AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   36 / 77

105K to 108K   out of 230.9K words

ɗaya kallon ya gundiri Maanal, dan jinsa take har cikin ɓargon jikinta da magudanan jini. Tuni ta daina karatun kallon rubutun kawai take, sai dai fuskarta ta sake tsukewa.
          A cike da ƙasaita ya miƙe daga jinginar da yay a jikin ƙofar hannayensa duka zube cikin aljihun farin jeans ɗin sa, daga sama ma baƙar rigace mai hi neck data ɗame masa murɗaɗɗan jikinsa, sai dai ya kawo jacket mai ƙyau baƙa da adon fari kaɗan a jikinta ya ɗaura. Kasancewar zip ɗin gabanta a buɗe yake har ƙasa ne ya bayyana rigar cikin da faffaɗan ƙirjinsa zuwa lafaffen cikinsa. Yanda yake takowa takalman ƙafarsa masu ƙyau da ɗaukar hankali na bada ƙara haka zuciyarta ke motsawa a ƙirjinta da ƙarfi. Cike da izza ya tura kujerar gaban gadon gab da gadon sosai da ƙafa, kafin ya matsa gab da gadon har Maanal najin tamkar zai faɗo mata akai sannan ya kai zaune. Yanda ya ɗan rankwafo a kanta sanda zai kai zaunen yasa hucin numfashinsa dakar fuskarta, yayinda ƙamshinsa ya gama mamaye illahirin iskar da take shaƙa. Dole ta ambaci sunan ALLAH a zuciyarta.
     Anan ɗin ma zaman ƙasaitar yayi, dan ya wani harɗe ƙafafu ɗaya kan ɗaya tare da kwantar da bayansa a jikin kujerar hannayensa duk biyu dafe da hannuwan kujerar. A har yanzu ɗin ma idanun nasa na'a kanta ne sai faman lumshesu yake da buɗewa daga cikin fari tas ɗin gilashinsa dake sake ƙawata masa fuska. Rumtse idanu Maanal tayi tana mai danne dukkan abinda ke yunƙuro mata. Batare data sake ko kallon sashen da yake ba a kausashe, a kuma tsiwace ta furta, “What are you looking for here?”.
        Maimakon bata amsar data buƙata sai kawai ya zuba ma lips ɗinta idanunsa har adams apple ɗinsa na ɗan motsawa a maƙoshinsa. Wani irin takaici ne ya sake ratsa Maanal. Tai wani irin juyowa da rinannun idanunta da suka juye lokaci guda ta saukesu a kansa. Slowly shima yaja nashi dake kallon lips ɗinta ya daidaitasu a cikin natan. Kallon cikin tsakkiyar idanu sukema juna. A hankali a hankali na Maanal suka fara ƙyalli alamar taruwar hawaye. Wani ɗan iskan murmushin gefen baki ya saki yana sassauta girman idanunsa dake cikin nata. Tamkar wanda akama dole ya motsa lips da Muryar nan nasa can ƙasa-ƙasa kamar abin dole ya furta, “Because you need me”.
       “Never! Har abada kai baka cikin abinda rayuwata take buƙata Ajwaad”.
       Wani ɗan killer Smile ya saki yana mai janye idanunsa gefe, fin sakan biyar sannan ya sake juyo da idanun nasa a kanta. “Really! You don't need me in your life?”.
     “Kana tantamar hakan ne?”.
  Ta faɗa a zafafe.
“Sosai ma kuwa? Inda har baƙya buƙatata in you life kuma da baki cigaba da ajiye wannan ba”. Ya ƙare maganar yana buɗe tafin hannunsa wani sliver agogo ya bayyana. Kallon agogon take zuciyarta na bugawa da ƙarfi a cikin ƙirjinta, agogonta ne fa, agogon da ta saka a randa zasuje Zaria ita da Ammie da Yaya Yazeed da Amrah. Tabbas tasan ta ciresa a hannunta, daga haka bata sake tuna ina yake ba. Kai hankalinta ma sam bai kai garesa ba sakamakon haɗuwa da RK da tai acan ya harmutso ta.....
      “Hyy”.
