Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rumbun QAYA Complete Hausa Novel by Zafafa Biyar

Author :  zafafa biyar Category :  Love

Chapter   43 / 57

126K to 129K   out of 168.6K words

ya samu wata babbar tasa ya zubo mata ruwa ya bata, sai da ta kafa kai ta fara sha sosai har ta kusan shayewa ma saboda tsabar ishirwar da take ji, karo mata yayi tayi alwala bayan ta dan kama ruwa sannan ta koma cikin dakin dan a yanayin wajen da yadda bata jin motsin komai sai kukan tsintsaye ko hanya suka bude mata suka ce ta tafi ba zata iya ba, wani irin waje ne me matukar abun tsoro, tayi mamaki kwarai yadda suka iya zama a wajen sai dai duba da yadda baban yake furta kalmomin sa ya tabbatar mata da bafulatani ne irin na rugar nan wanda suka iya rayuwa a jeji daga su sai dabbobin su. Dankwalin ta, ta cire ta zauna a zaune ta kabbara sallar dan bata jin zata iya yi a tsaye saboda yadda take jin jiri na dibar ta. Ta dade tana jero sallolin kafin ta idar ta kalli kwanon da ya ajiye mata a gefen ta, tana sallar. Jawo shi tayi ta bude sai taga shinkafa ce da mai da yaji, cikin sauri sauri ta hau ci saboda tsabar galabaita batayi tunanin komai ba dan ta riga ta lissafa ba zata yarda ta zauna a gidan nan ba dan haka dole tana bukatar kuzari sosai yadda zata iya tsere musu idan ta samu damar tserewar. Tas ta cinye bata rage komai ba, ta yi hamdala ta gyara dankwalin nata sosai ta kwanta lamo a kasan wajen tana ji aka rufo ta, ta waje tayi shiru tunanin halin da yaran suke ciki musamman raihana da ta kasance karama, bata da alamun yin bacci har dare ya tsala sosai sai kukan sauro da yake tashi kamar ana kada ganga, tashi tayi tunda da alwalar ta, ta cigaba da sallolin ta a tsaye dan dama dazu da rashin kuzari ya hanata yi a tsayen. Har gari yayi sha bata runtsa ba, bata kuma ji motsin kowa ba sai chan zuwa lokacin da rana ta daga sosai sannan taji ana bude kofar. Matashin nan ne ya shigo dauke da kwanon abinci ya dire mata fuskar sa a rufe da bakin abu dama kuma ba gane shi tayi jiya ba saboda babu isahshen hasken da zata iya tantance shi. Fita yayi tayi shiru bata da niyyar daukar abincin bare taci. Sakè rufe ta, taji yayi ya bar wajen chan bayan kusan awa guda taji an sakè bude ta, Yanzu bata d’ago ba tana a zaune a yadda take sai da taji muryar sa ta d’ago suka hada ido.

“Yi maza ki taso, karki bata lokaci har tazo ta same ki anan, zan bude miki hanya kiyi gabas zaki ga wata doguwar hanyar yar siririya kiyi ta binta zata fitar dake har titi, karki tsaya dan daf suke da isowa nan.”

A gigice ta mike tayi hanyar fita suka fita a tare ya fito da ita har waje ta bayan gidan sannan ya nuna mata hanyar da zata bi, zata tsaya yi masa godiya yace tayi sauri. Gudu ta shiga yi na fitar hankali baji ba gani tana gudu tana addua da karfi, ta sha wahala sosai dan sai da taji kamar kafafun ta ba ajikinta suke ba, amma ta daure ta cigaba da gudun har fara hango titin me dauke da motoci yan tsirari, murna ta hau yi ta kara daga kafarta sosai tana jin a ranta ta kubuta har ta karaso titin kanta tsaye ta fada kan kwaltar ba tare da ta duba ko taji karar motar da take shararo gudu na musamman. Shi kansa be lura da ita ba, dan ba hanya ce ta wuce war mutane a kafa ba, dan baya tunanin akwai wani kauye a kusa da wajen saboda hatsarin sa, highway ce dan haka a full speed yake tafiya abinda ya hanashi samun damar taka birki har yayi wani irin tafiyar yaji da ita, ta kwalla kara karar da ta ankarar dashi abinda ya faru.

