Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MATAR ABBANA Matar Da Ta Sauya Komai by Amnah El Yaqoub

Author :  Amnah El Yaqoub Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 14

9K to 12K   out of 40.1K words

zaman baqi,cikin sauri tafara gyara daurin dankwalinta daya fadi gefe tana kallonsa cikin tashin hankali."

"Hafeez kuwa kasa dagowa yayi,yana sunkuye yayinda hannayen sa suke kan table din dake gabansa,muddin yace zai miqe to gaban wandon sa zai iya tona masa asirin halin dayake ciki."

"Ahankali tataso tadawo gabansa tace""meyake damunka?"""

"Cikin tsananin damuwa yace""leave me alone please!,ki fice daga office dina, ki fice daga cikin rayuwata!!!"""

"Cikin sauri ta kalleshi, tunda take dashi bata taba ganinsa cikin wannan yanayin na 6acin rai ba,haqiqa ransa a6ace"

yake ta yanda jijiyoyin kansa duk sun futo har zuwa kan goshin sa.

"Wani irin hawaye yazubo daga idonta tace""Hafeez ni kake kora acikin rayuwarka? saboda kaga na damu dakai inason kasancewa dakai? wacce mace ce zata iya sadaukar ma da jikinta saboda soyaiyar datake ma? Amma ni nakawo kaina gareka shine kakemin abinda ranka yakeso,babu damuwa, dama zuwa nayi inyi ma sallama, nasamu canjin wajan aiki zuwa Germany,nayi tunanin zamuyi sallama cikin annushuwa da kewar juna,ashe bahaka bane,zanjiraka har zuwa lokacin da zaka amince da buqata ta. """

"Tana fadin haka tajuya tafice daga office din, ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yakai hannunsa zuwa kan mararsa"

"yaji abun yariqe babu alamun sauka,cikin tsananin damuwa ya runtse idonsa yana tunanin mafita, yariga yasan cewa tun kafin yakai shekarun balaga yake buqatar mace,amma bayajin akwai yarinyar da zatayi nasarar sace zuciyar sa saboda mata yawancin su halinsu daya ne,wani lokacin basu da Imani ko kad'an,yanajin dadin yanda suke tafiyar da rayuwar su cikin kwanciyar hankali iya su hudu, shi da Kaka dakuma qannan sa yanbiyu, bayason sanadin mace wannan walwalar data dawo cikin gidansu ta rushe irin wasu shekaru abaya wanda baya qaunar tunawa dasu."

"Cikin sauri yabude wata locker yadauki wani magani yasha, sannan yasamu ya zauna yariqe kansa da hannunsa"

"bibbiyu, ba'a ta6a masa wannan wajan bama kullum yana cikin sha'awa to inaga anzo an ta6o masa shi, ahankali yagama yanke wa kansa shawara gara ya tattara yabar qasar,taron saukar 'yanbiyu da yayi niyar qin zuwa gara yaje ko zai samu ya Kaucewa matan dasuke kawo masa Hari, idan baiyi da gaske ba dole watarana zasu maidashi dis virgin, wanda shi kuma bayason hakan,dalilin dayasa kenan duk sati yana cikin yin azumin litinin da alhamis."

*** *** ***

"Ta Rasulu tasake karyar dubulan din dake hannunta sannan ta kalli Hafeeza tace""Abun naku yayi dadi kuwa,ga"

"zaqi kamar sikarin"""

"Hafeeza tace""Maman Fadila ce tayi,kowa cewa yake yayi dad'i, nima tanayi ina ganin yanda takeyi yanzu harna koya"""

"Inna tace""dama mezai hana ki koya,aigara dakika zuba mata ido kikaga yanda takeyi, kinga idan Allah yasa kikai aure"

"saiki dingayin na siyarwa akai miki shago, idan Allah yakawo kasuwa sai kiga kin samu sana'ah, wai saurayin naki kuna waya kuwa kwana biyun nan?""( )"

"Hafeeza ta girgiza kanta sannan tace""a a bamuyi waya ba"""

"Cikin mamaki Inna tace""A a, to besan zakiyi sauka bane ko Yaya?"""

