AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   53 / 77

156K to 159K   out of 230.9K words

murna da addu'ar haihuwar ɗa namiji. Ita dai Ammie ko tari bata musu ba, duk taɓarar iskancin da amarya keyi bata nuna tasan suna numfashi a gidan ba ma. Sai da ciki ya shiga wata biyar sannan ya ɗauketa suka wuce Giro, dawowar da basu sake yi ba sai da ta haihu akasha shagalin suna a Giro dan buri ya cika an haifi Namiji. Ashe duk wannan abun da ake Baabu na cikin Kano, tunda ya kai amarya gida Gwaggo ta sharɗanta masa hanashi komawa wajen Ammie wai har sai in matarsa ta haihu. Ammie bata taɓa sanin haka ba sai bayan dawowarsu da jinjiri da Gwaggo, wai itama ta dawo nan Kano da zama, ashe aure dai ya ƙare tsakaninta da Baba Haruna duk kuma akan Ammie ne, dan bayan tahowar su Ammie a wancan karon ansha fitina Baba Haruna ya saki Gwaggo shine fa ta ɗau alwashin yanda ya saketa itama sai an saki Ammie, idan kuwa ma ba'a saketan ba sai ta ɗanɗana fiye da abinda itama ta ɗanɗana. Wannan duk shine tushen matsalar da suke ciki a yanzu shiyyasa Amarya data san komai ta koma gefe ta nutsu tana shan kallo dan tace faɗan na manya ne ba nata bane.
      Dawowar Gwaggo Kano ba ƙaramin tashin hankali su Ammie suka shiga ba ita da yaranta. Musamman Maanal mai bakin tsiwa datai matuƙar tsanar Gwaggo, kuma a zahiri take nunawa bata ɓoyewa. Yayinda Gwaggo itama ta tsani Maanal fiye da su Shahidah, ta kuma tsani Ajwaad, dan shima a dalilin ƙin Maanal da su Ammie daya ga Gwaggo nayi ƙuru-ƙuru ya sashi tsanar matar, dan sam Ajwaad baya son mugu da mugunta. Rayuwa tayi tsanani wa Ammie, uwar miji, da miji da kishiya sun saka rayuwarta gaba data ƴaƴanta. Shekaru kusan huɗu bata kwanciya da miji, baya shiga ɗakinta. Yanzu kuma haihuwar namiji tasa kullum cikin aibanta mata yara suke da shegantasu, dan akwai randa Baabu da bakinsa yace yana tantanamar ma su Shahidah ƴaƴansa ne. Wannan abu ya girgiza Ammie, ya sakata kuka mai tsanani da sake jin sabuwar kewar iyayenta data rasa. Amma ya zatai, haka ta haƙura ta share hawayenta ta barma ALLAH komai. A wajen Oum da Abah kawai take samun sauƙi da soyayya da ƙauna ita da yaranta.
         Kammala secondary ɗin Shahidah yasa Abah tada zancen aurenta da Fadeel. Dan yace za'a fara nasu, ita kuma Amaal sai Fwazan ya kammala. A ɗan tsukun Fadeel yazo gida hutu, dama can shi da Shahidah tuni sun ƙulle, dan haka aka saka ranar aurensu ya koma saudia. Bayan komawar tasa Shima Fwazan ya shiga lallaɓa Oum akan kawai a haɗe nasa dana Amaal lokaci ɗaya dana Babban Yaya, sai su tafi jami'ar tare. Dan shi rashin ƙyawun result daya samu yasa dole ya ƙara shekara ɗaya a ƙasa sai da ya canja ssce ɗinsa duka.  Duk da a lokacin ita Amaal na ss2 sai yace kawai tayi exam ɗin itama su wuce tare. Oum ta tunkari Abah da zancen, yay shiru yana nazari, sai zuwa can yace ta bashi lokaci zai yi magana da Baabu, kuma zai kira Baba Haruna a waya....