****Nannauyar ajiyar zuciya Hydar ya sauke kafin yace

“Labarin mutuwar ammmy shine abinda ya taba faruwa damu wanda ya samu a cikin matsanancin tashin hankali, mun sha wahala matuka kafin rayuwar mu ta dawo daidai, munyi kuka tamkar idanun mu zasu rufe saboda azaba, amma Ya zamuyi? Haka Allah ya tsara, abin tashin hankalin shine rashin ganin gawar ta, yafi komai daga mana hankali.”

“Allah ya gafarta mata zububanta, Allah yasa muyi kyakkyawan karshe.” Aryan yace muryar sa a ciki

“Amin.”

“Gobe Friday, zaka iya shigowa kano? Nayi maka booking flight din yamma, idan ka bar Office ka shigo akwai abinda nake son nuna maka.”

“Ok, ba damuwa zan yi kokari nazo.”

“Nagode sosai, Nagode da bani lokacin ka.”

“Babu bukatar godiya,kai dai ka kula min da kanwata, shine kawai.”

“Ko? Zan duba yiwuwar hakan toh.”

“Karka manta dai, kanwar maza ce.”

“Haka kace dai.”

“Haka ne ma, bari na koma Office na bar ayyuka.”

“Ok, sai ka shigo.”

Suka ajiya wayar.

Hoton dake kan system din ya sake budewa sosai, ya kara kallon sa sannan ya fita ya bude dayan, ya tabbatar da dukkan information din daya ne kafin ya kashe system din ya maida ita back seat din ya d’ago kujerar daidai sannan ya kashe AC motar ya kashe motar ya fito rike da wayar sa ta office a hannu dan da suna magana da hydar kiran zainab ya shigo sai dai be daga ba. Kofar jikin gate din ya tura ya shiga gidan ya hangi motar Adam a parking area ya wuce ciki ya shiga falon. Babu kowa kamar ko da yaushe sai tv dake a kunne tana ta fama ita kadai, kashe ta yayi ya kunna hasken falon wanda yake da a kashe sannan ya haura saman zuwa bedroom dinsa. A falon saman ya tarar da Adam yana waya yana daga muryar cikin tashin hankali dan da gaske karamar magana tana neman zama babba babu labarin Hajiya zeenat babu dalilin ta wanda babu wanda yake zargi illa Aryan gashi ya rasa yadda zai masa ya gano wani. Wuce shi Aryan yayi kamar be ganshi ba yayi saurin shan gabansa yana katse wayar. Wani kallo Aryan din ya watsa masa kafin ya giciye shi ya saka key zai bude dakin kasa Adam din ya rike kofar yana tare shi

“Ina ka kai min uwata?”

“Uwarka? Wacece kuma haka?”

“Baka sani ba? Ko da yake ba zaka sani ba tunda ba wai ka wani san dadin iyaye bane ko kuma kasan shakuwar dake tsakanin uwa da danta.”

Kamar an soke shi da mashi haka Aryan yaji maganar, tayi masifar taba shi amma sai ya dake ya fuske tamkar be ji me Adam din yace ba, ya sa hannu ya fincike hannun sa ya hankade shi baya ya shige dakin gami da banko kofar yana jin Adam din na dura duren ashar ya dafe kansa ya jingina da kofar kirjinsa na wani irin harbawa. Ya dan dade a tsaye a wajen kafin ya karasa gaban side drawers dinsa ya ciro maganin sa ya dauki ruwa yasha sannan ya rage rigar jikinsa ya kwanta a saman gadon ya jawo wayarsa ya kunno karatun alkurani me girma yana saurara a hankali nutsuwa na shigar sa tana ratsa shi har ya samu ya dawo daidai.
Kusan awar shi daya a kwance ba bacci yake ba kawai yana sakawa da warware abinda yake shiri yi ne a cikin yan kwanakin nan, yana kuma fatan ya samu nasara. Yunwa ce ta soma nukurkusarsa, baya son sakè haduwa da Adam bare har ya biye masa su yi musayar magana Shiyasa ya dade a kwancen ma. A tunanin sa ya tafi dan haka ya dauki jallabiyar sa me gajeran hannu ya zura akan farar singlet dinsa ya sakko kasan zuwa dinning area, ya samu an jere abincin akan dinning din sai dai babu plate. Kitchen din ya nufa ya bude wajen da plates din suke ya dauko zai fito Kamal ya kirashi sai ya tsaya rike da plate din a jikin sink ya daga wayar.

