Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rumbun QAYA Complete Hausa Novel by Zafafa Biyar

Author :  zafafa biyar Category :  Love

Chapter   54 / 57

159K to 162K   out of 168.6K words

yayi, suka shiga dakin sannan yace

“Haba ammyn yara, haba Aishatu.”

“Me nayi kuma?”

“Yadda kika amsa ne, sam be ji dadi ba. Kuma da kin dan kara zama.”

“Ba muharrami na bane da zan zauna muyi ta musayar wayu ai, kaga kuma Yanzu akwai surkuta a tsakani.”

“Aisha!!”

“Gaskiya fa.”

“Allah ya shirya min ke.” Ya fita yana murmushi. Yasan duk abin nan tana yi ne kawai domin ran ta a bace yake, dan yasan tafi jin haushin abinda Daddyn yayi mata akan na hajiya zeenat. Saboda ita dama chan tasan zata aikata fiye da haka, amma me yasa daddy zai wulakanta su, ya ajiye duk alakar nan ya rufe idon sa ya kore su.
Duk a kunyace Daddyn yake, ya kasa sakewa sam tunda suka shiga ciki, kwata kwata be ji haushin abinda Ammyn tayi ba, ya chanchanci fiye da hakan, dan yayi musu abinda yafi haka. Dawowar Abbyn ta dan sa ya sake har suka shiga hirar rayuwa da sauran abubuwa, wanda ya dauke su lokaci me tsawo,har Dadah ta dawo suka gaisa ta shiga ciki, ta samu ammy tana ta faman fushi akan zuwan Daddyn, baki ta bata ta dan kwantar mata da hankali sannan tace ta taimaka su hada musu abincj musamman tunda daga tafiya yake kuma doguwar tafiya. Kitchen din suka shiga ta baya, daidai lokacin me taya ammyn Aiki tazo, sai ta koma ciki ta barta da Dadan tana guiding dinta suka dafa abincin me dan karan dadi.

Duk da yasan ya kamata ace Ya tafi ko dan gajiyar da ya kwaso, amma Ya kasa tafiya. Idan yaje gidan ma be san me zai yi ba, dan gaba daya gidan yayi masa baki yanzu.

“Kasan abinda ya faru da zeenatu kuwa?”

Girgiza kai daddy yayi

“Me Ya same ta?”

“Kamal be sanar da kai ba ko nabeela kenan.”

“Gaskia.”

“Ai tsautsayi ta hadu dashi, ko nace Kaddara. Mota ta bige ta kuma me motar ya gudu, in ta kaice maka labari Yanzu haka ma an yanke kafar, sai dai suna zargin kamar Har da ciwon hauka yana damun ta. Ni dai ban je na ganta ba, haka dai na samu labari.”

“Abinda ya chanchanta gareta kenan, ni bani da wani information akan ta da rayuwar ta tun bayan da na tafi, tun da zamu wuce na rubuta takardar saki na bawa Kamal nace ya bata, idan ta fito daga prison din dan na tabbatar sai ta fito, daga nan bamu sake maganar ta da kowa ba, dan sun san bana so.”

“Ta fito din kam, sai dai tun ranar da aka fito din baa sake sanin in da take ba, Ana zargin kamar dauke ta akayi, sai gashi kuma yan sanda sun kawo ta a karye cikin mawuyacin hali.


“Abinda ya dace da ita kenan Barr. Matar nan ta cutar da rayuka da yawa, tabbas nasan a karshe mutuwar wulakanci zatayi.”

“Kaje ka ganta.”

“Zanje, ko dan naga yadda rayuwa ta maida ita. Amma tare da kai zamu da hajiya aisha.”

“Aisha zata kuwa?”

“Zata, kasan ta da saukin kai.”

“Yanzu ai tayi tauri.” Yace yana dariya

“Rayuwa ce ta maida ita hakan.”

Shigowar da tayi yasa su yin shiru, ta ajiye musu flasks din abincin. Sannan ta sakè fita. Tare suka ci abincin, wanda rabon daddy da yaci abincj me yawa irin haka ya manta, sai yaji kamar an dawo rayuwar su ta baya ne, babu abinda ya faru.

“Allah ya jikanki Khadija. Allah yasa kina aljanna.”

Yace a sanyaye,

“Amin ya Allah.”

