Author : HAFSAT UMAR DANGORO Category : African Stories & Novels
hankalinta yatashi cikin sauri tashiga cewa " sannu Habib ,sannu
kaji"Habib kuwa daker ya iya bude Baki yace yauwa,sannan ya Dora da cewa "Dan Allah
kada kisake kulle kofarnan ki taimakeni zuwa dakina kinji" kada kikasheni Dan Allah
ki kamani muje na wanke jikina" kwallar da ke makale a kwance acikin idon saliha ne
ya karasa zubo mata, tace"kayi hakuri kaji ko insha Allah bazan sake kawoka Nan
dakinba, tana maganar tana rike hannusa ta taimaka masa ya tashi shuka fara tafiya,
gani tai Habib ya zuba mata ido Yana kallonta "ga mamakin ta sai taga Yana
sakarmata murmushi Amma duk da Haka bata kulashiba itadai kawai ta dauka cewa Habib
zafin ciwone yasashi yake murmushi"
Saliha kam bayan sun karasa dakin Habib ta ajiyeshi a gefan gado,sannan ta tsaya
tace "Bari na kawomaka ko shariye kadansamu kasha, murmushi yayi tare da taune lebe
daya ya daga mata Kai alamar takawo,
Fita tayi ta hado masa shayi me kauri ta kawo masa,ta ajiye lokacin har yashiga
yayi wanka yafito,bayan ta ajiyene ta juya zata futa Habib ya Kira sunan ta
"saliha" yafada dakarfi"saliha kam juyowa tai da sauri tare da furta "ma,am
"lafi..... Bata karasa furta abin da zata ceba ya caka mata wukar dake hannunsa
adaidai cikinta, bayan ya lumamata ita aciki ne ya zaro ta yakara sokamata a gefan
cikinta Babu tausayi Babu imani, ya cigaba da danna wukar harsai da tashiga ciki,
wasu hawayene masu azaba sukashiga zarya a kuncin saliha suna diga a kasa,domin
tsabar azaba Tama kasa furta komai saidai kawai tsiramasa manyan idanunta da tai
take kallon wannan fuskartashi Yana sakarmata murmushin mugunta, Habib kuwa zuwa
yanzu zuciyarsa ta Gama harzika hakanyasa ya zare wukar daga jikinta ,yasaketa ta
fadi kasa Tana tafaman juyi zuciyarta na tafasa, dukda zafi daradadin da takeji
idanunta Basu hanata kallon fuskar Habib ba, magana yasoma yimata Yana cewa " hmm
yarinya kenan haryanzu bikisan wakika aura ba ,bakisan wanene Habib ba abaki kawai
kikejin sunana,Amma bakisanniba ,Wai harni Habib zaki saka wankin kayanki, nihabib
zaki kaiwancen dakin ki kulle,uhm Ada nayi tunanin na barki bazan kasheki ba, Sabi
da Ina tsammanin ke yarinya ce,saikuma naga idan ban kasheki ba zaki jamini matsala
babba, sannan zaki tonamin asiri,ni Habib Babu Wanda yaisa yace zai munwayo,karnake
kallonki yarinya Yana Gama fadar Haka ya dauki wayarsa,ya dannan Kira bugu daya
tashiga yadaga"yace zaka iya shigowa yanzu,Yana fadar Haka ya katse wayar" ba,afi
minti 1ba aka turo kofar dakin subiyune suka shigo kana ganinsu kaga tantiran "yan
duniya, sannan kaga Yan daba,durkusawa sukayi cak suka dauki saliha suka dorata
akan wani dankaramin gado dasuka shigo dashi,daya daga cikine ya dakko farin kelle
ya daure gurinda aka soka wukar sannan suka kalli Habib suka ce"yallabai yaza,ai da
ita?" Habib ne ya kallesu yace "Ina doctor faruq ?" Eh doctor Yana ta can baya
yanajiranmu domin yace da sassafe gobe zai huce meduguri" oky " kudauketa ku kaita
gurinsa duk yadda za,ayi kada ta mutu,ayimata ayki idan ta warke,inason ku ganama
duk wata azaba kowacce kalace,harsai tafada muku wacece ita"oky sir suka amsa gaba
yansu suka futa tare da saliha, ajikin falon gidan akwai wata kofa waddda bakowane
zaikula da itaba har sai kanutsu ,budewa sukayi sannan suka rufe ta,saigasu a bayan
gidan inda Babu komai sai jeji,motarsu da suka ajiye ta baya ita suka bude suka
dora saliha akan gadon marasa lafiya doctor Kuma yashiga aykin da akasashi, tafiya
suka shiga yi suna ta zuga gudu har suka fita daga cikin mutane ma,ana suka kusan
futa daga kano zuwa wata kasar daban....
