Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin KENAN 2 HAUSA READ Complete Hausa Novel by Sumayya Abdulkadir Takori

Author :  sumayya Abdulkadir Takori Category :  Romance

Chapter   8 / 11

21K to 24K   out of 31.5K words

idan an shiga renakun sati".
Amina ta girgiza kai, "What a simple politician!'. Tana so ta ce, 'Ina matarsa da zai yi wannan aikin mai gajiyarwa na Amina?' Ta ga cewa hakan ba huruminta ba ne, ta ja baki ta yi shiru. Ita tunda ta zo ma ba ta ga matar ba, kodayake ta ji Hajiya tace ta je Saudiyyah. Yau zata dawo. Gashi ita kuma zata tafi. Za ta so ganin wace ce matar Ji-kas???
Lallai za ta kasance babbar 'yar kwalisa kamarsa, ma'abocin ado kamar Dawisu.
Ya soma taku zai tadda kofa yana latsa wayar hannunsa.
"Akilu ya zo daukarki, ki same shi a falon farko kafin Ameena ta tashi".
Ta mike tana tura 'yar jakar matafiyanta mai tayoyi (trolley) ita ma ta yi kofar. To bai fice ba, ya tsaya a bakin kofar yanata waya, sai ta dan dakata daga nesa kadan. Ya gama ya rufe wayar ya sanya a aljihu, hannunsa na dama na bisa 'handle' din kofar. Ba tareda ya juyo ba ya tambayeta.
"Ranar lahadi karfe nawa zai zo ya dauke ki?"
"Karfe shidda na yamma".
Ya juyo gaba daya ya zuba mata fararen idanunsa na  yan sakanni, kafin yace.
 Na dauka za ki ce karfe goma na safe?"
Amina ta yi murmushi har kumatunanta suka lotsa kanta a kasa, cike da girmamawa take magana.
"Ina kiwo ne ranka ya dade, bayan ganin Goggo, I want to spend some time with them".
"Kiwon na mene ne?"
"Tantabaru (pigeons)".
Ya yi dan faffadan murmushi wanda har ya bayyanar da fararen jerarrun hakoransa wanda ba kasafai yake yi ba, sosai abin ya birge shi. Yana sha awar sana o i na kiwon gida irin wadannan, wannan dalilin nema yasa yanada gidan gona na kiwon dabbobi da tsuntsayen gida nashi na kansa. Amma babu tantabaru a ciki.
"Zan sayawa tawa Ameenar aure biyu, ita ma ta kiwata, nawa ne kudinsu?"
Amina ta girgiza kai,
"Ba na sayarwa ba ne. Amma ita zan ba ta kyauta".
"Godiya ta ke Dr. Amina, ina son account number".
"In wata ya kusa cika zan bayar ba yanzu ba......"
Ya tare ta, "Ba albashi zan saka ba, sakon mahaifiyarki ne".
Amina ta girgiza kai,
"Zan so kada hakan ya shiga tsakaninmu Your Excellency. Banda albashina babu wani abu makamancin wannan da zai hada mu".
Ya dan daga kafada, alamar baida damuwa akan hakan, ya kuma tattare gira cikin mamakinta da jin haushin kalaman ta, amma ya shanye, ko kadan fuskarsa bata nuna komai ba. Ya bude kofar saura kadan ya fita ya dan dakata yayi magana cikin tsare gida.
"Ki je Akilu na jiranki, yanzu za ki ga ta tashi. Naki asusun ma in kin ga dama kada ki bayar".
Ya sa kai ya fita. Da alamu bai ji dadin maganganunta ba.
Duk kuma sai ta ji ba dadi, ta shiga damuwa. Amma ita iyakar gaskiyar abin da ke ranta ta fada, ba ta zo don cin daular gidan gwamnati ba. Ta zo neman guminta ne, gumin nata kawai take son ci, don haka a sanyaye ta tura jakarta ta fito zuwa inda direban ke jiranta. Ta gaishe shi don ya manyanta.
Ya amsa da karramawa, ya karbi jakarta ya sanya a mota ta shiga suka tafi.
****

