Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MATAR ABBANA Matar Da Ta Sauya Komai by Amnah El Yaqoub

Author :  Amnah El Yaqoub Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 14

12K to 15K   out of 40.1K words

sun dauki lokaci ahaka sannan yatashi daga jikinta yace""Nasameku lafiya Kaka?"""

"Cikin farinciki Hajiya Kaka tace"" ras!,kalau muke Hafeezu,Yaya wajan aikin naku?"""

"Fuskarsa a kame kamar Koda yaushe yace""Alhamdulillah"""

"Kaka ta kalleshi tace""Hafeezu kullum fuskar ka a cunkushe yau daya de kayi fara'ah mana gaka ga"

"yan'uwanka,menene yafi gida da yan'uwa dad'i?"""

"Ataqaice yace mata""to Kaka"""

"Kaka ta girgiza kanta sannan ta dora hannunta akan murdaddan dantsan hannunsa tace""Kaga yanda kasake zama"

"gardi? mutane dayawa cewa zasuyi kafi shekara talatin"""

"Dan qaramin murmushi yayi kawai yace""uhm """

Sannan yafara qoqarin cire agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa.

"Husna ta kawo masa ruwan gora ta zuba masa a cup, sannan ta zauna tad'aga dinkin su da suka karbo daga wajan"

"tela cikin shagwa6a tace""Kaka Allah wannan dinkin kamar na koma na maida masa nakeji"""

"Kafin Kaka tayi magana itama Hassana tace""eh wallahi, yatashi yamana kaya da uban fadi kamar buhu,kiga fa yanda"

"yabar wajan hips dinnan da fad'i to tayaya zamu cika wannan wajan,? Kuma fa saida ya gwada mu, amma yamana wannan wajan hips din me girma,ina mu ina wannan abun, wannan ai saide Hips din HAFEEZA 'yar ajinmu, tana sakawa zata cika shi, dan Allah Kaka ki barmu muje mu maida masa ya rage mana"""

Ta qarasa maganar cikin shagwa6a.

"Hafeez ya kallesu sai yanzu yasake ganin yanda yaran suka sake zama cikakkun yanmata,sai wata ta6ara suke suna"

"shagwa6a, haushi ya kamashi da alama Kaka tagama sangarta yaran,ji yanda suke shagwa6a saikace qananun Yara,ji yake kamar ya lakad'a musu d'an iskan duka, yatsani sakarci a rayuwar sa.( )"

"Baqin ciki ne ya hanashi magana,Yara ko kunyar sa basaji agabansa suke maganar Qugu harda kawo zancen Qugun"

wata sakarya.( )

"Ahankali yatashi yawuce dakinsa yana 6alle botiran gaban suit dinsa,Kaka ta bishi da kallo harya shige dakinsa, sannan tadawo da kallonta wajan 'yanbiyu tace""rashin aure yana damun Hafeezu, gaba d'aya a firgice yake""( )"

"Ko minti biyu beyi da shiga dakin nasaba yafuto yana kallon 'yanbiyu fuskarsa a daure yace""Meyasa baku gyara"

"dakin nanba?"""

"Cikin sauri Husna tace"" Yaya zamu gyara Kaka tace mu barshi karmu gyara wai....wai..."""

"Takasa qarasa maganar kamar yanda Kaka tace idan yayi aure matarsa saita gyara masa, shakkar sa yasa ta qare"

maganar tata da wai... wai...

"Kaka ta kalli Husna tace"" wa? ni?, to yaushe akai hakan bansaniba?, gaskiya bansan anyi ba""( )"

tafadi hakan tana kawar da kanta gefe.

"Hafeez yadawo cikin falon ya zauna ya d'ora qafa d'aya kan d'aya fuskarsa a d'inke,yanda ya 6alle botiran gaban"

rigarsa hakan ne yabawa lallausan gashin dake kwance a qirjinsa damar bayyana.

"Yanda sukaga fuskarsa a daure to tsaf zai iya kai musu duka, hakan yasa sum-sum suka wuce dakin nasa suka fara"

gyara wa.

