Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MATAR ABBANA Matar Da Ta Sauya Komai by Amnah El Yaqoub

Author :  Amnah El Yaqoub Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 14

15K to 18K   out of 40.1K words

dan lipstick data saka shima d'an kad'an.

"Maman Fadila ce ta shigo gidan itama tana jiranta, daga nan suka dunguma suka tafi."

"Duk yanda take komai cikin sauri saida ta makara,tana zuwa makarantar shugaban makaranta yafara yimata fada kasancewar ita kadai ce bata zo dawuri ba, bayan dogon bayani da yayi musu kai tsaye suka qarasa wajan da aka tanada domin yin taron,gaba dayan su daliban rumfa daya aka ware musu da kujerun da kowacce zata zauna, banda sauran mutane suma dasuke cikin tasu Rumfar, wajan yacika sosai kamar me, manya-manyan baqi sun samu halartar taron saukar kasancewar islamiyar tasu babbar makaranta ce."

Malaman makarantar aka bawa dama daya daga cikinsu yayi bayanin muhinmancin ilmi dakuma muhinmancin

"karatun Alqur'ani, yayi da larabci sannan ya fassara da hausa."

daga nan aka kira Sunanta amatsayin daliba ta farko dazata fara karatu.

"Tunda suka zauna awajan kanta yake qasa tana karanta (Bismillahirrahmanir-Rahim) acikin zuciyar ta,saboda"

"gabanta banda fad'uwa babu abinda yake,bata ta6a shiga cikin babban taro kamar wannan ba,taso ace had'a baki zasuyi gaba dayansu daliban malami guda daya ya karanta suma su karanta kamar yanda wasu makarantun sukeyi, to saide tasu makarantar tazo musu ta daban, hakan yasa take karanta Basmala kasancewar duk wanda yakejin fad'uwar gaba kokuma yakejin tsoron tunkarar wani abu kamar jarabawa ko wani abu daban, to muddin yakama Basmala yana maimaitawa acikin zuciyar sa insha Allahu zaiyi komai nasa cikin nutsuwa kuma zaiji fad'uwar gaban ta ragu."

"kasancewar tariga tasan itace zata fara karatun hakan yasa gabanta yaketa faduwa, kokadan bata fahimtar jawabin"

"da'ake awajan, saide ta tsinkayi me jawabi yana kiran HAFEEZA KHALID USMAN amatsayin dalibar farko dazata fara karatun Alqur'ani."

"Wata daliba dake gefenta tace""Hafeeza kitashi"""

"Ahankali ta miqe da Bismillah abakinta, tafara tafiya cikin nutsuwa kanta aqasa harta qarasa inda aka tanada domin"

tsayawar dalibai masu sauka.

"Tunda tataso idonsa yake kanta,yana zaune akan akujerun da'aka tanada domin baqi na musanman, gabansa ne yayi"

"wata irin faduwa ganinta awajan,cikin tsananin mamaki yasake kallon ta yana gyara zamansa aransa yace dama itace?, ahankali ya maimaita sunan nata acan qasan maqoshin sa HAFEEZA...."

"Cikin nutsuwa tafara rera karatun Alqur'ani cikin zazzaqar muryar ta, lokaci daya wajan yayi tsit kowa yana sauraron"

"karatun nata, Alhaji ISAH YUNUSA babban dan majalissar yankin daya halarci wajan saukar, tun taso war yarinyar yaji ta birgeshi, da alama tanada nutsuwa sosai, lokaci daya ransa ya kwadaitu da aurenta."

"Hafeeza kuwa cikin fitar da makaarij take rera karatun ta kamar karta daina,zaqin muryar tata yasa Hafeez dake"

"zaune agefen Kaka acikin Rumfar da aka sauki manyan baqi ya lumshe idonsa yana sauraron karatun nata, a tarihin rayuwar sa zai iya cewa bai ta6a jin karatun wata mace dayayi masa dadi kamar nata ba."

