RUMBUN QAYA BY zafafa biyar

Author :  zafafa biyar Category :  Love

Chapter   57 / 57

168K to 168.6K   out of 168.6K words

kuma dawo da tsohuwar abota tsakanin hydar da Aryan dan kullum suna tare a gida ko a Office.

A bangaren Adam, ya fito bayan daddy ya yi magana da Lamido akan akan case din an kuma duba laifin nasa an hukuntashi daidai da laifin sa sannan ya biya tara wadda Daddyn ne ya biya. Haka shima Muhammad akayi da Zainab aka kaisu court aka yanke musu hukuncin su daidai da laifin da suka aikata.

Ita kuwa me gayya me aiki, uwar mugaye da tsinannu duniya ta gamu da daidai da abinda ta aikata domin sai da aka sake mata aikin kafar aka sakè yanke ta har zuwa cinya Ya zama baki daya bata da kafa kwata kwata, ga haukan da ya sake mata karfi sosai daga Akth din dawanau aka wuce da ita aka bata daki ita kadai saboda yadda take fizgar gashin kanta da yadda take yaga kayan da duk aka saka mata tana surutai tana tonawa kanta asiirin abinta ta aikata a baya, sau daya Aryan suka je da raihana suka ganta Raihana sai da tayi kuka shi kuwa Aryan ko gezau zuciyar shi ta riga ta bushe. Shi dai tunda burin sa ya cika dan hatta barrister din nan da sukayi aiki tare da Hajiya zeenat din sai da aka kamo shi aka yanke masa hukunci daidai dashi. Zuwan Aryan ya sake rikitata, ta dinga kiran sunan sa tana cizgar gashin kanta, daga ranar aka hana kowa ma zuwa ganin ta.

******Tana tsaye a jikin sink din kitchen tana wanke bowl din cereal din Hanan, suka shigo ya doro ta a saman kafadar sa tana ta yi masa gwaranci. Dogon wando cotton ne a jikin sa babu ko riga suka shigo kitchen din ya dora Hanan a saman cabinet din kitchen din ya riko kugun raihanan ya juyo da ita suka saka dariya a tare

“Kai da yarinyar ka kun fiye rigima wallahi, ina zaman zama na kun sani Aiki.”

“Ya zaki damu? Umm?”

“Bada sadakar ku zanyi na huta kawai.”

“Ke Babyna, Yanzu zaki iya bada mu sadaka? Kalle mu fa, innocent babies dinki.”

“Ga shi nan ai, face dinka ne da ita. Ku narke ma mutum ido ko be niyyar abu ba yayi muku.”

“Eh Munji, Yanzu dai a bamu abincin mu, idan kuma muka ga dama muce a mana wani daban.”

“Allah ya baku hakuri, tasha friso din yanzu dai.”

“Nifa me zaki bani?”

“Ko zaka sha oat?”

“Um um, ni sai dai ki bani wannan.”

Ya nuna kirjin ta,

“Kana da matsala.” Tayi saurin daukar gwangwanin friso din da bowl din ta zame ta barshi a tsaye yana mata dariya. Daukar yar su yayi suka koma falo still yana dariya a hankali. Ta fito ta ajiye masa bowl din a gabansa tasa spoon tace

“Gashi nan.”

“Mun gode Mamin mu.”

Ya kwaikwayi karamar murya ya fada, murmushi tayi ya mayar mata, tayi hanyar bedroom dinsu tana cigaba da murmushin







Alhamdulillah!!! Dukkan godiya ta tabbata da Allah ubangiji, da ya bani ikon kammala wannan littafin wanda ya ja ni har zuwa in da ban yi zato ko tsammani ba, ina rokon dukkannin wanda na batawa da ya yafe min, ina kuma fatan kun amfana da wani Darasi a ciki komai kankantar sa

Duk abinda kuka gani na kuskure ku dauke shi a matsayin ajizanci na dan Adam. Allah ya shirya mana zuri’ah ya raba mu da sharrin masu sharri, ya hada mu da masu son mu na gaskiya ya yafe mana zunuban mu. Sai watarana idan allah ya Kaddara saduwar mu. Nagode Nagode Nagode. Zafafa biyar na matukar godiya. Na yafe ma duk wanda Ya bata min.

Ma’assalam. Rano😍

57 / 57