“Ina ka shiga ne wai?”

Kamal yace yana fitowa daga meeting din da sukayi, a gajiya yake tikis dan ya matsu da kiran Aryan din ne ma Shiyasa amma da kashe wayar zai kawai ya koma ya kwanta dan kusan kwana uku kenan basa samun isashen bacci akan wani case da sukeyi

“Na dan kwanta ne, Yanzu kuma na sakko zan yi lunch .”

“Ok, kunyi magana da Ya nabeela ?”

“Eh munyi, kasan ta. Komai ma abun damuwa me a wajen ta.”

“Dole ne ai, ni kaina na damu din, kawai dan ni namiji ne. Please Aryan Karki yi wani abu, akwai shirin da nake akan case din nan, amma for now don’t make any move.”

“Ok.” Yace a gajarce

“Good.”

“Em akwai abinda nake so dama na fada maka.”

“Ok, ina ji.”

“I think na gano in da Ammy take.”

“Wait what!? Are you serious?”

“Yeah, ba kace I should take over ba, so na gano in da take, kuma na gama planning yadda zamu je mu ganta, ni da hydar.”

“Ku jira ni, zan shigo Sunday sai muje.”

“Saturday zamu je, zai shigo kano gobe sai muje Saturday.”

“Noo ku jira ni.”

“Why? Ba zan iya yi ni kadai ba? Dole sai kazo?”

“Zaka iya, but Inaso nazo nima.”

“Wannan karon dai just allow me please.”

“Aryan?”

“Pleaseee.”

“Ok,ok. Shikenan.”

“Yauwa, Atleast nayi wani abu, Inaso raihana ta kara sakin jiki dani, idan hakan ta faru zata kara yarda dani. Zata yarda ni ma I’m a good person, ba Halin mu daya da daddy ba.”

“Naji naji, don’t change the topic. Na gaji tikis zan je na huta, zamuyi magana anjima.”

“Ok.” Yace ya katse wayar. Da sauri Adam dake makale a jikin kofar kitchen din ya bar wajen yana wani irin murmushi.
_**RQ_**

56


****Katse wayar yayi ya fito zuwa dining ya zauna gami da jawo warmers din ya bud'e ya zuba abincin dan madaidaci ya yi bismillah ya shiga ci a hankali yana danna wayarsa da yake kokarin tura mata sako. Yaci ba laifi dan ba wani breakfast yayi sosai ba ya ture plate din yana mikewa, ya koma tsakiyar falon ya zauna a cikin kujerun falon da ya dade be yi irin zaman ba.

***A firgice ta farka daga baccin da take, ta kwala sunan Aryan dan dama da sunan nasa baccin yaci karfin ta. Ladi ce ta shigo da saurin, ta zura mata ido tana kallon ta kafin ta kurma uban ihu bayan ta lura da in da take. Tashi tayi tana yunkurin kakkabe jikinta saboda wani irin mugun kyankyamin wajen da take da yadda dakin yayi mugun datti.

"Ahe kin farka." Ladi tace tana matsowa kusa da ita, da sauri Hajiya Zeenat ta daka mata tsawa tana kallon ta cikin yanayin kyankyamin tace

"Karki kuskura ki matso kusa dani."

"Aradun Allah sai na matso ki, mune yanzu dangin ki tare damu zakiyi rayuwa."

"Inji uban wa, na rantse da Allah kika sake matso ni sai nasa anyi maganin ki."

"Tab lallai, baki san ma wacece ni ba."

Kallon banza Hajiya Zeenat tayi mata, ta yi hanyar fita daga dakin a fusace, dariya ladi tasa tana gyara daurin zanin ta, ta bita da kallo dan tasan ko kusa bata isa ta zura kafarta waje daga dakin ba. A tsorace ta juyo dakin gami banko kyauren da ya kusa karyewa jikinta na rawa tace

"Menene a waje?"