"Hafeeza tasaki murmushi wanda yakawo lotsawar dimples dinta, tace"" Yasani Inna, Nafada masa, kuma yacemin"

"insha Allah zaije wajan sassafe,zaiyi min vedio a wayarsa idan ina karatun qur'ani"""

"Inna tasaki baki galala tana kallon Hafeeza sannan tace""narasa wacce irin yarinya ce ke Hafeeza, waishi haka ake"

"soyaiya ne kwandalar sa bazatai ciwo a wajanki ba? kekuma sakarya wato za'a miki vedio har wani washe baki kike,Allah yaji qan ubanki Haladu kullum idan zaizo wajena zance da baqar Leda yake zuwa, yasan zakiyi saukar amma be baki ko taro ba?"""

"Hafeeza tace""Inna cemin yayi nayi haquri rannan yasamu dubu d'ari amma ya kyautar dasu atake"""

"Inna ta kalli Hafeeza tace""Yakyautar da dubu d'ari? Kud'i har dubu d'ari kuma duka ya kyautar dasu 'yarnan?""( )"

"Hafeeza tayi shiru takasa magana, Inna taci gaba da fadin"" ke Hafeeza wannan saurayin naki maqaryaci ne""( )"

"Hafeeza tace""Inna ba qarya yake ba, nasan Gaddafi bazai min qarya ba"""

"Inna tace""Hafeeza zaki rufemin baki kokuwa saina doke miki bakin? tayaya ne zai dauki dubu d'ari kacokam yayi"

"kyautar ta? awannan yanayin? Kuma kika yarda? dayayi kyautar meyasa ke ya manta dake bai baki ba amma yasan yazo yabaki labari?"""

"Hafeeza tace"" Inna in zaka so mutum kasoshi dan Allah,kiyarda nasan bazai min qarya ba"""

"Inna tace""yo tayaya zan yarda Hafeeza? bama wani sashe na kudin ba ace dubu d'ari ka kyautar da'ita atake su waye"

"iyayenka? Shiyasa kusan kullum yake miki qaryar yana Abuja, saide in da dubu darin daya samu yake zaryar kudin mota zuwa Abujan, shiyasa yanzu ya tsugunna tunda kud'in yaqare""( )"

"Hafeeza de tayi shiru batace komai ba,duk wannan fadan da Inna takeyi ko kad'an ba taga laifin Gaddafi ba, asali ma"

"abun hannunsa baya birgeta, yanda ya'iya karatun Alqur'ani yafi komai daukar hankalin ta, shiyasa take mutuwar son sa ta gagara sauraron kowa."

"Inna tace""ga kudi can ki dauka kije kisiyo wake ki gyara"""

"Hafeeza taturo d'an qanqanin siririn bakinta gaba tace""Inna wake kuma?"""

"Inna tace"" gashi kuwa kinbawa kanki amsa?"""

"""Inna jibi fa Saukarmu kuma yanzu goben ma sai munyi qosai?"""

"""idan bamuyi sana'ah ba dame zamu rufawa kanmu asiri? kitashi kije kisiyo nace"""

"Cikin fishi ta dauki kud'in tafice daga gidan, bata zame ko'ina ba sai gidan Maqociyar su Maman Fadila."

"Maman Fadila tana ganinta tace""Alhamdulillah dama gidanku zanje yanzu,Baban Fadila ne ya siyo miki takalmi, Nima ga material na dinka miki,kinga material din yayi Kala da hijabin da'aka raba muku a islamiya wanda zaku saka awajan sauka,kinga saiki saka material d'in naki"""

"Lokaci d'aya farinciki ya mamayeta, ta daka tsalle ta rungume Maman Fadila tana zuba mata godia, Maman Fadila"

"tayi murmushi tace""ni ki daina yimin godia Hafeeza kamar qanwata haka nake jinki,yanzu de meyafaru kika shigo da 6acin rai?"""

