Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Mar Atussaliha Book 1 and 2 Takun Farko Complete Hausa Novel by Hafsat UMAR Dangoro

Author :  HAFSAT UMAR DANGORO Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 11

6K to 9K   out of 31.5K words

fadawa wadannan maganganu''hmm Nagode ''kuma kije wallahi Indai
rashin kunya ce'' jurar ki wataran sai ansamu wan da zai koya miki hankali'' ki
rike wannan a zuciyarki'' domin nasan komai daran dadewa zakituno da abin da na
fadamiki'' tana gama fada mata haka''ta shige dan kwangon dakinsu'' ta barta a
tsaye tana huci'' zama tayi a gurin ta saka kuka'' tana ta tunane tunane kamar
wadda zatai hauka''.... Atakaice dai saliha anan gurin ta kwana dan ko runtsawa
batayi ba sai dai bacci barawo idan ya dauketa''...


To washe gari su baffanta suka yo sammako suka taho daga kauye'' tun karfe 7suka
taho basu isoba sai misalin karfe 2na rana '' suna zuwa suka tarar da har magabatan
Habib su iso harma da Habib din'' yasha farar shadda'' sai washe baki yake da alama
dai akwai wata makarkashiya dayake kullawa' masha Allah yau take ranar juma'a inda
ake shaida daurin aurena Saliha Usman aliyu'' da angonta Habib Alhasan madaki''akan
newa dubu dari 2''lakadan ba ajalan ba''masha Allah.

pege 9

Lokacin da sanar War daurin hauren tazo kunnen saliha'' sai da ta gigice'' dajin
sunan habib ''hakama Hafsah wadda tasan komai a tsakaninsu'' innalillahi
wainnailaihirraju un'' Hafsah nashiga uku'' Habib ne ,nasan ya aureni ne domin ya
wulakanta rayuwata innalillahi wainnailaihirraju un... Tana tsaka da yin salatin
nan sai ga baffan ta yashigo'' yana zuwa yace'' Saliha ,tace na'am baffa'' maza
kije mijinki yana son magana dake'' jikin Saliha na rawa zuciyar ta na dukan
uku'uku ta mike jiki babu kwari'' tafuta kofar gida'' tana fita sukayi idon hudu''
dashi ya sakar mata wani mayau darin murmushi wan da ita kanta batasan me murmushi
yake nufiba'' ahaka dai ta daure ta kara sa inda yake''ta tsuguna zata gaisheshi
yayi saurin dakatar da ita yace'' au ashe daman kina da tarbiyya'' ay nazata iya
masu tarbiyya ne suke iya gaishe da wan da kashin kare ya fisu daraja'' walhi sai
na koya miki tarbiyyar da kika yi missing dinta a baya, sai na nuna miki Ni Habib
dan duniya ne nafiki duniyan ci'' kuma daga rana irin tayau kifara irga'' ranakun
mutuwar ki'' Ni bani zankasheki ba amma wahala zata kasheki'' yana gama fadar haka
yayi tsaki ya ce karuwa kawai me bin mata'' daganan kuma yasa hannu a aljihu ya
debo bandir din kudi ya mika mata ''dakamar bazata karba ba '' sai tajuya taka duk
idon mutane akansu yake'' hakan yasata sa hannu ta amsa'' ta juya zata tafi'' yace
kuma ki shirya anjima za,a zo adaukar mini ke amarsuna ,yayi murmushi ya kashe mata
ido daya ya bargurin''....

Tsayawa tai tabi bayansa da kallo''tana nazarin abin da Habib zai iya aikata
mata'' tabbas tun yanzu tafara gasgata maganar Safiyya''datace in dai rashin
mutuncine zata samu ubanta ''ay ko gashi tasamu tunkan taje ko ina.

