar. Anyi lallashin, an daka, anyi kurarin duk a banza. Hakan yasa Alhaji Aliyu roƙar Baabu damar maida Maanal makarantar su Ajwaad ɗin, kasancewar itama tana tare da Nursery, primary harda da secondary ne a tare. Daƙyar Baabu ya yarda dan bashi da yanda ya iya, haka aka maida Maanal makarantar su Ajwaad amma a ɓangaren Nursery. Shiko yana a primary 3 ne. To ashe rigima bata ƙare ba, dan kuwa Maanal sam bata zama ajinsu saina su Ajwaad. Anyi-anyi amma taƙi, da malaman sukaga tanada ƙwalwar karatu matuƙa, dan duk abinda akayi kafin kace me ta ɗaukesa a kanta harma tafi wasu ƴan ajin sai kawai aka ƙyaleta. Dan koma an kaita can ɗin ba zama take yi ba, sai dai taita jibgar ƴaƴan jama'a tana kukan ita dai wajen AA zataje. (Dan itace ta saka masa AA daga ji Oum ta faɗa ta kama ta haye tana kiransa AA).
Hajiya Maanalu mai abin mamaki kenan. Dan daga Nursery 2 dai tuni tayi jumping zuwa primary 3 abinta. Hakama a islamiyya tuni ta koma ajin su Ajwaad. Dambe da rigima kuwa sai abinda ya ƙaru. Duk da tana a cikin waɗanda suka girmeta kullum cikin takalar tsiya take. Taimaka rashin kunya kace zaka daketa ka gamu da Ajwaad. Dan duk abinda zai taɓa Maanal a duniyar nan Ajwaad baya ƙaunarsa. Hatta Ammie idan ta daki Maanal sai taga fushi a fuskarsa. Idan ko su Shahidah ne duk da sun girmesa koda yake kusan sa'an Amaal ne yana girmeta kaɗan sai fa yarama mata. Idan kuwa yana gidan tai laifi Ammie tace zata daketa sai yaje yace shi a dakesa a maimakonta, idan kuma ta riga ta ritsata tana duka zaije ya kareta shi a dake san. Idan abu aka bama ɗaya ɗaya bazai taɓa cinsa ba sai ɗaya na nan. Hatta da kaya ya koma yanzu iri ɗaya ake musu, idan kuma ya banbanta na mace da namiji kamar atamfa, lass, yadi to dole a ɗakko kala guda. Ajwaad shine tsifar kan Maanal, shine rakata kitso, shine wankin ƙananun kayanta irinsu pant, hula, vest da sauransu. Haka shima nashi idan zai yi tare zasuyi tana jagwalgwalo. Tun ana ɗaukar abun nasu wasa har kowa ya fahimci ba wasan bane aka kawo ido aka zuba musu. Sai dai iyayen na matuƙar kulawa da duk wani motsinsu saboda tsoron bin wata hanya mara ma'ana da a yanzu har yaran akan samu a ciki....
Alhamdullah a yanzu dai haka Maanal nada shekara tara cif a duniya, yayinda Ajwaad keda goma sha biyar. Suna a ajin ƙarshe na primary. Kasancewar Ajwaad nada tsayi kamar ƴan uwansa tuni ya tserema Maanal a girman jiki fintinkau duk da dama can ya fitan. Itako tana tsaka tsaki a tsayi saboda bata gama girma ba, gata muguwar siririya kamar ka hureta ta zube a ƙasa. Zuwa yanzu shaƙuwarsu ta sake wuce inda ake tunanani, baka isa kaji kansu ba. Hatta abinci tare suke cin abinsu. A hakan ma dan ana tsaye a kansu wasu abubuwan da yawa ana ƙoƙarin hanasu da tunatar da su halacci da haramcin dake a tsakanin iyakar da alaƙarsu zata yiwu. Kuma Alhamdullah suna fahimta da kiyaye abubuwa da dama duk da bawai sun balaga bane ba. Garama shi Ajwaad alamomin hakan sun fara kusantoshi yanzu...
__________________★
Yanda take tura baki gaba ya sashi tsayawa yana kallonta. Sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga agogon falon. Ganinfa idan ya biye mata makara zasuyi ya sashi duƙawa. Dariya ta saki da siririyar muryarta kafin ta ɗane bayan nasa. Lunch box ɗinta da school bag ɗin dake ajiye ya tattara ya ɗiba sannan ya miƙe. Dariyarta tasa Ammie dake kitchen leƙowa. Takaici ya sata tsayawa kawai tana kallonsu, sai da ya kai ƙofa yana ƙoƙarin fita ta dakatar da shi.
