SANADIN KENAN 2 HAUSA READ BY TAKORI.doc

Author :  sumayya Abdulkadir Takori Category :  Romance

Chapter   4 / 11

9K to 12K   out of 31.5K words

alkhairi, Amina kanta ta yi murna, na gaya mata babanta ya zama Gwamna. Allah ya taya ka riko, Ya kare ka a duk inda ka shiga, Ya kauda idon makiya da mahassada a kanka".
"Amin Hajiya ta. Allah ya bar min ke".
Abin da ya tura mata kenan.
Ya kira Baba suka shiga hira, Baba na ba shi labarin yadda gumurzun zaben ya gudana da ruwan masoyan da Allah ya ba shi. Ya kare da cewa,
"Bana jin ka Ma'arouf, amma ka san mutanen da za ka dora a karkashinka".
Sai na wata wai ita Laila, kwata-kwata ya manta da ita, sai yanzu ya tuna ashe fa yana da mata. A wurinsa duk wanda ba zai ji kan Amina ba, ya tausaya mata ba masoyinsa ba ne. Amma ita wannan ya zai yi da ita? Ta zame masa dole.
Ya bude sakon nata a nitse.
"Duk da na san fushi ka ke da ni, ina yi mana congratulation. Ka dawo da Amina zan kula da ita wallahi".
Ya amsa da gajeren sako.
"Thank you".
A zuciyarsa ya ce, "Ta baya ta rago. Da ban san badininki ba ne".
Haka ya yi ta bin 'yan uwa da abokan arziki yana amsa wayoyinsu da sakonninsu, babu nuna kosawa ko girman kai. Har ya zo kan na Dr. Usman.
"Monday din nan zan yi wa Dr. Amina magana insha Allah. Heartiest congratulation".

Ya sauka a filin jirgin sama daga kasar Saudi lafiya. Jama'a jingim suka zo tarensa, suka isar da shi har gidansa na Bauchi. Laila ba ta san da zuwansa ba, ta cika gidan da kawayenta ana taya ta murna, kuma kowacce tana fadin abin da ta ke so Lailan ta yi mata da sun shiga ofis.
A haka ya tarar da su sun cika masa falo. Ji ya yi kamar ya fatattake su, sai ya tuna shi din fa dan siyasa ne, ba shi da wannan damar. Suka gaisa sama-sama ya wuce.
Laila ta tsallake su ta bi shi. Ita ba ta san dukkansu daga masu auren har marasa auren kishinta suke yi ba. Wannan 'handsome governor' ita ke da shi, ita kadai ranta, sannan gidan gwamnati za ta koma nan ma ita kadai. Hassada da bakin ciki duk ya lullube su.
Ga shi kuma tunda ta bi shi daki ta manta da su, ba su gama alkawarirrikan mukaman da za ta nema musu wajen maigirma Gwamnan ba. Da suka gaji da zama dole suka tattara suka tafi cike da bacin rai.
A can (master bedroom) din Ma'arouf hakuri Lailan ta zube tana bashi, a kan kasa kulawa da Amina da ta yi. Ajizanci ne irin na dan Adam, amma ba don ba ta son Amina ba. Abinka da mace da mijinta, dole ya sauko ya karbi tuban nata, ko ba komai yana bukatarta a lokacin tunda ba shi da wata matar sai ita, girman kai ba nasa ba ne. Amma ba don zuciyarsa ta yarda da ita 100% ba ko ya manta da girman abinda tayi masa.. Tana nan dai a matsayin matarsa amma ba aminiya ba, wadda zai dauki amanar gidansa ya baiwa, ko ya yi (sharing) wani abu muhimmi daga (personal life) dinsa da ita ba.
Laila ta kasa bari ko tsarkake jikinsu su yi, ta soma fada masa abin da ke cinta a zucci. Wato tana so ya ba ta shugabar  family support programme' da za ta bude don ci gaban mata.
Dariya ta kama shi, ya yi abarsa sosai, "Da dai kin tsaya kin yi karatun yadda ya kamata ne, amma yanzu ba ki da maraba da dan sakandire tunda ko takardar tsire ba ki da ita".
Laila ta kulu, ta sanshi da yaba magana a gare ta in ta yi masa ba daidai ba, duk dai akan ta ki ta tsaya tayi karatu, amma ta yau ta fi kowacce yi mata zafi. Ta kuma rantse sai ya ba ta wannan mukamin in dai maganin mata na aiki kamar yadda su Nazi suka zuzzuga ta.