Shiko Habib zama yayi ya rike kansa Yana tsara irin karyayyakin da zaiyi ya
fitar dakansa daga zargi, dafarko dai jinin yafara gogewa ya gera gurin tass sannan
ya dauke wukar daga gurin ,komai na gurin yageru Babu ko alamar anyanki mutum a
gurin, sai da yatabbatar ya saita komai sannan ya dauki waya ya danna numbar wayar
ya juneid,yashiga Kira , juneid kam Yana zaune gaban Miro ana gyramasa Kai saiga
Kiran Habib ya shigo ,Kiran farko ya daga ya Kara a kunne sa tare dacewa "hello
brother,kuka Habib ya saki Yana cewa" Dan Allah Yaya juneid kataimaka min,wallahi
kaga nazo gida tun jiya amma Banga saliha ba Kuma natambayi me gadi yacemin Bata
fita ba,Dan Allah kazo ka taimaka ,kasanarwa dasu momy "arazane juneid yace" what"
ta bata to inazata kenan Kuma katambayi gidansu batajeba "eh Yaya bankiraba Amma
Zan je yanzu dan Allah nidan kataimaka anemota yasake fashewa dawani sabon kukan"
allah sarki bawan allah juneid ne yashiga cewa" kayi hakuri dan,uwa ka kwantar da
hankalinka insha Allah za,aganta kaji ,kajirani yanzu zanzo gidan, yafada tare da
katse wayar ya Mike ya dakko jallabiya fara ya saka futa...
Shiko Habib Yana kashe wayar tsalle yashiga yi Yana cewa, honi habibu
masifa,'meja Dani saiya shirya wallahi,ayanzukam Babu me zangina,tunda dai har
nanuna musu Ina jin tsoran saliha Kuma ita take azaftar Dani ay Babu Wanda zaiyi
tunanin na ayka shegiya gurin da ba,a dawowa🤣
Juneid ne yasauka kasa gurin iyayensa yake sanar musu da abin da yafaru, gaba
kidayanzu hankalinsu ya tashi Babu shiri suka tashi suka shirya,aka nufi gidansu
saliha,bayan sun Isa gidan ne suka sanarwa da mahaifiyar su saliha abin da yafaru
atake a gurin ta yenke jiki ta fadi sumammiya, hankalin safiya kuwa idan yayi dubu
yatashi, nan ta Mike tsaye tashiga kunnamusu uwar ashariya tana cewa duk ma inda
kuka kaimin "yar,uwata tunwuri kufitomin da ita ,shegu mugaye kawai,danginku dangin
tsiyane wallahi natsani "yan ahalinku azzalumai kawai,wallahi sai kufitomin da
"yar,uwata,momy ce tashiga rarrashin ta tana bata hakura sannan tace sukama umman
su da ta fadi akaita asibi ti aceto rayuwarta amma sam safiyya taki saima cigaba da
tayi da zage zagenta tana cewa"kull Allah ya kiyaye inbari wannan mummunan hannun
naki ya tabamin mahaifiyata salon itama ku kashemin ita mugaye Allah ya wadaran
halinku, ta karashe maganarta tare da yin tsaki tabarsu a gurin, suko dady da momy
wadan da tun dazu sukayi mutuwar tsaye suna kallon ikon Allah ,yanzu da sukaji zagi
sum sum suka kama hanya suka fuce, bakin gidan suka tadda juneid da Habib suna
jiran fitowarsu ,suna karasawa inda suke cikin sauri Habib yace Anganta tanacen ko"
uhm momy tadanyi murmushi ta jijjiga Kai alamar a,a sainnan suka shiga mota suka
bar gurin....