Gajiya tai datsaiwa a gurin don idan tacigaba da tsayuwa hawaye zai iya zubomata
abin da yafi sauki ta koma gida tanemi shawarar hafsa''

Shiga tai gidan'' ta samu hafsa'' a zaune ta yi tagumi''karasawa tayi ta kamo
hannunta suka fito waje'' tafiya suka shigayi har sai da suka isa wani lungu inda
babu kowa sannan saliha tace'' Hafsah nashiga uku'' bana fadamiki ba''Habib bazai
aureni ba sai da wata munifar'' dan Allah ki bani shawara'' yazanyi ne'' hafsa''
kodai na gudune?" Me ki gudu idan kika gudu ina zaki'' haba saliha kidai sake
tunani'' uhm,to ya kikeso nayi dan Allah Hafsah ki taimaka kifadamin yazanyi'' idan
kuma bazaki iya taimakona ba gwara na gudo'' don wallahi Habib bazai barni ba
kasheni kawai zai'' hmm saliha ,naam hafsa'' tayi magana cikin kaguwa'' inason ki
saurareni kiji mezan fada miki'' wannan fa abu da kika ga ya faru ''daman can Allah
ya tsara haka saita faru arayuwarki ''allah ya tsara dole sai kin zama matar Habib
''karki wani saka damuwa a zuciyarki kawata'' inason ki dake kamar yadda nasanki
baki da tsoro to inason idan Habib ''ya cemiki (A)kicemasa (Z)don billahillaxi da
alamun Habib akwai abin da yatama''kada kiji wani tsoro'' wuya bata kisa'' ko da
kin mutu'' a dakin mujinki kika mutu ba adakin wani katon ba''yanzu idan kikace
zaki gudu'' bafata nake miki'' ba ,ki hadu da wasu mugayen suyimiki fayde ko su
illata ki'' inga ya sun cuceki'' to ko kinga da wannan gwra zaman gidan Habib'' ko
banza zakici ki sha'' kimore'' habama sai na koyamiki abin da zakiyi sai kace ba
kike islamiyya ba ''kinga mukoma gida kada azo ana nemanki'' .uhm saliha tayi
ajiyar zuciya ta goge hawayen ta'' suka koma gida,...


*Anisa Anisa, meyasameki haka'' fadamin kukan mekikeyi'' yanaganki da jakar
kaya niki__niki kodai fateeman ce ta koroni?" Anisa a guje tasaki jakar ta fada kan
kirjin Hajiya Adama ta rungumeta'' tasaki kuka me sauti''zuciyarta na tukuki''
hankalin adamane ya tashi sosai'' tarasama mezatai'' bakinta har rawa yake daker
ta iya buda baki tace'' wai Anisa lafiya me akai miki'' kifadamin kinkasa magana''
ko wani abunne ya samu Habib''...?
Mami'' sun cuceni'' sai da suka bari nayi nisa akan soyayyar shi'' Meyasa
za,ayimin haka ''mami menarasa na ''ya mace''mene bani dashi?" Dallah Malama ki
fahimtar dani meyake faruwa ban gane ba'' suwaye'' suka cuceki'' zaki fadamin ko
saina ci ubanki a gidannan'' mami yau aka daura auren yaya Habib da wata, what
''hajiya Adama ta zazzaro ido tace'' kan kutumar uban can'' ammafa za a maimaita
yakin Badar '' me aurefa wai dagaske kike ko dai fada kikayi Anisa ,anya kuwa kinji
daidai'' za,ayi auren Habib dinne bansani ba''wallahi Allah mami da gaske nake
miki'' tarkashi ayko yau '' za ayi yakin duniya a gidan Alhassan'' Ni za aywa
tijara '' Ni Adama '' toni ba,a taboni bama hawa nake ballantana an tabani'' jar
uba'' Anisa'' huce'' muje gidan wallahi basu isa su wulakanta min zuri aba'' nafisu
dabbanta wallahi marabar mu da tinkiya wajan hauka'' Ni mutumce'' ita dabba, mota
suka shiga ''suka figa'' har cikin gidan su Habib'' ko motar bata tsaya ta gama
parking ba ''tafigi hannun Anisa tayi cikin gidan tana kwallawa Fateema'' kira''
kina ina bakar munafuka'' Fateema'' kufito ayita ta kare'' don wallahi yau
''mutuncin ma bansan shiba'' Fateema''munafuka ki fito ko na shigo ciki na koya
miki hankali...


