Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin KENAN 2 HAUSA READ Complete Hausa Novel by Sumayya Abdulkadir Takori

Author :  sumayya Abdulkadir Takori Category :  Romance

Chapter   9 / 11

24K to 27K   out of 31.5K words

bata nuna hakan ba. Da tace hakan, sai shima ya kai duban sa ga t.vn sannan ya dauke kai yana cigaba da murmushi. Sai a lokacin ya samu yin magana don kare kansa da yarda da wasu kalubalen nata.
 Sana o i na kokarin taimakon kai da kai ko na gado a kauyuka dole ne Amina, ba dole saida taimakon gwamnati ba. Bazai yiwu ace gwamnati ta karade al ummar jihar ta bakidaya ta iya baiwa kowa dake jihar sana a ita kadai ba, dole sai da kokarin sana o i na taimakon kai da kai al umma zatayi surviving. Don haka ki cire wannan daga lissafi. Sauran abubuwan da kika zano duk suna kan hanya kuma nagode da wannan kyakkyawan tunasarwa taki. Insha Allahu zaki ga chanji .
Ya mike ya nufi kofa yana fadin  na barku lafiya, mu kwana lafiya, Allah ya tashe mu lafiya .
Amina tace  Amin . Ta bi bayansa ta rufo kofar da mukulli kamar yadda ta saba ta dawo ta kashe wuta da kayan kallo suka kwanta.
Sati biyu bayan wannan maganar da suka yi, Amina ta samu labari a bakin Ilya an sauke kwamishinan kananan hukumomi an nada sabo, an sauke mai bada shawara kan cigaban karkara an nada sabo. Idan ta murdo (BATV) ko (Bauchi TV) babu abinda take gani sai ayyukan cigaban karkara da kananan hukumomi sak! Wadanda ta ambata. Sosai taji dadi a ranta. She feel honoured! Jin dadin cewa ita mutum ce mai daraja da martabar data isa ta baiwa gwamna shawara ya dauka.
Saidai bata ji dadin sauke wadannan masu mukaman ba, data yi masa maganar, yace da ita, ba akan abinda suka tattauna bane, ya kama su ne da almundahana, domin ya fidda wasu zunzurutun kudi ya basu domin inganta wutar lantarki da gyaran kwalbati a kananan hukumomi da kauyukan dake karkashinsu gabadaya ya bincika ya kuma je da kansa ya tarar ko daya basu yi ba. Kudi kuma babu su sama ko kasa.
A sannan ne Ameena ta samu kwanciyar hankali domin bazata so ta zama sanadin hanyar abincin wani ba.
*****
A karo na biyu, ya samu lokaci ya sake yin magana da likita Amina.
 Sai wane hange kike dashi? Don na lura bayan ilmin likitanci kinada ilmin zamantakewa da siyasa (sociology and political science). Ina barar karin idea .
Amina tayi dariya  Your Excellency har nawa abin yake? Karambani ne kawai irin nawa koko ince gyara ne nayi muku, tunani na ne kawai nayi sharing da kai, wanda na tabbata zai zo daya dana jama a da yawa masu bibiyar ayyukan ku. Yace  naji, ina son karin karambanin domin wannan din an yaba dashi sosai, mun kara samun magoya baya a dalilinsa fiye da zaton ki. So  hurry up! Lokutana a kididdige suke .
Amina ta nisa  Mai girma Gwamna a daga darajar albashin malaman makaranta, don Allah. A karawa iyayenmu  yan pansho wani tagomashin, duba da cewa basu da wata hanya sai wannan ga tarin iyali, sunyi rauni basu da karfin nema ta wata hanyar karfin.
Da wuya ka samu malamin makarantar dake da motar kansa wadda zai ce sana ar koyarwa ta samar da ita gareshi. Shiyasa kowa ya raina sana ar, matasa ke gudunta. A kalla ace an fitar da wani tsari da za a basu motoci nasu na kansu a dinga cire kaso daya bisa uku daga albashin su tsayin wasu adadin shekaru da za a kidaya zai ishe su gama biyan bashin. In akayi haka an taimake su. Fresh graduates zasu daina gudun koyarwa a jihar mu kuma zasu kara himma.