Safiyya kam bayan tafiyarsu momy me ta tashi ta debo ruwa ta zubawa ummansu,
saigashi ta farfado,idanuwanta cike tab da hawaye zuciyarta na tafasa,takalli
safiyya tace " shin dagaskene saliha ta bata,kodai sunkashemin itane,tasake rushewa
dakuka tace"kingani ko,Kinga irinta ko safiya bana fadamiki ba gashinan kunjefata
cikin masifa da bala,I wallahi Harcikin zuciyata bazan taba yarda "yata saliha bata
taiba,kawai dai Habib yakashemin e tane, wallahi Habib bazai Gama da duniya lafiya
ba ,inan Ina jira nasan "yata jarumace koma jajurtacciyace a kan komai,insha Allah
saliha tanan da ranta kema safiyya kidaina kuka insha Allah yar,uwarki zata dawo
lafiya...
Tom izuwa yanzu kam labarin batan saliha yagama zagaye ilahirin garin Kano
gashi harta motar da Aka saka saliha tafita daga cikin ka no balle ace za,a iya
kamashi,Kai narakaice muku motar su doctor faruq,takusan Isa cikin garin
meduguri,..
Allha sarki baiwar Allah tana kwance acikin motar cikin jini Rai a hannun Allah
tana faman futar da numfashi daker,tana ambatar sunan ubangijin da ya haliccemu,
shikuwa doctor faruq ya dage sai koka ri yake domin ya ceto ranta, " saliha kam
runtse idonta tai ta bude tana kallon doctor faruq,yadda yake jufa Sabi da aykin da
yake mata, azuciyar ta kuwa cewa take ya Allah kamar yadda bawannan naka ya dauki
aykin da kabashi da baiwa yamai dashi ta gurba tacciyar hanya ya ke ayki a
karkashin masu aykata laifi allah Kai gaggawar tona masa asiri......
MAR'ATUSSALIHA BOOK 2
10...
AFTER TWO days......
*Abu buwa fa sai Kara ta azzara suke inda aka nemi saliha kasa ko sama aka
rasa,Abu kamar mafarki,gabakidaya hankalin su juneid ya tashi, musamman ma hankalin
safiyya da mahaifiyarsu,komai ya dainamusu dadi abin duniya ya hadu ya musu
yawa,tun suna kallon abin kamar wasa yanzu kam sun tabbatar da ba aga saliha
ba,gashi gidan t.v da raidio da kadashin kewaye Babu inda labarin batan saliha
bejeba ,Hatta cikin gidan saliha an zuba matakan tsaro a cikin gidan ta ko Ina sai
bincike akeyi, ayanzu Habib takai takawo yasa ankama megadin gidan sa angarka meshi
bejiba be gani ba, Kai natakaice muku ayanzu hajiya adama da yarta Anisa suna
hannun hukuma Ana bincike akansu ,sakamakon "yar tsamar da aka samu tsakanin su da
su momy akan auren Anisa da juneid da Kuma Habib Ana zarginsu da sace saliha
amaryar Habib...
Zaune suke suna faman ganamusu azaba ta kowace irin siga, Hatta jikin su Saïda
jini ya fito tukunna sojojin Nan suka daina dukansu, sun dakesu iya karfinsu domin
sufadi gaskiyar inda suka Kai saliha Amma amsa dayace suke bayarwa itace"basu da
masani ya akan batan saliha, dady dai dayaga za,a kashemasa kanwarsa tilo guda daya
yasa aka dakesu,Amma duk da Haka anisa faduwa t'ai agurin sumammiya bata ko motsi,
hajiya adama Tana kuka haka aka sata a mita sai asbiti,Babu irin zagin da su Habib
Basu Sha agutinta ba, juneid dai yaji ciwon zagin da tamusu ,Amma shi Habib ko
ajikinsa saima Kara cewa dayake Bekamata asakesuba sai sunfito masa da
matarsa ,Babu tausayi Babu imani agaban idonsa aka yanke yatsan megafinsa guda daya
duk Dan yafadi gaskiyar inda saliha take" Allah sarki bawan Allah yamarasa mezaice
tsabar azaba da tashin hankali Kira yake kawai su kasheshi,habib kam murmushin
gefan fuska yayi ,yakalli sojan yace,ku sakeshi haka,Amma duk da Haka banhakura ba
Hutu nabashi zuwanan da sati daya yafadi inda suka kaimin matata...