Pege 10

Dasauri Hajiya fateema ta fito ''tana bata hakuri dan tasan za,a tuna''dan Allah
kiyi hakuri Adama abi abun asannu'' bazan bi asannun ba'' anki abi adun asannu'' Ni
zaku raina wa hankali'' walhi daidai nake da kugun ku daga ke har dannaki''
''yartawa zaku wulakan ta'' to wallahi ko yasaki'' waccan ''yar matsiyatan ya auri
Anisa,ko kuma yanzu na nunamuku Anisa na da gata'' aykin banza sai da kuka bari ta
gama zama ta wahalar da kanta taki kowa tace saishi''sanan kawai rana daya ku aurar
da danku ga wata.....

Dan Allah Adama kiyi hakuri''komai kikaga yafaru akwai sila''daman Allah ya ruga
ya tsara Anisa ba matar Habib bace'' dallacan tafi can''kirifemin baki''ay komai
daman yafaru akwai sila Kuma kece'' idan da kince ''yar,uwarsa zai aura ai da bazai
kiba'' sabo da tsabar bakin hali irin naku na ''yayan talakawa'' ay tun da yaya ya
auro diyar talaka munta samun talakawa a zuri'ar mu'' ke adama !!!ya daka mata
tsawa ya hade rai'' tare da karasowa gurin yace'' Adama matar tawa kike fadawa
wadannan maganganun?" Ashe dama baki da hankali'' haba yaya ni baka ga abin da
tamin ba'' sabo da tsabar rashin adalci tasan Anisa nason Habib amma takasa hanashi
auren waccan ''yar talakawan''Ni ban ma yadda da wanan matar takaba idan aka bibiya
ma ''yar uwasu ce'' dan nasan kaf danginsu babu masu ku 蓷 i bal...... Aykafin ta
karasa maganar ta taji saukar wani gigitaccen mari a kuncinta'' hagu da dama'' Waye
Abba ne'' afusace adama ta daga ido tana kallonta, dan tun da take da dan,uwanta
betaba sa hannu ya mareta ba sai yau'' jiki asanyaye'' tace yaya Ni kamara''?" Akan
na fadi gaskiya'' namareki Adama kiyi duk abin da zakiyi''akai badai akan Habibu
bane ''yace bayason Anisa ''gawadda yakeso sai na hanashi abin da yakeso ''to bari
kiji ko mace an daina yimata auren dole ballakuma namiji'' namijin ma dana '' idan
yazama dole sai jinina zata aura''tajira dawowar juneid muddum ya nuna yana sonta''
nikuma na amince zan auramata dana juneid''

A gigice Fateema''ta kalli Abba tace'' alhj juneid fa kace'' habibu ma be aure
Anisa ba sai juneid da ya shiga gari ya zagaye kasashen ketare yaga ''yanmata kala
da ban da ban'' banjin zai amince da auren Anisa''

Hajiya Adama kam bata karacewa komai ba''taja hannun Anisa'' suka fuce daga gidan''

Tun da suka koma gida Adama ke kaiwa da kawowa'' tana tafa hannu, Anisa na zaune
agefe tana bin ta da kallo'' jiki babu kwari Anisa tace dan Allah mami kiyi
hakuri''nasan duk wannan abin Ni naja miki ''har Abba ya mareki''idan akan yaya
Habib ne na hakura, no Anisa'' badai ance za ajira dawowar juneid ba '' mujira ya
dawo dan wallahi bazakiyi dakon banzaba'' A,a mami bana tunanin ya juneid zai
soni'' tun da Habib besoni ba juneid bazai taba sonaba , saboda yafi Habib komai na
rayuwa ''hatta kyau da duri da tsarin halitta Habib mummuna za,a kira shi agaban
juneid ''kuma wasa kukeyi''kawai ku bari na hakura'' walhi bazai yuwuba '' don
yanzu aka fara wasan'' dole sai Habib ko juneid ya soki...