  ____________★

         Kamar yanda suka saba tashi sallar asubahi kullum yauma hakanne. Saida Fwazan ya fara yo alwala sannan babban yaya ya shiga. Ajwaad shine ƙarshe, sai wani ciccin magani yake. Ya girma sosai a tsaye, dan a yanzu shi da mutuniyar tasa suna js3 ne. Suna shirin tafiya ss. Shekarun girma sun gama bayyana mai, dan har wani ɗan tsigin gemu ya ajiye (kamar jelar tsatso inji Ibro.😂 ALLAH ya gafarta masa da iyayenmu baki ɗaya 🙏).
     Yanda yake tafiya kamar mara laka a jiki ya saka Fawzan sarkin tsokana faɗin, “Wai na Lilly kodai barcin nan bai isheka bane ba?”. Harrarsa kawai ya ɗanyi ya wuce abinsa, dama Fawzan tsokana, Ajwaad miskilanci. Haka suke kullum, sai ya ƙuresa ne yake tanka masa. Juyawa Fawzan yay ga babban yaya dake canja kayansa zuwa jallabiya, shi kam tako ina ya zama cikakken saurayi, ga cikar kamala da nutsuwa ta sake baibayesa,  duk da shima Fawzan ɗin tsokanar ce kawai, amma a nutsensa yake. Har sun kammala shiryawa yau ma Ajwaad na cikin bayi, babban yaya ya dubi fawzan da faɗin, “Wai mike damun auta ne yanzu?. Da babu wanda ya kaishi himma shirin fita sallar asuba, amma tunda nazo garin nan naga sai mun fita yake fitowa”.
      Murmushi Fawzan yayi da ɗan sosa kai, sai kuma ya ɗage kafaɗa da faɗin, “Maybe yana wani uzirin ne”.
    “Kamar ya?”.
  Shiru Fawzan yayi saboda fitowar Ajwaad daga bayin a tunaninsa sun fita ɗin. Turus ya tsaya yana kallonsu, suma duk sai suka zuba masa ido........✍️



✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖7️⃣1️⃣


______________


.........Wani irin gumtse baki Fawzan yay yana danne dariyarsa da tsiya-tsiya. Idanunsa ƙyam akan sumar kan Ajwaad da yake gogewa da towel, a jikinsa kuma rigar wanka. Aiko Ajwaad yay wani irin masifar yin kicin-kicin da fuska tamakar zai sakar musu kuka. Yayinda Babban Yaya daya gama masa kallon tsaf shima ya ɗauke idanunsa yana murmushi. Hanyar fita ya nufa abinsa yana faɗin, “Ka same mu a falo idan ka shirya, dan kullum Abah yana maganar rashin fitowar ka tare damu, yana ganin kamar ma baka samun sallar”. Daga haka ya fice bai jira amsar sa ba. Shima sai Fawzan yabi bayansa, sai da yaje ƙofa zai fita sannan ya ɗan juyo ya sake kallon Ajwaad ɗin da har yanzu ya kasa motsawa daga inda yake. “Ka lallaɓa ni na faɗama Oum a haɗa auren ka da namu ka huta da wannan wankan asubar wlhy, dan Lilly dai ta isa aure shekara goma sha biyar ai ba laifi”.
      Wata muguwar harara Ajwaad ya wurga masa, dan haka suke kamar abokai, to dama tsiran nasu ba wani yawane da shi ba. Ficewa Fawzan yay da sauri yana sake gumtse dariya. Koda ya fito inda babban yaya ke jiransu sai ya haɗiye dariyan. Kallonsa babban yaya ya ɗanyi sai kuma ya kauda kai. Cikin ɗan jin nauyin abinda zai faɗa ya ce, “Tun yaushe Ajwaad ya fara wannan wankan asubar?”.
             Batare da Fawzan ya kallesa ba shima ɗin ya ce, “Ai tun bayan wucewarka saudia babu jimawa. Kaga kuwa fin shekara biyu kenan”.
    Karan farko babban yaya ya dubi Fawzan ɗin, “Amma su Oum sun sani?”.
        “Haba babban yaya yaza'ai su sani. Nima da muke ɗaki ɗaya baifi shekara ɗaya dana fahimta yana yi ba. Kuma ban taɓa nuna masa nasan yanayi ba. Sai dai cikin hikima na sake nusar da shi sake nesanta alaƙarsa da Lilly duk da zuwa yanzu duk abinda ya haramta garesu basa yinsa. Kamar taɓa jikin juna, shigowa ɗakin mu sai da dalili, yimata tsifar kai da wanke mata underwear, zama kusa da juna gab, itama kuma Oum tana matuƙar saka musu ido akan hakan. Duk da Alhamdullah suma tuni duk wannan abubuwan sun daina shi gaskiya”.
       “Alhamdullahi naji daɗin hakan, amma duk da haka soyayyar dake tsakaninsu mai ƙarfi ce, barinsu a haka tunda har alamu sun nuna shi mai yawan buƙata ne yana da ƙyau su Oum su musu aure kawai, hakan shine babbar masalaha. Duk da nasan yanayin da yake ciki normal ne ga duk namiji irinsa dake a irin gaɓar waɗan nan shekarun na farkon balaga. Amma da alama shi yana cikin jinsin da al'amarinsu keda girma, dan ni da kai duk bamu tsinta kammu a irin wannan yanayin mai tsanani haka ba gaskiya”.
      “Tabbas hakane babban yaya. Kuma kayi tunani mai ƙyau. Sai ka samu lokaci kafin ka koma kuyi maganar da Oum”.
      “In sha ALLAHU ”.
Ya faɗa yana miƙewa saboda fitowar Ajwaad. Babu wanda ya yarda ya kalla a cikinsu saima faman sake haɗe fuska yake yi. A tare suka fita gwanin sha'awa, hakan yasa Mamy da tun fara maganar tasu take tsaye tana jinsu ta sauke wani irin nannauyan numfashi. Dama ta fito ne daga sashen Abah zata koma nata ɗakin. Shi kuma ya fita ta ƙofar baya zasu haɗu da yaran su wuce massallaci...

