Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BURIN FANSA BOOK Complete Complete Hausa Novel by HAUWA ISAH Ja'o

Author :  HAUWA ISAH JA'O Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 9

6K to 9K   out of 27K words

Junaid wannan file d'in yana d'auke da duk dukiyar da muka mallaka nida Aliyu! A halin yanzu nasu Hydar ne , wannan kuma laptop d'in yana d'auke da wasu bayanai ! A kowanne lokaci ina kwana da shi cikin firgice ne don haka ina so ka rik'e Amana! Kar ka bari wani ya gani domin kuwa a wannan zamanin kowa ba abun yarda bane! I believe kai kad'ai ne zaka rike amanar Mu nida Aliyu ,any time za'a iya zuwa neman wannan system d'in kada ka sake su sameshi ! Ni nasan menene a ciki don haka be careful ka rik'e with care!!"""

"Junaid ya ce "" Toh amma Madame why me? "" shhhhh Kaidai kawai kayi abunda tace maka"

",Kaje ka Adana wannan abun tunda ta fad'a maka!! Maza tashi Kaje!!!"" Aliyu ne yayi wannan maganar , ba musu Junaid ya fice da sauri ya shiga motar sa ya fita ,bai wani bar k'ofar gidan ba kawai ya hango wata bak'ar jeep ta nufi k'ofar gidan don haka ya kashe Wutar motar sa ya kwanta a ciki yana lek'o wa a hankali........."

"[10/20, 10:08 AM] +234 701 661 4602: BURIN FANSA "

NA HAUWA ISAH JA'O ( 2016)



"Sun gama bincika ko ina basu samu kowa ba , Motocin wasu soji ne suka fara shigowa cikin gidan ganin haka yasa duk suka haura suka fice daga gidan ta inda su Junaid suke ba tare da sun lura suna wajen ba , wata k'atuwar mota ce bak'a kamar bus ta zo da gudu ta daukesu suka bar wajen cikin tsananin speed."

Gaba d'aya sojojin suka bazu a gidan suna dube dube daidai lokacin Ambulance ta shigo

",baka ganin komai se walwalin sirens."

"Captain Junaid ya rik'e yaran suka fito daga inda suke b'oye ,da sauri wasu Sojojin suka nufo su tare da wasu Nurses guda biyu suna sanye da kayan soji amma kuma da lab coat a jikin su , yaran suka karb'a daga hannun Junaid ,Hydar ya wafce da gudu ya nufi cikin gida ,suma suka bishi a baya , Bai tsaya ko ina ba se d'akin su Dad ,nan ya same su kwance shame shame , likitoci biyu suka dukufa suna duba lafiyar su , dukkan su suna Numfashi don haka aka makala musu Oxygen mask aka fita da su , gaba d'aya unguwar cike take da sojoji. Wayar junaid ne tayi k'ara jiki na rawa ya d'aga ya kara a kunne "" Sir ! Yanzu an kaisu asibiti ! Ok se ka iso sir!!!"" Yana kai wannan ya katse wayar ya kama hannun Hydar ,Zainab kuwa tuntuni daman tana hannun sa tayi lamo kamar mara lpya , Direct motar sa ya nufa ya sa su sannan ya d'aura ma"

"zainab seat belt ,ya shiga suka bi bayan Ambulance d'in zuwa Asibiti............."

"Har k'arfe Hud'u na safe babu bayani akan kowanne d'aya daga cikin su, Sukayi Alwala shida Hydar sukabar zainab tare da wasu Sargent's suka fita masallaci , Hydar babu irin adduar da bai yi ba , Fitowan su daga masallaci basu ma k'arasa cikin asibitin ba , General ya iso ,gaba d'aya sojoji ne a harabar asibitin tun daga waje har ciki kowa fuska a d'aure babu annuri , da gudu Hydar ya nufi inda yake yana fad'in "" Uncle !! Na gansu sune "" Da sauri General ya rufe"

"masa baki ya durk'usa a gaban shi yace "" Keep it in your heart ,we'll talk about it later! Kar kayi magana a nan d'ana "" kai Hydar ya girgiza yana share hawayen shi , kafin k'arfe bakwai press sun cika bakin asibitin ,kowa yana son d'aura trending story d'in nan , Captain Junaid ya fito kenan zai yi waya yaga Press dank'are a k'ofa har ture junan su suke yi ,,bak'in gilashin shi ya Zara ya sa a fuskar sa sannan ya fara sauk'owa daga benen ,microphone kuwa kamar zasu chusa masa a baki kowa da tasa tambayar , wasu de fatan su Lt Aliyu is still Alive wasu kuwa"

"So suke suji menene ya haddasa wannan murder d'in da akayi attempting yi!!"""

