Author : HAFSAT UMAR DANGORO Category : African Stories & Novels
cewa saliha" to to angama hajiya"yafada
tare da share zufar da ta karyo masa , murmushin gefan fuska yadanyi sannan tace
"Kuma ni dakai babu rabuwa Babu kishiya,mutu karaba, "dasauri ya amshe harda yimata
murmushin karfin hali yace Kuma takalmin kazaba, Allah ya jadaren hajiya ta Amarya
kuma uwargida a gidan Habib matata tadanan acikin mata, saliha dai bata saurareshi
ba ta shige daki tace inajiran yanzu kakawomin breakfast,angama ranki yadade
hajjaju"yatashi da sauri ya shige kicin....
Yana shiga kicin din ya samu guri ya zauna,ya saki kuka zuciyarsa kuwa kamar
ta fito waje Sabi da azaba"sai dayayi kuka me isarsa sannan ya share hawayensa ya
Mike,yashiga malkada kayanmuya,sannan ya tafi ya kunna gas yadora ,indomi domin ita
kadai ya iya girkawa, bayan yadora ne, ya dakko albasa yafara yankawa,Yana tsaka da
yankawa ya zaftare hannunsa,saiga jini ya fara zuba,Nan take hankalin Habib ya
tashi,ya shiga neman abinda zai kulle,can gefe ya hango wani audiga da sauri ya
dauka ya baybaye gurin da ita,sannan ya dakko albasar yashiga wankewa bayan yagama
ya zubata a indomin, yakoma gefe ya Dora da kukansa Yana tsaka da yin kukan yaji
kamar indomin tana kamawa,ay dasauri ya nufi gurin ya sa hannunsa wai zai sauke,nan
take ya kone,wata uwar Kara ya kwada ya koma gefe ya zauna yagama hucewa sanan ya
dawo ya dauki tumma ya sauketa, gabakidaya acikin plate ya juye aciki,sanan ya
kashe gas din,yasa cokali a ciki,ya nufi dakin saliha Yana shiga yasameta zaune a
kan kujera idonta n'a kan t v dake manne ajikin bangon dakin,karasawa yayi ya dora
plate din akan table din dake gabanta,sana ya koma ya dakko shayi hadin kauri ya
kawo mata,juyawa yayi zaitafi ya tsinkayo muryarta tana cewa "Ina zaka ay baka
gamaba dasaura,kashiga bedroom Dina ka gyramin kafin nagama inaso zandan
kishingida, batare da yace komai ba yazo ya huce ta gabanta zuwa bedroom dinta
yashiga aykin gyrawa.....
Yana tsaka da geran dakin saliha ta shigo ta kwaso masa fant da bureziya nata da
kuma Kayan bacci ta kawo maso ta wanke, Habib ne ya tsaya ya kafeta da ido can Kuma
sai yace "ay Naga da injin wanki a gidannan meyasa bazan ki wankeba sai ni
zanwanke, batarai tayi tace " to bazan wanke ba Kai nakeso kawankemin ko baza ka
wanke bane, jiki n'a Bari Habib ya karbi kayan ya ajiye yace ,"wa ni na Isa nace
bazan wankeba ni awa, "oho dai kuma wallahi da hannunka nakeso ka wanke,yau inason
ka wanke fant da bureziyar karuwa", a gigice habib ya dago ya kalleta yace " da
hannnafa kikace, Wai Dan Allah bakije islamiya ba,kinmanta namijine sama da mace,ko
kinason tsinuwar mala'ku ta tabbata akankine, ko dai kinmanta ni mijinkine" "au au
kamanta kace har aba da bazan taba zama matar kaba kawai ni baiwa ce ka auro,ba
matar aureba" to aynima yanzu bawa na aura ba mijin aureba, tanakai wa Nan amaganar
ta tayi taki ta fuce ta bar gurin, shiko Habib zama yayi ya zabga tagumi domin
yamarasa meyake damunsa,izuwa yanzu kam yayi danasani yafi a'irga tabbas bature
yayi gaskiya dayace idan kasan abin da zaka fada wa mutum,to bakasan irin abin da
za a dawo maka dashiba ,shiyasa ubangiji yakecewa,idan kaga bawana Yana aikata
barna to karka muzanta shi koka zageshi, idan zaka iya kayimasa addu,a...