     A haka ranar Ajwaad ya yini yana faman fushi da kowa. Sai da Maanal ta shigo bayan azhar ta samesa a falo kwance. Sunje anguwa ne ita da Ammie tun safe, sai yanzu ne suke dawowa. Ko gida batabi Ammie sun shiga ba ta bama Amaal kayan da suka sayo a kasuwa na haɗin turare da Ammie keyi da kayan gyaran jiki ta shigo gidan su Ajwaad ɗin. Dan tasan zai shiga gidan nemanta. Itama kuma missing ɗinsa take ji sosai duk yau baya ganshi ba kasancewar fitar sassafe sukayi.
      Itama dai tayi girma Masha ALLAH. Dan maƙerin bufurci ya fara bayyana kansa gareta ƙirji masha ALLAH. Tayi tsaho ƙyawunta ya sake fitowa. Sai dai tana nan kamar a hure babu wani ƙiba. Sai da ta zauna a kujerar kusa da shi tana faɗin, “Wash ALLAH na ni Manalu”. Sai kuma ta ɗan dubesa ganin baiko motsa ba har lokacin idanunsa a lumshe. Ƙaramar harara ta masa, sannan ta ɗauke goran ruwan daya aje kusa da shi yasha kusan rabi ta buɗe ta shanye sauran tana sauke numfashi da ajiyar zuciya. Sauran ɗan ruwan daya maƙale a goran ta zazzaga masa saman ƙyaƙyƙyawar miskilar fuskarsa. Dole idanunsa suka fara motsawa kafin ya buɗesu a hankali a kanta. Sai ta sake zuba masa ƴar harara, a shagwaɓe ta ce, “Besty ni kake wani shahararrenwa?”. Ta ƙare maganar da tura baki. Sake lumshe idanun yay tare da ɗan matsesu waje guda, sai kuma ya buɗe. Shima hararrar tata ya ɗanyi, kafin can ƙasa-ƙasa ya furta, “An shareki ɗin. Ni da kika tashi fitarki kin sanar dani zaki fita?”.
       Sai da ta sake tura bakin sannan ta ce, “To ba Ammie bace tace sai na rakata kasuwa. Kuma ko lafiya ma banda shi cikina namin ciwo ga zazzaɓi ina ji amma tace langyare nake son yi mata dan tace na rakata. Shine kawai na bita gashi nan kaina ciwo yake min kuma ina jin ciwon cikin har yanzu”.
         Yanzu kam yinƙurawa yay ya tashi zaune da ƙyau. Cikin bata dukkan hankalinsa da damuwa a fuskarsa ya kai yatsansa ɗaya saman goshinta. Zafi kuwa rauu dan idanunta ma har sun sirka. Miƙewa yay kamar da ɗan faɗa-faɗa yana faɗin, “Shine kuma kika zo nan kika zauna baki nema wajen kwanciya da magani ba?”.
        Komai batace ba sai ɓata fuska data sake yi. Rankwashi yay kamar zai kai mata a saman kai sai tai sauri ta kauce tana matse ido. Bai rankwashe tan ba sai harara daya zuba mata ya wuce ƙaton fright ɗinsu dake a dining. Sai gashi ya dawo da first ald box ɗin su da goran ruwa marasa sanyi. Zama yay a inda ya tashi sannan ya buɗe box ɗin yana duba magungunan ciki. Maganin zazzaɓi ya ciro ya bata, harta kai zata zuba a baki ya dakatar da ita da faɗin, “Kinci abinci?”.
     Kanta ta ɗan girgiza masa. A shagwaɓe tace, “Shayi kawai nasha, sai wani ɗan a wara a kasuwa kuma nayi aman shi”.
      “Kina wasa da kanki ko?”.