*Wllhi umma yakasheta kidaina saka ran ganin saliha araye ,yakamata ace umma
mu fita miyaki Habib ,umma Habib mugune nafikowa sanin wane Habib Dan Allah umma ki
yarjemin naje na kasheshi inyaso Nima akasheni,wallahi umma nagaji daganin zubar
hawayenki ,yaushene zakiyi bacci me dadi batare da kinyi mafarki Mara
dadiba,yaushene zuciyarmu zata samu Salama ,umma dan Allah kidaina kuka ,kidaina
banaso zuciyata tafasa take umma, shikkenan Wai yakashemin "yar,uwata eh umma
kiyimin magana mana,ina yakaimin ita ,ni inaso ko da gawarta ce magani naji sanyi,
shin kinmanta abin dayafaru ?" Afusace umma ta Mike ta kalli safiyya ido cikin
ido ,tace ban Manta ba kuma bazan taba mantawa ba,safiyya ki kwantar da hankalinki
nace nayar da da saliha nasan "yata bata mutuba itadin jarumace kyutace wadda
ubangiji ya bani, nayi Imani Habib bazai kashe saliha ba nasan shi yanada wayo
sosai" yanaso yasan ko ita wacece meyasa tashiga rayuwarsa,wadannan tambayoyin
gudabiyu kawai yakeso ta amsa masa ya kashe ta,ayanzu inaji ajikina Habib ya dauke
saliha daga wannan garin ,babban abin da Habib be Dani ba da shashancin da yayi
saliha bazata taba zama agurinsu ba dole sai ta gudu,wuyarta suce zasu mata
Dole ,nasan aljanunta Dole sutashi daganan kuma zata dawo idan kuma tadawo Habib
zata fara tunkara.... Safiyya ki kwantar da hankalinki wannan abin da nafada Miki
shine zaifaru" safiyyace ta goge hawayen idonta tace,to umma meyasa kinsan da hakan
kike kuka ,bayan kinsan zubar hawayenki na dagamin hankali?" Uhmm umma tayi
murmushi tace "safiyya kenan, kinsan meyasa nake kuka uhm inakuka ne kawai sabi da
hango irin azabar da Habib yayiwa saliha har suka samu nasarar kaita wani
gurin,amma bayan Haka da Babu abin da zaisani kuka....
IN the morning....
Wani gurine Wanda koda dabba dayake da Rai tsoran shiga jejin yake ya zauna, Sabi
da tsabar mugganan abubuwan da ake aukatawa agurin yayi yawa, agurin daki dayane
wan da dagashi Babu wani,dakin yakasance bashi da maraba da kurkuku,gashi da duhun
gaske,daga cikin abin da suke a dakin n'a farko akwai hayakin tumfafiya da mangelo
dakuma wata bakar laya wadda suka kasance tsarine daga muggan aljanu kowane irin
aljajune Babu yadda za ayi sutashi harsai anfito dakai daga cikin dakin, wannan
dakin idan Kai mutumne me aljanu kana saka tafin kafarka aciki to kayi bankwana da
aljani harsai ka an fito dakai tukunna zasu dawo jikinka, idan kuma mutum yakasance
shi aljanine ba mutumba to idan yariga tashi ga yayi bankwana da duniyar mutane,
wannan dalilin shiyasa Habib yakirawo doctor faruq yasa yayi mata allurar bacci
tunkafin su karasa...
