AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 77

66K to 69K   out of 230.9K words

daga bayanta. Jitai gaba ɗaya kamar ta daburce, ga zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri har numfashinta na neman fara yin sama-sama. Babu alamar wasa ko ragi a tare da ita ta juya ga tsohon nan, hannu ta ɗaga da nufin nunashi a hankali taji saukar wani tattausan hannu ya riƙe mata yatsu, batare da cewa komai ba yaja hannun nata. Ƙoƙarin fisgewa ta fara sai dai bai bata damar hakan ba har ya iso da ita jikin mota. Sai lokacin ta iya zuba masa manyan idanunta da suka kaɗa, shima kallon nata yake cikin ido. Kusan minti ɗaya suna kallon juna kafin ya zare kayan hannunta tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Get in”.
        Rasama mi zata ce masa tayi, dan sam babu ko ɗigon wargi a fuskarsa. Yayi masifar yin kicin-kicin da ita kamar zatai aman wuta. Bai kuma sake cemata komai ba ya zagaya ɗaya side ɗin ya shiga mazauninsa ya ɗauke kai. Dattijon Alhajin nan dake tsaye ransa a matuƙar ɓace ya sake takowa inda Maanal take. Ai yana buɗe baki zaiyi magana kawai ta shige motar, shiko AS ya rufe mata murfin ruf tare da kallon Alhaji fuska da murmushi ya furta, “Bye bye grandpa”. Shima ya zagaya ya shige motar driver yaja suka wuce.
      Da wani irin kallon ɓacin rai dattijon yabi motar da kallo, sai kuma ya jinjina kansa tare da cije lips da ƙarfi ya koma tashi motar. Da sauri driver ɗinsa ya buɗe masa ya shiga ya maida ya rufe suma suka bar wajen....

        Sosai Maanal ta takure jikinta waje guda, yayinda idanunta ke'a lumshe bugun zuciyarta kuwa gaba ɗaya ya sauya daga normal bugu. Ambaton sunan ALLAH kawai takeyi tare da ƙoƙarin danne kukan dake son kufce mata.
      AA Darma dake a gefenta kam tunda ta shigo bai ko kalleta ba. Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ne ga document ɗin hannunsa da dama shi yake dubawa kafin suga Maanal ɗin, koda yake bama shine ya ganta ba, AS ne ya ganta cike da mamaki ya furta (kai wannan ai Sister Maanal ce Alhaji Bukar ya tsare a hanya halan bata sami abin hawa bane har yanzu). Driver na tambayar AS wacece ita ɗin AA Darman ya daka masa tsawa akan su dakata, shine dalilin tsayawar tasu.
        A yanzun ma driver ne cikin ɗari-ɗari ya furta, “Sir! Zamu fara saukeka ne kafin a kaita?”.
     Shiru bashi da alamar amsawa. Sai da ya mula dan kansa batare da ya bar abinda yake ba ya bashi amsa a taƙaice. “Fara ajiye ta”.
     “Okay sir. Sister ina muka nufa?”. Ya maida akalar tambayarsa akan Maanal. Shiru bata amsa ba sai da ya sake maimaita tambayar sannan ta dawo hayyacinta. Cikin ƙoƙarin danne komai da yanayin nan nata na kamewa ta furta, “Samu waje kawai zan sauka na ƙarasa a taxi”.
      Kallon AA Darma drivern yay ta mirror ɗin gaba da tunanin ko zaiyi magana. Amma sai yaga ko kallon inda wani cikinsu yake bai yiba ma. Dan haka sai ya kalla AS cikin marairaicewa. Murmushi AS yayi tare da juyowa saitin inda Maanal ɗin take, “Please Sister Maanal bafa zamu ajiyeki ko'ina ba sai gida”.
      Rasama mi zatace tayi, sai kawai ta faɗa masa sunan anguwar a taƙaice. Bai gaji ba ya sake tambayar street, nan ma kamar bazata kula shi ba sai kuma dai ta faɗa. Daga haka bata sake magana ba ta maida idanunta ta rufe. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso abinka da lafiyayyar mota a saman lafiyayyar kwalta. Shigowarsu cikin street ɗin ya sa AS sake mata tambayar inda za'a sauketa. A taƙaice ta ce “Nan ma yayi”. Shi dai driver tunda taƙi faɗar no ɗin gidan da zataje ai sai kawai ya samu waje ya tsaya abinsa. Itako ta kama handle ɗin motar ta buɗe da nufin fita. Sai kuma ta ɗan juyi domin ɗaukar kayanta da AA Darma ya amsa a ɗazun akai rashin Sa'a shima ya kawo hannu kan kayan da nufin ɗauke file ɗin daya ɗora kawai ta riƙe masa hannu. Da sauri ta jiyo jin ta kama abu, dai-dai shima yana kallon hannun nasa da yaji an cafke. A tare suka dubi hannun sai kuma suka kalli juna. Maanal ta saurin yarfar da hannun tamkar wadda ta kama wuta, yayinda shi kuma ya wani irin dunƙule hannun nasa waje guda tare da dimtse lips ɗinsa da hakori tamkar zai kai naushi. Sauka Maanal ɗin tayi tare da zare kayan nata ta ajiye masa file ɗin batare data sake gigin kallon ko inda yake ba taima AS godiya da driver tai gaba abinta ko waiwayen motar bata sake yi ba. Shima driver sai kawai ta tada motar suka wuce.
       Tunda suka tafin AA Darma hannun nasa kawai ya zuba ma ido tamkar mai karanta wani abu a jikinsa ko cigaba da ganin hannun Maanal ɗin. Kamar ance ya kalla inda ta tashi idonsa ya sauka akan ɗan abin hannunta da alama wajen yarfar da hannu da tai sanda ta kama nashi ya cire batare data kula ba. Hannu ya kai a hankali ya ɗauka ɗan hannun ya juya. Mai ƙyau ne sosai kalar golden, an masa kwalliya da fararen stones, da gani ba wani mai tsada bane, amma yayi ƙyau sosai. Yanda ya tsirama ɗan hannun ido yana kalli da jujjuyashi haka su AS ke kallonsa zuciyarsu cike da gulma, suna ganin zai ɗago suka kama kansu. Shi ko a cikin aljihun jacket ɗin suit ɗinsa na ciki ya cusa ɗan hannun kawai ya gyara zamansa......