"Hajiya Kaka dake zaune agefe tajuya ta kalli Hafeez taga idonsa a lumshe, ta dauke kanta tana girgiza kai, tayi"

"tunanin yanda yarinyar take karatu hakan zai dauki hankalin sa ta yanda zai zuba mata ido yana kallonta ko Allah zaisa adace, saide abun mamakin saita ga kamar ma yarinyar bata birgeshi ba."

"Har Hafeeza tagama karatu taje ta zauna mutane basu daina kallonta ba, Ta Rasulu da Kawu Hamza da matar kawu"

"Hamza da yaransa da kuma maman Fadila duk suna waje daya basu samu wajan zama ba, daga tsaye suke hango komai ( )"

Gaddafi kuwa sai washe baki yake yanajin wani irin dadi aransa yana Alfahri kasancewar sa saurayi awajan Hafeeza.

"Kasancewar daliban basu da yawa mutum biyu ne sukai karatun, daga Hafeeza sai wani namiji guda daya daga cikin"

dalibai maza guda biyar da'akai saukar dasu.

"daga nan aka bawa shugaban makaranta dama yafuto yayi Nasa jawabin, yabada tarihin makarantar kanta."

"Sannan aka bawa wani Babban malami shima yayi fadakarwa sosai akan amfanin ilmi, sannan matemakin shugaban makaranta yafara kiran dalibai daya bayan daya ko wacce ana bata allon sauka dakuma certificate."

"Bayan angama basu ko wacce takoma ta zauna, Babban limamin unguwar yazo gabansu ya zauna yafara karantawa"

"suma suna biyawa, masu camera kuwa sai zagayasu suke suna daukar su."

"daga qarshe kuma baqin da aka gayyata suka fara bawa Dalibai gudunmawa ta kyauta,cikin daliban da suka samu babbar kyauta harda Hafeeza, wadda Alhaji Isah Yunusa dan majalissa yabata kyautar zunzurutun kudi har naira million biyu tareda kujerar Umarah."

Inna tanajin kud'in tayi Suman tsaye har saida Maman Fadila datake yiwa Hafeeza video ta taro ta saboda qiris

yarage tafad'i qasa.( )

"daga nan manyan baqi suka fara sanarwa kowa da irin kyautar dayake yiwa makaranta, wannan yace yabada sadakar"

"dubu Hamsin, wasu dubu goma, wasu dubu dari biyu, wasu dubu biyar, harda Mata masu bada dubu daya, wannan duka kyautar makaranta ce."

"ma'ajin makaranta ne yatashi yafara rabawa manyan baki wasu fararen takardu masu dauke da number account din makaranta ajiki, idan da wanda zasuyi transfer saisu tura, cikin wanda aka bawa paper harda Hajiya Kaka data hakimce akujera."

"Anbawa shugaban makaranta damar jawabi dakuma godia ga baqin dasuka samu zuwa, wani kudin yasake shigowa"

"cikin asusun makarantar, ma'aji ya matso kusa da me gabatarwa yayi masa bayani, me gabatarwa yace""to Alhamdulillah masha Allah, muna kan rufe babin godia ga manyan mutanan dasuka yimana kyautar girmamawa dakuma kyautar kudi, sai kuma gashi wani bawan Allah wanda ya nemi a 6oye sunansa yaturo wa wannan makaranta tamu kudi har naira million goma Sha biyar, million goma na makaranta, sannan dalibar data fara karatun Alqur'ani wato Hafeeza Khalid yace abata million biyar sadaka fisabilillah"""

Lokaci daya waje ya kaure da ihun murna kowa sai kabbara yakeyi.

"Hafeez yayi sauri yamaida wayarsa cikin aljihun wandon sa ganin kaka ta zubawa wayar tasa ido tana kallo kamar tana so ta gano cewa shine yayi wannan kyautar, shikuma ba komai ne yasa yayiwa yarinyar kyautar ba saboda yaga kamar tanada karancin hijabai, kud'in zai Isa tasake dinka wasu hijaban.( )"

Ta Rasulu tanajin wannan kyauta tafashe da kuka wiwi.( )

Yayinda Hafeeza ta sunkuyar da kanta qasa tana goge hawayen idonta.