"Dr Lloyd kwararren likita ne wajen fitar da harsashi, shi kad'ai ne kuma se wasu likitoci guda biyu masu taimaka masa. ""Anyi nasarar cire harsashin daga jikin su baki d'aya , Amma sedai Mun rasa d'aya daga cikin su!! Am sorry "" Maganar da likitan ya fad'a shi ya zaburar da Hydar dake zaune kan kujera ya mik'e da gudu ya doke likitan har saida suka zube a k'asa , da sauri General da Captain Junaid suka rirriqe shi yana fisgewa yana fad'in "" You are lying !! Jiya ma an harbesu basu mutu ba se yanzu!!"" General ya zaro ido waje ya juya yana kallon Junaid"

"yace "" Am afraid Yaron nan zai iya samun matsala a kwakwalwa!! Take him out of here!! """

"Junaid ya rik'e Hydar da k'arfi zai fitar da shi amma ena ,ya ci k'arfin sa ya ruga da gudu ya bud'e k'ofar ward d'in ya shiga , mutum biyu ne kwance d'aya an rufe da mayafi d'aya kuma na kwance da drip! Hydar ya ruga da gudu gun wanda Aka rufe ya janye zanin , wani duka k'irjin"

"shi ya fara Nan ya fara k'ira "" Dad! DAD!! DAD!!!! KA TASHI PLS PLS PLS WAKE UP!!!"""

"Fareedah dake sanye da drip ta fara bud'e idanuwan ta a hankali ,sannan ta juyo kanta zuwa side d'in da take jin Hayaniyar , Dishi dishi take ganin Hydar ,da kyar sight d'in ta ya dawo me kyau idonta ya sauk'a a kan Gawar Aliyu da ke kwance , basu ankara ba suka ji fad'uwar ta daga saman gadon , da sauri nurses Suka zo zasu riketa ta d'aga musu hannu Da gudu Hydar ya rungume ta Zainab ma haka ,Junaid gaba d'aya kuka ya ci k'arfin sa don haka ya fice . fuskar Aliyu ta shafa hawaye na gangaro mata bata iya yi wani magana ba ta sulale a wajen itama ta"

fad'i.................

=ØŠÝ<Øõß Mayjiddah jao<Øõß=ØŠÝ

"[10/20, 10:08 AM] +234 701 661 4602: BURIN FANSA "

NA HAUWA ISAH JA'O ( 2016)

31<Øžß



FLASH BACK

.......

"Junaid na fita Fareedah ta mik'e ta nufi hanyar bedroom d'in ta ,Murmushi Aliyu yayi ya girgiza kai k'asa k'asa yace "" Very hard to convince"" ya mik'e ya k'arasa cikin falon ya d'aga zainab da tuni tayi bacci sannan ya cewa Hydar "" Hey soldier !! Seven am tomorrow zan kai ku schl maza gashi muje ciki"" Hydar ya d'ago fuska da d'an dakile yace "" Ok dad! Just five minutes pls!!! "" Aliyu yayi murmushi yace "" Nooooo!!!! Tashi muje no five minutes!!! "" yana maganar yana janyo hannun Hydar bai tsaya ko ina ba se d'akin su ,nan ya iske Hindatu tana ninke kaya yace "" Haba Hindatu wannan kayan can't they wait until morning? Dare yayi Kije ki huta mana! Before that ki rufe min k'ofar parlour yau sam babu kowa a waje nace suje su huta a gida ,so ki rufe"

k'ofar da kyau. Ba musu ta fita don aiwatar da abunda ya umarceta.......