"Jeki ki gani mana, aradun Allah sai ta cinye ki tas har kashin ki."

"Dan Allah menene? Kamar kura na gani."

"Ba kamar ba, itace wallahi. Kuma an riga na sanar da ita da kin fito tayi kalaci dake."

"Na shiga uku, abinda yaron nan zai min Kenan?"

"Ke kika san shi, kinga tafiya ta gashi nan garin buga kyauren kin kusan balla shi, idan ya karasa ballewa aradun Allah har cikin dakin nan sai ta shigo ta shinshina ki kuma."

Da sauri Hajiya Zeenat ta damke ta ganin zata fita ta barta ita kadai, wani kallo Ladi tayi mata me cike da izgili tace

"Ke da kika ce kar na matso ki, uban mi yasa zaki rike ni?"

"Kiyi min rai, wallahi zan baki kudi, idan har kika taimake ni duk wata matsalar ki ta kau, sai kin zama abun kwatance a garin nan amma dan Allah ki barni na tafi, ba zan iya rayuwa anan ba."

"Mu da muke rayuwa a wajen uban mi ya cinye mu?"

"Dan Allah ni dai, kinji kanwata dan Allah."

"Alkuran ko me zaki bani ba zan taimaka miki ba. Kuma kika sake rike ni idan zan fita sai na kira kurar nan ta shigo, zan bawa lantis tuwon dawa ta kawo miki da ruwan randa me sonyi, idan kin ci, cikinki, idan baki ci ba ma dai cikin ki."

Sai ta juya ta fita gami da barin kofar a bud'e. Da sauri Hajiya Zeenat ta mayar da kyauren ta rufe cikin tsananin tashin hankali, lallai Aryan ya shirya tozarta ta, dama tasan halin yaron shegen taurin kai da kafiya, amma bata taba tunanin zai mata wannan azabar ba. In da ta tashi ta koma ta zauna cikin tsananin tsoro hankalin ta na kan kofar tana jin gunjin kurar da take a sake tana shawagin ta kamar yadda akuya ke yawo a tsakar gida. Taba kyauren akayi ta tsorata sai ga ladidi ta shigo da wata mummunar langa da ruwa a Kofin silba ta dire mata a gabanta tana kallon ta.

"Taimako na zakiyi dan Allah, zan baki kudi da duk wani jin dadin duniya, waya kawai zaki samo min dan Allah."

"Bamu da netiwok a garin nan ai, sai an je chan hayi ake samu ayi waya, su waye ma masu wayar a kaf garin nan? Basu fi mutum hudu ba."

"Na shiga uku, Aryan!!!"

"Inna Ladi tace idan kin cinye ki taba kyauren nan zan zo na dauki langar."

"Ki zauna anan toh dan Allah karki tafi."

"Chab, so kike taci ubana Kenan."

"Toh ya sunan kauyan nan?"

"Oho nima ban sani ba."

"Shegu marasa iya magana." Hajiya Zeenat tace k'asa k'asa cikin bacin rai, juyawa Landis tayi ta fice tana kada kugu. Zame dankwalin kanta Hajiya Zeenat tayi dan wani irin tururin zafi ne ke fitowa daga cikin jikin ta. Da dan kwalin ta dinga kokarin firfita ta dan ja kwanon kad'an ta bud'e tuwon da sauri ta rufe ganin wata irin miya tsululu kamar an wanke kai, kwalla ce ta taru a idonta, lallai Aryan ya gama cutar ta, cuta me tsananin gaske, ba kuma zata kyale shi ba wallahi sai ta nuna masa ita uwar dakin sa ce a rashin mutunci. Tun da magribar fari sauro ya fara gud'a acikin kunnuwan Hajiya Zeenat, ta shiga aikin kore su amma ko gezau kamar ma kara turosu ake yi ga wani irin shegen kuka da suke kamar zasu ci babu sannan ga kukan da cikin ta yake yi dan daga prison take dole tana tare da yunwa. Bata yi tunanin yin sallah ba ko kad'an dan bata bukatar abinda zai fitar da ita waje. Ladi ce ta dawo dakin dauke da yar karamar touchlight ta haska.