Bayan angama karbar kyautar kudade daga nan aka fara saida calendar mai dauke da photon dalibai ajiki.

"Hafeez ya kalli Hajiya Kaka yace""kin riqe takardar account, ki basu takardar su tunda bazaki iya tura musu ba"""

"Hajiya Kaka ta harareshi tace""saikace kai?"""

"daga nan ta daga murya ta Kira me gabatarwa, Yana zuwa wajanta tace""bawan Allah ka daga murya kafada a"

"speaker cewa Hajiya Rabi'atu kakar Hassana da Hussaina wadda akafi sani da Hajiya Kaka, ta sai calendar naira dubu Dari"""

"Aikuwa ya karbi kudi Yakoma tsakiyar taro yafada kamar yanda Hajiya Kaka takeso, su Hassana suna zance qasa qasa"

saiji sukai sunansu yafado cikin kwatancen Kaka.

"me gabatarwa yadawo yakawo wa Hajiya Kaka Calendar ta, Hajiya Kaka ta kar6a sannan tayi wa Hafeez wani kallo"

"me alamun nafi qarfin raini ta kauda kai, shi kuwa dariya ma ta bashi, amma kasancewar miskilin mutum ne saiya yi dan murmushi kadan ya basar."

"daga nan akayi Addu'ar tashi daga taro, aka sallami dalibai kowa ya nufi wajan 'yan'uwansa."

"Hafeeza tafuto zata nemi su Inna, 'yanbiyu suka tareta Husna tace""Hafeeza tsaya ki mana photo"""

"Tafadi haka tana miqa mata wayar hannunta iPhone me camera uku, Hafeeza ta kar6i wayar tana murmushi har"

dimples dinta suna lotsawa.

"Hassana ta rungume Husna sannan itama tace""kuma ki tabbatar munyi kyau sosai ehe, idan bamuyi kyau ba saikin sake mana sabo"""

Hafeeza ta girgiza kanta tana murmushi sannan tafara qoqarin yimusu photon da qyar kasancewar bata ta6a riqe

"babbar waya irin wannan ba, tarasa yanda zatayi ta dauki photon, batasan yanda ake photon ba."

"Su Husna suka sauya style, Hassana tace""kin dauka?"""

"Hafeeza tace""A a ban dauka ba"""

"Husna tace""har yanzu de baki dauka ba?""( )"

"Lokaci d'aya Hafeeza duk ta rikice, tarasa yanda zatayi, yanda ta rikice din saita sake yiwa Hafeez kyau wanda yake"

"tsaye ajikin motarsu yana kallonta,mayan kayan dake jikinsa sun sake qawata kyansa,sosai ya shagala wajan kallonta saide miskilancin sa ba zaisa ka gane cewa kallon arziqi yake mata ba."

"Cikin zazzaqar muryar ta tace""narasa yanda zanyi ne, ku sake matsawa kusa"""

Cikin sauri 'yanbiyu suka matsa suka sake rungume juna.

"Hafeeza ta qoqarta ta dauke su, sannan cikin zazzaqar muryar ta, tasake cewa ""kuyi murmushi to,kekuma Husna"

"gyara tsayuwarki"""

"Duk abinda take fada musu haka sukayi, sannan ta dauka tabasu wayar domin su gani, kokadan bata lura da Hafeez dake tsaye agefe ba,shima Koda wasa baiyi gigin yimata magana ba,gaba daya ya shagala a kallonta, wani side na zuciyarsa yanajin tausayin yarinyar,dazu da safe yaganta tana suyar qosai, sannan yanzu gata awajan sauka, hakan yana nufin saida tagama yin sana'ar tasu sannan tataho wajan saukar."