. Ton su doctor faruq harsun ido cikin jejin zasu shiga kenan saiga Kiran Habib
yayigo Kai tsaye, doctor ya daga tare dacewa "yallabai mun isofa, murmushi Habib
yayi tare da cewa , "ba kun iso din ba tana hayyacinta ko kum haryanzu bacci take,
dariya doctor ya kwashe da ita yace"hhh ay ita data tashi sai karfe 10 na safiyar
gibe" "yauwa doctor aykinka Yana kyau yanzu Ina son kusaka ta acikin wannan dakin"
doctor ne ya zaro ido yace" yallabai asata anan dakin fa kace damatsala fa indai
Aka sata zamu iya rasata "bangane ba mekake nufi Habib yayi tambayar "ina nufin
zata iya mutuwa ,wannan dakin dakin hatsarine kaikanka kasani, muddum aljani
yashiga baya dawowa balle ita " dariya Habib yayi yace badamuwa kusaka ta akwai
aljanu ajikinta Babu abin da zai sameta sai dai ku ne matsalar,yanzu abin da zakuyi
duk inda Macé me aljanu take kunema a garinnan ,sai na biyata ta dinga fito da ita
duk lokacin da zaku sata tafadamana gaskiya, okay na gane Babu damuwa za,ayi yadda
kace, Yana Gama fadar Haka ya katse wayar tare da janyo gadon daga bayanmotar
asbitin,ya gara tayoyin gadon zuwa cikin dakin saiga saliha aciki a kwance ko motsi
batayi baywar allah
Tirkashi ana wata ga wata...
Abangaren Anisa da mahaifiyata kuwa"kullum cikin kuka hajiya adama take sakamo
kon abinda Habib ya sa akamusu abin yayi mata ciwo sosai ,koda barene akasaba dashi
yazama dan,uwa Bekamata ayimasa irin abin da akamusu ba, balle ita da take kanwar
mahaifinsa, tabbas bazata taba mantawa da wanan abin ba ,Kuma bazata taba yafe duk
wani cinkashi da akamata akan abin da batasan hawa ba batasan sauka ba, tana
tsaka da wanan tunannin taji sallamar su momy a asbitin da ita da juneid da Kuma
Habib da dady, karasowa sukayi kusa da inda gadon da aka kwantar da anisa take suka
tsaya tare da cewa "Mami ya me jiki" cikin masifa hajiya adama ta Mike tace
bansani ba"mugaye kawai bansani ba anfada muku muna bukatar sananuku ne bamaso,
kodai kunzone kukara tozartamu, to Bari kuji ni adama daya akemin ba,a nabiyu dan
Haka kufita kokuma namuku ihun zaku kashemin "yata, duk dama bansan dawace tsiyar
kuka zoba ,bansani ba ma zuwa kukayi ku karasa min ita, to wallahi munfi karfinku
namanmu daci gareshi ,kumatsa daga kan ta karnaje kunyi guzirin wani sharrin tafada
a fusace!!! Kwallar da ke kwance a idon dady ce ta karasa fitowa ya kurawa kanwar
tashi ido yace" yanzu ni Adama kike kora daga inda kike, karki Manta nifa
dan'uwanki ne ciki daya muka fito amma kidinga aybata dani da zuri,a ta akanme
zamucutar da ku" rufemun baki !!!!!!! Tafada tare da zaro ido,kamar wata aljana
tace ni zakayiwa dadin baki" au ashe kamanta ni din"yar,uwarka ce danka agaban
idonka yasa akadin ga ganamana azaba akan abin da bamu aykata ba ,narasa menayiwa
yaranka sun tsanemu to tunka fin ku kashemu nayenke alakar da ke tsakanin mu
daku ,dagayau ni Adama bani da kowa sai Allah sai Kuma yata daya da Allah ya bani
"ko a hanya kada kasake nuna kasanni kufita !!! Tanuna musu hanyar fita.... Dady
kam jin wadannan bakaken maganganun da take jifansa da sune yasa kansa yashiga
juyawa, yafara ganin bijibji" luuuu yatafi zai fada dasauri juneid ya rukoshi tare
da nufar hanyar fita daga dakin dashi, suma ragowar binsu sukai, suka shiga mota
suka dauki hanyar gida kowannensu jiki Babu kwari Amma Banda mutum daya shine Habib
da hakanma yafi masa dadi ,Sabi da dole yasan tunda dady rashin lafiyarsa tatashi
Babu yadda za,ai acigaba da bincike akansu ,harsai dady yasamu lafiya,kafin Nan
Kuma yariga da yagama bincikensa akan saliha ,yakasheta kawai Adawo musu da
gawarta, kokuma ya hullawa namin daji gawar sucinye....