MAR'ATUSSALIHA BOOK 2
7...
Tom bayan Habib yagama gyran dakin, ya kwashi wanki ya futa harabar gidan, zama
yayi ya soma wankin,yanayi Yana yayyatsine fuska shi adole me kyenkemi,jiyayi anyi
hown megadi ya bude kofa dasauri ya daga kansa ya zubawa get din ido gomin ganin
Wanda zai shigo, motar munir ce ,bayan ya shigo yayi parking,ya fito,karaf idonsa
ya Kai kan Habib da yake Daman wanki Yana zufa, abin mamaki yatsaya Yana kallon
ikon Allah,megadine ya karaso kusa da shi yace ranka ya Dade ,Naga katsaya kana
kallon yallabai,da sauri munir yace" kai uban me kake daba zaka karbi wanki kayiba
kabarshi Yana wanki sabi da bakasan aykinka ba" "wallahi naje nace yakawo nayi masa
ya dakamin tsawa har da cemin idan nasake ko kallon inda yake saiya koreni daga
ayki" munir besake cemasa, komaiba ya nufi inda ya ga Habib,Yana karasawa daf dashi
gamamakin sa saiga Kayan mata yake wankewa,cikin mamaki munir yace "Bross mezangani
Haka wayasaka wankin Kayan mata" shuru Habib yayi masa daga bisani kuma ya dago
tare da yimasa murmushin karfin hali yace "aykin lada nake..
"Aykin ladafa kace,Kai yanzu Habib duk ayyukannan na duniya da,akesamun lada
bazakai ba,sai dai wankin Kayan mata" "tukunnama Wace shegiyar ce ta saka ka
wanki!!!!! ?" Dasauri Habib ya rufemasa Baki ,Sabi da sauri ma harda kumfa ya
watsamasa a Baki,yace" Kai baka da hankali wacece shegiyar kakulla ba,acewa mutum
shege ,kadaina " baki da hanci munir ya saka Yana kallonsa cikin mamaki,domin shi
yanzu lamarin Habib tsoro yake basa,gaba kidaya ya zama kamar zararre gawani Baki
da yayi,ya rame,magana yafarayi yace",waini bross meyake faruwa ne gaba kidaya ka
canza "why" hmm kawai yace yayi masa banza yacigaba da wankinsa har yagama minir
Yana binsa da kallo..
Yana Nan zaune ya tsinkayo muryar saliha tana cewa "Wai baka Gama bane,tun dazu Ina
jira kazo ka gyra falonnan yayi datti,murya narawa Habib yace,Kiyi hakuri hajjajuna
sabi ,hudu nayi sabo da sufita sosai Bari nazo nayi sharar, ",
Munir dake zaune yayi mutuwar tsaye kallon abin yake kamar a mafarki yamarasa me
zauce,hakanne yasa yamike tsaye,ya kalli Habib yace,bross ni zan huce idan kagama
bautar kaje Momy na kiranka tace tun shekaranjiya take kiranka wayarka a
rufe,danhaka tana son ganinka,ni kaga tafiyata"sai anijima Jani talau, murmushi
Habib yayi yace ,"nafika ko agirin Allah tun da ni yanzu aykin lada nake,kaikuma
nasa ido "Yana kaiwa Nan a maganarsa ya shige cikingidan...
Yana shiga cikin gidan ya dakko tsintsiya yashiga share falon bayan yagama ya
shiga yin mopping sannan ya koma gefan kujera ya zauna ya huta...
Tashi yayi ya shiga bathroom yayi wanka ,bayan ya Gama yafito ya saka doguwar riga
milik me kwai da sheki,gaban mudubi ya karasa,yadan shafa Mai daga Nan Kuma ya fesa
turare ya fito,afalo yasameta a zaune,wannan karon ba kallo take ba karatun qur,Ani
mwgirma take cikin voice dinta me dadin gaske,karasawa yayi gabanta ya zauna har ta
kammala ayar karshe ashafin tacikin suratul Maryam" dago ido tai ta kalkeshi ko
kiftawa Babu tace "lafiya inazaka" kodai gurin Amaryarka zaka?" Tayi maganar tare
da sakar sa murmushi, murmushi ya danyi sannan yace"a,a momy ce takeson ganina"
kinsan dai n'a miki alkawarin babuke babu kishiya hajjajuna, "au hakane rom
shikkenan Adawo lafiya,kuma karka dade don inaso kazo ka doramin abincin dare" oky
badamuwa insha Allah bazan dadeba ,Yana gama fadar Haka ya Mike ya nufi hanyar futa
daga falon.