****
Dr. Amina Mas'ud tana (ward round) ranar litinin da safe aka aiko wata nurse ta gaya mata Dr. Turaki na nemanta in ta gama abin da ta ke yi. Ta amsa da, "Toh", ta ci gaba da duba marassa lafiyanta har ta gama, sannan ta nufi ofishin (consultant) din nasu. Zuciyar ta cike da tunanin ko menene dalilin kiran kasancewar bai cika yin hakan ba in ba da dalili mai muhimmanci ba.
Da sallama ta bude kofar, ya amsa, "Have a seat please". Ya fada yana mai nuna mata kujerar dake fuskantarsa.
Amina ta zauna sannan ta gaishe shi. Ya amsa cikin sakin fuska ya dora da fadin.
"Dr. Amina, na san kin san Engnr. Ma'arouf Ji-kas ba sai na gabatar da shi a gare ki ba?".
Amina ta gyada kai.
"Na sanshi a bakin Yayana Ilya dai, da kafafen sadarwa. Saboda son da Yayana Ilya ke masa sai da ya tattage mu muka je muka sanya masa kuri'a har da Goggo.
An shaide shi da cewa, mutumin kirki ne, that's all i know about him, bayan wannan ban san komai da ya dangance shi ba Dr".
"Da kyau, kin taba sanin yana da (paralysed daughter) mai shekaru biyar?"
"Gaskiya ban sani ba, don ban san personal life dinsa ba. May be Ilya ya sani sabida shige-shigensa a kansa".
Ya yi murmushi,
"Ilya namu. To shi ne yake neman wani taimako daga gare ki, kodayake ta wani fannin ba za a kira shi taimako ba, tunda abu ne da ba kyauta za ki yi shi ba. You are on your profession, yana so ki koma gidansa da zama ki ci gaba da bawa yarinyarsa 'treatment' a gida zuwa shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Kin san dai yadda Paralysis yake ba abu ne da za a ce yau ko gobe an tashi ba, tunda warkewarsa ba shi da kayyadadden lokaci.
Ya yi alkawarin ninka miki albashin da gwamnati ke biyanki sau hudu a kowanne wata. Duk 'weekend' za ki tafi gida ki dawo Lahadi da yamma. Na yarda da kwarewarki a kan aikinki da sadaukarwarki shi ya sa na zabo ki cikin dubu. A ganina wannan wata hanyar samun alkhairi ce mai dimbin yawa gare ki da iyayenki. Amma za mu ba ki lokaci ki yi tunani, ki kuma nemi amincewar magabatanki ko ya ki ka gani?"
Amina ta nisa, tunda ya fara magana ba ta katse shi ba. Lallai ilimi mai zurfi ya yi a rayuwa. Albashi sau hudun nawa ashe ba da jimawa ba burina zai cika a kan Goggona? Allah ya sa ta amince.
****
An rantsar da shuwagabannin Najeriya a rana daya. Litinin 2/2 His Excellency Ma'arouf Habibou Ji-kas, ya shiga ofishinsa cikin nasara.
Cikin dan lokaci komai ya yi 'settling'. Su Laila an yi hijira zuwa 'Government House' abin ba a cewa komai. Domin wani gammon girman kai ta nada ta dauka ta aza a kanta fiye da na matar shugaban kasa suka shiga  government house tare.
Danginta babu wanda ya isa ya rabe ta. Mahaifiyarta kadai ta ke wa ihsani, shi uban ta ma manta da shi. Kannenta da suke uba daya Sadiya da Asiya ba irin rokon da basu yi mata ta waya ba kan suzo ayi bikin rantsarwa da tarewa dasu ta ce sam! Bata gayyatar kauyawa gidanta. Kafin zuwan wannan ranar duk sanda Ma'arouf ya ce ya kamata ta je gida ta gaida iyaye da dangi, sai ta ce masa gobe za a sauke kayan da ta yi (order) har ya gaji ya rabu da ita.