Goggo na alwala a gindin famfo, Amina ta yi sallama. Goggo ta dakata ta amsa tana kallon mai shigowa. Aminanta ce, tayi wani kyau mai sanyi, hatta muryarta ta canza.
Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, da gudu Amina ta yar da jakar hannunta ta sheka ta rungume Goggonta.
"Na yi kewarki Goggo, na ji dadin samunki lafiya".
Goggo ta yi murmushi, "Cika ni to in karasa alwalata. Ke kam, ban san yaushe za ki girma ba".
Ta cika ta tana dariya, ta nufi dakin tantabarunta.
Tana ciki tana duba lafiyar kowannensu, Ilya ya yi sallama ya shigo. Ya ce, "Aha! Wannan sassanyan kamshin na san daga inda ya fito. Barka da zuwa Hajiya Dr. Amina". Ya fadi tare da dunkule hannu hadi da rankwafawa alamar jinjina.
Amina ta ce, "Umh, Ilyan Goggo na Baban Ameena. How I wish zan iya dumi da shi in ba shi labarinka ko watarana ya kira ka ku gaisa".
Ilya ya gintse fuska, "Kina nufin ba kya ganinsa? Na dauka tuni an wuce gurin kin gabatar da ni?"
Amina ta girgiza kai, "Oh-oh! Mutumin nan ina ganinsa dare da rana, as if ganin nasa ya fi komai arha. Amma wallahi Ilya bana iya doguwar hira da shi, kamar wani babban Zaki ko Giwa yake zama a idanuna. In ba a kan abin da ya zama dole ba, bana iya bude baki a gabansa.
Gara yau zan ce mun yi zancen mintuna biyar amma ya zama dole ne, saboda mahaifiyarsa da nake amfani da ita wajen jakadanci a tsakaninmu ta tafi. Hirar kuma ta tantabaru ce, karshe kuma bata kare da dadi ba, baram-baram muka rabu a kan account number".
Ta kwashe yadda suka yi ta gaya masa.
"Ba ki kyauta ba Amina".
Goggo dake gefe tana jin su ta fada, "Tunda ya ce ki ba shi sai ki ba shi ba kawai? Ba abokin musunki ba ne. Watakila shi bai saba da a yi masa musu ba ma. Ba a mayar da hannun kyauta baya, musamman kyautar manyan mutane, kuma ya ce ba ke zai yi wa ba, a nan ya nuna girmamawa ne ga mahaifiyarki.
Ba wai na damu da abin da zai banin ba ne, amma kin san ko me zai bada din girmansa ne. Ba abinda zai tsikari abin da yake da shi ba ne, hanya ce ta kyautatawa wanda ya kyautata maka ka ji dadin taimakon da yake yi maka".
Ilya saboda kuluwa harararta kawai yake yi.
"Kyale ta Goggo, shashasha 'yar bukulu. Ni na yi nan Goggo kada zuciyata ta buga. Talatu ba ta jin dadi shi ya sa ba ta zo ba, ina da abubuwan yi da yawa".
Ya shuri takalmansa ya fice kamar kububuwa, ji yake kamar ya kirbi Amina ko ya huce. Shi ba abin da za a bayar din ne ya dame shi ba, a'ah, ita wace ce da za ta yi wa masoyinsa musu, har ta bata masa rai?
Ina ruwan Ilya mai soyayyar babu gaira babu dalili alhalin ba a san da kai ba.
Haka Amina ta shiga hidindimunta a gidansu kamar yadda ta saba, jefi-jefi Ameena karama na fado mata a rai.
Ta debi kyawawan Tantabaru aure biyu manya-manya ta saka a karamin keji ta ajiye don cika alkawarin da ta yi. In dare ya yi zama ta ke a gefen gadonta ta shiga bincike cikin manya-manyan littattafan (Physiotherapy) don kara wa kanta sani a kan lalurar Paralysis. Ba ta da buri a yanzu irin na samun lafiyar Ameena Ma'arouf, tana tausaya mata amma ta fi tausaya wa ubanta, wanda ba shi da kwanciyar hankali sam saboda ita. Don ma dai an ce zuciyar shuwagabanni mai fadi da zurfi ce, da suke iya daukar large abubuwa ba tare da kowanne ya gogi dan uwansa ba.
Goggo ta ba ta wasu addu'o'i ta ce, a cikin zam-zam za ta dinga tofawa tana shafe mata gabbai da su in tana yi mata gashin kashi.