Bayan futar Habib saliha ce zaune tana tinanin irin abin da ya faru da ita da Habib
ayau tabbas tasan Bata kyauta masaba, Amma Babu yadda ta iya idan ba ita ba Babu
wan da zai iya koyawa Habib hankali,yanzu gashi ko banza ya Dan fara hankali,tafada
a kasan zuciyata tare dacewa hm yanzu muka fara wasan..
__________________________________________________malan ke zaune acikin iyalansa
Yana bawa matarsa labarin abin da yafaru dasu a gidan Habib ba Karan tsorata matar
malan taiba, sannan taci dariya,Amma Babu damar yin dariya yadda zata isheta,Sabi
da malan Yana zaune karyace tamasa rashin kunya, kallonsa tayi race " Amma dai maln
zaka koma kataimakeshi ko da Basu Gama barin jikinta ba,me Wai me kike nufi"? "Ina
nufin aljanun baiwar Allah Nan tana bukatar taimakon kafa malan "wani inkinganni
alahira kaini akai ay ni dazuwa gidan habibu har abada,ke koyanzu n'a hadu da
wannan yarinyar me suffar aljanu saina gudu wllhi,hmm dan bikisan wahalar danasha
bane..
To Habib Yana Isa gida, Afalo ya samu momy da juneid a zaune suna
magana,Yana shiga dauke da sallama abainsa yace "assalamualaikum "wa
alaikumussalam" momy ta amsa tare da cewa"Dan halaq yanzunna muke zancenka,nakecewa
juneid yaje yadubamin Kai lafiya"Murmushi Habib yay yace lafiya kalau momy kawai da
saliha ce take tsoron zama agida ita kadai shiyasa nake zama, Kuma dama yau ko Baki
kirani ba zanzo domin na gaisheki" jum Junaid yayi Yana tunani anyakuwa ba akwai
wata matsalar ba Amma dai shikkenan zai tambaya yaji, tashi yayi tsam ya nufi sama
tare dacewa Habib idan kungama gaisawa da mom inason ganinka," okay Babu damuwa
"yafada tare da zama a gaban momynsa yace " momy Ina wuni "lafiya kalau abee Ina
matar taka kunanan dai lafiya?" Lafiya kalau Alhamdulillah momy" yayi maganar tare
da sunnar da Kai.
Zama sukai shuru aguri,tako momy ta zubawa danan ta ido ganinn yadda duk
yacanza yayi Baki ya rame sai kace mejinyar kanjamau, gyran murya tayi sanan yace
abee a kwanakin Nan Ina fuskantar yanayinka Naga gaba daya duk ka canza meyake
faruwa ne? Banaso ka boyemin komai nifa mahaifiyar kace jibi fa duk yadda ka lalace
kamar ba Dana Habib ba ,kai da ake ganin ango acikin walwala da annushuwa, dakuma
farinciki ,har ma aga yayi kiba yacanza, amma Naga Kai angoncin naka nadaban ne
daga ace yau yau kana gadon asbiti, sai ace jibi baka da lafiya gata Kuma naganka
ajare" kwallar da ta cicciko ce a idon Habib ta karasa jubowa,ya bude Baki da
niyyar yin magana yasaki kuka kamar karamin yaro' Nan take hankalin momy yatashi
Dan tun da take da Habib rabon dataga yayi kuka har tamanta sai dai shi yabawa wani
kuka,Amma waiyyau shine agabanta take zubar da hawaye sabi da wani abun" habibu
fadamin meyake faruwane ? Momy najawo wa kaina masifa da bala'i naje na auro"yar
aljanu Dan Allah momy ki taimakeni kice Mata na mutu,Kinga saiki boyeni Dan Allah
kinji momy "what!!!!!! "Yar aljanu Kuma bangane inda kadosa ba Habib nifa banfahim
ci zancenka ba, kafahim tar Dani akan wa kake magana?" Momy akan saliha mana
matata, kiyi hakuri momy banfada miki abin dayasa na takura sauna auri yarinyar Nan
ba,kintina wata yarinya da tacemin kashin kare yafini daraja !!!!! "Eh natuna Habib