"Hafeeza ta Yatsina fuskarta tace"" Wai Inna ce tace naje nasiyo wake gobe zamuyi qosai, shine nazo in fada miki ko"

"zaki mata magana,jibi fa saukar mu, kuma dan Allah kamar mu mukafi kowa neman kudi kwana biyun ma ba zamuyi haquri ba?"""

"Maman Fadila tayi murmushi tace""Haba Hafeeza,yanzu idan badan kuna wannan sana'ar ba tayaya zaki kai kud'in"

"saukar ki makaranta? Nan jiya Baban Fadila ya zauna yana yabonki yana cewa bakida girman kai kina kokarin nema muku abinda zaku rufawa kanku asiri to yanzu kuma karki bani kunya mana,Inna kamar mahaifiyar ki ce,duk abinda tafada miki me dadi da marar dadi kiyi haquri wataran sai labari,idan Gaddafi ya shirya ma rana daya zamu dauke ki mu kaiki can gidansa saide kizowa Inna ziyara"""

"Hafeeza tanajin wannan maganar kunya ta kamata,ta kalli Maman Fadila tace"" Maman Fadila nawane Sauran kudin"

"dakika ragemin wanda zan sai kayan kwalliya dashi?"""

"Maman Fadila tace"" Dubu uku da dari takwas ne, kona dauko miki Zaki biya ta shagon ki siyo?"""

"Hafeeza ta Girgiza kanta tace""a a, kawai ni abar kayan kwalliyar, kibawa yaro ya siyo nama kiyi wa Gaddafi Farfesu anjima zaizo da daddare, kinga saina hada da kayan rabon nabashi nasa tun yau ko?"""

"Maman Fadila tace""haba Hafeeza,kayan kwalliyar ma idan kin siya ai shi zakiyi wa kwalliyar,ki bar kudinki kisai kayan"

"kwalliya irin na yanmata, Shikuma idan yazo saiki zo ki dauki qullin kayan rabon ki bashi"""

"Lokaci daya Hafeeza ta sauya,cikin damuwa tace""Maman Fadila idan na kashewa Gaddafi kudi ban fadi ba, Dan Allah"

"ki barni ayi masa Farfesun tunda ni kwalliya ba damuna tayi ba"""

"Maman Fadila ta saki Ajiyar zuciya tace""eto hakane, shima kuma tunda saukar taku tazo ai nasan zai bada"

"contribution dinsa kinga sai mu sai lemon talakawa dashi"""

"Cikin murna Hafeeza tace""niko be bani komai bama babu komai"""

"Maman Fadila tace""um su Hafeeza masoya, irin wannan soyaiya haka"""

"kunya ta kama Hafeeza, cikin sauri tafice daga gidan tatafi wajan siyo wake tana dariya."

*** *** ***

"Da yamma suna zaune afalo duka su ukun,Kaka ta zubawa tv ido tana kallo, Husna ta ajiye wayar hannunta wadda"

"tagama karanta azkar din yamma, ta kalli Hassana tace""Sister kitashi muje mu gyara wa Yaya dakinsa,kinga baya raina datti ko Ya yake,karyazo gobe yace bamu gyara masa dakin sa da kyau ba, kekuma kin zauna sai faman karatu kike, jibi de zamuyi saukar nan kowa ya huta"""

"Kaka ta kallesu tace""gyaran dakin me? har wani gyaran daki zaku masa? meya hana yayi aure matarsa ta masa?"