Ya faɗa a hasale. Ita dai batace komai ba. Cikin ɗan haushi-haushi yace, “Kisha maganin na samo miki tea kisha sannan kici abinci dan cikinki yanzu ya gama cinkushewa”.
     Maganin ta zuba ya bata ruwa ta sha, kafin ya miƙe zuwa kitchen ɗinsu. Tea ya haɗa ya fito batare da yayma Mamy dake a kitchen ɗin tana girki ita da masu aiki magana ba. Itama ko kallonsa bata yi ba. Oum bata nan ita da Babban yaya sukaje gidan Babba Sardauna shine ya tuƙata. Fawzan kuwa yana ɗaki yana barci abinsa. Lokacin daya dawo ya sami Maanal ta kifa kanta a hannun kujera tai shiru, ta cusa hannunta ta riƙe cikinta. Cikin sauri ya ƙaraso yana kiran sunanta. Cikin dauriya ta ɗago idanunta har sun kaɗa, sai ta sakar masa murmushi dan bata son tayar masa da hankali.
      “Cikin ne?”.
  Da sauri ta girgiza masa kai tana amsar shayin da faɗin, “A'a barci ne kawai ke ɗibata”.
    Badan ya yarda ba ya barta, sai dai ya zuba mata ido tana shan shayin. Ai kamar jira tana gama shan shayin ta miƙa masa cup ɗin cikin yay mata wani irin ƙullewa. Ba shiri ta dafe shi da duka hannayenta tana fasa ƙara. Wani irin zabura AA yay a rikice yay kanta, sai dai ya kasa sauke hannunsa a jikinta sai faman jera mata tambaya yake jikinsa na rawa. Dai-dai nan kamar an jeho Oum da Babban Yaya sai gasu sun shigo, itama Mamy da mai aiki da ƙarar Maanal ɗin ta isa kunnesu suka fito daga kitchen ɗin.  Duk kan Maanal ɗin sukayi, dan harta faɗo ƙasa tana haure-haure. Kafin ma kace mi ta sassanƙame musu alamar suma.
    Hankalinsu ne yay masifar tashi musamman Ajwaad da Oum. Sai Babban yaya ne yay ƙarfin halin faɗin, “A kaita mota suje asibiti”.
    Da sauri Oum ta ce, “Kira Doctor dai Fadeel”. Baiyi musu ba yay kiran Family doctor ɗinsu. Yayinda tace ma Ajwaad daya rikice shi kuma ya ɗaukar mata Maanal zuwa ɗaki. A saman gadon Oum aka shimfiɗar da ita sannan Mamy ta shafa mata ruwa. Wani irin wahallen numfashi ta kawo, sai kuma ta fashe da kuka tana matse cikinta da damƙe hannun Oum. Isowar Doctor ta sakasu fitowa aka bar Oum da Ajwaad da yaƙi fitowa. Bayan doctor ya dubata ya tabbatarma Oum zata fara first period nata ne fa. Allura yay mata har biyu, cikin ƙanƙanin lokaci sai barci. Daga ita har Ajwaad ajiyar zuciya suka shiga saukewa a jajjere. Kafin Oum taima doctor daya sake musu bayanin komai godiya. Sai da ya fita ta samu damar kiran wayar Ammie ta sanar mata. Addu'a kawai Ammien tayi ta cigaba da aikinta tana sauraren masifar da Gwaggo keyi tunda ta shigo gidan. Dama duk randa ta fita kasuwa ta sayo kayan sana'arta babu zaman lafiya. Gwaggo ta dinga zage-zage kenan da jifan Ammie da munanan kalamai harda faɗin bin maza take fita yi. Ammie dai bata kulata ba dan dama haka take yi yanzu. Hatta shi kansa Baabu ɗin ta tattarashi ta watsar a gefe kawai.....