"Kaka kuwa kallonsa tayi taga ran nan nasa yayi baqiqqirin, tasaki ajiyar zuciya tana kawar dakai."

"juyawa yayi ya kalleta suna hada ido tasake kawar dakai, ya dauki fillon kujera yanufota dashi kamar zai jefa Mata"

"yace""keko"""

"Hajiya Kaka tasake daure fuska tace""Toni nasan yaushe akai hakanne?"""

"Kansa ya Girgiza kawai,domin kuwa yasan aikin ta ne."

"Kasancewar dakin nasa ba datti yayi sosai ba, hakan yasa cikin qanqanin lokaci suka gama gyara masa, babu musu"

"yatashi yashige, saida ya sakawa qofar d'an qaramin falon nasa key,sannan yashiga can cikin dakin shima yasaka key, yasaki ajiyar zuciya yafara zare kayan jikinsa saida yacire komai yadawo naked,sannan yashiga wankan sa."

"Yadade yana lailaye jikinsa da mayuka da turaruka masu shegen dad'in qamshi,kafin ya kalli qirar jikinsa a cikin"

"babban madubin dayake dakin nasa,shi kansa yasan cewa Allah yamasa halitta ta Ingarman namiji me jini ajika,yanada cikakkiyar lafiya hakan yasa Koda yaushe yakejin sa akan network, yasan cewa abunda Hajiya Ramla tagani Kenan shiyasa ta liqe masa,har yanzu yanajin baqin ciki idan yatuna yanda tasa qazamin hannunta ta ta6a masa abunsa,Allah ma ya kiyaye ba hannun nata ta zira cikin wandon sa ta ta6a abun skin to skin ba, ya tabbatar da haka tayi da shikkenan tagama cutarsa duniya da lahira, qarin baqin cikin ma yanda yakasa yimata musu alokacin."

"Dan qaramin tsaki yasaki sannan ya dauki pant irin na maza yasaka, yadauki gajeren wando yasake sakawa, sannan"

ya shirya tsaf cikin qananun kaya yafuto daga dakin nasa yanata zuba uban qamshi.

"Zama yayi akusa da Kaka sannan ya kalli Hassana yace""ke bani abinci"""

"Hassana ta kalli Kaka, sannan ta dawo da duban ta gareshi tace""Yaya wallahi Kaka ce ta hanamu, saida na cewa"

"Husna muje muyi shopping saboda girkin da za'a ma, shine Kaka tace kar muyi, saika kawo matar aure tukunna"""

"Hassana tana gama fadar haka falon nasu yayi tsit. , Hafeez ya juya ya kalli Kaka,cikin sauri Kaka ta dauke kanta"

tana ta6e baki. ( )

"Zamansa ya gyara sosai yana kallonta sannan yace""saboda naqi yin aure horon yunwa za'a fara min a gidan nan?,"

"zanzo daga wata qasa amma kinamin horon yunwa Kaka?"""

"Kaka tace"" ikon Allah, wai duk yaushe akai hakanne? ban ta6a jiba"""

"Husna tace""lalle ma Kaka,yazaki zame ki barmu aciki? kece fa kikace karmuyi,za'a yi order fizza"""

"Kaka tace"" mecece wata Fizza kuma ni Rabi'atu? inani ina wata Fizza saboda Allah?""( )"

"Kafin 'yanbiyu subata amsa tajuya ta kalli Hafeez tace"" kaikuma nadawo gareka, dakake cewa saboda kaqi yin aure"

"nakema horon yunwa ai zancen bana kaqi yin aure bane, baka dai samu wacce zata amince tayi haquri ta aureka bane saboda baqin miskilancin ka"""

"Hafeez yasaki ajiyar zuciya ya lumshe idonsa batare daya tanka ba, yana jinsu su ukun suka shiga kitchen suka shirya"

"masa abincin da yafi so, bayan sun ajiye masa abincin ko kallonsu baiyi ba,saida Kaka tayi da gaske, ta lallasheshi kamar Baby, sannan yatashi yafara cin abincin kamar bayaso, ganin haka yasa Kaka ta kar6i spoon din tafara bashi abincin da kanta."