Lokacin da Ma'arouf Ji-kas ya zo nadin kwamishinoninsa, ya rangadawa Dr. Usman Turaki kujerar kwamishinan lafiya. Ya kuma baiwa Umar Bolori Special Adviser Health don nuna godiyarsa kan yadda ya kula masa da Amina a asibiti, sauran duk na jikinsa ne, abokan karatu ne, malaman sa na jami a ne, kawayen A isha ne da yan uwanta bai manta dasu ba, duk ya nemo wasu daga cikinsu ya basu mukamai manya da kanana wadanda ya yarda da amanarsu da ingancin kwalayensu. Komai ya tafi daidai, mulkin gwamnatin Habibu Ji-kas, ya soma kankama a jihar Bauchi.

*** *** ***
FLASHBACK
Amina da Goggonta, tare da Inna Zulai da Goggo ta kirawo don ta taya ta jin wannan almara, ko kuwa rashin kan-gado da Amina ta zo mata da shi.
"In ban da rashin kan-gado irin naki Amina, ina hankalina zai kwanta kina kwance wani muhalli daban da nawa, alhalin na san ban yi miki aure ba?" Goggo ta fada cike da damuwa, muryarta a sanyaye, muryar tata ta nuna tsananin damuwar da zancen da Aminan tazo mata dashi ya jefa ta a ciki.
Goggo Zulai ta ce, "Da ma a ce aurenki zai yi ne don ki kula da diyar da ya fi armashin ji".
Amina ta jefa wa Inna Zulai harara ta gefen ido, ganin tana tufka tana warware mata.
Amina ta gyara zama, "Goggo a kan aikina nake. Mu ne Proffessionals din da ake 'hiring' har gida mu kula da mai lalurar shanyewar barin jiki If a person can afford (idan mutum zai iya biya), sannan ban bar aikina na gwamnati ba, za a bada arona shekara daya ne in daina karbar albashin gwamnati in karbi na wadanda suka haye ni.
Ki kwantar da hankalinki Goggo, duk karshen sati zan taho gida in koma lahadi da yamma. Sannan fa akwai matar aure a gidan, kuma Goggo ai gidan gwamnati ya wuce duk yadda ki ke tsammani. Girmansa da fadinsa in ba kai ka nemi mutum ba babu abin da zai hada ku. Albashina za a ninka sau hudu Goggo, ba da jimawa ba Allah zai cika min burin da na ke da shi a kanki. Ki barni na yi aikina Goggo, in har kin yarda a kan-kanki cewa, kin ba ni tarbiyya yadda ya kamata.
Duk inda na shiga zan iya kula da kaina Goggo, zan nuna tarbiyyar da ki ka yi min da yardar Allah ba zan ba ki kunya ba. Hakan ba zai yiwu ba ba tare da na samu goyon baya da kwarin gwiwarki da albarkarki ba Goggo.
Shekaru bakwai ina karatu a jami'a, ba ki taba samun wani abin Allah-wadai daga gare ni ba sai don zan je aiki na shekara daya duk karshen sati ina tare da ke? Da zan yi hidimar kasa Gombe na tafi, duk ba ki nuna damuwa ba Goggo sai wannan?"
Goggo ta nisa, "Amina, ke yarinya ce, mutane da halayensu canzawa suke kamar wahainiya in suka samu daular duniya. Ina tsoronki da shiga daular nan Amina, kada halayenki da tarbiyyarki su canza..."
Kamin Amina ta ce komai, Ilya ya yi sallama ya shigo. Amina ta gode Allah a zuciyarta, ta tabbata mai taya ta wannan battle (yakin) da wadannan dattijan masu tsoron duniya da abin da ke cikinta ya zo.