      Ni dai nace, “Hummm. Idan tayi wari dai maji🤪🏃”.

_____________★

        “Wai ni wannan yaron zaima gadara? Ni nan! Ni a garin Abuja”.
   Abokansa uku da suka zuba masa ido cikin mamaki ɗaya daga cikinsu ya ce, “Sen.. Bukar wai kai da waye haka? Ka shigo kamar wanda aka wancalo kuma kanata kai kawo da zantukan da bamu gane ba”.
     Tsaki mai ƙarfi ya sake ja, sai kuma ya ɗauka bottle na ruwa ya ɓalle murfin ya hau kwankwaɗa. Tas ya shanye yay jifa da robar, kafin ya dubi abokan nasa ɗaya bayan ɗaya yana furzar da huci. “Wannan yaron ɗan gidan Darma mana, lokaci yayi da zan koya masa darasin rayuwa. Saboda na fahimci tashen balagar iskanci ne ke ɗibarsa da giyar ƴan kuɗaɗen da yake gani ya tara kamar yaje dai-dai da kowa....”
       “Halan AA!? Dan nasan shine tsageran cikin ƴaƴan Darma”. Ɗaya daga cikin abokan nasa ya faɗa shima cikin ɓacin rai.
    “In ba shi ɗin ba sai wa? Wato wannan yaron shifa jinsa yake dai-dai da kowa yanzu a garin Abuja. Haka ranar Alhaji Badamasi yace min ya masa rashin mutunci. Wai yaje masa da business amma yaƙi ƙarɓa harda gaya masa baƙar magana. Tsageran cin yaron kullum sake ƙaruwa yake yi”.
        “Kufa daina ɓata bakin ku, wannan yaron duk abinda yake ɗaurin ƙugu ya samu, ba daga kowa ba kuma sai Mr president, tunda ya ɗauki muƙamin nan ya bashi yake jin kansa dai-dai da kowa. Sannan kaima kayi ganganci, da girmanka da mutuncinka a ƙasar nan bama garin Abuja ba minene na sauka yima yarinya magana. Ko ƴar uban waye zaka aika a ɗakko maka ita har gidane balle nasan bai wuce karuwan dake tsayawa a wajen bane ba. Na gaya maka kana gidanka kwance duk ƴar da kake so za'a kawo maka amma ban san miya kaika wannan kwamacalar ba haka”.
          “Karka ɓata min rai kai kuma, ai na faɗa muku yarinyar tafiya kawai take ina zaton daga cikin wani Companyn ta fito ne, kuma a yanda nake cikin ɓadda kamar nan kaima kasan babu yanda za'ai wani ya ganeni, koshi bana tunanin yasan nine akwai dai wata tsakaninsa da yarinyar shima ɗan iska, saboda naji wannan shegen yaron daya maida kamar bindinsa ya kira sunanta wai Sister Maanal”.
      “Eh to da gaskiyarka akwai alaƙa kam, amma bincike ya kamata muyi”.
   Duk sun gamsu da yin hakan, daga nan suka saki zancen suka fara wanda ya tarasu a wajen. Dan dama meeting ne zasuyi daya shafesu. Su duka biyar ɗin manyan ƴan siyasa ne kuma ƴan kasuwa a bayan fage, a wata fuskar kuma dattijan ƙasa wai....