Sai da akayi sallar azahar sannan ya fito ya tafi, ba a san ransa ba, ya wuce gidan nasu da babu kowa a yanzu sai masu aiki saboda kula da gidan, wanka yayi yana komawa dan ko wayar sa be kunna ba sai ya huta sosai. Kwanciya yayi ya dan yi bacci zuwa laasar sai ya tashi.

Kafin ya tashi Ya nabeela da yaran da khadijan Kamal sun iso gidan, suka yi zaman su a falo dan sun san bacci yake yi. Suna zaune bayan an idar da laasar sai gashi ya fito, cike da mamaki yake kallon su, su amna suka tafi da gudu suka rungume shi ya daga su sama yana dariya.

“Maimakon ku tashe ni.” Yace yana karaso wa falon rike da yaran

“Munsan hutawa kake, kuma ba sauri muke ba.”

“Lallai kun kyauta. Sannun ku da zuwa.”

“Ina wuni?” Khadija ta gaishe shi a tsugune

“Lafiya lou ‘yata. Kuna lafiya?”

“Alhamdulillah.”

“Daddy barka da yamma.”

Ya nabeela tace tana murmushin jin dadin yadda Daddyn ya chanja

“Barka dai Nabeela, kuna lafiya?”

“Alhamdulillah wallahi, ya karfin jiki? Allah ya sa kaffara ne.”

“Kalle ni fa, ke kin ga alamun ciwo? Ai na warke sarai wallahi. Alhamdulillah.”

“Allah ya kara sauk.” Suka hada baki da Khadija suka fada

“Amin, Allah yayi muku albarka.”

“Dr yace yana maka sannu da zuwa Daddy.”

“Likita bokan turai, Nagode masa.”

“‘Yata kuna lafiya dai ko? Babu wata matsala?”

“Babu komai Daddy.”

“Toh Masha Allah, haka nake son ji”

“Miko min wayata a ciki Nabeela, nasan an kikkira ni.”

Tashi tayi ta dauko masa wayar sannan ta dauko kayan abincin da suka dafo masa ta kawo tsakiyar falon. Kamal ya fara kira sannan ya kira Aryan sai brothers dinsa da abokan hurda wanda yaga sakon su. Har dare su Ya nabeela na gidan sun tattauna maganar hajiya zeenat da Adam ma daga nan yace zai je ya ganta gobe daga nan ya wuce company.

****Washegari Khadija da Ya nabeela suka tafi garin su Kamal, wuni Ya nabeela tayi ta juyo in da ita kuma Khadijan zatayi musu kwana biyu daga nan taje gidan su itama tayi kwana biyu sai ta bi kamal din domin zai kwana biyu kafin ya dawo wanda yake saka ran dawowar sa ce gaba daya. Yana so ya dawo da babansa cikin kanon ma kusa dashi sannan ga Daddy ma yana so ya dawo su cigaba da rayuwa tare su cigaba da gina company su.

****Tana cikin tsananin azaba lokacin da Daddyn ya karaso, kuka take wiwi tana jin kamar a karasa guntule kafar a huta saboda ciwon da take mata na balai, a nutse take yau ba kamar kullum ba, abun ya dan sake ta dan dama zuwa yake yana tafiya. Sarai ta gane shi sanda ya shigo, sai ta rude ta fara kokarin mikewa, da sauri aka rirrikete akakwantar da ita saboda ba zai yiwu ta tashi a haka ba, ga hannu a nannade ga kafa a nannade da wanne zata iya? Karaso wa yayi ciki har gaban gadon ta da yake dakin mutane da yawa ne duk kowa ya basu hankalin sa yana kallon su. A tsaye ya tsaya daga gefen gadon yana kallon yadda ta koma cikin dan kankanin lokaci Allah ya chanja mata kamannin ta baki daya. Bubbuga kanta ta hau yi a jikin karfen gadon ya girgiza kai yace

“Ya jikin nata!?”

“Da sauki toh, an gode Allah.”

Be ce Allah ya kara sauki ba, ya zura hannun sa a aljihu ya ciro envelope guda biyu ya ajiye mata a gefen gadon yana kallon yadda take kallon sa amma ta masa magana, ya lura kamar bata iya magana ma gaba daya sai dai yunkurin yi din.