"Idonsa ya lumshe kad'an yana tuno shekarun baya yanda rayuwa ta kasance masa,yatuna yanda yake daukar qosai a kansa yana yawo dashi waje-waje."

"Cikin sauri yadawo daga tunanin daya tafi kasancewar yaji zuciyar sa tafara tafarfasa akan rayuwar daya tuno, fuskarsa babu yabo babu fallasa yakai dubansa zuwa ga 'yanbiyu anan yaga suna yin selfie tareda Hafeeza, murmushin daya gani kwance akan fuskarta shine yasa haka nan ya tsinci kansa cikin farinciki."

"Maman Fadila ce tazo ta janye ta suka nufi wajansu Inna, har zuwa wannan lokacin Ta Rasulu kuka take, kawu"

"Hamza dake tsaye a gefenta shida matarsa Maryama sai baki suke bata akan tayi haquri tadena kuka, daqyar aka samu tayi shiru sannan suka had'u waje daya gaba dayansu, Hafeeza tashiga Tsakiyar su, Maman Fadila kuma tafara yimusu photuna."

*** *** ***

"Da daddare suna zaune afalo gaba d'ayansu, kayan shan'iska ne ajikin 'yanbiyu, Kaka kuwa Hijabi ne ajikinta tana jan"

carbi.

'yanbiyu ne suke zancen taron saukar su ta dazu.

Hafeez yana zaune agefe wando ne ajikinsa three quarter da wata riga wadda batada maraba da singlet saboda

"yanda dantsan hannunsa yake abude, hatta nipples dinsa kana ganin tsininsu ta cikin rigar saboda yanda rigar take ba kauri."

"Jarida ce a hannunsa yana dubawa amma gaba daya idonsa ne akan takardar, tunanin sa dakuma jinsa yana wajan 'yanbiyu saboda yanaso yasake jin sunyi zancen Hafeeza ko zaiji wani abu daga cikin halayen yarinyar."

"Kaka ta ajiye carbin hannunta ta shafa Addu'ah sannan tacire Hijabin jikinta ta kalli 'yanbiyu tace""Allah de kuma"

"yakawo muku mazaje nagari, wannan yarinya data fara karatu dazu da zafe awajan sauka, haqiqa wannan kyautar data samu nasan ba saboda karatun ne kadai ba, harda masu sonta""( )"

"Hassana tace""ai Hafeeza tasamu kudi gaskiya,Kaka itace fa wannan wadda muke fada miki ta'iya karatun Alqur'ani,"

"kuma suma malaman namu sai nan-nan suke da'ita daga gani sonta suke"""

"Gaban Hafeez yayi wata irin muguwar faduwa, yasaki dan qaramin tsaki sannan yasake bude wani shafin jaridar."

"Kaka tace""Allah sarki ashe itace, amma daga gani tanada nutsuwa yarinyar,kuma kana kallonta zaka tabbatar ba"

"asalin yar qasar nan bace gaskiya,kode ruwa biyu ce kokuma daga wata qasar sukazo, ni naso inji wanda yabata million biyar dinnan,ai kyautar farko ance d'an majalissa ne yabata"""

Hafeez ya d'an kalli Kaka sannan ya dauke kansa.

"Kafin 'yanbiyu su sake magana wayar Hafeez dake gefe tafara ringing, cikin nutsuwa da aji irin nasa yadauki wayar"

"tareda fadin ""I.B kaga saqon dana turo mane?"""

"Daga d'aya 6angaren I.B yace""nagani, naje nakai masa, na sameshi cikin aminci, yana lafiya babu wata matsala"""

"Ahankali ya lumshe idonsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya, batare dayace komai ba yakashe wayar."

"Kafin wani daga cikinsu yayi magana wata Babbar mata tashigo falon, zata iya kaiwa kimanin shekara Arba'in dawani"

"abu, Hafeez yanajin muryar ta yagane ta,ko a mafarki bazai ta6a mantawa da muryar taba, lokaci daya fuskarsa ta sauya ya runtse idonsa, kokadan bayason ganinta."