Kayi amfani da  scientific management theory wadda Frederick Winslow Taylor ya samar wajen kara himmar malaman makaranta wadda aka fi sani da Taylorism. Har ila yau, ka hada da  human relation movement din ban ce a barta ba (Elton Mayor) . A dinga sanya al amuran  education a gaba-gaba ba  infrastructure and tourism kadai ba. Duk da nasan tourism din shine fuskarmu, amma malamai sune tushe kuma kashin bayan kowacce al umma.
A dabbaqa muhimmancin ilmi kafin komai. Wannan tunanina ne amma fa. Kowa yanada damar yin nasa hangen, wannan na Amina ne .
Ya cure yatsunsa cikin na juna ya kaisu habar sa yana cigaba da kallonta, wani zubin ya girgiza kai wani zubin yayi murmushi har ta gama. Hatta yadda take zaro kalaman tana fadin su sala-sala abin a tsaya a saurare ta ne, banda sanyin muryarta da zazzaqan turancin ta. Abinda yace a karshe kawai shine.
 Noted! .
Daga ranar Amina ta zama wata mai baiwa gwamna shawara mai zaman kanta a cikin gida. Banbancin ta da (special advisers) shine ita bata da ofis kuma ba a bata albashi. In ya dawo ya shigo ganin Amina su kan tattauna al amuran siyasar sa. In al amura sun sha kansa sun sanya shi cikin damuwa sai ya samu kansa da gayawa Dr. Amina. Abin mamaki sai ta bashi mafita, wadda in ya bi sai ya ga ta bille dashi.
Sannu a hankali shakuwa mai tsanani ta fara shiga tsakaninsu. Ma arouf ya soma jin Ameena sosai a ransa da ilahirin gangar jikinsa. In fita ya yi, Allah-Allah yake ya dawo gida ya tadda Ameena da Ameena. Sosai al amarin ya sauya salo a bangaren Ma arouf Jikas. Jin Amina yake wata mutum mai amfani da muhimmanci a gareshi.
Watanni na nausawa al amarin na kara rikide masa. Tun Laila bata damuwa da yawan kebewarsu har ta soma darsawa zuciyarta kishi da zargi. Saboda in ya dawo kafin ya shiga ko ina a gidan sai ya fito daga dakin su, in zai fita su yake fara gani, al amarin nan ya soma damun ta, zaman Ameena tare dasu duk da hutu ne a gareta ya soma ci mata tuwo a kwarya.
Ta fannin Ameena, bazan iya cewa ba. Kasancewar ta wata mace data dauki soyayya ta ninke a takarda ta adana a fayal ta sanya a karkashin gado, bata santa ba, bata mafarkin yin ta, don har gobe bata ga namijin da yayi daidai da rayuwar ta ba. A ganinta the best is yet to come! Duk da alkawarin da ta yiwa Goggo, don haka ga Amina, a yanzu ko zatayi aure zatayi ne domin Goggo, don farantawa Goggo. Bata taba darsawa ranta komai akan Ma arouf ba don hankalinta ma bai taba yin nisan kiwon kawowa ranta miji kamarsa ba. Balle tayi wani tunani shigen hakan akansa. Don haka mu amalar data ke yi dashi na shugaba da ma aikacinsa ne, (Oga, Boss, Ubangida da yaron sa) inji hausawa.
Har gobe wannan girman nasa da kima da take gani yana nan cikin idanunta sai ma abinda ya karu. Saidai zuwa halin da ake ciki yanzu ta rage jin nauyin sa. Tunda yanzun tana iya tunkararsa da magana face to face suyi magana mai tsayi da ma ana. Watannin ta bakwai kenan tareda su tana aiki a gidan gwamnati ba tareda ta taba karbar ko sisi ba, bata kuma taba damuwa ba. Damuwar ta yanzun tana ga chanjin dake akwai cikin kwayar idanun Ogan ta.....!!!
