Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MATAR ABBANA Matar Da Ta Sauya Komai by Amnah El Yaqoub

Author :  Amnah El Yaqoub Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 14

24K to 27K   out of 40.1K words

ta saudia, yanzu Yaya za'ai da wannan kudin?"""

"Inna tace"" eh ai naga wani malami yazo ya dauketa wai zasuje ayi mata fasfo(passport), Hamza ina ganin kawai"

"karaba wannan kudin agyara mana gidan nan, inda muke yoyo da damuna duk agyara mana, sannan asiya mata kayan dakin, duk dade bamu San yaushe ne auren zaizo ba"""

"Kawu Hamza ya sunkuyar da kansa cikin damuwa sannan ya dago yace""da nayi tunanin in hadata dawani yaro, da"

"farko na yaba da hankalin yaron, to dana sameshi da maganar saiyace min bayaso"""

"Inna ta gyara zama tace""dan waye?"""

"Kawu Hamza yace"" acan layin suke, bansani ba ko zaki San kakar yaron, gidan Hajiya Rabi'atu, na yiwa Hafeeza"

"sha'awar yaron saboda naga bashida hayaniya kamar de ita,sannan itama Hafeeza zataji dadin zama dashi, amma yaron nan yadubi idona yace bai amince ba,anawa tunanin duk wanda ya dauki kyautar 'yarsa yabaka ai yayima komai arayuwa"""

"Inna tace""wai gidan Matar da ake cewa Hajiya Kaka?, gidan ta kake nufi?"""

"Kawu Hamza yace"" eh gidan ne"""

"Inna tace""ai Hajiya Kaka yayanta manya ne,gaskiya ba yaronta bane inaga jikanta ne, amma kuma Hamza, wani"

"hanzari ba gudu ba gara fa da ba'a yi wannan hadin ba, saboda inajin rade-radin cewa Hajiya Kaka tanada wani jikanta Babba, kuma iyayen yaron suna nan araye,amma baya Shiri dasu, wanne da ne zaiyi watsi da iyayensa ya wanye lafiya aduniyar nan Hamza? to ai har gara Gaddafin data liqewa""( )"

"Kawu Hamza yayi murmushi yace""Ta Rasulu wannan duk zancen mutane ne,sanin gaskiyar al'amari sai Allah sai"

"kuma tsatstsauran bincike,babu damuwa Allah yasa hakane yafi Alkhairi, Allah yabata nagari, idan kuma Gaddafin ne Allah yabasu Zaman lafiya"""

"Inna tace""Amin"""

"Hafeeza datake zaune agefe tana jinsu, saide tunda suka fara maganar gabanta yake faduwa,batasan wacece Hajiya"

"Kaka ba, bata gane akan waye suke magana ba, amma koma wanene shi ta tabbatar bazata juyawa Gaddafi baya saboda shi ba."

"Da daddare suna kwance a gidan sauro Hafeeza tana tattara tilun gashin kanta tana daure shi, Inna ta kalleta"

"tace""jiya na kwanta da safa a qafata gaba daya sai naji ni adaure"""

"Hafeeza tace""to Inna ai gara haka, ko sauro yashigo bazai cijeki ba, kinyi maganin sauro"""

"Inna tasake gyara kwanciyar ta tace""ba saboda sauro nasaka ba, abinda yasa nasaka qafata ce take kama gidan"

"sauron saboda kaushi""( )"

Hafeeza tayi murmushi batare da tace komai ba.

"Inna tace""Hafeeza gobe da sassafe kije wajanda kike soya qosai, kitafi da Almajirai kisa su tone duk wannan baqar"

"qasar da muka tarawa Alhaji na sidi a qofar gidansa, naje har gida nayi masa godia nace to mungode shekara da shekaru muna sana'ah a qofar gidan duk mun baqanta masa qasar qofar gida yace babu komai, wannan bulon damuke amfani kisa Almajiran su debesu gaba daya"""

"Hafeeza tace""uhm..."""