Ita ma tana yarda da abin da suke hangowar kawai tana kare kanta ne don ta yarda da kanta kuma tana son yin aikin ko burin da ta ke da shi a kan Goggo ya cika. Ba tana son yi don amfanin kanta ba ne, za ta yi ne don samun cikar burin da ta ke da shi a kan Goggonta tun tana karama, wanda daga ita sai Ubangijinta suka san me take son yiwa Goggon.
Goggon da ba ta yi karatun zamani ba, amma ta tsaya (against all odds) ta cika mata burinta, har ga shi yau al'umma na amfana da ita, ya kuma zame mata hanyar samu na har abada, ya zama silar dogaro da kai a gare ta.
Kullum ta dauki albashi cikin asusunta sai ta tuna Babanta, sai ta ce, "Ina ma kana raye Baba? In rashin kudi ne ya sa ka sha wahalhalun da ka sha a rayuwarka, yau ga kudin na samar maka ba ni da abin da zan yi da su. To bari in yi ta tara su, in yaso Goggo ta amfana a karashen rayuwarta. Ni ba abinda zanyi dasu, Goggo ta min komai, tana kan yimin, Alhamdulillah! Goggo is a blessing, from almighty Allah to Amina!!!". Abinda take fadi a zuciyarta kenan.
Ilya ya shigo ya zauna a gefe, "Wai me ku ke tattaunawa ne ana ganina aka yi wani gumm?"
Goggo ba ta tanka ba, don ta san shi sarai, muddin ya ji a kan aikin wa ake wannan takaddamar Amina ta yi nasara akansu ta gama, don kaifin bakinsa wajen yarje mata sai ya fi na kowa.
Inna Zulai da bata san waye Ilya ba ta dan soma harhada masa abin da ta fahimta.
"Wai Gwamna Ji-kas ke son daukar Amina aiki, ta kula da diyarsa mai shanyayyen jiki, amma dole sai ta koma gidansa don ya rabo yarinyar da gadon asibiti, zai dinga ninka mata albashinta na asibiti sau hudu duk wata, Goggo ta kasa amin......"
Ilya ya kasa tsayawa ya ji karshen zancen, ya daka tsalle ya dire ya ce, "Tabdijan! To shi ne ku ka sa Dr. Amina a tsakiya kuna son yi mana sagegeduwa? To ke Amina yanzu wai me ki ke ce musu sun ki yarda? To ke Goggo in wannan damar ta wuce Amina anya kin yi wa kanki adalci ganin wahalar da ki ka ci kamin Amina ta zama likita? To wai ma in tambaye ku, ina ruwan Ji-kas da Amina in ya dauke ta aiki cikin gidansa? An ce maku ba shi da mata ne, ko manemin mata ne? To in SANADIN hakan ne Allah zai bai wa Amina miji sai ku sa kafa ku shure alherin Allah? Kai ban taba jin Goggo kin ba ni takaici irin na yau ba. Kin biye wa Inna Zulai kifin rijiya kuna ta bata yawun bakinku a kan alherin da ya zo har gida ya same ku.
Shin wa ya ce muku Amina ita ce kadai likitar mataccen kashi a jihar Bauchi? Don kun samu Allah ya zabo ta cikin dubu ya ba ta shi ne za ku tsaya kuna kasa ta a kan faranti tana lallashinku kuna togewa? Dr. Amina, adana yawun bakinki zai yi miki amfani a gaba, bar ni da su. Ku gaya min duk abin da ku ke gujewa na shigar Dr. Amina gidan gwamnati......."
Amina ban da dariya ba abin da ta ke, ganin yadda Ilya ya takarkare yanata zubo magana kamar wani lakcara. Goggo da Inna sun kirne fuska sai jifansa suke da harara. Shi kuwa ya kai hannuwa kirji ya harde shi a dole jira yake su ba shi amsa.