???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ****
Abinda basu sani ba shi ne, wadannan manyan  yan siyasar da Ma arouf ya sauke daga muqamansu sun ja gefe su da magoya bayan su suna kokarin kafa sabuwar jam iyyar adawa mai karfi wadda zata tuzge gemun (NPC) wato jam iyyar Ma arouf. A cewar su Ma arouf yayi musu butulci. Dasu aka fadi aka tashi aka sha rana kafin ya samu kujerarsa, amma yanzu yayi kaurin wuyan da zai iya tsigesu bayan amintaka tun ta jami a. Sun sha alwashin ko zasuyi yawo tsirara Ma arouf bazaiyi ta-zarce ba (wanda babban burinsa kenan yanzu kuma burin al ummar Bauchi birni da kauye). Tunda dukkan sirrikansa sun san su sunyi alkawarin rarake kasan sa a zabe mai zuwa.
*****
Asabar ce sassanya kuma ranar hutu ga dukkan ma aikata, abincin maraice yake baiwa Ameena don baza a kirashi abincin safe ba tunda ta karya kumallo da jimawa tun takwas na safe, yanzun kuwa ana maganar karfe goma sha daya ne na rana, bayan ya dawo da ita daga zagayen da yake yi da ita cikin wheel chair daga bakin ruwa (swimming pool), chips (dankalin turawa soyayye) mai tsananin laushi yake bata, duk da laushin nasa sai ya murza mata shi da hannunsa don ta ji saukin ci, yadda ya ga Dr. Amina na yi mata.
Tun ranar juma'a yake jin kansa cikin wata irin kewa da sanyin jiki, wadanda ya rasa daga ina suka zo. Ya san dai ba tafiyar Laila garin Ji-kas ba ne ya haifar da hakan ba, don ta saba tafiye-tafiyenta tun ma kafin ya zama gwamna bai taba jin komai ba.
Yau din ya bude mata wuta ne a kan dole ta je mahaifarta ta kwana biyu, shi ba zai dauki wofintar da iyaye ba saboda rashin hankali irin nata, idan kuma ba za ta je ta kwana ba, to ta tattara yanata-yanata ta san inda dare ya yi mata.
Dole kan ba yadda za ta yi tana zumbure zumbure ta debi kayan sanyawarta kala biyu, aka cika boot din  hummer jeep' da kayan abinci da sitturu, shadda bandir-bandir ta kame a bayan mota da 'yar sandarta mace a gaban mota, aka nufi Ji-kas da ita.
Wannan ya faru ne ranar Juma a kwana daya da dawowarta daga wata tafiya data yi Dubai inda ta kara komawa check-up. Don haka weekend din daga shi sai little Ameena suka yi shi, ya dauke ta suka koma nashi dakin, a can suka kwana.
Ko wanka ya kasa yi mata, tun bayan tafiyar Amina ta wannan satin, ba shi da wannan kuzarin. Yana jinsa (incomplete) tamkar wani bari na jikinsa ya mutu shi ma. Ya kuma laluba a zuciya da gangar jikinnasa ya kasa gane abin da ya haifar da hakan.
Al'amarin ya ci gaba to such an extent that..... ya taho dakin da Ameena da Dr. Amina suke, yana dube-dube, domin ya ji a jikinsa kamar a can din ne ya rasa abin da ya maida shi incomplete.
Ya tsaya ya zuba dukkan hannauwansa biyu a aljihun bakin wandon jeans da ke jikinsa yana dube-dube. Ga injinan aikinta nan ba ta tafi da su ba. A can kan madubi kayan shafarta ne da turare guda daya da wani deo-spray zungurere (right guard) shima guda daya. Ya karasa gaban madubin ya daga turaren ya kai hancin sa ya sunsuna.