"batare data tanka ba, saboda tafara karanta addu'ar bacci acikin zuciyar ta."

*** *** ***

"Cikin dare yana bacci wani irin masifaffan ciwon ciki ya ta dashi, mararsa ta riqe yarasa yanda zaiyi sai hada gumi"

yake.

Cikin tsananin tashin hankali ya janyo wayarsa ya dokawa Kaka kira.

"Kaka tana bacci taji qaran waya, tamiqe ta zauna tana fadin ""la'ila ha illallahu,Muhammadur rasu lullah"""

"Ta juya gefenta ba taga Hassana ba, da alama yau ta gudu wajan Hussaina acan dakinsu zata kwana,tayi sauri ta dauki wayar ta Kara a kunne, daga nasa 6angaren yace""Kaka zan mutu"""

"Gabanta ya yanke yafadi tace""Hafeezu!, gani nan zuwa"""

"Cikin azama tatashi tafuto daga nata dakin tashiga nasa,ta kunna wutar dakin anan tayi tozali da abun Hafeez ya"

"miqe qyam, gabanta yasake faduwa kanta ya Sara, ta kalli Hafeez din taga yana runtse idonsa ga gumi ya jiqe masa fuska sharkaf kamar an watsa masa ruwa, cikin sauri ta qarasa taja bargo ta rufe masa jikinsa duk da akwai jallabiya ajikinsa, sannan ta dauki wayarsa tace""nemo min lambar Jamilu in kirashi"""

Kansa ya girgiza alamun bazai iyaba.

"Cikin sauri tafuto daga dakin tashiga dakinsu Hassana, tatashi Hussaina cikin magagin bacci Hussaina ta kamo mata"

"number, sannan Kaka tafuto daga dakin ta zauna afalo da wayar a kunnanta, harta kusa katsewa sannan jamilu ya dauka, cikin muryar sa me yanayin bacci yace""gaye ya ne?"""

"Kaka tace"" Jamilu ba Gayen bane kakar Gayen ce da kanta""( )"

"Jamilu yayi sauri yabude idonsa, yace""Kaka meyafaru? lafiya kuwa?"""

"Kaka tace""abokinka yana nan rai a hannun Allah, inaga de lalurar sa dayake fama da'ita ne tadawo masa,dan naga"

"yanayin jikin nasa sai ahankali,idan zai iyu de kazo"""

"Jamilu yace""to gani nan zuwa"""

"Yakashe wayar yasauko daga gadonsa ya zura jallabiya, yadauki abubuwan da yasan cewa zasu iya buqata, sannan"

"yafuto acikin wannan dare, yanufo gidansu."

"Kaka kuwa shayi ta hado masa da lemon tsami aciki, takoma dakin, anan ta ganshi ya kifa cikinsa ya kwanta akan"

"abun nasa, yayinda kansa yake cikin fillo yana yamutsa fuskarsa cikin azaba."

"Zama tayi akusa dashi tace""Hafeezu tashi kasha wannan shayin"""

"Cikin dauriya yace""Kaka mutuwa zanyi bazan iya shaba"""

"Kaka ta ajiye shayin tace""ni fa duk yanda nake dakai banason ka dinga kawo min zancen mutuwa Hafeezu,gaba"

"dayanku kaida qanannka kuna nan tare dani babu inda zaku tafi ku barni, Hafeezu idan nace kayi aure bakason maganar,yanzu wannan abun dame yayi kama Hafeezu?"""

"Suna cikin wannan magana Jamilu yashigo, yadora hannunsa awuyan Hafeez yaji babu zazza6i sosai, ya yaye bargon"

"anan yayi tozali da abu me girma, cikin nutsuwa ya maida bargon ya rufe, sannan yahada allura yayi masa, yana tunanin da alamun maganin da Hafeez din yakesha ne yaqare shiyasa har akazo kan wannan ga6ar, kuma rannan yaje asbiti kafin yadawo ya nemi Hafeez yarasa, yabude brief case dinsa yabawa Kaka wasu magunguna yace""gashi, dasafe a bashi wannan yasha, insha Allah zai samu sauqi, yanzu ma idan allurar ta sakeshi zaiji sauqi insha Allah"""

"Kaka tace""to shi wannan ciwo na Hafeezu babu makari ne Jamilu?"""