   Ya katse mata tunani cike da son tunzurata. Harararsa kuwa tayi ta ɗauke kanta gefe batare da ta ce komai ba. Murmushin sake samun nasara ya saki kaɗan yana wani ƙanƙance idanunsa a kanta.
          “Wannan pretending ɗin naki ya isa haka. K Bestyn AA ce har yanzu, ko ki yarda ko karki yarda idanunki na nuna hakan ga kowa......”
     Wani irin wurgar da littafin hannunta tayi, a bazata kawai ta ganta a gabansa ta dirgo daga gadon. Wani irin lumshe idanu yay ya sake buɗewa sakamakon shigar ƙamshinta mai daɗi cikin hancinsa. So yana matuƙar son traditional perfumes, zai iya cewa ma itace ta koya masa amfani da su ita da Oum..........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖4️⃣8️⃣


______________


........Akan ƙyawawan ƙafafunta da ƙumbunan ke a gyare fes-fes suna ƙyalli ya saukesu. Kafin ya tafi da kallonsa har saman baƙin wandon data saka irin mai manne jikin nan, yana gab da gwiwarta rigar asibitin ta bayyana, itace har zuwa sama fara da ɗigo-ɗigon jaa, tsabar neman magana da salon iskanci ya wani sauke a saman ƙirjinta ya kafe wajen da ido tare da ɗan datse lips ɗinsa. Da sauri ta koma saman gadon taja bargo ta lulluɓe jikinta gaba ɗaya tana furta, “ALLAH ya isa wlhy da mun kallon da musulunci ya haramta”.
      Murmushi yay mai fidda ɗan sauti sai dai sam haƙwaransa basu bayyana ba. Sai kuma ya taɓe bakinsa cikin halin ko in kula ya furta, “Daga baya kenan. Idan kin manta bari na tuna miki na san komai A to Z tun kan ki zama abin kallo. Ko kin manta wannan hannun ya miki wanka, ya wanke miki pupu, ya share miki majina, ya wanke miki pants, ya wanke miki blood na period. Ya.....”
     “That's enough malam. Kuma ka bar ɗakin nan tun kafin na maka ihu wlhy.”
      Murmushi ya sake yi yana taɓe baki da wani ɗan ɗage gira. Babu alamar zai ma motsa balle yayi abinda tace ɗin. Saima cikin tsareta da idanunsa da suka kaɗe ga jijiyoyin kansa duk sun sake fitowa. Muryarsa can ƙasa ya ce, “Ke baki gajiya da faɗa? Why are you being stubborn ne?”.
      Harara ta balla masa da faɗin, “Anyi faɗan da taurin kan, in baka son a maka ka fita rayuwata mana”.
Sai da ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akanta. Yanda yake mata wani shegen kallo tamkar idanunsa zasu narke a kanta ya saka tsigar jikinta tashi, kauda kanta tayi gefe da sauri, shi kuma ya ɗan ciza lips ɗinsa yana wani jan numfashi a hankali.
“Nima ki fita tawa rayuwan mana. Kinbi duk kin hanani sukuni, kin hanani aure, kin sa duk nabi na tsani yaran mutane babu hujja”.
Ai bama tasan sanda ta wara manyan idanunta a kansa ba tana harararsa, rasa abin cewa yasata faɗin, “ALLAH zai saka min sharrin nan da ka min”. Sai kuma ta sake sakkowa a gadon tare da fisgan hijjab ɗin sallarta ta saka. Ƙofa ta nufa fuuu dan gara dai ta bar masa ɗakin kawai sai yaci kansa yasha baƙin ruwa. Sai dai me ƙofar gam alamar saida ya rufe sannan. Ranta ne ya sake ɓaci, har takai hannu zata bubbuga sai kuma ta fasa saboda tunawa a asibiti suke kada ta shiga hakkin sauran majiyata. Dawowa tai inda yake cikin da tsantsar masifa da tsiwa ta balbalesa da masifa.