"babu wanda zai gyara masa daki""( )"

"Husna ta kalleta tace""Kaka an dade ba'a gyara masa dakin bafa"""

"Kaka tace""wanne irin dadewa? Naga ga dakin nasa nan ko giftawa kazo yi ta wajan qamshi ne yake tashi"""

"Hassana ta ajiye Alqur'anin hannunta tace""muje driver yakaimu supermarket muyi cefane nasan yanason farfesun"

"kaza sai muyi masa mai dad'i dan yasan cewa muma yanzu mun qware a girki"""

"Kaka ta kalli Hassana tace""wacce irin kaza kuma ana zaune lafiya? ku kuwa kuhuta mana, kullum kuna cikin girki ku"

"rabu dashi goben kafin jirgin su ya sauka sai muyi order ko Fizza ce"""

"Hassana da Husna suka kalli Kaka,zasu gyara masa daki tahana su tace idan yanaso yayi aure matarsa ta gyara masa,"

"yanzu suna qoqarin siyo abun cefane suyi masa girki shima ta hana, basusan me Kaka tataka ba."

"Husna tasaki murmushi takoma cikin kujera tayi kwanciyar ta,cikin zuciyarta kuwa Allah-Allah take gobe tayi domin taga yanda Kaka zata qare tsakanin ta da Yaya Hafeez."

*** *** ***

"Kamar yanda tasaba sassafe tafita wajan suyar qosanta, kamar kullum yauma Hijabi ne ajikinta dogo har"

"qasa,hijabin yayi wa farar fatar ta kyau sosai mai launin ruwan toka me duhu,kyakykywar doguwar fuskar ta tayi kyau sosai acikin hijabin,mutane ne zagaye da'ita tana zuba musu qosai akan takarda sannan tasaka acikin Leda tabasu, yayinda wasu samari agefe suke tsaye suna jiranta wasu a mashin wasu kuma zaune suke daga gefe suna jira tasaka musu suci abunsu anan."

"Wani dayake zaune akan machine yana jira asaka masa yazuba mata ido yana kallon kyakykywar fuskarta, dad'i"

"yakeji idan yana ganin yanda take komai cikin nutsuwa da kamewa, bayaso yabar wajan yadena kallonta hakan yasa dazaran layi yazo kansa saiyace kada ta damu ta sallami wasu tukunna shiba sauri yake ba( )"

"Adede lokacin motocinsa guda uku da sukaje dauko shi daga Airport sukazo wucewa ta wajan,hankalinsa yanakan"

"jaridar dake hannunsa yana dubawa,daga tinted glass din motar tasa kamar wasa yaga uban mutane sun taru awajan, hakan ne yadauki hankalinsa har ya ajiye jaridar hannunsa akan cinyarsa yamaida hankalinsa wajan yanaso yaga me akeyi awajan da mutane suka taru har haka, adede lokacin yaron da Hafeeza ta zubawa qosai ya matsa daga wajan har fuskarta tayi nasarar bayyana."

"Cikin sauri Hafeez yasake gyara zamansa yana kallonta, qosan daya gani agabanta tana soyawa shine yasa lokaci daya yaji wata irin fad'uwar gaba wadda ya dade rabon da yaji irinta,wannan qosan datake soyawa shine yatuno masa da wasu shekaru dasuka shud'e acan baya tun kafin a haifi 'yanbiyu."

"Fuskarsa babu walwala ya kalli Danladi driver yace""juya baya Danladi"""

"Cikin bin umarnin sa Danladi yace""to Yalla6ai"""

"Yayi kwana, suma sauran motocin dasuke bayansu sukai kwana,suka sake dawowa cikin layin akaro na biyu,suna"

"zuwa daidai wajanda Hafeeza take soya qosai ya tattara nutsuwar sa ya maida wajan,adede lokacin ta dago kyakykywar fuskar ta tana magana da wata mata dazata kai Yara makaranta da alama yaran nata ta tsaya zata siyasa qosan."