"Dr. Jamil yayi murmushi yace"" Kaka ki masa aure kawai,shine abun nasa zai rissina insha Allah"""

"Cikin damuwa Kaka tace""to Jamilu mun gode, muje na rakaka qofar gida"""

"Cikin sauri yace""Haba Kaka, kiyi zamanki tareda driver nafuto, Allah yabashi lafiya"""

"Kaka ta yiwa jamilu godia sannan tasake gyara wa Hafeez bargon jikinsa, tasake qara masa qarfin esi, sannan tafuto"

"daga dakin, bayan taga bacci me nauyi ya daukeshi."

"Cikin ikon Allah zuwa asuba yaji shi kalau yadawo normal babu ciwon cikin ko kad'an,saide kafin yayi sallar asuba"

"saida yayi wanka, bayan ya idar da sallah zama yayi a daki dayake agida yayi sallah ba'a masallaci ba,gari yanayin Haske, yafuto daga dakin kai tsaye yashiga mota yafice daga gidan."

"Su Hassana da suke gyaran gidan Kaka tafuto daga dakin Hafeez tana sallallami, Hussaina tace""Kaka me aka miki?"""

"Hajiya Kaka tace"" ku taimakeni jama'ah, ina Hafeezu yashiga ne?"""

"Hussaina tace"" kamarya? haba Kaka kamar wani yaro, may be yafita wani waje"""

"Kaka ta zauna agefen hannun kujera tace""bazaki gane ba,bashida lafiya jiya kwana mukai bamu runtsa ba""( )"

"Hassana dake goge dining table tace""Kaka yanzu fa kika tashi, na tabbatar sallar asuba ma kin makara, kuma kince"

"kwana kukai baku runtsa ba"""

"Kaka tace""keni banason jarabar musun tsiya,kiramin shi a wayarki inji ina yake"""

*** *** ***

"Yana futowa daga gida kai tsaye inda yasaba ganinta yawuce,yau akusa da inda take soya qosai ya faka motarsa, ya"

"zauna acikin motar yana Addu'ah Allah yasa tafuto,yau sosai yakejin qwarin gwiwar yimata magana kamar yanda Babban abokinsa Ib yabashi shawara."

"Wayarsa dake gefe tafara qara, yaduba yaga Hassana ce,yasa hannu yakashe wayar baki daya."

"Kasancewar hankalinsa yana kan wayarsa yana kasheta,hakan yasa dagowar da zaiyi yaganta awajan tareda wasu"

"Almajirai su biyu, akan idonsa Almajiran suka fara tone duk wata baqar qasa me maiqo data dade awajan, sannan suka debe qasar suka tafi zasu zubar, ita kuma tafara qoqarin motsa manyan dutsinan datake amfani dasu wajan dora abun soya, gabansa ne yafara wani irin fad'uwa, ya lumshe idonsa yana karanta duk addu'ar da tazo bakinsa,fuskarsa babu alamun dariya kokuma sakewa kamar de yanda take kullum, haka yabude motar yafuto,hannunsa zube cikin aljihun wandon sa,kai tsaye wajanda take tsugunne ya tunkara,saida yaje gab da ita sannan yaja ya tsaya yazuba mata ido yana kallonta,fuskarta kamar kullum babu kwalliya ko daya, amma tayi kyau cikin hijabin dayake jikinta."

"Jin takun mutum daga gefenta yasa ta dago fararen manyan idonta ta kalleshi,idonsu ya sarqe dana juna, lokaci daya"

"ta tuna haduwarta dashi a asbiti, kuma agabansa ne tabawa Fadila nono,nan da nan tashin hankali ya wanzu a fuskarta, gabanta yafara fadawa,wani irin tsoro ya kamata tanajin tsoron karfa ace mutumin nan ya santa."