"Da yamma yasake wanka yashirya cikin manyan kaya,farar shadda ce a jikinsa harda babbar Riga, yayi kyau sosai"

"kamar ranar daurin aurensa, sosai turare yake ambaliyar qamshi a jikinsa yafuto zai tafi masallaci wayarsa tana kan kunnansa yana magana da Babban abokinsa Ma'aruf."

"Kaka tace""dakata Hafeezu"""

Juyowa yayi ya kalleta bayan ya kashe wayar.

"Kaka tace""ina zakaje haka kayi wannan kwalliya?"""

"Ataqaice yace"" zanje masallaci"""

"Cikin hikima irinta tsofaffi Kaka tace""to Hafeezu acire wannan d'an kunnan mana,ai zakafi kyau idan ka cireshi, ga"

"wannan fenti daka fente jiki dashi Hafeezu kamar ba namu ba""( )"

"Girarsa guda d'aya yadage yana kallonta da mamaki, sannan yasaka hannu yacire d'an kunnan yabata, batare dayace"

uffan ba yafice daga falon.

"Kasancewar yashiga masallacin da wuri hakan yasa yasamu sahun farko, bayan an idar da sallah anyi Addu'ah"

"yatashi ya qarasa wajan liman yabashi hannu suka gaisa, sannan yasaka hannu a aljihun rigar shaddar dake jikinsa yadauko Dala d'ari biyu canjajju 'yan dala goma-goma yabawa liman cikin ajin sa dakuma miskilanci yace""gashi ayi sadaka"""

"Liman yayi qasa da murya yayi godia, Hafeez baice komai ba yafuto daga cikin masallacin mutane kuwa sai kallonsa"

suke.

"Liman yatashi tsaye ya nunawa jama'ah kudin, a kayiwa Hafeez Addu'ah sosai, sannan aka raba kudi wasu suka samu"

dala ashirin-ashirin wasu kuma suka samu dala goma-goma.

"Acikin wanda suka samu dala ashirin harda Kawu Hamza,Qanin mahaifin Hafeeza."

Bayan jama'ah sun futo daga masallaci kawu Hamza ma yafuto shida abokinsa Malam Musa.

"Suna cikin tafiya zuwa gida saboda akwai 'yar tafiya tsakanin su da masallacin, Kawu Hamza ya kalli abokinsa"

"yace""Malam Musa, Wato wannan matashin yaron daya bada sadaka yanzu,na dade ina tunani akansa,yaron yana birgeni,sannan na yaba da hankalin sa,yanada nutsuwa sosai, ina yawan ganinsa duk lokacin daya shigo gari,naga kamar bashida hayaniya, shiyasa nake masa sha'awar yarinyar nan Hafeeza 'yar wajan Yayana Haladu wanda yarasu, inaso naje nasamu yaron inyi masa tayin aurenta tunda yin hakan ba laifi bane a addinance"""

"Malam Musa ya jinjina kansa sannan ya gyada kai yace"" eh yin hakan ba laifi bane,inda ace iyayen Yara zasu Dinga"

"irin wannan tunanin inde har sun yaba da hankalin matasan kuma sun San za'a riqe musu yaransu da amana to kaga aida ansamu sauqin rashin aure awajan matasa,amma maganar gaskiya Hamza, karka fara wannan hadin, saboda yarinyar nan Hafeeza marainiya ce,daga kai sai Ta Rasulu kawai kuka rage mata,karka dauketa kabawa wannan yaron saboda wannan yaron dakake gani iyayensa suna raye, yana rayuwane da yan'uwansa guda biyu dakuma Kakarsa anan, har yanzu ba'a san dalilin dayasa baya tare da iyayensa ba, kuma daga majiya me qarfi ance yaron baya shiri da iyayensa,yanada matsala dasu"""

(malam Musa kallamu ka 6aro aiki )

Complete document 1k

8621296018

Amina Muhammad fcmb

"kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034"