“Allah yayi miki abinda kikayi ma Bayin Allah da yawa zeenatu, ni IBRAHIM na sakè ki saki uku,ga takardar nan Allah ya sa wannan shine silar shiryuwarki idan zaki shiryu, dan bana jin zaki taba shiryiwa a rayuwar ki.”

Wanda suke gefen gadon suka yi saurin toshe baki cike da mamakin mutumin, ace mace na wannan mawuyacin Halin amma ka saketa har saki uku? Lallai maza mugaye ne. Yana jin kananun maganganun da suka soma tashi a dakin, da ihun da ta saka amma yayi biris, ya fice da sauri yana jin zuciyar sa fes kamar an zare masa babban nauyi da ya to kare zuciyar.

“Lallai maza sai a bar su, Yanzu saboda ta gamu da wannan kaddarar shine zai guje ta?”

“Ai haka Halin maza yake, sai dai Allah ya bi mata hakkin ta.”

Maganganu dai kala kala hadda nurses din ma da akan idon su abin ya faru. Matar dake kula da ita ce ganin maganganun sun yi yawa tace

“Idan kunsan abubuwan da ta aikata, bana jin zaku iya cigaba da zama da ita a dakin nan, wannan matar da kuke gani, tayi abinda zaa kirashi da karshen zalunci, samun muguwa azzalumar mace irin zeenatu sai an tona, dan haka kar kuyi saurin yanke ma mutum hukunci, abinda alhaji Ya aikata shine daidai.”

Tsit kake ji babu wanda ya sake magana, sai yan kananu dake tashi kasa kasa, sai kuma aka koma tunanin irin abin da tayi har haka amma dai babu amsa.
**RQ**

Page 73


***Duk abinda ya kamata ayi masa an yi masa ya kuma samu sauki sosai, kamar bashi ba dan sakayau yake jin sa sosai. Kwana uku suka kara bayan tafiyar daddy duk wasu tests da ya kamata ayi masa an masa na kai da na jiki gaba daya ba. Ranar da akayi discharging dinsu suka koma hotel din da suka sauka. Tana da lura da yanayin sa, he’s so happy and eager ranar. Wanka ta yi ta shirya kanta cikin riga zuwa guiwa da wandon palazzo mustard ta kama gashin kanta da new ribbon bayan ta wanke shi tas da shampoo da conditioner masu dadin kamshi, sannan tasa head band akan yellow tayi kyau kamar wata yar baby. Daga kasa ya hawo bayan ya sake kara musu kwanakin zama a hotel din zuwa sati daya. A shirya ta sameta ya tsaya jikkn kofar ya kasa karasowa yana mata wani irin kallo. A yan kwanakin nan da ya zauna da ita a hospital din ya sake shakuwa sosai da ita, ya kara karantar kyawawan halayenta da nutsuwar ta. Komai a nutse take kuma duk abinda yake so da Ya nuna alamu zata tashi tayi masa.

“Sanyiiiii.” Tace tana jan maganar a shagwabe ganin ya bar musu kofar a bude

“Ohh! “ yace da sauri ya saki kofar ya shigo.

“I was carried away by your beauty.” Yace yana murmushi, murmushin tayi itama ya tsaya a gabanta yana kallon gashin kanta da yake ta sheke da kyalli.

“Kin yi kyau.”

“Um thank you.”

“Me zamuyi Yanzu?” Yace yana kallon ta

“Wanka, abinci.”

“Bacci fa?” Yace yana kashe mata ido

“Um um, ni yunwa nakeji.”

“Toh toh, let’s eat.”

Yace yana mika mata hannu. Mikewa tayi suka karasa wajen abincin da sukayo order sa da suna dawowa, chips da peppersoup din kayan ciki suka ci da fresh milk ya dinga zuba mata tun tana masa kara har tace ta koshi. Tissue yasa ya goge mata bakin sannan yayi kissing lips din nata a hankali.

“I love you.” Yace yana kama hannun ta, ta runtse idonta a hankali ta bude shi

“Thank you for everything.”

Ya dora

“Kafin kizo rayuwata, bansan wacce irin rayuwa nake ba, my life has no meaning, bana jin dadin komai da kowa, I hate everything wallahi.”

“Amma yanzu ina ji na fresh and new, am in love.”

“Um really?.”

“Sosai, baki ga alama ba?”

“Na gani.”