“Yanzu Ajwaad bazaka hutama ranka ba dai?. Ka sauketa ta taka da ƙafarta, dan ubanta ba tun jiya ta taka ƙafar ba”.
Cikin yanayinsa na sanyin murya ya ce, “Ayya Ammie ALLAH ƙafan bai sakin mataba har yanzu. Bari muje su yaya Fadeel na jiranmu a mota”. Kafin ma ta sake cewa wani abu harya fice. Kai kawai Ammie ta girgiza tana komawarta, dan babu abinda suke buƙata yaran nan sai addu'a. Idan ta tuna mutuwa zata iya ɗaukar wani a ciki tabar wani har tausayi suke bata. Idan kaga Ajwaad na farin ciki ko surutu to tare yake da Maanal. Dan duk rashin son maganarsa sai da ta sakashi ringa yi, idan ma baiyi ba addabarsa take har sai ya tanka zata barsa. Kokuma taje ta takalo masa faɗan da dole ya tafi ramo mata......✍️.
😀😂🤣Eh lalle su Maanal an tsula tsiya a nahiyar arewacin Najeriya 😆🏃
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖5️⃣6️⃣
______________
........Tuni su Fawzan har sun shiga mota. Da sauri driver ya amshi kayan hannunsa, shi kuma ya ƙarasa gaba ya buɗe ya sakata dan nan ne wajen zamanta dama. Sai da ya gyara mata skirt ɗin ta sannan ya rufe ya zagaya kusa da ƴan uwansa ya zauna. Cikin tsokana da dariya Fawzan ya ce, “Oh oh Lilly bestyn Auta (Dan haka suke kiranta). Auta bestyn Lilly. Idan yaran nan kuka girma munada kallo a anguwar nan wlhy. ALLAH yasa dai kar ku haɗiye juna ko ku ƙone mu saboda eh......” ya ƙare maganar cikin shaƙiyanci. Banza Ajwaad ya masa, sai ma ƙoƙarin fiddo books ɗin Maanal yake yana dubawa. Yayinda Fadeel da suke kira (Babban yaya) yay ƴar dariya, hakama driver. Tsagal Maanal ta ce, “Yaya F minene eh...? Kuma sai mu cinye kammu kamar mayu”.
Dariya Fawzan ɗin ya sake kwashewa da shi. Tare da faɗin, “Lilly ba yanzu zaki san eh.. ba. Sai nan gaba. Ke dai ALLAH yabar tare”.
Cikin rashin damuwa tace, “Amin”. Sai kuma tai kneeling a kan kujerar ta saitin Ajwaad da yay kamar baya a motar tana lekensa. Cike da shagwaɓa ta ce, “Besty!”.
Ɗagowa yay kawai ya kalleta batare daya amsa ba. Wuyansa ta nuna masa tare da faɗin, “Baka sa tie ɗinka ba fa”.
Kansa ya maida ya cigaba da gyara mata abinda batai dai-dai ba a assignment ɗin da aka basu da tayi, dan jiya fushin faɗan da yayo mata bai tsaya ya koya mata ba sai Amaal ce ta mata. Kafin a hankali ya ce, “Zan saka sai mun sauka”.
“Ohhh”.
Ta faɗa tana cigaba da kallonsa. Duk abinda taga zai gyara mata sai tayi tambaya. Shi kuma ya bata amsa. Har ya kammala ya maida books ɗin shima ya maida hankali a kanta. Gaba ɗaya ta addabesu da surutu. Baka jin muryar kowa sai tata. Sai ko dariyar driver da Fawzan masu tayata dan shima Babban Yaya halinsa kusan irin na Ajwaad ne. Baida yawan magana. A haka dai har suka iso makarantar dan akwai ɗan nisa. Kasancewar a tsohuwar anguwarsu makarantar take. Ƙyawunta da son da suke mata yasa iyayen basu canja musu ita ba. Kullum driver zai kawosu ya dawo ya ɗaukesu.