__________★

         Har akai la'asar Maanal na barci a ɗakin Oum, a kuma lokacine rikici ya ɓarke can a gidan su Maanal tsakanin Ammie da Babu. Dan amaryarsa ce tai kiransa a waya ta tsara masa ƙarya da gaskiya akan wai ga Ammie ta saka Gwaggo a gaba tanata zagi. A fusace ya baro wajen aiki ya nufo gida. Babu wani ƙwaƙwƙwaran bincike kawai yana zuwa ya kama marin Ammie. Shine Amaal ta fallo ta sanar ma Oum. A rikice ta wuce gidan ko Mamy bata sani ba....

          Ana idar da sallar Asr ɗin shima Ajwaad ya nufo gida. Dan hankalinsa duk yana kan Maanal. Kansa tsaye ɗakin Oum ya nufo, hakan yay dai-dai da farkawar Maanal a firgice. Silmiyowa tayi daga saman gadon Oum ta durƙushe ƙasa, hakan yasa Ajwaad ƙarasowa gareta da sauri yana tambayarta. Sai dai batako samu bashi amsa ba ta shiga kwara amai. Gaba ɗaya duk sai ya rikice yanata jera mata sannu. Itako aman take sosai. Sai da ta gama ta koma gefe ta kwanta yaraf tana maida numfashi. Sannun yaketa jera mata, yanda fuskarsa ta koma sai ka ɗauka ma shike ciwon. Sai kuma ya miƙa mata hannu yana faɗin, “Tashi muje ki wanke baki”.
     Kanta ta girgiza masa. Da ƙyar ta iya furta, “Zan huta tukkuna”. Bai matsa mata ba, ya fita ya ɗakko abu ya fara gyara wajen. Ya gama ya maida komai zai dawo ɗakin yaci karo da fasa ƙararata. Ai a ɗari ya ƙarasa faɗowa ɗakin. Tana a inda ya barta, sai dai kallon hannunta take da duk ya ɓaci da jini. Hannun ta nuna masa tana sake fashewa da kuka, sai kuma ta miƙe a galabaice tana kallon gadon. Ashe har nan akwai jinin lurane basuyi ba tun ɗazun. Ganin tana niyyar nufar ƙofa yay saurin riƙota. Cikin son ganin ta kwantar da hankalinta ya ce, “Relax!”.
      Kuka ta sake fashe masa da shi tana ƙoƙarin fisge hannunta, “Na shiga uku Besty jini fa? Jini Oum kizo jini”.
        “Nace ki nutsu ko!!”.
   Ya faɗa a tsawacen daya sakata nutsuwar dole. Sai dai jikinta rawa yake sosai tana cigaba da kallon hannun. Bakin gadon yace ta zauna amma taƙi, sai ya ƙyaleta kawai. Batare daya kalleta ba dan haka kawai yaji kamar yana jin nauyinta ya ce, “Ki jirani anan ina zuwa”. Daga haka ya nufi toilet ɗin Oum. Ruwa masu zafi ya haɗa mata, sannan ya sake dawowa inda take. Har yanzu tanata kallon hannun tana hawaye. Murya ya kwantar kamar bashi ke faɗa ba ɗazun.
        “Kinga ki nutsu Besty ba wani ciwo bane ba fa. Dama doctor ya sanar mana zaki fara proud ne shiyyasa kike jin ciwon ciki. Shine sai yanzun yazo. Ki tashi kije bayi ga ruwa can na haɗa miki ki cire wannan kayan ki gyara jikinki kafin Oum ta dawo taje wajen Ammie ne. In kuma kina son sai kowa yazo ya ganki a haka ne to?”.
     Da sauri ta girgiza masa kai tana miƙewa ta faɗa Bayin........✍️



✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH

53 / 77