"Wata tsohuwa ce tazo wucewa ta hanyar,ta kalli Uwar motar datake adane agefe, sannan ta kalli Hafeeza da Hafeez"

"tayi murmushi sannan tace""masha Allah kun dace kuwa"""

"Cikin sauri suka juya suka kalleta gaba dayansu, ganin yanda suke kallonta yasa tasake magana tayi tunanin Hafeeza"

"suyar qosai tafuto kamar kullum, hakan yasa tace""inma ba saurayin ki bane to me irin wannan motar tunda ya tsaya awannan wajan to yau zakiyi ciniki"""

"Hafeeza ta kawar da kanta gefe tareda daure fuskarta, ta d'an dage Hijabin ta kad'an tafara qoqarin ture dutsin"

"datake suya zuwa gefe, lokaci daya idon Hafeez ya sauka akan bajajjan hips dinta sakamakon dan janye hijabin datayi, sosai yake kallon qugun nata yakasa dauke idonsa akanta."

"Hafeeza ta juyo ta kalleshi nan take ta kamashi yana kallon qugunta,cikin sauri ta saki hijabin nata sannan cikin zazzaqar muryar ta tace""miye hakan?"""

"Hafeez ya d'an gyara tsayuwar sa sannan yayi gyaran murya, duk da gabansa yana fad'uwa haka ya dake"

"yace""Normal"""

"Hafeeza tasaki ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kansa, tarasa tsaiwar meyake mata awajan,gashi yazuba"

"mata ido sai kallonta yake, gaba daya saita jita wani iri atakure,kafin tagama tunanin datake sai taji Hafeez yace""Dama nace a asbiti """

"Iya abinda yafada kenan,gabanta yayi wani irin luguden faduwa,ta zaro idonta, sannan ta juya ta kalleshi tareda dora"

"d'an yatsanta akan pink lips dinta tace"" Kamin shiru""( )"

"Mamaki da wata irin dariya ta kama Hafeez,ya d'an dage girarsa guda daya,yaga alama kamar batason yayi mata"

"maganar asbitin,duba da yanda gaba daya ta rikice sai zare ido take."

"Ahankali yatako yaqaraso wajanta ya tsugunna dab da ita kamar jikinsu zai hadu dana juna,har yanzu fuskarsa a"

"daure take babu walwala saide shi a hakan fuskar asake take,hannunsa ya dora akan dutsin da hannunta yake kai,da hannu daya ya juyo da dutsin bai damu da baqin dayake jikin dutsin ba,cikin dakewa dakuma saka qwarin gwiwa yace""ina zankai miki?"""

"Cikin sauri ta girgiza kanta gabanta yana fad'uwa,kusancin nasu yasake takura ta,bata ta6a kusanci da namiji har"

"hakaba,ahankali tadan ja baya ta matsa daga kusa dashi,gashi taga layin nasu shiru kamar an hana kowa wucewa,Hafeez ya kalleta yaga yanda gumi yake yanke mata agaban goshinta,yazubawa d'an qaramin bakinta ido yana kallo,sannan ya maida idonsa kan gashin idonta masu ban sha'awa, yaga yanda take matsawa daga kusa dashi,ya d'an ta6e bakinsa, cikin wata irin muryar rada wadda sai iya su biyu shida ita ne zasu iya jin abinda suke fada yace""ina son qosai,dayawa nakeso kiyi,sannan kiyimin sadaka dashi, but... wannan yarinyar ta hannunki a asbiti """

"Gaban Hafeeza yasake faduwa,taga alamun mutumin nan tona mata asiri yakeson yi,cikin sauri tafara kad'e"

hannunta zata tashi tabar masa wajan.