*****
Ranar Lahadi karfe shidda daidai na yamma kuwa suka ji dirin mota a kofar gida. Aka aiko yaro wai Akilu yazo daukar Amina. Ta tattara  yan komatsanta cikin  handbag dinta tayi sallama da Goggo da Talatu yaron ya fitar mata da trolley din kofar gida. Akilu ya karba ya sanya a mota, Ilya baya nan balle su tafi tare, tana fitowa Akilu ya karbi kejin tantabarun hannunta ya sanya a bayan motar ya bude mata kofa ta shiga, ya zagaya ya shiga mazauninsa ya tada motar suka hau titi, Amina tana rokonsa kada ya kara bude mata kofa, domin a haife ya haife ta.
Babu inda ake bincikarsu har suka tadda  mansion din masu gidan.
Dakinsu ta nufa kai tsaye da kejin tantabarunta a hannu. Babu kowa a dakin sai Ameena, tana ganinta fuskarta ta yalwata, daga kwancen da take ta daga hannunta daya mai lafiyar tace  aunty .
Amina ta aje kejin a kan mudubi, ta karasa ta tayar da ita zaune, ta dora ta a cinyoyinta ta rungume ta a jikinta, sai kuma ta sunkuce ta sai bandaki, ta wanke ta tas! Ta yi mata duk abin da ta saba yi mata sannan ta fito da ita. Tana cikin yi mata gashin kashi, bayan ta shirya ta cikin sababbin tufafi taji an murda kofar an shigo. Kamshin turaren sa ne ya ankarar da ita cewa shine. Ya shigo da sallamar sa ciki-ciki, mai nuna har yanzu fushi yake da mai dakin.
Ta amsa, ba tareda ta juyo ba don bata distracting aikinta, ko ya zauna ko bai zauna ba? Bazata ce ba! Ta cigaba da abinda takeyi. Ya harde hannu a kirji yana kallon su, sai a lokacin ta tuna fushi yakeyi da ita, da abinda Goggo tace akan  argument din nasu da ta je gida, na (account number), ta dakata da abinda takeyi ta shiga nutsuwarta sosai ta juyo sai karaf! Idanunsu suka hadu dana juna, tayi saurin sunkuyar da kai kamar yadda ta saba in tana gabansa, bata iya kallonsa ko na minti daya directly cikin idanunsa, a bisa dalilai masu yawa da har yau bata gama iyakance su ba.
Da murya irin ta wanda yayi laifi ya kuma yarda daga baya yayi laifin ya amshi laifin nasa, yana so yayi repenting in za a bashi dama tace.
 Ga tattabarun Amina na kawo as promised . Ta nuna kejin dake kan mudubi da dan alinta.
Sai ya manta da fushin nasa kuma sosai ta bashi dariya amma ya dake. Ya karasa ga kejin da sauri ya durkusa yana kallon kyawawan tantabarun yana murmushi with admiration, sai kuma ya bude kejin ya fito da aure daya farare kal da dabbare dabbaren baki kadan a jikin su ya dora a cinyar sa yana shafa bayan su a hankali, abun mamaki basu tashi ba, Amina ta cire fukafikin tashin kafin ta dauko su. Yace.
 Beautiful, Amina ta gode. Amma ba a tukunya ake kiwon su ba?
 Eh, a tukunya ne, na sa a kejin ne don inji saukin daukowa, sai a nemi tukunyar a sanya su . Ya maida su kejin ya dauka ya fita, yana fadin.
 Yau dinnan kuwa. Mu wuni lafiya. Little Ameena stay blessed! Daddy luv you much! Ameena karama tayi murmushi ta daga masa hannunta mai lafiyar. Bata yi magana ba. Don dama maganar jefi-jefi take yinta. Amma tana jin komai tana kuma fahimta.
****