    Wai.... Ne ma kenan ba manyan ƙasar bane🏃 Bily wataran sai kinci duka idan baki kiyayi bakinki ba😌.

_________★

      Maanal kam data shiga gida tamkar wadda aka koro har ta bama maigadi tsoro waje ta samu a harabar gidan ta zauna, sai da ta huta taci kukanta sosai ta ɗan samu nutsuwa sannan ta miƙe. Wajen fanfo da ake bama flowers ruwa taje ta wanke fuskarta sannan ta shiga ciki. Turus taja ta tsaya tana kallon Huznah dake zaune a falo tana cin abinci. Yayinda su Barrah dake homework sukayo kanta da gudu suna mata oyoyo.....
      Rungumesu tai idanunta na kan Huznah ɗin da itama ita take kallo, dai-dai nan Shahidah ta fito daga kitchen. “Aini yanzu nake tunanin zuwa na biki kafin Daddynsu Barrah ya dawo gidan nan”.
    Shahidah ta katsema Maanal da Huznah kallon-kallon da sukema juna da furucinta. Dan murmushi Maanal ɗin tayi da kaiwa zaune tana faɗin, “Didi ai nima kaɗan ya rage na kiraki a waya, ashe wajen nan haka ake wahalar taxi”.
       “Ai dolene, waje duk ma'aikatu ke kuwa. Ya aikin?”.
   “Alhamdullah ya naku?”.
  “Yana can mun baro sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu. Bakiga baƙuwa ba ne?”.
     Sam Maanal babu ruwanta da ɓoye-ɓoye dan ita ƴar sak ce, sai ta ɗan kalli inda Huznah take da faɗin, “Na ganta Didi. Mamaki ne ya kasheni ai na kasa magana. Sannu da zuwa”.
     Cikin ɗan basarwa Huznah ta ce, “Yauwa sannunki kema”. Daga haka ta maida kanta ga abincinta. Itama Maanal sai bata sake magana ba ta miƙe.
     “Didi bara na ɗan watsa ruwa, ina Linda dan ALLAH ta dama min kunun gyaɗa kafin na fito, Barrah jeki gaya mata”..
    Amsawa Barrahn tai tare da miƙewa ta nufi kitchen ɗin da ɗan gudu tana jiran Linda, ita kuma tai hanyar ɗakinta.........✍️


✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖3️⃣2️⃣


......Da mamaki Maanal ta dinga bin akwatin Huznah da aka kai ɗakinta da kallo, sai dai batace komai ba ta tuɓe kayanta ta nufi bathroom. Wanka tayo da alwala, sai da ta gyara jikinta tsaf tai sallar isha'i sannan ta dawo falon. Kunun da ta saka Linda ta haɗa mata kawai ta ɗan sha, sai magungunanta da Shahidah ke bata da kanta dan ma kada tai wasa. Suna nan suna ƴar hira ita da Shahidahn dan Huznah ba saka musu baki take ba sai ma latse-latse take a waya kamar bata falon mai gidan ya dawo...
     Dalilin dawowar tasa yasa Shahidah shigewa part ɗinsa, aka bar su Maanal kawai. Sai itama ta miƙe ta taimakawa Linda suka kwashe su Barrah da sukai barci a falon. Daga haka tacema Huznah ita zata shige ta kwanta. A ciki Huznah ta amsa mata, Maanal bata damu ba tai wucewarta. Ita kuma ta rakata da harara. Maanal na shiga ɗakin kiran RK ya shigo mata, bata ɗaga ba sai da takai kwance, ta gaisheshi a mutunce kamar yanda ta saba, daga haka ta fara mata hira da albishir ɗin gobe in sha ALLAHU yana hanya. Ganin yanata jan hirar ta fara masa hamma, dole yay mata sallama. Kamar jira sai ga Yazeed shima ya kira, jitai kamar zatai kuka, haka dai ta ɗaga.
      “Dawa kike waya haka Maanal?”.
   Furucinsa na farko kenan maimakon amsa mata sallamar da tai masa, muryarsa a cinkushe. Sai da ta ɗan yi jimm kafin a nutsenta ta bashi amsa da, “Rafeeq ne!”.
      “Rafeeq!?”.
  Sai da ta ɗan lumshe ido saboda yanda ya maimaita sunan RK ɗin a kausashe yanzu kafin ta ce, “Uhhum!”.
       “Okay yayi ƙyau”. Ya faɗa yana yanke wayar. Shiru tayi na mamakinsa, Yazeed mutum ne mai nutsuwa da fahimta, sannan yana da haƙuri, zata iya cewa tunda ta haɗu da RK bai taɓa tunkararta akan al'amarinsa ba sai dai can a tsakaninsu. Amma yau minene ya hasalashi haka? Kai ita kam taga takanta. RK ya nuna fushi idan ya ganta da Yazeed ko tana waya da shi, yanzu shima kuma ga Yazeed ɗin zai fara nashi. Ita kam dan ALLAH karsu rikita mata lissafi mana, suma barta da abinda ya dameta...
       Tana cikin wannan yanayin Huznah ta shigo, bata mata sallama ba dan haka itama tai kamar bata san da shigowarta ba. A gadarance ta jefa wayarta saman gadon, fuuu ta wuce bathroom, ita dai Maanal binta tayi da kallon mamaki, bata jimaba ta fito, ta buɗe akwatinta ta canja kaya sannan ta hawo gadon. A mamakin Maanal dai taji Huznah na jera fillos a tsakkiyarsu, sai kawai abin ya bata mamaki ta saki murmushi. Bata kulata ba tai addu'a taja barko.
    Barci take son yi saboda gajiya da tayi ga gobe ma dole ta fita aiki, amma Huznah ta hanata sai charting take, kuma voice note. Tun Maanal na dauriya har dai ta miƙe tsam a gadon ta koma saman sofa doguwa dake a ɗakin, kwanciyar bata mata wani daɗi ba amma ta haƙura anan ɗin duk da nan ɗin ma ba tsira tai ba tana jin Huznah ɗin da bata fasa abinda take ba harda su ɓaɓɓaka dariya kamar ba dare ba. Daga ƙarshe bata san sanda tayi barci ba ita dai, dan itama ALLAH ya taimaketa barcin yay awon gaba da ita. Da asuba kuma koda ta tasheta ƙin tashi tayi, sai kawai ta ƙyaleta. Har gari ya waye tai shirin fita aiki Huznah taƙi tashi salla. Sai kawai ta fice abinta tana nema mata shiriyar UBANGIJI.