"Kiritta ce ko musulma?"

"Ban..." Da ban sani ba zata ce, sai kuma ta tuna, ta ja tsaki cikin kunar Tai tace

"Ina zanyi alwalar?"

"Taso muje, ni shaf na manta ma ashe kina sallah, da naji baki magana ba na dauka kiritta ce."

"Amma ai kinsan ni mace ce ko?"

"Taso kafin K'adari ya dawo da kurar nan, sun dan fita shawagi sai kiyi da jiki."

Da sauri Hajiya Zeenat ta mike tabi bayanta dan dama fitsari take ji, sai data fara tabbatar da babu kurar sannan ta yarda ta fito ta rakata kofar bayin da babu ko rufi sai dan zagaye shi da wanda idan kana tsaye tsaf za'a hango ka. Gefe ta samu tayi fitsarin dan babu yadda zatayi, ta fito tayi alwalar sannan ta koma ciki. Wata tsohuwar darduma ladi ta kawo mata tace ta barshi zata shinfida dankwalin ta, juyawa tayi da kayarta ta bar mata touchlight din ta yi sallar sharp sharp ta idar ta zauna jigum sai taji motsi alamun wanda aka ce ya fita da kurar ya dawo, kara nutsuwa tayi ta dauki ruwan a ba yadda zatayi tasha kad'an ta ajiye.
Kayan abincin da Aryan yasa a siyo mata Buba ya kawo dama abinda ya fitar dashi tun rana kenan, maimakon akai dakin da take sai Ladi tace akai mata dakin ta dan so take sai ta koya mata hankali sannan zata kyale ta, katifar dai da maganin sauro ta bawa ladidi ta kai mata ta shinfida mata da sabon bedsheet dan karami sai pure water leda biyar. Ta dan ji dama dama da aka kawo karamar katifar da ruwa da maganin sauro, sai dai kuma taji babu dadi dan alamu sun nuna bata da shirin tafiya yanzu kenan.

***Kamar yadda Aryan suka tsara da Hydar haka akayi daga office ya wuce airport kai tsaye yana zuwa suka taso zuwa Kano. Yana sauka ya wuce gidan Adda Maimuna bayan ya kira Muhammad ya sanar dashi zuwan sa. Sai da ya isa gidan ya huta sannan ya kira Aryan yace masa ya sauka. Gashi nan zai zo ya dauke shi yace masa sannan suka ajiye wayar. Muhammad da suke zaune tare ya kalle shi cikin son Karin bayani yace

"Kamar dan rainin hankalin nan ko?"

"Wai Aryan?"

"Eh shi, guy din nan ko? Hmm amma ba komai haka Allah ya kaddara."

"Toh ya za'a yi da abinda Allah ya kaddara?"

"Haka ne, amma ni sam be yi mun ba, bai kuma dace da Raihana ba, sai uban girman kai da nuna shi ya isa."

"Calm down bro, komai ya wuce please a daina tuna baya, Allah zai musanya maka da mafi alkhairi ."

"It's hard ai, kawai kai dai ayi sha'ani."

"Na sani, ayi hakuri dai."

"Wai ko tsoron sa kake ne?"

"Tsoro? Me yasa zanji tsoron sa?" Yace a dan hasale dan dama akwai shi da saurin tunzura kamar Aryan din

"Naga kana goyon bayan sa ne."

"Yanzu shi yake auren kanwata, ko ina so ko bana so I have to respect the fact that mijin tane."

"Ok ok, naji shikenan?"

Mikewa Hydar yayi dan har ga Allah Muhammad din ya bashi haushi sosai.

"Na fita ba lallai na dawo yau ba, zan samu hotel na zauna kawai."

"Saboda nayi magana?"

"Yes, bana so a zarge ni da abinda bashi bane ba."

Sai ya fita, ya bar Muhammad din a tsaye. Biyo shi yayi ya tarar dashi a waje yana jiran Aryan din ya tsaya gefensa yana kallon yanayin fuskar

43 / 57