BACK TO STORY.....

"Junaid yana ganin sun shiga gidan nan ya ciro wayar sa yana k'iran numbern Lieutenant amma babu amsa , wajen fifteen missed calls don haka ya tura briefcase d'in k'ark'ashi kujeran motar sa ya d'auko bindian shi ,unfortunately babu bullet a ciki ,ya doki motar da bindigan ya jefar , daga nan ya d'auko wayarsa ya fara laluben numbern LIEUTENANT GENERAL YUSUF MAINASARA , koda ya d'aga kafin Junaid yayi magana se yaji Muryar Col Aliyu yana fad'in What exactly do. You want? , nan ya kashe da wuri ya rasa ma ya zaiyi don haka ya k'ira Major general gaba d'aya, jiki na rawa yace "" Sir this is captain Junaid speaking sir!!! We need cover"

"up!! Lieutenant Aliyu is in danger ,yanzu na k'ira Lt general Yusuf amma ,ba response ( Don't"

really know why junaid lied dat Yousuf did not respond)

"General ya mik'e a fusace ya ce what?!! I'll send my boys but you have to do something coz it will take some time before they reach there "" junaid ya amsa da Yes sir!! Copy that Sir!!!"" Ya kashe wayar ya fita cikin sand'a yana ta dube duben k'ofar gidan, Duk saida ya k'arewa position na CCTV cameras sannan ya d'irka ta saman dogon ginin da ke wajen don gate d'in akwai masu tsaron wajen , Cikin flowers d'in backyard d'in ya fad'o ta cikin flowers d'in ya gama k'arewa mutanen kallo nan ya ga sun janyo Body d'in wata mace sun nufo inda yake , sake"

lumawa yayi cikin flower d'in suka zo daf inda yake suka yi wurgi da ita.

"Idanuwa ya zaro waje yace "" Hindatu???!!! ,luckily se yaga still tana numfashi, da sauri ya fito ya tab'a ta ,a zabure ta rik'e hannun shi tace "" Ka tttaimake su yallabai!! Zzzzaaa su khkashe y'all!!!!!a Daga nan bata sake magana ba ,junaid ya damk'e hannayen shi ya rumtse"

"idanuwan shi yace "" Ya ilahi!!! Da sauri ya mik'e bayan ya rufe mata ido ya rufe fuskar ta da jacket d'in shi , wani sangami ya hango se kai kawo yake ta wajen backyard cikin sand'a ya bi ta bayan shi ya murd'e masa wuya sannan ya bud'e k'ofar bayan ya d'auke bindigan sangamin , hanyar da ya d'auka direct hanyar flat d'in su Fareedah ya d'auka daga nesa yana hango k'ofar su lieutenant rabi a bud'e ,cikin sand'a ya je ya d'an rakab'e yana kallon abunda yake faruwa a"

ciki...

"Lieutenant Aliyu na hango zaune a k'asa se Fareedah dake kwance malamala cikin Jini , mutanen bayan su kawai Junaid ya iya hangowa , Zuciyarsa harbawa kawai take yi especially lokacin da ya had'a ido da Aliyu , har ya yanke shawarar shigowa Aliyu ya ce ( a fakaice) A'a!!! Wannan ba hurumin ka bane ,!!! Yara!!! "" Junaid yana jin Kalmar Yara ya tuno da su Hydar, juyawar da zaiyi su kuma sun fito daga d'aki har zainab hannun su sark'e da na juna ,Maryam se k'ira take Mommy I can't sleep, I am having nightmare!! "" Junaid ya zaro ido waje yana waving musu hannu yana cewa su koma amma ina !! Da suka hango shi duk se suka zubo da gudu suka rungume shi , Hydar zai yi magana da sauri Junaid ya rufe bakin su Daidai lokacin za'a harbe Lt Aliyu , Hydar ya had'a ido da baban shi ,Aliyu ya zaro ido waje yace "" No!! Pls get out of here !! A nan ne d'aya daga cikin su ya juyo suka yi ido hud'u da su Junaid Hydar na"

k'ok'arin fisgewa ya shiga d'akin zainab kuwa ta 'kank'ame Junaid tana kuka.