Yanzun ma dai shine ya goyata, Fawzan ya taya shi da ɗaukar bags ɗin su da lunch box ɗin abinci data kasance ɗaya. Sai da ya rakasu har aji da kayan sannan ya wuce sashensu na yan secondary inda baban yaya Fadeel ya nufa. Ajwaad kam na sauke Maanal a mazauninsu dan kujerarsu ɗaya ta jawo bag ɗinsa. Zip ɗin baya ta buɗe ta ciro gogaggen tie dan uniform ɗin nasu kamar suit suke. Sai dai na mata skirt ne na maza wando. Zama yay a kujera tana daga saman desk ya miƙo mata wuyansa. Tsaf ta ɗaura masa dan tuni ta iya. Idan ka gansu dolene su birgeka kamar ba ƙananan yara ba. Ta gama ta gyara masa rigar da faɗin, “Wai Besty mi akai maka kake ta fushi. Inma dan ƙafatace ba nace maka na daina jin zafin ba. Tun jiya fa ka daina dariya why?”.
Shiru yay baice mata komai ba. Hakan yasa takai hannu saman sumarsa daya gyara ta shiga harmutsata. Hannunta yay ƙoƙarin riƙewa amma taƙi ta bari. Dole sai da yay dariyar da take so sannan ta barshi. Cikin dariya ya ce, “Besty wannan wane kalar kuturun wulaƙanci ne”.
Itama cikin dariyar ta amsa masa da, “Kamafi ƙyau a haka ALLAH”.
Rankwashi ya kai mata, ta kauce. Yay ƴar ƙwafa da faɗin, “Zan rama ALLAH ya kaimu Friday”.
“Mi zakayi?”.
Ta tambaya tana ƙoƙarin ɓare lollipop daga cikin ledanshi.
“Meyi baya faɗa ai”.
Ya bata amsa yana fige alawar ya saka a baki. Hararsa tayi, shima ya rama. Sai kuma suka ƙyalƙyale da dariya. Saida sukayi mai isarsu sannan ta zare alawar daga bakinsa ta sha. Sake maida masa tayi a bakin. Haka sukaita yi har suka shanye kafin malami ya shigo musu su nutsu kamar basu ba.
Kowa yasan a ajin basa taɓuwa. Maanal rashin kunya da tsokanar masifa, gashi itace ƴar ƙaramar ajin dan duk sun girmeta tunda rigimarta ce ya kawota cikinsu ba shekarunta ba. Ka taɓata ka haɗu da AA. Yanada zuciya ga ƙarfi, dan in har ka taɓa Maanal ka taɓoma kanka kuwa. Gashi da shegen naci akan faɗa dan baya barin saita kwana. Surutun Maanal yasa kullum sai an sakata a cikin ƴan surutu na ajin. Idan kayi surutu naira ashirin, in sha ALLAHU kafin a tashi sai ta tara ɗari biyu. Idan ance ta bayar taƙi biya, idan shugaban ajin ya biye mata suyi faɗa AA ya kamashi ya daka. Dole class master ɗin su ya maida shugabancin ajin akan Maanal ɗin, aiko tunda ta samu damar nan take tsula tsiyarta. Ta cikama ƴan aji kunne da surutu su suyi ta maka sunanka. Azo biyan kuɗi kaƙi biya Ajwaad yay maganinka. Hakan yasa ake tsoronsu, ta gefen ƙoƙari kuwa sune masu zuwa na ɗaya dana biyu, basu taɓa tsallake wannan positions ɗin ba. Ada kafin Maanal tazo ajin AA ke ɗaukar na farko, wata yarinya na ɗaukar na biyu. Amma tunda Maanal tazo shikenan fa matdayin yarinyar ya rushe. Kullum sune dai su biyun nan, babu ƙoƙarin da wasu basuyi ba ganin an turesu amma abin ya gagara.
Ada saboda kalar fatarsu tazo ɗaya kowa ɗauka yake Maanal ƙanwar su AA ce ta jini. Duk da babu ta inda suke kamanni na halitta sai dai fatansu yana kama sosai. Sai da tafiya tai tafiya kowa ya fahimci yanda alaƙar take. Duk da su ɗin yara ne da yawan mutane kai tsaye suke fassara alaƙar zuwa wani abu daban. Duk da su dai yaran babu wani abu makamancin hakan a tattare da furucinsu na baki, mawuyacine ma ace su sun san minene wata soyayya, amma hatta iyayensu na ganin zuwa nan gaba Wannan shaƙuwar zata iya rikiɗewa ta koma hakan....
(To bari muga ko hakan zata kasance😀🏃.)