       Yanzu kam gaba ɗaya dauriyarsa ƙwacewa tai, dole ya kai hannu saman kansa dake wani irin sara masa da masifar ƙarfi ya dafe, dama tuni dauriya kawai yake yi, shi kaɗai yasan azabar da kan nan ke masa, dan shi dama a ciwonsa ciwon kai yafi yawa. Sam masifa ta rufema Maanal ido, sai cigaba da zazzaga masa take, “Please Besty my head ki daina min ihu”.
      “Anƙi a daina, tunda baka so ka fita mana, waya kawo ka nan ɗin?”.
      “Ya ALLAH” ya faɗa da wata sassanyar murya yana kai ɗayan hannun ma ya tallafe kan gaba ɗaya. Dan da gaske ji yake kamar kwalwar ciki zata zazzago.
      A karo na farko gaban Maanal ya faɗi, dan yanda ya kira sunan ALLAH ɗin da tallafe kan sai kuma hankalinta ya tashi. A hankali ta fara haɗiye masifar tata tana kallonsa. Yayinda shi kuma ke cigaba da jujuya kansa a cikin hannayensa yana cigaba da kiran sunan ALLAH, sai kuma ya koma faɗin, “Please Besty my head, kaina Besty zai fashe ki riƙe min, dan ALLAH ki riƙe min”.
          Ai tsabar yanda jikin Maanal ke rawa batama san takai hannunta saman nashi ba, ta ture ta maye gurbinsa da nata tare da duƙawa a gabansa tana leƙen fuskarsa da faɗin, “Na shiga uku mike damunka? Miya samu kan naka? Ka tashi muje wajen likita na roƙeka”. Sai hawaye sharrr.
       Bai iya ya motsa ba, sai hannunta dake a saman kan nasa da sanyinsa ke wani ratsashi ya sake dannewa da nasa da ƙyau. Yayinda ita kuma zafin kan da yanda jijiyoyin ke harbawa ke ratsata. Matuƙar firgici ta shiga, dan tun tana hawaye har kukan nata ya fara fidda sauti. Da ƙyar ya ɗaga idanunsa da suka gama kaɗewa ya kalleta, cikin motsa lips ɗin da ƙyar tare da ɗan jujjuya kai ya ce, “Stop crying, bafa da yawa bane”.
            Kukan ta sake fashewa da shi da faɗin, “Hakanne bada yawa ba, kaga yanda idonka yay ja kanka yayi zafi? Nidai ka bari naje na kira maka Rafeeq...” tai maganar tana ƙoƙarin miƙewa da son cire hannunta dake a saman goshinsa. Da sauri ya riƙo ɗayan hannun nata yana jujjuya kai, sai kuma miya tuna ya saki hannun yana faɗin, “Am sorry”. Itama kamar wadda ya fargar sai tai saurin janye ɗayan dake a saman kansan, ta ɗan ja jikinta baya. Murmushi ya ɗan yi, sai kuma ya miƙe still dai hannunsa dafe da kan nasa ya ɗan raɓa ta gefenta ya zauna a gadon jiyyarta yana faɗin, “Help me naɗan kwanta anan ko zai sauka”.
        Batace komai ba ta matsa masa, kwanciyar yay rigingine ya lumshe idanunsa hannunsa dafe da kan nasa. Tun tana kallonsa daga tsayen harta kai zaune a kujerar daya tashi dan itama sai taji kawai tana wani irin jin jiri, yayinda baya data shuɗe ke son maimaita mata kanta a zuciyarta. Haka suke ita da shi, da wahala ɗaya ya kwanta ciwo ɗayan bai kwanta ba shima. In ko ba haka ba dukkan hidimar mai ciwo ɗayan ne zai yi. Zata iya cewa fara kaiwar AA ɗin lokacin balaga ne yasa Oum ta fara saka idanu akan al'amuransu, harma takan kasance tare da su batare data barsu keɓewa su biyu kawai ba. Sai dai duk da haka ƙaddara bata barsu ba. (Ƙaddarah!) Zuciyarta ta maimaita kalmar da amsa kuwwa. Rimtse idanunta tayi da masifar ƙarfi sai kuma Zuciyarta ta fara zafi, (Eh tabbas batace ƙaddara kawai ba, harda ganganci da son zuciya daga AA ɗin, eh son zuciya, koma tace zalunci......) Hawaye suka shiga solalo mata masu shegen zafi. Zaram ta miƙe daga gaban nashi ta nufi window jikinta na rawa. Yanda ta tura kujerar da ƙarfi harta faɗi ya sanya AA buɗe idanunsa da ƙyar. Kallo ya bita da shi, sai kuma yay saurin rumtsewa jin abinda take faɗa cikin kuka mai tsanani daga inda take....