Captain Junaid da Hydar suka Hada baki wajen cewa ```Lt gen Yousuf mainasara?????```

"Junaid ya zari zainab a kafad'a ya Fisgo Hydar suka fara gudu , da gudu wayansu katti suka bi bayan su , kafin su iso Junaid ya koma wajen b'uyan sa na flowers shi da yaran suna kallon duk mutanen sun fito se dube dube suke yi , Daga nesa sukaji d'aya na cewa "" Babu wad'annan files d'in a gidan gaba d'aya! Dole Mu nemi wannan mutumin ko ma waye shi!!! , Junaid ya zaro ido yace "" Files!!so they are looking for the files??"" , d'ayan yana juyowa kawai Idanuwan Hydar"

"ya sauk'a a kan fuskar sa ,wa zai gani ?!!"

"Baki na karkarwa ya fara zufa , tabbas shine wanda ya harbi Dad first kafin sauran!! Nima de"

"Jeeddah nayi mamaki sosai ,koda yake ba abun mamaki bane idan har akayi la'akari da take"

taken Mk!!!! Readers M.K k'anin Aliyu shi Hydar ya gani!!!!!..................

=ØŠÝ<Øõß MAYJIDDAH JA'O<Øõß=ØŠÝ

"[10/20, 10:09 AM] +234 701 661 4602: BURIN FANSA "

NA HAUWA ISAH JA'O ( 2016)



"Stretchers biyu na hango an fito da su daga cikin asibitin , Press kam basu da aiki se"

"d'aukar hotuna ,wata journalist ta samu ta kutsa cikin su General ta ce"

""" Yallabai shin har kana da wani abu da zaka iya fad'a game da wannan aika aika da akayi da yayi sanadiyyar mutuwar Lieutenant Colonel Aliyu Abdoul-Rahman? Wadansu na fad'in cewa sakaci ne daga wajen ku manya ,da kuka kare kawunan ku da iyalan ku amma wad'anda suke k'asa da ku kuma kun yi sakaci da alamarin su ,domin labari yazo mana cewa babu mai gadi ko tsaro guda d'aya daga cikin sojoji da yake cikin gidan a lokacin da abun ya faru , while wasu suna tunanin mak'ark'ashiya ce daga wajen ku manya idan akayi la'akari da rashin kawo agajin"

"gaggawa da kukayi har se bayan da aka gama aiwatar da murder d'in """

"Murmushin takaici ne ya taho ya ma rasa yanda zaiyi , hawaye masu zafi suka gangaro daga idanuwan shi ,yace "" YES!! YES!! we are Selfish but not like you are!! Ku dai burin ku kusamu labari jikin ku na rawa ku d'aura a gidan TV ,jarida magazines !! Har wawa kuke yi ya zama kune first wanda zai fara d'aura most trending Breaking news!! Shin kun tab'a tunanin menene muke yi kokuma wani k'ok'ari mukeyi don ganin Mun kare ku? Ku kanku baku tsira ba! Balle kuma mu!! Duk abunda kuka ga ya faru iko ne na Allah ,haka yaso alamarin sa! Kuma wannan itace k'addara!! Kin yi magana akan kariya ko kun manta mune Muke b'ata lokacin mu muke bada rayuwar mu don kare ku? Aliyu ya mutu amma kuma HIS SPIRIT IS STILL WITH"

US!!! wannan ma ta dalilin neman ma k'asarsa tsaro hakan ta faru !!!

"Kin kuma yi magana akan wai Mun cika gidan mu da masu gadi sojoji! Shi kuma ya kasance mutum ne mai sanin hakkin dan Adam!! Yayinda yake tare da nashi iyalan ya kuma san muhimmancin su ,sam bai yadda ba ya tauye wa wasu hakki! Shin mu da shi waye mafi samun kariya ? Idan kikayi la'akari da namu masu tsaron ,kullum a waje d'aya bakya tunanin Muma idan suka gaji wataran zasu juya kan mu!!!? ANSWER ME!!!! Toh ki sani! Aliyu ya bambanta da"

ku domin Mutum ne mai adalci ga dukkan mu!!!