fahimtar Dani saime yafaru "momy nikuma shine naki hakura sai danasan yadda nayi na
aureta domin na Rama abin da taimin, Ashe aljana ce dan Allah momy kitaimakeni zata
kasheni wallahi ki boyeni kice na mutu" "kujini da shashan rayo sawani abu kake
kamar danshekara 10 d'Allah kadawo hayyacinka mana"Kai nake fadawa kabi duniya a
sannu, bakomai ne ake ramawa ba dagacikin imanin mutum, akwai haruri amma Kai
bazakaji fada ba ida anmaka ko, ka adole dangidan shahararren mekudi, to Bari kaji
abee anyi Wanda yaninka mahaifinka kudi mutumin da yakasance besan adadin kudadensa
ba,kafadamin ina yake yanzu Hatta iyalansa ina ganin basa aduniyar nan koda tashin
labarin su bakaji ayanxu habibu kaji tsoron allah sannan karike addu,,a idan Kai
Haka babu abin da zaisame ka"katashi kabani guri dan ni banyarda da wannan zancen
nakaba"... Tashi Habib yayi jiki babu kwari tanufi sama gurin yayansa juneid,Yana
shiga yasame shi zaune a gefan gado,ya kurawa computer ido, sallama yayi masa
sannan ya karasa yanemi guri gefansa ya zauna" yace " Yaya juneid Ina yini "lafiya
kalau Habib " yauwa Daman sonake na tambayeka kafin na zo katsina kacemin bakason
matarka Kai Sabi da daukar fansa ka aureta dan karama abin da taimaka" nadan zaku
iya shiryawa kukoma rayuwa cikin farinciki kamar kowanne ma'airata "bana tunanin
kaidai Habib zaka iya hakura kafadamin gaskiya menene yake faruwa agidanka" nasan
Haka kurum bazaka kizuwa gidaba bayan kasan bani da lafiya"bama hakaba jibi yadda
kabi karame kayi Baki ,Uhm. Habib yayi murmushi yace Yaya kenan bawani Abu bane
kawai dai itace take jin tsiran gidan shiyasa bana zuwa nake zama nakula da ita,
"dariyace ta kubucewa juneid wadda bemasan lokacin da tafito ba yace "Habib nizaka
rainawa hankali bayan nasan ka nasan halinka,Kai tunkafin kazo duniya nazo ta
narigaka shan iskar duniya idan zaka fadamin gaskiya kafadamin idan kuma bazaka
fadamin ba gahanya nan Allah ya Kara dankon kauna da kurawa "Allah ya barku tare
har'abada " what!!! ba aminba Yaya "wallahi sai yanxu natabbatar baka Sona Kai
makiyi nane " bangane nu makiyinka bane addu,a fa namaka me kyau"to indai wanan
addu'ar ce banaso ni dazama da waccan aljanar har abada bazamu taba zama guri
dayaba ,Kai bakasan akan Kaya nakeba shine har dacewa Allah ya barmu tare ,badai
Nina wallhai sai dai inkai allha ya barku tare.....
Hhhhhh juneid yayi dariya yace uhm ni dama nasan akwai abin dayake
faruwa ,allah sarki dan,uwa kayi Shirin mugunta Kuma abin yakare akanka ,kaikana
abinka Ashe aljana ka auro,to Allah ya kiyaye gaba " au yanzu ya juneid abin da
zakace kenan kanagani fa yanzu jirana ma take na koma na Dora mata abincin dare
yakarasa maganar kamar zaiyi kuka, "hm Habib ni kam babu abin da zan iya cemaka
yanzu Dan komai ya faru da Kai kaka jawa kanka, abun da zance maka shine kacigaba
da hakuri har lokacin da Allah zaisa tagane gaskiyar kaimijinta ne tafara maka
biyya"me wai ni inzaman aure da karuwa allah ya kiyaye inazauna da ita zaman aure
ni ka batamin rai wallahi Kai kullum nazo gaisheka sai ka batamin rai,Yana gama
fadar Haka ya Mike tsaye yanufi hanyar fita....