        “Dan ALLAH ka tafi, ka tafi nesa dani bana son ganinka. Ka barni naci gaba da rayuwata cikin salama. Namaka alkawarin zan bar aiki a companyn ka. Bana son tuna komai, bana so, ka daina kusantoni, ka barni, dan ALLAH ka barni na roƙe ka Ajwaad....”
       “Besty!” ya faɗa a can ƙasan maƙoshi daga bayanta batare data san sanda ya baro gadon yazo wajen ba. Kuka ta sake fashewa da shi tare da durƙushewa a wajen, “Ka daina kirana da wannan sunan, ka tafi kawai, ka tafi Ajwaad....”
       “Zan tafi, amma ki saurareni kona minti biyar ne”.
    “Bazan iya ba, baka da sauran space na lokacina, sam baka da shi.” sai kuma ta juyo tana daga durƙushen ta haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo🙏. “Na roƙeka ka barni Ajwaad. Ka yi nesa dani, bana buƙatar jin komai daga gareka, bazan iya baka komai ƙanƙantar lokacina ba a yanzu”.
        Da ƙyar ya iya haɗiye abinda ya riƙe masa maƙoshi, ya lumshe idanunsa da sukai mugun kaɗewa mai ban tsoro daban tashin hankali ya sake buɗewa a kanta. Cikin wani irin murya mai matuƙar laushi da sanyi ya ce, “Kin fi son mu cigaba da kasancewa a wannan matsayar kenan? Mu cigaba da ɓatama waɗanda ke bibiyar rayuwarmu lokacinsu. Yes muna ɓata musu lokaci ne kema kin sani, dan in har bani ne MIJINKI ba, wani bai isa ya zama ba!!.” ya ƙare furucin ƙarshe a kausashe.
Ɗago kai tai da sauri tana kallonsa da jajayen idanunta. Shima ɗin kallonta yake da wani mugun kallon tabbatarwa. Amma ta dake a kausashe ta ce, “Mi kake nufi Ajwaad?!”.
Shima a kausashen ya ce, “Abinda kikaji na faɗa shi nake nufi. In dai ni Ajwaad Aliyu Darma ina numfashi a doron wannan ƙasar, wani banza wofi bazai taɓa aurenki ba Maanal. Dan haka tun kafin dare yay musu ki sanar da su suje su nema matan aurensu. Ki kuma sani ko mutuwa nayi kika auri wani in sha ALLAHU sai na hanaku zaman lafiya da fatalwata. Idan kuma kinji wasa bismillah, ga fili gamai doki”. Ya ƙare maganar yana miƙewa da kaɗa mata yatsarsa manuniya a saitin fuska tamkar zai tsokale mata idanu.