"Lastly kin yi magana akan sakaci!! Ina so ki sani!! Abuja zuwa Kaduna in the middle of the night,is not like Bedroom to bathroom!!! Ba haka zamu shigo babu shiri ba! Shin kuma in ma Mun zo da wuri idan Allah ya k'addara abun se ya faru ke zaki chanza ne! Kai fa? Ku fa????"

"Zaku chanza ne???"""

"Duk wajen ya d'au silence kamar babu kowa , General ya dubi matar yace "" Akwai wata tambaya ko kuwa zan iya tafiya!? "" Ba tare da ta kalleshi ba kanta a k'asa ta matsa suma sauran jiki a sanyaye suka dare gida biyu , General ya wuce tare da Captain Junaid da su Hydar , Y'an Jaridar duk suka shiga motar su kowa yabi bayan su General Ambulance na tsakiya , ko ina kuwa da tsaro tun daga Asibitin har Unguwar GRA dake kaduna , wasu sojojin ne tsaye a bakin gate d'in gidan ,da gudu gudu suka bud'e gate d'in motocin suka yi ciki aka yi parking , daga ,bayan an fitar da gawar su Fareedah wani Soja ya zo da sauri ya yi wata"

magana da General......

"Zainab na tsaye ta ga duk basa kallon ta da sauri da nufi cikin gida ,direct d'akin granny ta nufa ,babu kowa a ciki ,wajen ma duk a birkice kamar an yi kokawa ,tab'e baki tayi ta fito da guntun hawayen ta tana k'iran Granny, Matar General da ta iso ,ita tayi ta lallashin Zainab har"

"aka samu tayi bacci ,su duka babu wanda yasan whereabouts of Granny!!!................"

=ØŠÝ<Øõß Mayjiddah ja'o<Øõß=ØŠÝ

"[10/20, 10:09 AM] +234 701 661 4602: BURIN FANSA "

NA HAUWA ISAH JA'O ( 2016)



""" Wai kayi hauka ne!!? Me kuma zamuyi da wannan tsohuwar? You should have finished her!"

"Me ya rage mata? Ban tausaya wa mai juna biyu bama balle wannan!!"" Don BK ne yake magana a fusace ta waya."

"M.K yace "" Na barta ne saboda bata san ina cikin su ba ,besides tun da taga Aliyu a Kwance cikin Jini ta fita hayyacin ta , ai ni inaga a woman at the age of 70 bata da wani amfani , saboda haka ne ma zan je in ajiyeta a asylum coz I can't hurt her ,ai ita ta haifeni!!"" Don BK ya jinjina kai sannan yace "" Kai da yarka yanzu kunada lasisi na dindindin a k'asar ingila, zakaje Janaiza Yayan ka da matar sa , sannan kuma zaka ajiye aiki ,duk wani abun buk'ata Mun tanada maka shi!!"" Murmushi M.K yayi yace "" Da kyau Don!!! Consider it done!! "" daga nan ya katse wayar sa"

",ya juya yana kallon Granny da ke jingine a cikin mota ta k'urawa madubin motar ido ,idan ba ka"

"lura ba ,zaka yi zaton ma bata da rai!!""............"

"Bayan an yi Janaizar su har an dawo ne M.K ya iso , with his crocodile tears wai ya je wani meeting ne da safe bai ji labarin abunda ya faru ba , Hydar ya damk'e hannun shi zai zabura"

",junaid ya rik'e shi ,haushi yasa ya fisge hannun sa ya ruga da gudu yayi cikin gida. D'akin su Dad ya shiga ya rakab'e a lungun gado ya kifa kai Zainab da taga wucewar sa kasancewar ita d'aya ce a falon ta mik'e da gigin baccin ta ,ta shigo dakin, jin an bud'e k'ofa yasa Hydar yayi"

wuf ya d'auki lamp ya d'aga zai wurgo .

"Ihun da tayi ne yasa yayi saurin ajiyewa, da gudu ta nufo inda yake ta rungume shi tana fad'in"

""" Bro meyasa zaka jefeni? "" zaunar da ita yayi a k'asa shima ya

3 / 9