Amnah El Yaqoub
'<Øûß

"[5/25, 10:51 AM] El Yaqoub: MATAR ABBANA "

(Luv Story)

Writing By Amnah El Yaqoub

Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update

https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45

6

"Kawu Hamza yayi murmushi Sannan ya d'an bugi kafadar abokinsa yace""Haba Malam Musa, yaushe zakai duba da"

"maganar mutane akan sha'anin aure? to inde zaka saurari jita-jitar mutane kwata-kwata bazakai auren 'yarka ba"""

"Malam Musa yace""Hamza,yarinyar nanfa Amanace a wajanku damu baki daya, tunda marainiya ce da munqi da"

"munso muma ai iyayenta ne,bazai iyu mu zuba ido ka dauketa kakaita cikin matsala ba,nafadama gaskiya yaron nan yanada matsala da iyayensa kuma daga majiya me qarfi naji hakan, to saboda me munaji muna gani zamu bari kadauki marainiyar yarinya kakaita cikin matsala? kasake duba wannan maganar de"""

"Kawu Hamza yayi murmushi yace""karka samu damuwa abokina,Alkhairin da nakeson hadawa insha Allah saina baka"

"mamaki,zakaga yanda Hafeeza zatai zamanta lafiya adakin mijinta,babu ruwana da maganar mutane tunda ba shi yaron ne da bakinsa yafada min haka ba,saboda haka kayi musu Addu'ah kawai"""

"Malam Musa yace""Hamza kenan, dama tayaya yaro zai fadama damuwar sa dakansa?, mude mun fadi gaskiya,"

"yanzu kuma duk abinda zai biyo baya, idone namu"""

*** *** ***

"Da daddare suna zaune aqofar gida suna fira, cikin soyaiya ya kalleta yace""Malama sai murmushi kike kode murnar"

"saukar goben ce?"""

"Hafeeza tasa hannu ta rufe fuskar ta cikin kunya tace""saboda Ganinka ne"""

"Wani irin dadi ya kama Gaddafi,cikin sauri yasake gyara zamansa yace""waida gaske kike Hafeeza tah?''"

"Dan kallon sa tayi kadan sannan tace""da gaske nake, gashi wannan nakane, dazu muka dafama, wannan kuma kayan"

"rabon sauka ne na dibar ma naka"""

"ta qarasa maganar tana bashi dan qaramin kwanon silba me kyau da dahuwar nama aciki,sai kuma ledar thank you"

guda biyu ancikasu da snacks din da sukai saboda rabawa gobe.

"Hannun Gaddafi har rawa yake wajan kar6ar kayan, ya dora kwanon silbar akan cinyarsa, sannan yabude ledojin suma yagani, ya washe baki yace""lala lala, wai duk wannan awajan saukar taku zaku raba?"""

"Kafin ta bashi amsa ya ajiye ledar yaci gaba da fadin""bari muga menene acikin kwanon"""

"yana budewa wani irin qamshi yadaki hancinsa, ya shaqa ya d'ago Kansa yana jinjina kai sannan yakai dubansa"

"gareta yace"" yau kinaji dani Malama, menene tukwicin wannan kyautar?"""

"Hafeeza ta Girgiza kanta tace""Babu komai"""

"Gaddafi yayi murmushi yace""a a wannan kayan ai dole abiya tukwicin su"""

"bai jira amsar taba yasaka cokalin da'aka hado masa dashi yafara cin naman, yacika baki da tsokar nama yace""Um um um um"" sannan ya jinjina Kansa yanaji kamar kunnansa zai cire."

"ya juyo ya kalleta yace""amma yayi dadi sosai,Kinaji dani Hafeeza tah"""

"Hafeeza tayi murmushi tana kallon sa, tanajin wata soyaiyar sa tana sake shiga ranta."

"Shikuwaa sosai yakecin naman, saida ya cinye tas, yasha ruwan pure water data kawo masa guda daya, sannan ya kalleta yace""gaskiya yayi dadi sosai,yanzu wannan naman nawa Kika kashe?"""