"Fad'uwar gabansa bata sauyaba, saima sake jin wata fad'uwar gaban dayayi sanadin kallon fuskar yarinyar,ahankali"

"yasaki wani irin murmushi, ya kalli driver akaro na biyu yace"" Danladi asake juyawa"" ( )"

"Danladi yayi murmushi yasake juyowa akaro na biyu, suna sake juyowa wajan yace""dakata"""

"Danladi yacika umarni ya tsaida mota, sauran motocin ma suka tsaya suna mamakin yanda suke maimaita hanya"

"daya, sun wuce akaron farko,sannan sun sake dawowa akaro na biyu, sau uku kenan suna zagaya wajan."

"Kafin su gama mamaki sukaga Danladi yafuto da sauri yabudewa Yalla6ai mota, cikin sauri suka futo daga tasu motar suna qoqarin tambayar sa ko akwai abinda yakeso,da hannunsa ya dakatar dasu hakan yasa dole suka tsaya,."

"Ahankali yasaka hannunsa yacire jacket din jikinsa,hakan yasa nan take kallo daya zaka masa ka hango yanda jikinsa"

"ya mummurde tacikin suit din musanman dantsan hannunsa,ta gefensa wuyansa kuwa ga zanen tattoo nan yafuto sosai kamar ba dan Musulmai ba, yayinda kunnansa na dama yake saqale da dankunne, hannunsa d'aya yazura cikin aljihun wandon sa sannan yanufi wajanda Hafeeza take suya gadan-gadan."

"mamaki yagama kashe dandazon mutanan dasuka rakoshi suna tunanin me Oga Hafeez zaiyi awajan yarinyar,?"

"shi Kansa Hafeez tafiya kawai yake,banda fad'uwa babu abinda gabansa yakeyi, wanda shi akaran kansa yarasa dalilin fad'uwar gaban."

Complete document 1k

8621296018

Amina Muhammad fcmb

"kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034"

Amnah El Yaqoub
'<Øûß

"[5/24, 10:40 AM] El Yaqoub: MATAR ABBANA "

(Luv Story)

Writing By Amnah El Yaqoub

Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update

https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45

5

Shi Kansa Danladi driver mamaki yake me yalla6ai zaiyi da qosai? kode shima yana so ne kamar yanda Hajiya Kaka

take yawan aikoshi wajan yarinyar siyan qosai?

kasancewar babu wanda zai bashi amsar tambayar sa yaja bakinsa ya tsuke.

"Hafeez kuwa, bai daina jin fad'uwar gaba ba har saida yaje wajan,daga gefenta ya tsaya shima kamar yanda yaga"

"sauran mutane sun tsatstsaya, mutane da yawa kuwa sai kallonsa suke, daga cikinsu wasu tunani suke da alama ba musulmi bane irin kiristan nan ne masu zama acikin hausawa saboda sunga dankunne guda daya a maqale a kunnansa na hagu, ga kuma zanen tattoo a hannun sa kasancewar ya d'an tattare hannun rigar tasa kadan."

"Tunda ya tsaya awajan idonsa akanta yake,ba komai ne yafi daukar hankalinsa da'ita ba sai idonta, idanuwan nata sunyi masa kyau kamar idon jarumar fina-finan India wato Ashwariya, ba normal idone kamar na kowa ba."

"Ganin tana qoqarin tsame na cikin man da alama yagama soyuwa hakan yasa ya laluba cikin aljihun wandon sa yaji wayam babu kud'i sai wata takarda dayaji guda daya,sai yanzu ne yake tunanin mema yakawo shi ne?."

"Ahankali yasake shafa dayan aljihunsa, ya dauko wallet dinsa yabude, saide itama babu kudi sai dubu daya aciki, yayi"

"mamakin ma yanda akai yasamu dubu dayan aciki saboda yariga yasan cewa shiba ta'ammali yake da kud'i a hannu ba saide transfer kawai kokuma yabada Atm dinsa,inde ya zauna da kudi kuma takarda to saide dollars."