"Hafeez yaga alama kamar so take ta gudu tabar wajan,gashi yanason suci gaba da magana, bayason tatafi batare"

"daya sake jin zazzaqar muryar ta ba, hakan yasa cikin sauri yaciro dala dari daga aljihun wandon sa yabata tare da fadin ""gashi, kiyimin qosai, kuma kibani canji"""

"Bata kalli kudin dayake bata ba,so take kawai su rabu ko zata samu yadena tuna mata zancen asbitin nan,cikin sauri"

"ta bude yar qaramar fos din dake cinyarta,Hafeez yana kallonta yaga akwai sababbin kudi acikin fos din miqaqqu."

"sai lokacin ta dago kanta ta kalli kudin dayake bata,taga dala ce, kuma tasan cewa dala dari de ba qaramin kudi bane, cikin sauri ta girgiza kanta tace""ni banda canji"""

"Hafeez ya kalli d'an qaramin bakinta sannan yace""kamarya? baga kud'i nan ina gani ba?"""

"Hafeeza ta daure fuska sannan ta kawar da kanta gefe tace"" sababbin kudi ne,tarasu nake saboda bikin wani yayana"""

"Cikin dabara yace""inane gidanku sai inzo in kar6i canjina?"""

"Ahankali tajuya ta masa wani kallo sannan tace"" kaga riqe kudin ka kawai,zanyi ma sadakar kyauta"""

"Cikin sauri shima yace""bangane ba? ni banason kyautar ki,kawai ki riqe kudin nan kiyi qosai kiyimin sadaka kuma ni"

"inason canji na, canji na kawai zaki bani"""

"Hafeeza tasaki ajiyar zuciya sannan ta lumshe idonta tabude su tareda juya idanuwan nata cikin wani irin salo, hakan"

"datayi ba qaramin tafiya da imanin Hafeez tayi ba, ta matsu yatafi, hakan yasa tace""ka riqe kudin ka,zanyi qosan da kudi na, nikuma zanzo na kar6a awajanka"""

"Cikin wani irin jin dadi yace""Really?"""

"Cikin zaquwa yatafi tagyada masa kanta,ahankali yajuya cikin motarsa yadauko mata wani Kati wanda address din"

"gidan yake jiki ya ajiye mata agabanta, daga haka bai sake cemata komai ba yajuya yashiga motarsa yatafi, sai alokacin tasaki wata irin ajiyar zuciya, tadafe kanta daya fara yimata ciwo,sai yanzu tayi dana sanin abinda ta aikata a asbiti,gashi yanzu wannan bawan Allah yana bibiyarta,kuma duk yanda akai da alama yasanta, idan be santa ba tayaya zai zo har inda take sana'ah?"

"Cikin tashin hankali tatashi tabar wajan ko ta kan dutsin datakeson janye wa bata biba,kai tsaye ta nufi gidan Maman"

"Fadila, adede lokacin Baban Fadila yafita kasuwa , ita kuma Maman Fadila tana zaune tana karyawa da taliya da Manja."

"Hafeeza tana qarasowa ta zauna awajan tare fashewa da wani irin kuka,sosai take kuka harda shashsheka."

"Maman Fadila tafara Salati sannan tatashi ta wanko hannunta ta zauna agefen Hafeeza tace""Hafeeza keda waye?"

"menene ya hadaki da Inna yau kuma?"""

Hafeeza tayi shiru taci gaba da kuka.

"Maman Fadila tace""kode wani ne ya dakeki?"""

"Cikin sauri ta girgiza kanta, sannan ta dago idonta daya fara yin ja, ta kalli Maman Hafeeza tace""dan Allah kiyi"

"haquri,rannan ne danakai Fadila asbiti, sai take ta kuka, shine shine nabata ta tsotsa"""

"Mama Fadila tarasa gane kan maganar,me aka bawa Fadilan ta tsotsa?, cikin rashin sani tace""kika bata me?"""