"Hafeeza tace""meyafaru? amma de ba biyana zakayi ba ko?"""

"Cikin Jin dadi yace""a a, dama kawai tambaya nayi"""

"daga nan ya kalli agogon wayarsa ya miqe yace""to zan wuce Malama, dan Allah ki gaida Inna, kice Mata ina Mata"

"Allah yasanya Alkhairin saukar gobe"""

"kokadan Hafeeza bataji komai aranta ba, asali ma bataji soyaiyar sa ta ragu aranta ba, abinda tasani shine tana sonsa"

"dan Allah, tana sonsa saboda ya'iya rera karatun Alqur'ani."

sallama suka qarasa Gaddafi ya dauki ledojin data kawo masa yatafi dashi.

"tana shiga gida Maman Fadila dake zaune suna fira da Ta Rasulu ta kalleta tace""A'a, masoya har kin dawo?"""

"Hafeeza ta cire Hijabin jikinta ta ajiye sannan ta zauna akan babbar tabarmar dasuke zaune tace""nadawo, yatafi gida"

"shima"""

"Maman Fadila ta sake kallon ta tace""ya haka? Hafeeza yanaganki hannu Rabbana? babu abinda yabaki?"""

tun kafin Hafeeza tace wani abu Inna Ta Rasulu ta kwashe da wata irin dariya harda tafa hannayenta biyu tafara rera

"waqa tace""munaji muna gani muna kuma saurare "" "

*** *** ***

"Washegari sauka,tun qarfe hudu na dare Hafeeza tatashi tayi nafila bata koma bacci ba tana zaune tanata tulawar"

"karatun Alqur'ani,har aka idar da sallar asuba sannan tafuto tafara gyara gidan nasu, bayan tagama gyaran gidan ta zauna a tsakar gida tayi tagumi hannu bibbiyu tana kallon malkaden waken dake gabanta, shawarar da Maman Fadila tabata akan rashin son yin suyar qosai shi take tuna wa, wannan qosan da batason zuwa ta siyar shine yarufa musu asiri itada Inna, dashi sukeci dashi suke sha, tun tasowar ta bata ta6a ganin wani daga unguwa yakawo musu tallafin ko fallen zani ba, haka tataso acikin gwagwarmayar rayuwa harta kawo yanzu."

"Ahankali tasaki ajiyar zuciya tasake jin wani qwarin gwiwar yashige ta akan sana'ar tasu, cikin hanzari tatashi ta"

"shirya tsaf, cikin dogon hijabin ta, tahada kayanta tafice wajan sana'ar su, abinda tasa aranta shine koda qosan be qare da wuri ba zatayi haquri harya qare sannan tazo ta shirya tatafi wajan saukar tasu, saboda inda ace ba suyi qosan ba kuma babu Kawu Hamza to babu yanda za'ai tasamu damar shiga cikin sauran dalibai da za'ayi saukar dasu"

*** *** ***

"Tunda sukai sallar asuba basu koma bacci ba, gaba d'ayansu su ukun suka shiga kitchen suna yin donut da cake"

"dakuma sauran kayan rabo da zasu rabawa jama'arsu bayan angama sauka, hakan yasa suka zama busy kowa da aikin da yake a kitchen din, suna aikinsu cikin sauri saboda kada lokaci ya qure musu."

"Cikin hanzari yafuto daga cikin dakinsa yana Sanye da baqaqen kaya riga da wando,kayan nasa sunada laushi sosai"

"kuma roba ne, hakan yasa wandon ya d'an kamashi wanda tsawon sa bai sauko har can qasa ba, da kad'an ya wuce gwiwar sa,rigar kuma tana hade da hula daga Qasan hular akwai zare guda biyu wanda mutum zai iya daure hular a kansa da wannan zaren,kayan sunyi mutuqar yimasa kyau kamar ka saceshi,saurin dayake yasa yafuto yana qoqarin daura agogo a tsintsiyar hannunsa me cikeda gargasa."