********************************abangaren anisa kuwa tanemi yafiyar mahaifiyar
ta sunciga ba da zamansu subiyu rayuwarsu sukeyi cikin farinciki da annushuwa
musamman yadda hajiya adama taga "yar Tata ta hakura da auren juneid da Habib sai
itama hankalinta ya kwanta.
To yau kamar kullum suna zaune a falo suna Hira Anisa ta kalli mahaifiyata tace
"Mami "naam Anisa"inason nakoma school nayi digiri tunta dai yanzu Naga ba aure
zanyi ba, inason asamamin konda makarantar kwanace a zariya ko kano naje nayi
digiri, Ina tinanin zanfi maida hankali nayi karatu can Kuma hankalina zaifi
kwanciya, shiru hajiya adama tayi,nadan wani lokacin daga baya kuma ta dago ta
kalli anisa tace" Tom shikkenan anisa zan duba magani zuwa gobe idan abin zaiyuwu"
murmushi anisa tayi tare da cewa Allah ya nunamana goben darai da lafiya....
8..
__________________Tom bayan Habib ya Isa gida,azaube ya samu saliha ta sha kunu,ta
hade girar sama data kasa Tana jiran dawowar sa,Yana shiga yayi sallama" shiru bata
amsaba saima masifa da ta fara masa da kwandon bala'i tace"Habib Ina kaje ,banace
kadawo dawuri zaka doramin abincin dare ba,saibi da tsabar ka ajiye shanyani sai
karfe ,10 na dare zaka dawo Ina katsaya" Tana magana Tana hura hanci kamar wata
uwarsa,Habib kam zuwa yanzu yagama tsorata da lamarin saliha, sannan ya fahimci
inda ta dosa,sotake kawai ta kashehi ta huta,to ko indai hakane maganarsa gwara ta
kasheshi kwai ya bi masoyiyarsa hankalinsa yafi kwanciyar" saliha kuwa ganin yadda
ya tsareta da ido Yana kallonta ne yasa tace" Habib tunanin mekakeyi da bazaka iya
cemin nayi hakuri ba!!! Rausayar da muya yayi yace"Dan Allah kiyi hakuri hajjajuna
wallahi ban iya girki bane,shiyasa naki dawowa da wuri,ni abu buyu naiya girkawa
daga taliya sai indomi, bayannan ban iya komai ba, Dan Allah kiyimin afuwa kafin
inshigo gidannan sai da na tsaya gurin wani maisai da abinci natambayeshi idan zai
koyamin,kuma yace zai koyamin gobe na fara zuwa..
Memakon wannan abin da yayi yasa saliha ta tausaya masa ,saima ta juyar da kanta
gefe tasaki murmushi tace "Allah ya kaimu, oya muje mu kwanta,"agigice Habib ya
dago ido ya kalleta yace,"mukwanta Kuma Aina zan kwanta tab Allah ya kiyaye na
kwanta dake"
"Au Allah yakiyaye ma zakace "banace kadainamin taurin kaiba,saikuma na dagaka
na doka dakasa kafi kowa zama abin tausayi"to ba irin kwanciyar aure nake
nufiba ,Wace zata Kwanta da Kai Allah ya kiyaye Nima na kwanta da Kai gado daya,Kai
da ba mijina ba kaifa bawanane ,yanzumma bautar zamuje kayimini bawani abuba ay
bacci agidannan kadainashi, zamuje ka dauki mifici kamin furfita harnayi bacci"
"Furfita fa kikace, naga akwai fanka adakin sannan akwai AC meyasa bazaki
kunnaba "
"Banyi ra,ayiba kuma bansaba da fanka ko AC ba gidanmu babu damifici nake fifita
agida Dan Haka Dole kamin furfita da wayasa kaje hargidan iyayene ka dakkoni dan
bazance auroni kaiba, idan da kasan bazaka jurewa wahalaba da baka auro "yar
talakawa ba, kaje ka auro "yarmasu kudi,wadda ubanta ya Tara,Kai nifa bada banba ma
sainace aje ayo odar sauraye akawomin sudinga cizona sabi da nasaba kwana acikinsu,
wallahi ko kazaba na kaika dakin kiwona da kasa Aka ginamaka/ kokuma ka kwana
kanamin furfita,zabi daya...