"Cikin kuka Hafeeza tace""nabata Nono, shikuma yaganni, shine yau yabiyo ni,wai namasa qosai harda cewa nafada"

"masa gidanmu zaizo ya kar6i canjin sa,kuma ya tsugunna agabana kusa dani kamar zai rungume ni,shikkenan yanzu kallon yar'iska zai dinga yimin"""

(finally de Hafeez yayi magana da Hafeeza. )

(Yaya batun soyaiyar Hafeeza da Gaddafi? kuna ganin Hafeez zaiyi nasarar sace zuciyar ta? )

(Yaya batun maganar Hajiya Kaka da tace zata nema masa aure?)

karku manta Hafeez ya watsawa kawu Hamza qasa a'ido

Wai ma menene yake faruwa ne tsakanin Hafeez da iyayensa?

(Alhamdulillah free page yaqare)

Complete document 1k

8621296018

Amina Muhammad fcmb

"kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034"

Amnah El Yaqoub
'<Øûß

"[6/14, 2:25 PM] El Yaqoub:"

"Cikin tsoratar wa Maman Fadila tafara tafa hannayenta tana salati,duk da dariya da take son qwace mata haka ta danne dariyarta tace""Hafeeza!!!?"""

Hafeeza tana jin yanayin yanda Maman Fadila takira sunanta tasake fashewa da wani irin kuka.

"Maman Fadila tace"" yanzu de ita Fadila tariga tasha Fata,amma nangaba ko zatayi kukan me, karki sake bata nono tasha, Hafeeza wannan aina mijinki ne bana Fadila ba,shiyake da damar dazai sha amma ba Fadila ba"""

"Cikin taqaici Hafeeza ta dago ido ta kalleta idanunta duk hawaye tace""ni kidena cemin wani zaisha min abuna"""

"Maman Fadila tayi murmushi tace""nadena, amma inde ba so kike maganar Inna ta Rasulu datake cewa Saura zaki"

"kai gidan mijinki ta tabbata ba,tokidena bawa Fadila nono,Shikuma abinda na lura dashi shine abinda yagani a asbiti ne yake so yasake gani shiyasa yabiyo ki,saboda haka kiyi hankali dashi ki kumayi taka tsantsan"""

"Hafeeza tashare hawayen idonta tareda ajiyar zuciya tace"" ni dama ba ruwana dashi,qosan ma ba zanyi ba,yaje"

"yanemi wata tayi masa"""

"Maman Fadila tace""waida gaske qosan yace kiyi?"""

"Hafeeza tafada mata yanda sukai itada Hafeez, dangane da batun sadakar qosai."

"Maman Fadila tace"" a a karkice haka Hafeeza,batun sadaka tunda kin riga kinyi masa alqawari to kiyi masa, baki san buqatar sa akan sadakar ba,kuma aiba had'uwa zakiyi dashi ba,kiyi qosan ki masa sadakar, kema Allah zai baki Lada, batun kudin dakika kashe kuma karki kuskura ki hadu dashi da daddare idan zaki kar6a,ki nemi wata tarakaki kije ki kar6i kudinki kokuma kije da rana atsaka, idon kowa akanku babu yanda za'ai inma da wata manufa yazo yayi miki wani abu"""

Sai a wannan lokacin Hafeeza tasaki wata irin zuciya sannan ta gyad'a kanta alamun amsawa.

*** *** ***

"Cikin wani irin farinciki da annashuwa yake driving dinsa har wani shafa lallausar sumar Kansa yake,ya dade rabon"

"daya tsinci Kansa a'irin wannan farincikin,sai faman ajiyar zuciya yake kamar an sauke masa wani nannauyen dutse daga kan faffadan qirjinsa."

"Yana shiga ya gansu afalo suna kallo, cikin nutsuwa ya zauna akan kujera tareda ajiye wa Kaka goro cikin gajerar"

"maganar sa ta kullum kullum yace""gashi"""

"Kaka ta kar6a tareda washe baki tadauki guda daya ta saka abakinta tadan karya tareda kallon sa tace""kamar kasan nemanka nake, dama kwana biyu banci qosai ba,nace tunda Hafeezu ya warke

9 / 14