INDIA

Zaune yake akan wata blue din kujera ''yar madaidai ciya, me masifar laushi''
hannunsa douke da jarida karama'' ya kuramata manyan idanuwan sa masu kama da na
mage'' zama nayi na karemasa kallo tun daga kansa har 茩 afarsa , farine tass kana
ganinsa kaga balarabe sannan kuma bature'' yana da dogon hanci'' tamkar biro'' don
tsayi da tsini'' labbn sa ko''in da kasan sweet sabo da laushi'' gasu jajur'' kanan
yana yin zanan love'' masu kyau ''gawani gashin baki da gemu da ya karawa fuskar sa
kyau da kwarjini'' 茩 wayar idonsa ba baka bace'' blue color ce'' me dan rashin
farifari acikinta'' gashin kansa yana da tsaya'' baki me laushin gaske sai sheki
yakeyi'' yasha gyara '' dogone sosai ,mutum me kyau da kwarjini ga haiba''suffar
jikinsa me kyau ce'' sana. Duk gabansa a murde suke, kirjinsa ma kadai abin
kallone'' wow masha Allah ya hadu'' komai nashi me kyau ne inda kasan shiyayi
kansa'' ayadda na fasalta mukushi kenan amma a zahiri yafi hala kyau'' dan narasa
tayadda zan kwatan tamuku kyaun da Allah ya masa.



Pege 11

Hello , my name is isha'' duk maganar da take shi dai juneid idon sa na kan
jari da be dago'' ya kalleta ba'' har sai da taga ji da magana ,azafafe ta fisge
jaridar tace'' juneid'' magana fa nake maka'' kansa ya dago a hankula ya zuramata
wadannan manyan idanuwan nasa mekama da na aljanu'' ya watsamata harara''jiki na
rawa ta mika masa jari dar tace Am sorry '' banza ya mata bece komai ba ya karbi
jaridar sa ya mike ya bar gurin'' bayansa tanufa da kallo'' tare da runtse
idonta'' tace wow'' Juneid is very very beautiful'' atake a gurin ta hadiyi wani
azababben yawu jikake kukukut'' ta sharce gurin da ya tsatstsafo mata tace Juneid
sai na samu abin da nakeso '' kajira dawowata'' tana gama fadar haka ta bargurin...


Shiko juneid'' gurin Parking ya nufa'' zai shiga motarsa'' da sauri aka budemasa
kofar tare dacewa'' ranka ya dade ''allah ya karamaka lafiya danisan kwana'' ameen
kawai yace'' yashiga motar'' shima wan da ya bude din wata motar ya bude ya shiga''
sanna ragowar masu gadin juneid suma suka shiga tasu motar'' suka sakashi a tsakiya
suka bar gurin'' tafiya sukeyi sosai'' ba su tsaya a ko ina ba'' sai bakin wani
katafaren gida'' wan da Ni kaina nayi tunanin gabaki daya garin ne a gida Daya''
ashe gidan mutum dayane wato Juneid'' me gadine ya wangale musu get suka shiga''
masha ALLAH'' iya kacin gurin ajiye motocin ma abin kallone'' harabar gurin na
dauke da fulawoyi masu kyau da daukar hankali'' musamman ma gefan da ruwa yake sama
da kasa ''yana gudana a tsakiyar gurin'' bakaramin kyau yayiba ruwan na da launi
kala biyu'' launin farko farine na biyu kuma blue'' dasauri daya daga cikin masu
tsaronsa ''ya fito ya bude masa murfin motar ya fito'' yana tafiya kamar bazai
yitaba sabo da tsananin isa da kasaita'' har ya isa bakin kofar falon'' gidan'' tun
kan ya karasa kofar ta bude'' kofarma kadai abin kalloce''domin juyi takeyi tana
haske tana walwali'' kamar dai wadda aka sa mata wayarin a ciki'' shiga yayi ''ya
dan tsaya kadan ''sai ga wani basamu dan mutum nan ya karaso'' in da yake ya zame
rigar dake sanye a jikinsa'' yana cire masa ya tsaya cak'' tare da cewa'' Barka da
isowa yallabai'' daga kai kawai Juneid yayi ya huce'' wow masha Allah'' tarkashi
idan kaji ana cewa aljannar duniya to ga ta a cikin gidan Juneid'' falon'' gidan na
dauke da kujeru kala biyar'' na farko fararene inda suke a hannun yamma'' nabiyu
kuma milik inda suke a arewa '' na uku kuma blue color ne suna a hannun gabas'' na
hudu kuma Pink color ne suna a hannun kudu'' sai goldin me kelli da wasu fulawoyi a
jikinta'' ita kuma tana a tsakiyar kujerun'' kunga idan aka lissafa kujeru 22 ne a
tsakiyar falon'' gidan ahakama akwai fili'' sai wata plasma dake makale a jikin
bangun dakin ''in daka san allon karatu haka ta kusan cinye bangon dakin'' daga
gefan ta kuma flawar ce fara me ratsin ja a jikinta'' sai daya gefan kuma
matattakala ce wadda zata kaika zuwa saman bene '' gidan yana da hawa 25 wan da
kowanne daga cikin an kawatashi da duk wani dukiya na more rayuwa'' a gaskiya
tsayawa fasalta muku yanayin gidannan'' sai muahekara muna yin abu Daya'' amma
kowacce nabata dama ta fasalta shi a cikin idonta'' ta bani labari...