11.....
****su juneid suna Isa gida ,sukayi parking din motar sannan suka fito, kama dady
yayi suka nufi part dinsa dashi Yana masa sannu,itama momy bayansu tabi har suka
Isa bedroom din dady aka kwantar dashi, bayan anwantar dashine juneid yasamu guri a
kasa yazauna ,yazubawa dadyn Basu ido ganin yadda zafafan hawaye kefita daga cikin
idonsa ko tsayawa basayi,ya kurawa saman silif Yana kallo, momy ce ta soma magana
ta n'a kallonsa tace "haba abban juneid meyasa wannan abin zai dameka harya kusan
tada maka da ciwonka ,Dan Allah ka kwantar da hankalin ka" uhm dady yadanyi
murmushi yace "Bazaki gane ba ,itafa din kanwa tace jinina wadda mukafito ciki
daya,tun kafin iyayenmu su rasu suka bani amanar adama to meyasa zatace kada nakara
nuna nasanta, meyasa inason "yar,uwata,dady yasa hannu ya goge hawayen fuskarsa
yacigaba da cewa "haryanzu adama yarinyace batasan komai ba ,batason ratuwar duniya
ba,kwai dai tana cikintane Amma idan Banda abin ta tayaza,ai tace ni alhassan bana
sonta meyasa kowani taji ya fadi wannan maganar ay ta karyatashi, juneid ne ya dafa
kafadar abbansa yace" dady ka kwantar da hankalin ka insha Allah mami zata
fahimceka kuma ni juneid inama ka alkawar da cewa duk abin da yake faruwa insha
Allah,komai yakusa zuwa karshe,Bari natashi na fita akwai abin danakeson yi yanzu,
dagamasa Kai kawai dady yayi yabi batansa da kallo har juneid ya futa...
Shiko Habib Yana ajiye su dad ya juya yanufi gidan su munir ,Yana zuwa adakinsa
yasameshi a kwance Yana danna computer, dasallama dauke a bakinsa yashiga ya zauna
a gefansa, yace "barka da wannan lokacin abokina,"barkadai" yafada atakaice, Habib
ne ta kara kallonshi yace "wai munir bangane maka ba kwana biyun nan,gaba kidaya
duk ka canza meyake faruwa ne?"yanzufa ko gurina bakason zuwa ,Kuma nasan kaji
batan saliha Amma ko kazo katayani jaje Wai meye hakane,yanzuma nazo kana wani
batarai" kallonsa kawai munir yayi ya kaudakai yace"wani lokacin kasan ni banason
kallon mugayen mutane masu bakin hali" au munir kenan nikake nufi mugu me bakin
hali" murmushi munir yayi yace"ni kaji nace Kai kawai dai n'a fadi magana tane ko
dai ka tsargu?" A,a ni bance maka ba kawai dai Naga ni kake kallo kake fadar
maganar Kane shiyasa nazata da ni kake"a,a ni bada Kai nake ba,n'a Isa nace maka
Kai mugune,ay idan kewawan hakayene asameka Habib,domin Dani,unka ba duk mazane
suke da irunsu ba, Kai dai Allah ya baka ko mutuwa Kai za,ayi maka kekkewan
zato"kukukut Habib yahadiyi yawu me dumi tare da saka hannu ya goge zufar data
karyo masa,sannan ya runtse ido tare da tunano yadda Babu tausayi Babu imani ya
kumawa baiwar Allah wuka aciki,Kai inama,ace yadda munir yakemasa kekkewan zato
Haka halinsa yake,ko Babu komai yasan ya more rayuwa cikin jindadi "Yana tsaka da
fadawa duniyar tunani munir ya dan tabashiyace" haba Habib ta Ina baka labari kana
tafiya tunani, nikasan ma wani labari danajiyo dazu agidan redio" a,a sai kafada
Habib yafada yace inajinka" uhm Wai wani mutumine kowa Yana masa kallon me nutsuwa
da hankali da Imani, ashe ashe ba Haka yakeba sumu,sumu mugun ice be, Yana da wasu
mugayan halaye irinna dabbobi, kanaji ko ayanzu zancen danake