Sassanyan kamshinta na kullum shi ne a cikin turaren. An rubuta 'Davidoff (cool water)'. Kayan shafar duka sai da ya bi su ya sunsuna, ta yi gyaran gadon tsaf kamin ta fita. Ya karasa ya zauna a gefen gadon ya yi tagumi, ya dauki filonta ya rungume a cinyoyinsa, ya runtse idonsa.
Yanzu dai komai ya bayyana gare shi, babu sauran bincike ko hesitation (shakka). Dr. Amina Mas'ud yake kewa, bayan tarin nazarinta da ya yi watanni bakwai yana yi, ya lura daban ta ke da sauran mata. Abin da bai taba faruwa da shi a kan mace ba bayan Aisha. Ba kuma zai ji shi daidai (cikakke) ba, sai ta dawo cikin gidansa.
Komawa ya yi dakinsa ya dauko Ameena ya dawo da ita dakin. Ameenar ta tambaye shi, "Daddy, Aunty ta dawo ne?"
"A'ah Ameena, sai gobe da yamma za ta dawo. Mu koma can mu kwana, dakina akwai sanyi".
Ta yi shiru ba ta kara cewa komai ba, don da ma maganar jefi-jefi ta ke yinta.
Imagine! Ma arouf a dakin Amina  yar Goggo Hauwa, suka kwanta a lallausan gadon, ya karanta addu'o'i ya shafe ta da su, sannan ya yi azkar din dare da yake yi kamin ya kwanta. Ya ja lallausar duvet din gadon ya rufe su kasancewar lokacin sanyi ne.
A daddafe ya kai wayewar gari. Bai taba ganin dare mai nisan wannan ba. Washegari Lahadi, bayan sun karya shi da Ameena ya dauki wayarsa ya kunna, ya kira Kwamishinan lafiyansa Dr. Usman Turaki.
Turaki ya daga yana fadin,
"Ya aka yi ka kunna waya yau lahadi Yaa Maulaya? Na gaya maka ka bar komai a hannunmu, samun wadataccen hutu a kowanne karshen sati yana da kyau a gare ka".
"Yaushe zan huta tunda ba a halicci dan Adam don ya huta ba? Daga wannan sai wancan. Babban farin cikina Ameena's condition is improving, bakinta ma ya bude tuntuni tana magana cikin kokarin likiciyarta. Da gaske ka ba ni physiotherapist kwararriya, wadda bayan likitanci tana da hikima da basira on her own unique way. Yanzu dai ba ni lambarta shi ne abin da ya sa na kira ka".
Dadi ya rufe Kwamishina Turaki, hamdala da tazbihi da addu a ya kama yi cikin ransa; Allah ya sa Amina ta zamo karshen matsalolin Habibu-Jikas. In abinda ya yi zargi ya zama tabbatacce bai san irin farin cikin da zai yi ba.
"Zan turo lambar yanzu (through text). Amma ya ya uwargida ta karbi zaman Amina a gidanta ne? Bamu taba yin zancen da kai ba".
"Ban gane ba? Kana nufin ni da gidana akwai mai ba ni 'do and don ts ne?'
"Ba haka nake nufi ba, ka san halin mata da kishi, za ta karbi abin the other way round".
"To ban samu matsala da ita ba gaskiya har yanzu akan zaman Dr. Amina. Saboda ba kowa ne mutum a idon Laila ba, balle har ya ishe ta kallo. Ta yi tafiya ranar da Aminan ta zo. Ranar da ta dawo kuma Aminan ta je gida, da ta dawo na dan gabatar mata da maganar Amina a gurguje lokacin zan fita, ba ta ce komai ba, harkokinta ta ci gaba da yi, amma bana jin har zuwa yau ko gaisawa sun taba yi, Laila ba ta zuwa inda ta ke saboda girman kai irin nata. Kuma bata cika zaman gida ba.
Ta sake komawa Saudiyyah ta dawo shekaranjiya, a ranar kuma ko hutawa ban bari tayi ba na kada ta Ji-kas ta gaida iyayenta, don ita ba ta san ya kamata ba sam sai an yi mata jan ido. Don haka abinda zan iya cewa shine har yau bamu zauna  specifically munyi magana akan Ameena ba amma ta san da zamanta cikin gidannan.