Tom bayan juneid ya hau matattakalar tsayawa yayi kawai akai'' sai gashi a saman
benen'' kai jama,a iya tsaruwar falonnan tafi takasa tsaruwa''karasa wa yayi ciki
da sauri'' wani mutum mesanye da jan kaya ya karaso'' ya zare masa wani don dake
cikin jikinsa ''yabarsa daga shi sai turoza'' na maza'' daga nan kuma ya daukeshi
be tsaya ko inaba sai bathroom'' yana ajiyesa ya fito ya jamasa kofar ya tsaya''
sai da yayi kusan minti 40 kafin juneid ya danna wata kararrawa ta sanarwa''
dasauri wannan mutumin ya juya'' ya dakko juneid daga bathroom'' ya lullube sa da
wani milik din tawul ''sannan ya daukeshi'' betsaya a ko ina ba sai bedroom'' yana
zuwa ya dora shi a kan kujerar dake gaban mudubi'' sannan ya fita''yana fita'' sai
wani ma ya shigo shikuma bakin kayane a jikinsa'' dasallama dauke a bakinsa
yashigo'' yace Allah ya kara lafiya yallabai'' sannan ya kama gashin kan juneid''ya
shiga busar masa dashi'' sannan ya debi mayuka iri daban daban ya shaida masa
akalla ''da nan kuma yadakko wata na ura'' ya dora masa a kansa ''bayan minti 3ya
ciremasa ''saiga kanya koma kamar namace'' sai shainin yake'' manjiki ya dakko ya
shafamasa a jikinsa'' bayan ya gama ne ya dauki juneid'' ya dorasa a kangado ya
jamasa bargo'' sannan ya tsaya a bakin kofa'' kamar wani sakago yana jira yayi
bacci ya tashi ya saka masa kaya''

TURkASHI'' tashin hankali wan da ba,a samashi rana''anyako juneid zaiso Anisa''馃
wanga mutum akwai iyayi da girman kai aradu.


'' SALIHA''

Tun da gari yafara duhu saliha tabi ta daga hankalinta ''tana ta kuka'' dontasan
wallahi me rabata da Habib sai Allah ''ya zatai tun da kaddarar tace auren Habib''
bayan sallar magariba motoci kusan guda 34su kayi parking a bakin layinsu''
saliha'' suna jiran afito da amarya'' ita ko saliha tana zaune a gaban
mahaifiyarsu''tana yimata nasiha akan zamanta kewar aure'' bayan angama yiwa saliha
nasihane'' aka fito da ita tana kuka'' Hafsah da Safiyya na rike da hannunta'' har
suka sata a mota'' ragowar mutanen gidan da makota suma suka shiga motocin aka tafi
kai amarya'' gaba daya ragowar motocin gidan amarya suka huce'' Amma banda motar
amarya da aka wuce da amarya gidan su Habib'' suna isa aka bude get'' sanan aka
fito da amarya '' zuwa ciki'' afalo'' suka samu su Hajiya fateema da ''yan,uwan ta
dana abba'' suna ta shewa'' karasawa akai da saliha gaban momy da Abba'' sukayi
mata nasiha me ratsa jiki'' daga nan kuma Abba yayi musu addu'ar Allah ya basu
zaman lafiya, sanan aka fito da amarya'' aka kaita gidanta da ke can cikingari'' ,
babu laifi gida yayi kyau ya tsaru'' babu abin da zamu ce sai dai addu,ar Allah ya
san ya alkairi'' bayan anje an ajiye amarya a kangadonta'' ango ya shigo da shi da
munir '' daga nan kuma kowa ya watse hatta munir bayan ya bawa Habib shawara akan
ya sassauta wa saliha'' muguntar da ya shirya mata''ya tafi''