Miƙewa tai itama a gabansa tana huci ga hawaye na zirara mata da gudun tsiya. Cike da tsiwa ta riƙe ƙugu da duka hannayenta biyu tana kallonsa babu ko gezau. “A tunaninka kana da wani ƙarfin yin duk abinda ka faɗa? Ka lalata min rayuwa sannan kai tunanin hanani auren wani? Shike nan mu zuba, nace mu zuba ni da kai dan ALLAH ɗan halak ka fasa, ka saka a ranka ni kuma Maanal Habib Umar Giro zanyi aure, kuma zan auri wanda kake da kusanci da shi wato Rafeeq. Ka fara shiri nan da wata biyu kacal, wata biyu....” ta ƙare maganar tana karkaɗa masa yatsarta itama da raɓashi zata wuce. Ai a wani irin fusace a kuma bazata taji an damƙo hijjab ɗinta an fisgota baya. Babu zato ta jita manne a jikin bango, duk da ko kaɗan jikinsa bai taɓa nata ba yanda yay mata rumfa da ingarman jikinsa saboda ya fita tsaho da cikar jiki nesa ba kusa ba, babu ta inda zata shaƙi iska ya masifar sake hargitsata. A kausashe a kuma faɗace, dan gaba ɗaya taswirar ƙyaƙyƙyawar fuskar sa ta canja. Ga jijiyoyin kansa sun sake fitowa, idanunsa sun masifar kaɗewa irin mai ban tsoro ɗin nan tamkar an watsa jini a cikinsu. Da kakkausar muryar da bata taɓa tunanin ya mallaka ba ya ce, “Idan kikace zaki zuba WASAN da ni kema kin san kece zaki sha wahala wlhy. Amma bismillah mu zuba ɗin, sai dai ki sani wani ɗan iska bai isa shiga GONAR dana jima da shiga ba har abada, yanda na fara mallaka ni zan cigaba da mallaka har ƙarshen numfashi.” Daga haka bai sake cewa komai ba ya juya ya fita a fusace kamar wani mafaraucin soji a daji.
Yana gama maida ƙofar ya rufe tai wani irin zubewa a wajen ta fashe da kuka jikinta na rawa. Kuka take sosai, kuka irin mai zuwa da dukkan ƙarfinka dana zuciya. Kuka mai ban tausayi. Ita wannan mutumin kema alfahari da abinda yay mata a baya, ita yake ma iƙirari akan abinda ya aikata mata. Ita Maanal. Wlhy dolene ta tabbatar masa shi ba kowa bane, bai kuma isa komai ba, tabbas zata tabbatar masa, dole ne ma ta bbatar masa, ta hanyar auren RAFEEQ ne kuma kawai zata tabbatar masan.
Ta jima a wajen tanayi, sai shigowar nurse ɗin dake kula da ita ne ya kawo ƙarshen yanayin. Hankali tashe tazo ta tadata a wajen, da taimakonta ta maidata gadon tana jera mata tambayoyi akan ko jikin nata ne. Kanta kawai ta iya girgiza mata. Sai kawai nurse ta shiga lallashinta, dan AA ne ya turota dama. Daɗaɗan kalamai ta dinga faɗama Maanal masu kwantar da zuciya, a hankali a hankali ta fara tsagaita kukan har tai shiru. Hawayenta ta share tas tare da sake yin lamo a gadon. Nurse ɗin ma tayi tunanin ko tayi barci ne sai ta lallaɓa ta fita dan akwai abinda zata ƙarasa sannan ta dawo.
      Kamar jira Nurse ɗin na fita RK na shigowa. Yayi sallama har fin sau uku da knocking amma shiru, sai ya ɗan kalla agogonsa da tunanin ko tayi barci. Ganin lokaci yaja sosai sai kawai ya yarda tayi barcin ne. Ƙofar ya ɗan tura ya leƙa, can ya hangota kwance a gado a lulluɓe, sai dai mi wani ƙamshin turare da ya san bai taɓa jinta da shi ba ne ya bugosa. Sai da gabansa ya faɗi, ai ba shiri ya shigo ɗakin da sauri. Tabbas ƙamshin turaren ne, turaren da in bai ƙarya ba a wajen AA kawai ya san shi.
     (AA!) Zuciyarsa ta sake maimaita masa sunan da amsa kuwwa. Sai kuma ya shiga waige-waige a ɗakin kamar zaiga AA ɗin a ciki. Duk abinda yake Maanal na jinsa, amma ta dake tai likimo kamar mai barci, dan bata son ya ganta a yanayin da take sam. Jin ya fice da sauri yasa ta lumshe idanunta da ƙarfi sauran hawayen dake a ciki suka wani zubo shaaa.....


____________★


Da ƙyar ya iya fita a taxi ɗin ya nufi gate ɗin gidan nasu, dama satan fitar yayi. Daga fitowa sallar isha'i ya maƙale yaƙi komawa ciki. Sai da ya tabbatar Abah da yayunsa sun shige sannan ya fito a massallacin ya tari taxi ya nufi asibitin dan kawai ya ganta. Tun safen da RK yazo gidan da batun nata

36 / 77