"Bai saurari mutanan dasuke jiranta ba,yasake matsawa kusa da'ita yamiqa mata dubu dayan, cikin muryar sa me aji"

"yace""Abani"""

"Duk da kud'i yake bata, Koda wasa bata dago kanta ta kalli wanda yake bata kud'in ba,kanta yana sunkuye, saide"

"wani daddadan qamshin Turare daya cika mata hanci wanda tunda take a tarihin rayuwarta zata iya cewa bata ta6a jin qamshin Turare me dadi kamar wannan ba, amma hakan baisa ta dago ta kalli mamallakin qamshin ba."

"Ahankali ta meqo siraran yatsun ta ta kar6i dubu d'ayan daya bata, sannan tafara zuba masa qosan,yanda ta sunkuyar da kanta tana zuba masa qosan hakan yasa hular hijabin jikinta ta danyi baya kadan, har sumar kanta me laushi tafara bayyana."

Harta gama zuba masa qosan tabashi idonsa yana kan lallausar sumar gashinta daya hango.

"Ahankali Yajuya yabar wajan, yana qarasawa wajan motocin da suka dauko shi aka bude masa yashiga motar, sannan suka dauki hanyar gida, Danladi driver mamaki yake kode duka jikokin Kaka suma sunyi gadon cin qosai ne kamar ita? yasan cewa rana daidai ne baya zuwa wajan yarinyar nan yana siyawa Hajiya Kaka qosai, to kuma yau abun mamaki yaga shima Oga kwata-kwatan da kansa ya yatsa yasiya, to Kaka yasiyawa Qosan kokuma shine zaici?. Bama wannan ne abun tambaya ba,duk saboda siyan qosai yasa suka sake zagaye layin har sau uku kokuma saboda yarinyar datake qosan ne?( )"

"Bai gama tunanin sa ba yaji Hafeez yace""dakata Danladi"""

"Cikin bin umarninsa ya dakata, Hafeez yamiqa masa ledar qosan dake hannunsa sannan yayi masa nuni dawani"

"almajiri yace"" kabashi wannan"""

"Babu musu Danladi ya kar6i qosan yabawa almajiri, sannan yadawo motar sukaci gaba da tafiya, tunani yaci gaba"

"dayi to idan Yalla6ai yabayar da sadakar qosan daya siya hakan yana nufin ba qosan ne ya birgeshi ba, yarinyar datake saida qosan ce ta birgeshi,idan hakane kuwa wannan aiba qaramin abun farinciki bane,duba da yanda Yalla6ai din hatta su mutanan gida sun san cewa ba ma'abocin shiga sabgar mata bane,da alama itade Malama mai qosai kakarta ta yanke saqa.( )"

"Suna qarasowa gida yadauki jacket din suit dinsa a hannunsa, yayinda hannunsa d'aya yake cikin aljihun wandon sa,"

cikin takunsa na qaqqarfan namiji yanufi falon nasu Danladi yana biye dashi da qaramar jakarsa.

"Yana shiga falon 'yanbiyu suka taho da gudu suna masa oyoyo, saide suna zuwa kusa dashi suka tsaya turus suka"

"kasa rungume shi, sai shine cikin aji ya d'an jasu zuwa jikinsa kad'an ya rungume su, lokaci daya kuma ya sakesu, fuskarsa babu walwala yace""ya kuke"""

"Atare suka had'a baki sukace ""Alhamdulillah Yaya"""

"Daga haka bai qaraba,yawuce kan kujera ya zauna, adede lokacin kaka ta futo daga dakinta tana dariya, cikin"

"farinciki ta nufeshi ta zauna akusa dashi sannan ta jashi jikinta ta rungume shi,babu musu ya kwantar da kansa akan qirjinta tareda lumshe idonsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya,ya dade rabon da yaji nutsuwa irinta yanzu daya ji shi ajikin kakar tasu, wadda ta maye musu gurbin uwa da uba,

4 / 14