"Matar taqaraso cikin falon, tana qoqarin zama akan kujera shikuma Hafeez yana qoqarin tashi,yanajin yanda 'yanbiyu suke qoqarin gaida matar, wadda ta kasance qanwar mahaifiyar su ce uwa d'aya uba d'aya,amma Hafeez ko kad'an baima nuna yasan taba, maganar fatar baki bata hadashi da itaba yabar jaridar dayake karantawa awajan yashige cikin dakinsa."

Kaka tabi bayan sa da kallo harya rufe qofar dakinsa.

"Cikin sanyin jiki tadawo da dubanta zuwa wajan 'yartata cikin tsananin damuwa dakuma sanyin jiki take duban ta, ta rasa yanda zatai ta gyara baya, tarasa yanda zatai ta dedeta kan ahalinta yazama daya,kuskure an riga anyi, saide ayi haquri a fuskanci gaba,inda ace zata iya maida hannun Agogo baya, to haqiqa da zata dawo da nasu agogon qaddarar baya domin ta gyara matsalolin cikin ahalinta."

(meyake faruwa da ahalin Hafeezu ne? )

(Jama'ah wa zai turamin 5 million Nima in sake hijabai )

Complete document 1k

8621296018

Amina Muhammad fcmb

"Kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034"

Amnah El Yaqoub
'<Øûß

"[5/26, 1:59 PM] El Yaqoub: MATAR ABBANA "

(Luv Story)

Writing By Amnah El Yaqoub

Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update

https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45

7

"Matar data shigo falon tayi murmushin yaqe ta kalli Kaka tace""Ummah ashe Hafeez yazo qasar"""

"Kaka tace""Hafeezu yazo SADIYA, su Hassana ne sukai masa magana nayi tunanin ma bazai samu zuwa ba, kuma sai"

"gashi yazo"""

"Cikin Sanyin jiki Wadda aka kira da Sadiya tace"" Allah sarki, nima tun safen naso zuwa kuma saboda yanayin abun"

"hawa yayi qaranci yanzu, ba'a samun fasinjoji masu yawa atasha, shiyasa na makara, Allah ya sanya Alkhairi"""

"Kaka tace""Amin Sadiya, amma ai zaki zauna damu muyi kwana biyu ko?"""

"Cikin sauri Sadiya tace"" a a Ummah,gobe zan tafi insha Allah"""

"Jikin kaka yasake yin sanyi kalau,tasan cewa ganin Hafeez yana gida ne shiyasa tace bazata zauna ba."

Kafin tasake wata maganar 'yanbiyu suka kawowa Aunty Sadiya abinci da abun Sha.

"Aunty Sadiya ta kallesu tana murmushi tace ""Husna da Hassana yanzu kuma an sauke,saura rubutawa kuma"""

"Kaka tayi murmushi tace""sa rubuta adakin mazajensu, aurensu zanyi, danma Husna babu mashinshini aida tuni anyi"

"auren"""

Kaka ta qarasa maganar cikin tsokana.

"Husna ta harari Kaka sannan tace""ko lokacin dakike yanmatanci Kaka baki kaini samari ba,samari suna nan dayawa"

"sai wanda nazaba"""

"Aunty Sadiya tayi dariya tace""Allah Husna, wato kema yanzu kinbi sahun Hassanarki bakinki yafara budewa. """

Gaba dayansu sukasa dariya kamar basuda wata matsala agabansu.

*** *** ***

"Suma su Hafeeza suna zaune a tsakar gidansu akan wata babbar tabarma, kasancewar kawu Hamza yasan cewa"

gidan nasu zai tara jama'ah hakan yasa bai samu zuwa ba sai wajan qarfe goma na dare mutane sun tafi gida sai Inna da Hafeeza kawai.

"Kawu Hamza ya kalli Inna yace""Yanzu Ta Rasulu Yaya kike ganin za'ayi da wannan kudin da Hafeeza tasamu idan"

"ankawo mana?"""