“Ehen, did you love me too?”

“Umm.” Tace a kunyace

“Say it please!”

“Nace um fa.”

“Fada zaki naji.”

“Kaje kayi wanka.”

“Um um, sai kin fada min. Idan ba haka ba…” sai ya kanne mata ido.

“I… love… you.!” Tace a tsinke Tayi saurin saka kanta acikin cinyoyinta tana dariya. Hannun ta ya rike ya d’ago kanta yana mata dariya

“Kamar yak’i?”

“Ni kunyar ka nake ji.”

“Zaki daina ne.” Yace yana cije lips din sa ya mike yana tattare rigar sa, ya cire ta ya ajiye ya wuce toilet daga shi sai boxers. Tashi tayi ta gyara wajen, tsoro na dan shigar ta saboda taga yanayin Aryan din tasan babu abinda zai saka ya daga mata kafa, tsoro ne fal zuciyar ta tana tuna wahalar da tasha ranar.

“Ko nayi amfani da intim din nan da Ya nabeela ta bani?” Tace a zuciyar ta, tana tsoro sosai gashi ta taba karantawa a wani littafi may be idan tayi amfani dashi ta samu dan sauki. Bude chan kasan akwatin ta tayi, ta dauko tana duba jikin kwalin wajen da aka rubuta natural gel, ta dan dudduba ta karanta instruction din, alamun zai fito taji, tayi saurin boyewa ta rufe akwatin tana mikewa. Sanye da bathing robe ya fito, ya tsaya gaban mirror yana kallon kansa, yana hango ta ta cikin mirror din tana ta kumbuya kumbuya, duk ta tsargu gani take kamar zai gane abinda tayi. Be kulata ba, ya shafa mai ya dauki pjs masu taushi da nauyi ya saka a jikinsa sannan ya feshe jikinsa da turarurruka masu kamshi.
A gefen gadon ta zauna rike da karamin alkurani izu biyu,karasowa yayi ya zauna a kusa da ita, ya gyara mata dan kwalin kanta da ya dan zame baya, a zuci take karantawa amma kuma ta kasa concentrating saboda kusancin dake tsakanin su, paji daya ta kai ta rufe ta ajiye.

“Har kin gama?” Yace yana kallon ta

“Um.”

“Ok, banji kira’ar taki ba ai, anjima da asuba zaki biya min naji, nasan ma kin fini iyawa.”

“A ah dai, nasan ka fini.”

“Zamu ji dai, sai muyi musaffa. Izunki nawa?”

“Nayi sauka, a hadda kuma izu na goma, ban dade da farawa ba.”

“Masha Allah, ashe malama ce.”

Murmushi tayi me sauti.

“Mu kwanta ko?” Yace yana kama hannun ta. Da sauri ta mike jin yadda cikin ta ya kada lokaci daya

“Zan je toilet.”

“Muje na rakaki.”

“Um um da kai na zanje.”

“Tohm ina jiran ki.” Yace kai tsaye yana haye wa gadon, ya lulluba da blanket ya zama saura fuskar sa kawai. Jiki a sanyaye ta wuce toilet din, tayi fitsari sannan tayi brush, sai ta tsaya tana jin kamar kar ta fito ko ta fito ta tarar yayi bacci. Da kyar ta daure ta fito ta tarar ya rage hasken dakin sai yar kadan da zata iya gani, wajen kayansu taje ta rasa me zata dauka ma, duk ta rikice.

“Kina neman wani abu ne?” Yace yana daga kwancen yana kallon ta sarai

“Um! Na ganshi ma.”

“Oya let’s sleep.”

“Ni kamar ma akan sofa zan kwana.” Tace tana yin hanyar wajen sofa din.

“Ok, zata ishemu ai.” Ya tashi daga gadon ya sakko.

“Na shige su.” Tace tana dafe kirjin ta. Cim mata yayi a wajen ya rikota zuwa jikinsa

“Tsoro na Kike ji?” Yace yana kallon fuskar ta. Gid’a masa kai tayi sai yayi murmushi

“Menene abun tsoron? Comman karki badani mana.”

“Ni wallahi tsoro nake ji.”

“Comman, babu abinda zai faru kinji? Please allow me to show you how much you mean to me.”

“Ki tausaya ma bawan Allah, maraya.”

“Wayo zaka min.”