"Kallon gefen kitchen din nasu yayi, kafin yayi magana 'yanbiyu suka gaidashi, Kaka ta kalleshi taga kamar sauri yake,"

"cikin hanzari tace""ina zakaje haka da sassafe Hafeezu?"""

"Saida ya runtse idonsa cikin taqaici saboda yanda ta furta sunan nasa,bayason wannan Hafeezun datake fada, idon"

"nasa ya bude sannan ya amsa mata cikin daure fuska kamar kullum yace""yanzu zan dawo Kaka,akwai abinda zan gani ne me muhinmanci"""

"Kafin Kaka tabashi amsa yayi wuf yafice daga falon nasu cikin sauri, yana futowa compound bai saurari kowa ba"

"yashiga motar da kansa sannan yafice cikin sauri, tuqi yake yana jin wani irin nishadi acikin zuciyarsa wanda yarasa meyasa yakejin hakan,agefe guda kuma ya kunna waqa acikin motar tasa sautin waqar yana tashi kad'an-kad'an."

"Bai zame ko'inaba sai wajan da Hafeeza take suyar qosai, daga nesa da'ita yayi parking motarsa, sannan yakashe"

"motar yana kallonta tacikin tinted glass din motar, wata irin wawiyar ajiyar zuciya ya sauke da idonsa ya sauka akan kyakykywar fuskarta, duk da fuskar tasa babu walwala akanta, ahankali can qasan maqoshin sa ya furta "" had'addiya ce"""

"Yasake gyara zamansa acikin motar tareda harde hannunsa akan qirjinsa yana faman kallonta,ya dade yana nazari"

"akanta, haka kuma baibar wajanba har saida yaga tagama saida qosan tas, sannan ahankali yaja motarsa yabar wajan batare dayaje inda take ba."

"Inna tayi mamakin yanda Hafeeza tafita suya bayan tasan cewa yau ce ranar saukar su,abun yabata mamaki sosai"

"kuma taji dadi aranta, tasan cewa haqiqa ita aka haifawa Hafeeza tunda gashi yarinyar kullum cikin fafutukar nema musu na abinci take, cikin sauri tatashi ta kar6i kayan hannunta tafara wanke wa ita kuma Hafeeza da gudu tashiga wanka saboda kada lokaci ya qure, garin gudu gefen zanin nata ya kunce kafin ta farga ta gyara har tsayaiyan nashanunta guda d'aya yafuto waje, cikin sauri ta zaro idonta waje tana kai dubanta wajan Inna, aikuwa komai daya faru akan idon Inna ne, cikin sauri Hafeeza ta runtse idonta, Inna ta dauraye babbar robar dasuke had'a wake aciki sannan ta girgiza kanta tace""ainace dama mijinki saura zaigani inde bazaki hankali ba Hafeeza,menene abun gudu a shiga wanka in banda sakarci? inda baqi mukai ma haka zaki kama gudu kwankwaso yana miki rawa kedama abu ba kad'an ba, kici gaba Allah yabaki sa'ah"""

"Hafeeza de tana jinta tayi shiru batace komai ba tashige cikin bandakin nasu, agurguje tayi wankan ta tafuto tashirya"

"cikin material d'in da Maman Fadila ta dinka mata,duk da Rigar tanada fad'i ba qaramin kyau tayi mata ba,riga ce me fad'i doguwa dakuma zare agaban rigar wanda zata kama ta daure acikinta, kamar yanda taga zaren agefen rigar itama ta kama ta daure shafaffen cikinta dashi, yanda ta daure rigar hakan yasa Hips dinta yasake futowa duk da Rigar tanada fad'i, dogon gashinta dayake daure tayi sauri ta kunce tashafa masa Vaseline sannan tasa mataji ta tajeshi daqyar, lokaci daya ya dauki wani irin sheqi kasancewar a wanke yake fes."

"Dogon hijabin saukar su gogegge ta dauka ta saka,lokaci daya zahirin kyawun ta yafuto acikin hijabin,tayi mutuqar"

kyau duk da ba kwalliya tayiba kawai gashin girarta ta taje saikuma

5 / 14