     Yau ma Shahidah ce ta ajiyeta a office sannan ta wuce nata aikin, tun a harabar companyn suke gaisawa da mutane har ta shigo. Dama dai tsakaninta da kowa gaisuwar ce, rashin yawan fara'arta da yawan magana ma kesa mafi yawansu ke kiranta da sunan mai girman kai. Ƴan rukuninsu mutum uku ne kawai sukazo, ta gaisa da su taja kujerarta ta zauna. Dama ita kaɗaice mace a cikinsu, shiyayasa daga gaisuwa sai zancen aiki ke haɗata da su. ALLAH kuma ya taimaketa kujerarta itace farkon shigowa, suma ganin yanda take haɗe fuska da kame kanta yasa suke shakkar shige mata duk da wasunsu na kwaɗayin hakan tun ma a ran farko da tazo. Aikinta ta kamayi kawai kamar yanda ta saba, a haka sauran suka iso, kowa yazo zata ɗago su gaisa daga haka ta maida kanta ga aikinta. Kusan eleven ta tashi zuwa office ɗin Director Mustapha. Duk da kallo suka bita, wanda ke zama kusa da ita cikin yin ƙasa da murya yace ma na kusa da shi, “Wato yarinyar nan akwai girman kai wlhy Ema..”.
     Caraf Yaqub da ke facing ɗinsa ya ce, “Ba wani girman kai wlhy, ta dai san kanta ne. Idan mace ta cika faran-faran ace ma ballagaza, idan ta kame kanta ace girman kai. Kufa lura ita kamar yanayintane ma haka, miskila ce kawai”.
     “Tab ai ni kuma bana son miskilar mace gaskiya. Ita mace ko yaya da sauƙin kai tafi daɗin rayuwa”.
    “A wajenka ba.....”
“Oh to kodai santa kake yine wai Yakub”.
       “To laifi ne idan na sota Zaharadeen, naga dai namiji ne ni. Kuma ɗin inda zata amsa muku son nata kuke shiyyasa kuke gulmarta. Yarinya na girmamaku amma bakwa gani. Yanzu da sakewa take cikinmu da surutu da fara'a sai kuma ace ta saki kanta a tsakkiyar maza. Ta kuma kama kanta kunzo kunayi da ita mtsooww!”.
    Ya miƙe ya bar musu wajen. Duk da kallo suka bisa, sai kuma suka kalla juna cikin yamutse fuska. “Wannan guy ɗin na kula fa son yarinyar nan yake”.
       “Oh kai sai yau ka gane, ai na jima da fahimtar hakan. Kuma banga laifinsa ba dan koni ALLAH na ƙyasa”.
     Dariya suka sanya a tare harda tafawa.

    Maanal kam da bata ma san sunai ba kanta tsaye office ɗin Designer Director Mustapha ta nufa. Tana shiga Elevator massage ya shigo wayarta, ƙoƙarin dubawa ta fara yi sai taga Yazeed ne. Nutsuwa tai a karanta saƙon, sai ya zam har elevator ɗin ta tsaya hankalinta nakan wayar, a haka tai ƙoƙarin fitowa batare da duban gabanta ba. A dai-dai lokacin da CEO AA Darma ke isowa ga elevator ɗin Assistant ɗinsa biye da shi. Ya riga ya kawo jiki, kamar yanda itama ta riga ta taho gashi hankalinta ba a wajen yake ba balle taja da baya kawai sai jitai ta bugi abu. A ɗan razane tayi baya, wayarta ta suɓuce ƙasa hakama gilashin idanunta da document ɗin duk suka tarwatse kasa.
     Sosai ta ɗago cikin ɓacin rai dan ganin wanene da wannan aikin bayan ta gama bin kayan da kallo ɗaya bayan ɗaya. Shima sai hakan ya zam dai-dai da tashi ɗagowar bayan ya gama bin kayan da kallo musamman zanen agogon da yay masifar ɗaukar hankalinsa. Wani kalar zubama juna ido sukai kowanne fuskarsa a matuƙar tamke, sai dai na Maanal ɗin ya ɗan cika da ruwan hawaye dan har ƙyallinsu ya nuna. Yanda tai masa ƙiri da idanu sai ka ɗauka zata fara zazzaga masa ruwan bala'i ne, dan tuni AS ɗinsa da wasu da suka zo wajen bayan faruwar accident ɗin duk sunyi kasare cikin ɗunbin mamaki suna son suga mizai faru. Amma mi, a mamakin

23 / 77