“Ba wani wayo, gaskiya ce. Kinga ni maraya ne.”

“Um.”

“Oya muje mu kwanta, na gaji sosai.”

Ba a san ranta ba, ta bishi suka kwanta din. Ya jawota jikinsa gaba daya, sannan ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idon sa.

***Idan tace tafi shan wahala yau batayi karya ba, tasha wahala fiye da wadda tasha a baya, dan gaba daya rikice mata Aryan din yayi, tun tana neman agaji har ta hakura ta cigaba da jan numfashi. Babu irin maganganun da be fada mata ba kuwa, tun tana fuskanta har ta daina ganewa, daga ganjn alamun sa shi kansa yafi samun abinda yake so a yau din, dan a wanchan lokaci shima wahalar yasha kamar ita, kuma be samu zuwa in da ya kamata ya je din ba sai a yau.
A gefenta ya kwanta yana maida numfashi yana jin yadda take jan kukan cikin dashewar murya, lalubo ta yayi ya jawota jikinsa ya matse ta yana cigaba da sauke numfashi. Sai da ya samu nutsuwa sannan ya shiga lallashin ta, tana kara volume cike da haushin sa.

“I’m very very sorry. Dan Allah Kiyi hakuri ki daina kukan.”

Banza tayi masa ta cigaba da kukan ta kawai, a maka laifi a isheka da turanci, sam bata ma fuskantar turancin a yanzu.

_”Duk yaya nabeela ce ta jawo min.”_ tace a ranta tana ayyana abinda ya farun da abinda Ya nabeelan ta bata, dan ta dan yi amfani dashi da ta tafi toilet din. Da ta sani bata yi amfani dashi ba, dan shine ya kara taimakawa wajen rikita Aryan din har yayi loosing control dinsa ya dinga zuba mata turanci kamar sarkin engila.

“Kinsan ina sonki ko? Ba zan yi abinda zan cutar dake ba.”

Kautar da kanta tayi gefe yana goge hawayen, ya juyo da ita tana kallon sa, sannan yayi kissing bakin ta yace

“I love you so much.”

Gumin saman goshin ta ya goge mata da hannun sa, sannan ya share mata hawayen saman fuskar ta.

“Kinga kowa fa ma da haka ya girma, kuma next time i promise you va zaki ji haka ba, yanzu ma dan an yi me gaba dayan ne.”

“Next time?” Tace tana kallon shi, daga mata kai yayi yana murmushi

“Next next next next time. Next time din to infinity, baya karewa.”

“Tab!” Tace tana turo baki

“Toh ki daina kuka, ba big deal bane ba, shikenan fa an kashe boss din.”

“Ni ka daina.” Tace tana kai masa duka a saman chest din sa

“Beat me, punch me idan zai sa ki daina kuka.”

Yace yana tura hannun nata jikin sa sosai. Dainawa tayi tana hararar sa, yayi murmushi kawai dan shi dariya take bashi sosai, ga wani irin happiness da yake ji. Da kyar ya lallabata tayi shiru, ya taimaka mata zuwa toilet sukayi wankan a tare tana tutture shi amma yayi biris, so yake yayi enjoying zaman nasu kar yazo yana cizon yatsa.

***Washegari ya tashi fresh, fuskar sa kamar gonar auduga saboda farin ciki, bata taba sanin yana da faraa irin haka ba, tare suka yi wankan safe suka shirya a tare duk da tana nokewa Amma ya hana mata hanyar da zata samu ma bare ta zuke, idan ta dan yi kamar zata ki, sai ya hade rai ya nuna sam be ma fuskanci abinda take son yin ba, dole kanwar naki yasa ta hakura take biye masa, dan hatta shafa mai shine ya shafa mata tana kunya tana komai, amma haka ta hakura. Sai da ya dan ci ladan wanka da shiryawar sa sannan sukayi breakfast suka yi shirin fita suka fice dan su zaga gari saboda akwai saukin sanyin yau.
Sky tower suka fara zuwa, sukayi hoto daga nan suka wuce memorial museum din Auckland, nan ma hotunan sukayi masu kyau suka karasa zoo suka ga dabbobi wanda ma basu taba gani ba. Daga nan suka wuce Le bistro des gourmets restaurant sukayi dinner a chan. Sai after 10 suka dawo

54 / 57