★★★
Kamar kullum ƙarfe uku dai-dai aka tashe su. Suna ƴan farko-farkon fitowa. Dan sun san driver ɗin su baya wasa. Ƙarfe biyu da rabi yake isowa. Uku a gate take masa. Ilai kuwa sun samesa inda yakan jirasu kullum. Dan su Fadeel ma har sun rigasu fitowa. Cike da tsokana Fawzan dake kallonsu ya ce, “A'a ƴar gurguwar Besty an warke ne?”.
Ƙafar tata ta kalla sai kuma ta kalla Bestyn nata. Harararta yay itako ta ƙyalƙyale da dariya tare da matsawa kusa da Fawzan. Nuni ta masa daya duƙo dan ya fita tsayi nesa ba kusa ba. Haka suke dogaye dan iyayensu ma duk dogayene. Shiyasa ko shi AA ɗin dake 15 years ya shallaketa sosai. A cikin kunne ta gwargwaɗama Fawzan, “Dama fa dan ya goyani ne Yaya F. Dan yanzu idan nace yamin goyo sai yace wai na girma. Kaga yanzu ai na samo dabara”.
Mi Fawzan zaiyi ba dariya ba. Harda kwanciya jikin mota. Yayinda Maanal ta shige mota da sauri itama tana tata. Tsaf AA ya fahimci abinda ta faɗa dan yana kallon motsin bakinta. Dan haka baice komai ba ya saka bags ɗin su da lunch box ɗin cikin booth kawai shima ya buɗe motar ya shiga. Dai-dai nan Yaya Fadeel ya iso shi da abokinsa. Ta saitin da Maanal take abokin nasa ya ɗan leƙa yana tsokanarta dan mutuniyarsa ce. Kafin ya mika mata chocolate da in dai suka haɗu sai ya bata. Cike da ɗoki ta masa godiya tare da bye-bye. Ta buɗe chocolate ɗin ta, kamar yanda suka sabama juna duk abinda ɗaya ya samu sai ya raba da ɗaya ta raba biyu ta juya ta miƙama Ajwaad rabi duk da tasan ba lallai yasha wannan ba. Ilai kuwa maimakon ya amsa harararta yayi ma. Ta taɓe baki kamar zatai kuka da faɗin, “Wai miyasa baka son amsar abun hannun Ya Abdull ne Besty?”.
Banza ya mata bai tanka ba. Maimakon hakan ma sai ya ciro headphone ɗin daya saka a kunnesa. Dariya Fawzan yay da faɗin, “Kishi mana Alaji. Kinga Lilly bani nasha tunda shi na mazan ya motsa”.
Bata wani fahimci mi Fawzan ɗin ke nufi ba ta miƙa masa duka chocolate ɗin ta juya itama a dole tayi fushi. Shiko ya ce, “Uhhm gaba takaini, ban nasha faɗan masoya hutu”.
Harararsa Babban Yaya yayi. Cikin ɗan zaro ido ya ce, “Babban Yaya mi kuma na maka kai kuma?”.
“Kai bakinka bashi da linzami ko?”.
Cewar Fadeel ɗin.
“To ayi haƙuri babban yaya na daina”.
Shiru motar tayi babu wanda ya sake magana har suka iso gida....
Fuuuu ta fice batare data kalla kowa a cikinsu ba ta shige gidansu. Shima motar ya buɗe batare da ya jira an shiga cikin gida ba kamar yanda aka saba ya shige da ƙafa. Oum na zaune a falo ya shigo. “Oum good afternoon ”. ya faɗa a taƙaice yana shigewa ɗakinsu, dan su duka su a ɗaki ɗaya suke amma kowa da gadonsa. Da kallo Oum ta bisa, sai kuma ta girgiza kai kawai dan tasan ɗayan biyu ne fushin Auta. Kodai wani ya taɓa Maanal, ko shi da ita sun samu saɓani. Shigowar su Yaya Fadeel ya katse tunaninta. Su duka ita suka nufa, cike da shawagwaɓa suka zauna a gefe da gefenta kowanne yasa kansa a kafaɗarta duk da sun fara zama samari, koma muce sun zama. Dan Fadeel yana shekarar ƙarshe ne a secondary, Fawzan na aji biyar. Fuskarta ɗauke da murmushi ta shafa kawunansu dake cike da suma. “Da alama yau sojin gidan nan sunyi laushi, dan