"Inna tace"" Haba Hamza,ai Kaine uba, Kaine zakasan abinda za'a yi dashi, nide fatana asamu adan gyara mana gidan"

"nan, saboda da damuna munayin yoyo sosai, wani lokacin Hafeeza a zaune take kwana"""

"Kawu Hamza yayi murmushi yace""to dama munyi magana da shugaban makarantar tasu, yacemin nasamo account"

"number da za'a tura mana kudin, ni ina ganin idan kudin sun shigo, kuyi tunanin wata sana'ar daban kufara, saiku ajiye wannan sana'ar qosan agefe, saikuma kayan dakinta da nakeso asiya a ajiye, kokuma abawa masu saida kayan kudin, idan aurenta yatashi kinga zuwa zamuyi mu dauka, duk da made bansani ba ko 'yartawa tanada saurayi"""

Ya qarasa maganar tasa cikin salon shan ciki yana kallon wajanda Hafeeza take zaune.

"Hafeeza tarufe fuskarta cikin kunya sannan tace""akwai Kawu"""

"Ta Rasulu ta ta6e baki tace""wannan saurayin naki Hafeeza dashi ai gara babu, saurayi kullum sai shegiyar fira"

"yakasa tsinana miki komai, kuma shi yaqi yaturo iyayensa ayi magana, kullum de gashinan sai aukin zuwa zance, shekaran jiya yazo ta kashe kudi ta tar6eshi, ya cinye komai bai bata ko kwabo ba, yanzu yauma dazun nan yazo be tsinana Mata komai ba sai alewa daya kawo Mata itama ba tafi ta dari biyu ba, nakusa nahana ki fita zancen ma,idan zai turo iyayensa yaturo ayi maganar aure,tun shekarar dakikai candy aketa soyaiyar nan,shi idan sallah tazo ko lallen sallah uwarsa ba kawo miki take ba, Shima bazakici sisin kwabonsa ba, to gara ayi daya, kode ki sallameshi kokuma yafuto yadaukeki ku tafi can gidansa saiku qarata da mammaqonsa tunda ahaka kikeson abinki"""

"Kawu Hamza yayi murmushi yatashi tsaye yana yimusu sallama, dama abinda yakeson ji Kenan, kuma yasamu amsar"

tambayar sa.

"Kawu Hamza yana fita maman Fadila tashigo gidan, Inna ta kalleta tace""Sa'adatu ina ki kabar mijin naki da wannan"

"daren kika futo?"""

"Maman Fadila tayi murmushi tana zama akan tabarma tace""Inna wallahi harna kwanta Baban Fadila yashigo, kaji ne"

"yashigo mana dasu shine na dauko muku kuma kuta6a"""

"Inna takai hannu ta dauki cinyar kaza takai bakinta sannan tace""haba Maman Fadila aida kinbari sai ahadu zuwa"

"safiya"""

"Maman Fadila da Hafeeza sukai dariya,ganin yanda Inna tafara cin naman kaza amma tana cewa da an barshi zuwa"

safe.

"Maman Fadila ta kalli Hafeeza tace""Hafeeza gobe akwai abinda zakiyi ne? inba abinda zakiyi kikai min Fadila asbiti"

"mana,za'a mata allura"""

"Inna tace"" ina zataje kuwa? ba inda zataje, saita shirya takai miki ita"""

"Maman Fadila tace"" Nima wanki zanyi da safen,kinga idan takai min ita kafin su dawo nagama wankin na rage wani"

"aikin"""

"Hafeeza tace""to Allah yakaimu"""

*** *** ***

"Washegari takama litinin, tunda aka idar da sallar asuba Hafeez bekoma bacci ba,sosai yayi nisa cikin tunanin ta,so"

"yake yaje wajanda take saida qosai ko Allah zaisa yasake ganinta, yarasa meyasa yakejin idan beyi magana da'ita ba

6 / 14