Runtse ido Habib yayi ya bude tare da furzar da iska daga bakinsa, ya daga Kai ya
kalli saliha wadda ke tsaye ta kuramasa ido Tana kallonsa Tana hura hanci,uhm yayi
murmushin karfin hali yace" shikkenan naji Zan kwana adakin can Amma ni bazan kwana
inamiki furfita ba" oky tafada tare da juyawa ta dauki Kee din dakin tafita Habib
Yana gaba Yana binsa abaya harsuka karasa wannan dakin me duhu Wanda Habib yasa Aka
Gina domin kiwon saliha ,bude dakin tayi yashiga,sannan ta kalleshi tace,"to
habibty na sai dasafe ko "batare da tajira me zaiceba ta datse dakin da kwado ta
juya jiki Babu kwari tashiga part di ta,daki tashiga ta dakko fulo tadawo falo ta
kwanta ,runtse idonta tayi,amma ta kasa bacci,kawai sai ta Mike Zane ta hada Kai da
gywa tasaki kuka,tana tunanin irin halinda habib zai shiga awannan dakin mekama da
kurkuku,Harcikin zuciyarta tana tausayinsa Amma Babu yadda ta iya dolene ta
koyamasa tarbiya tun da tafuskanci islamiya bata ratsashi ba...
Shiko Habib can kuryar bango ya nufa ya rakube Yana rawar sanyi, sabida lokacin
sanyine, gashi Babu abin da zairufa ga sauro sun dameshi, abubuwa sunmasa yawa ga
futsari yanaji Babu bandaki balle yashiga yayi abinka da be sababa duk inda sauro
ya cijeshi saiya kunbura gaba kidaya jikinsa ya hadu yarure koina sosawa yake Sabi
da azaba , Kai na takaicemuku karshe dai Habib sai a wando yasaki futsarinsa,
Daman ga lokacin sanyi gakuma jiki ya jike sharaf abin ba,a magana kamar yadda
Habib yaga dare haka yaga Rana koda sodaya bai runtsa a dakinnan ba yayi kukan
xuci yayi nafili har yagaji, wannan lokacin be ya fahimci bakain da saliha take
shiga idan ya kulleta a dakinnan, tabbas yayarda ya azaftar da ita,Ashe shi yanacan
Yana bacci hankalinsa kwance ita Kuma tna Nan ko baccinma batayiba,Kuma ahaka
zaisata shara da alki da sassafe tabbas idan benemi yafiyar wadan da ya zalinta ba
sai Allah ya saka musu da gaggawa, Haka dai Habib yaciga ba da tunaninsa dakuma
danasa ni har gari yawaye.
. Saliha kenan baiwar Allah Ashe itama kamar yadda Habib be bacciba haka itama
batayi Shiba ,Sabi da tsananin tunanin halinda habib yake alokacin,domin ta San
irin masifar da bala'i n da Tasha acikin wannan Dali ta wahala sosai,to itama kenan
da tasaba da wahala balle kuma Habib da yatashi cikin gata da daula.
9..
Mikewa tayi tadauki Kee din ta nufi dakin,bayan ta karasa ta saka kee ta bude
kofar, sannan ta shiga "innalillahi wa'inna ilaihirraju,un"ta furta tare da yadda
mukullum ta shiga cikin dakin a guje, inda Habib yake ta nufa,tashiga jijjigashi
Amma Habib shiru kakeshi baya ko motsawa, jikinsa kuwa duk cizon sauro abinka da
farar fata jikin yayi rudu rudu ga zarnin futsari ga wahalar da yasha, cikin sauri
saliha ta kofa part dinta ta be bo ruwa ta yayyafa masa,sai gashi yaja wani dogin
numfashi me karfi"tare da bude idanunsa wadan da suka kunbura sukayi jajur Sabi da
azaba, saliha ya kurawa ido yana kallo tsananin tashin hankalin da tashiga Sabi da
shi" itako saliha