Gida dai yazana daga saliha'' sai Habib kadai a gidan'' tana zaune a tsakiyar gado
fuskarta a rufe'' Habib ya funcike mayafin yace'' to uban mene kike kunshe a
mayafi'' kamar wata ta allah'' Ni dai kinsan babu abin da zanyi da kazamin jikinnan
naki'' wallah saina koya miki hankali '' kinga wancan dakin dana ce ayimin domin na
yi kiwon kaji aciki'' to wallahi ke zan yi kiwo aciki don kece kazartawa'' karuwa
kawai'' yayi tsaki ya futa.....
TURkASHI'' Habib waikai zuciyar mece dakai.

MAR'ATUSSALIHA
Pege 12

To saliha kam'' tana zaune har misalin karfe'' 12 na dare amma babu ango babu
labarinsa'' ganitai bazata iya jurewa ba,hankan yasa ta mike '' daga kan bed din''
ta fito falo''zaune ta sameshi''yana danna waya yana shan faro'' cikin tsiwa da
rashin kunya ta karasa gabansa ta rike kugu tace'' malam wai mekake nufi dani?"
Tafada tana murguda baki'' banza yayi mata bece komai ba'' ya cigaba da shan
ruwansa'' a fusace ta sa hannu ta fusge robar faron''tayi wurgi da ita gefe tace''
sai kafadamin dalilin da yasa ka aureni'' ran Habib ne ya faci sosai'' idon sa ya
kada yayi jajur'' juciyarsa na bugawa sama sama'' yamike ya tsinke ta da wani
gigitaccen mari jikake tasss''sai ga saliha akasa'' tamarasa a wace duniyar take
tsabar zafin marin'' ran shi a bace ya nuna ta da yatsa yace'' tambaya tamakike
Meyasa na aureki'' hmm to bari kiji Ni Habib ''bazan iya zaman aure'' da karuwa
kamar kiba'' abin da tasa na aureki'' domin na koyamiki hankali danna ga iyayenki
basu koya miki tarbiyya ba'' kada kisa a ranki wannan aure mukai''no bazan taba
zama da karuwa amatsayin matata ta sunna ba''idan akwai yarinyar da natsana a
duniya be huce'' keba saliha'' ancuceki da har iyayenki suka samiki sunan salihai
baki dace da sunan ba '' irinku tantiran ''yan iska sunan kafurai yacancanta a saka
muku'' tunda kunfita daga muslinci'' banza karuwar titi kawai wallahi duk ranar da
wannan kazamin hannun naki ya kuskura ya sake zuwa inda nake'' saina nunamiki
asalin ko Ni Habib wane''kuma kishirya daga gobe'' zaki fara aykin da kikazoyi''
sayanki nayi kedin ayanzu baiwata ce'' gobe kinga dakin kiwan kaji nanne
makwancinki'' na bangaren nawane ''meststssss yayi tsaki ya harbeta da 茩 afarsa ya
huce'''

Yana tafiya saliha ta 蓷 ora hannu aka ta saka ihu'' abin tausayi tana cewa nashiga
uku Ni saliha menayi wa Habib yakeneman kasheni'' shin yaushe nazama karuwa'' Allah
kana gani kuma kasan komai kai zaka fiddani daga zargin da yakemin''

3 / 11