Inna Zulai ta ce, "Sannu ubanmu. Rasa kunya beran tanka. Matse bakunanmu in muka ji zafi sai mu gaya maka abin da muke gujewa din na zuwan mace babu aure wani waje ta kwana".
Ilya ya gyara murya, ya dafa kirjinsa da hannun dama.
"A inda babu uba komai kankantar namiji uba ne. Don haka, ni Ilya uban Amina na amince diya ta Amina ta je aiki gidan Engineer Ji-kas. Da ta ke kwana a asibiti binta ku ke? Kai ni ba don kar a ce na yi rashin kunya ga iyaye ba, da sai in ce ban taba ganin gidadawan mutane irinku ba, ana kiranku gidan gwamnati kuna cewa ba za ku je ba......"
Goggo ta dauki kofi a gefenta ta jefa masa a baki. Inna Zulai da ta fi kusa da shi ludayi ta kai wa bakinsa ya kauce.
Amina cikin sassanyan muryarta ta ce, "Haba Yaya Ilya? Maimakon ka gyara duk ka kara damalmala al'amarin.
Goggo ku yi hakuri ni dai na gaya muku a kan aiki na nake neman amincewar ku inje gidan gwamna, da kuma wani kebantaccen uzuri da nake da shi a kan ki Goggo. Amma in ba ki amince ba na hakura Goggo, zan je gobe in fada wa Dr. Turaki ban samu amincewarki ba".
Jikin Goggo ya yi sanyi, ta san Aminanta har ga Allah ba ta da kwadayi. Ba ta nemi komai ta rasa ba, Amina gudun maza ta ke ba son kai kanta gare su ba. Amina na son aikinta fiye da komai a rayuwarta, a cewarta yana sanya mata nutsuwa, yana sa ta nishadi, yana sa ta farin ciki, yana raba ta da damuwa. Duk ta yarda da wannan, kawai burinta a yanzu Amina ta yi aure shi ne kwanciyar hankalinta, ba wai ba ta sonta da aikinta ba ne. Kuma ta yarda Amina yanzu ba ta korar masu sonta, sune suka dauke kafa.
Goggo ta nisa ta dubi Amina, Zulai da Ilya da duk suka zuba mata ido. Kowa ta bakinta yake son ji don a yanke maganar haka kowa ya huta.
"Amina, na yarda ki je aikin 'yar gwamna, amma a bisa alkawari guda daya".
Amina ta dago da nutsuwa a kan fuskarta.
"Wane alkawari ne Goggo? Insha Allahu zan cika miki shi muddin bai fi karfina ba".
"Ki je ki yi aikin na amince, amma idan kafin ki gama Allah ya kawo miki mijin aure za ki bar aikin ki yi aurenki. In ya so in mijin ya amince sai ki ci gaba".
Amina ta yi murmushi har gefen kumatunta biyu suka lotsa.
"Ai a bisa wannan alkawarin muke Goggo har gobe. Wallahi ba ni nake korarsu ba, su suke korar kansu. Amma na kara yi miki wannan alkawarin, ko yau na fara aikin gobe mijin ya zo, zan bar aikin na yi aure, ko wane ne shi".
Ilya ya ce, "A'ah Dr. Amina daina cewa ko wane ne, idan kuturu ya zo ko gyartai ba ruwan Goggo fa, ke za ki zauna da shi".
Goggo ba ta san sanda ta yi dariya ba, duk zukatansu suka yi dadi, don ba sa son ganinta cikin damuwa ko ya ya, walwalarta ita ce tasu.
Inna Zulai ta yi musu sallama, ta tashi tana fadin, "Kin bari sun kalallame ki da dadin bakinsu Goggo, ni na yi nan, tunda ko na sake cewa komai ma ba tasiri zai yi ba".
Ilya ya ce, "Haka ne Hajiya Inna. Gara ki adana yawun bakinki. Sai Ji-kas!

4 / 11