Duk lokacin dana so yin hakan sai wani uzurin ya sha kaina, ita kuma bata taba yimin maganar ta ba tun gabatarwar dana yi mata na Aminan a gurguje, wai ance ido da kunya, abinda tasan bazata yi bane don na samo mai yi kaga bata da  say .
Lambar Amina da nake nema a wajenka, zan tura Akilu ya dauko ta ne shi ne ya sa na ke bidar lambar tata don in gaya mata gashi nan zai taho. Ba zan iya bari sai yamma ba kamar yadda muke yi. Abubuwa da yawa ina kasa yi wa Ameena, ni da ita duk muna jigata".
Turaki ya jinjina kai zuciyarsa kal, a ransa ya ce, 'A juri zuwa rafi dai... Maigirma Gwamna, wanda bai iya kallon mata ba, yau yana bidar lambar wayar su... yake kuma zaune da wadda ya tabbatar ba sonsa ta ke ba, kudinsa ta ke so. Ina nan zaune za ka sake kira na with different story....! .
Sun gama magana da Dr. Usman din bayan nan ya tura masa lambar. Ya tsurawa lafiyayyun lambobin ido na layin mtn yana mai shawara da zuciyarsa kan ya kira, ko kada ya kira? Abu ne da bai taba yi wa wata mace a rayuwarsa ba bayan mahaifiyarsa sai ko A isha. Bai taba kiran Laila ba, ita ta ke kiransa koyaushe.
Me ya sa ya damu da Dr. Amina har haka? Kwarai yake son jin sassanyar muryarta, a wasu lokutan hakan na faruwa da shi duk sanda ta je gida. Bai dai taba tsananta a gare shi ba kamar yau, ko dai ya sa Turaki ya kira ta ya fada mata?
 Ma'arouf yarinyar nan wata iri ce da ba a gane kanta at times. Ita ce mutum ta farko da ta taba yi maka musu a rayuwarka. Idan tace bazata taho yanzun ba ya zaka ji a ranka kuma me zaka iya yi mata banda ranka ya baci a banza? Be careful da girmanka a idanunta! . Zuciyarsa ke karantowa, ta kuma yi sa ar yakar duk wani ego da ya kawo tunanin ayi kiran wayar.
Don haka maimakon kira, sai ya rubuta mata gajeren sako mai layi biyu kacal. Wanda bai kunshi wata ma ana ba.

'Ga Akilu nan ya taho daukarki yanzu, please don't ask me why?' Ji-Kas.

Amina na zuba wa tantabarunta abinci da ruwa a safiyar lahadi da waya a kunnenta, tana magana da wata abokiyar aikinta Dr. Nazifa da ke 'specialist hospital Bacas' tana gamawa kafin ta sauke wayar sakon ya shigo wayarta.
Ta ji karar shigowar tasa, don haka ta ajiye kwanon dawar da ke hannunta ta bude. Tun kafin ta karanta ta ji gabanta ya yanke ya fadi ganin sunan da ta yi saving watanni bakwai a baya ya bayyana, bata kuma taba amfani da shi ba (ba a kirata da lambar ba, itama bata kira ba ko yin sako); JIKAS!
Ba shakka ta firgita, tunda har ya yi mata sako da kansa wani muhimmin abu ne ganin bai taba yi ba a tsawon zamansu na watanni kusan bakawai. Tuni ta daburce. Allah ya sa ba wani abu ne ya samu Ameena ba. Tunaninta kenan. Da sauri ta karanta.
Ta yi dan jimmm! Tana nazari. Daga baya kuma ta fito ta gaya wa Goggo da ke kwabin  meatpie a madafi (kicin).
Goggo ta ce, "Ai sai ki yi sauri ki shirya Allah ya sa yarinyar lafiya ta

9 / 11