Haka Dr. Amina ta ci gaba da aiki a gidan gwamnati har tsayin watanni biyar. Ba ta taba karbar albashinta ba, saboda bai kara yi mata zancen account number ba. Ita kuma bata taba damuwa ba, a yadda zuciyarta ke son Amina Ma arouf ji takeyi kamar kyauta take yi mata wannan aikin sadakatul jariya ta manta da wani abu wai  pay . Mu amalarsu itada Ubangidanta mai wuyar fassarawa ce saboda kowannensu halinsa mai tsauri ne.
Abinda za a iya cewa shine, tsakanin Ma arouf da Amina babu shakuwa babu sakewa da juna amma kuma babu gaba ko daurewa juna fuska. Wato mu amalar ta tsaya a iya ginshikin ta (lafiyar Amina) bayan wannan babu wata, sai ganin mutuncin juna da girmama juna. Saboda kowannensu ya tsaya matsayin sa ya kuma rike mutuncin nasa.
Wata rana da daddare bayan sun ci abincin dare, Amina tace  Aunty kunna min T.V . Amina ta tashi ta jona talbijin din, ta murdo mata cartoon din da kullum shi take kallo (Tom&Jerry). Amma sai little Ameena ta girgiza kai  aunty yau mutane masu rai zaki budo min . Amina tayi dariya  Tom da Jerry ba masu rai bane yau ta dauki remote ta murdo mata (Bauchi State Television). Cikin sa a a lokacin an nuno Baban ta, inda ake nuna sababbin ayyukan sa na wannan watan dana watan da ya gabata. Na farko purifying ruwan sha da yayi a jihar, da kara habaka hanyoyin gudun sa ta yadda ya isa ga kowanne sako da kowanne lungu na cikin birnin Bauchi (capital city), sai sabunta tourist attractions na jihar musamman  Yankari Game Reserve , anyi sababbin motels da suits a cikinta, an sabunta ko ina an kara kula da dabbobin ciki, abincinsu da lafiyarsu, an karawa ma aikatan na Yankari albashi.
A cikin gari kuma, gashi an nuno shi yana bude sababbin shatale-tale (round-abouts) da gadoji (flyovers) na sama dana kasa da ya gina don rage cunkoson motoci da ababen hawa a cikin gari, an kara wa asibitocin gwamnati albashi, an samar da magunguna masu kyau kyauta ga marasa lafiya al ummar jihar ta Bauchi.
Amina tayi dan yi gajeren tsaki  mtsw! Ta dora kafarta daya kan daya ta cigaba da kallo. Haka kawai taji ayyukan ko daya basu yi mata ba, basu burge ta ba! A ganinta akwai gyara a cikin ayyukan da administration din ke aiwatarwa.
Amina karama na ta murna tana gaya mata.
 Daddy na ne, Aunty Daddy na ne fa ko baki gane shi bane?
Amina ta tura baki gaba kafin tace  na gane shi mana Amina tace  to ban ga kina murna ba tayi dariya tace  to ina murna Ameena gashi nayi dariya...... .
Suna haka yayi sallama tareda knocking ya dakata yana jiran su bashi umarnin shigowa. Lokacin sa ne na yin sallamar dare da little dinsa. Saida Amina ta bada izni ta hanyar cewa  yes sannan ya murdo kofar ya shigo.
Yau cikin wata irin shiga yake da Amina bata taba ganinsa da ita ba, wato shudin wandon jeans da  yar top ja mai farin rubutun hilfiger. Kullum cikin babban riga da  yar ciki da wando yake, wani lokacin kufta da wando na shadda ko yadi mai laushi da tsada (kaftan), bata taba ganin shi cikin wata shiga bayan wadannan ba sai yau. Sai ya zame mata yaro matashi dan shekaru talatin da daya ba magidanci Engnr. Ma arouf Ji-kas ba. Sai ta ga yayi mata wani irin kyau. Da ta kalle shi sai da ta sake maimaitawa abinda bata taba yi ba, amma tayi hanzarin dauke idonta kafin ya ankara da ta yi masa kallo na biyu.
Ya zauna kusa da little, ya dauki kanta ya dora bisa cinyar sa. Yace  Dear Ameena, kallo ake yi ne haka? Ta ce cikin  yar siririyar muryarta  Daddy kai muke kallo yace  koh? Let me join you my princess, me ake yi a TVn?
Ta ce  an ce Yankari Game Reserve...... His Excellency Ma arouf Ji-kas.....! Ya kyalkyale da dariya ya rike hannunta cikin nashi  sai kuma me? Ta yi dan tunani sannan tace  Daddy na manta sauran yace  Auntin ki ta tuna miki, kin ga ni ban gani ba gara ku bani labari .
Ta kai idonta ga Dr. Ameena  aunty sai ma me aka yi? Ameena dake sauraron su amma idonta na kan TV, ba tareda ta juyo ba take magana.
 Aikin duk na cikin birni ne Ameena (maraya) wanda ake kira urbanization (raya maraya). Ki gayawa Daddyn ki inada gyara in zai bani minti goma cikin muhimmin lokacinsa .
Amina little ta maida kallonta ga mahaifinta.
 Daddy ka bata minti goma .
Ya nutsu sosai idonsa akan Dr. Ameena. Yace da little.
 Amina, Na bawa Doctor (100 minutes)!
Dr. Amina taji dadin abinda yace. Ta juyo sosai daga fuskantar allon talbijin suka fuskanci juna, yana gefen gado ne da kan Amina akan cinyarsa, yayin da ita tana can gefe akan  resting chair , kafarta daya bisa daya da  remote control din talbijin a hannunta, sanye take da doguwar riga ruwan gwaiduwar kwai (beige colour) kirar Bahrain ta yi rolling da mayafin akanta da carbi a hannunta, da wuya ka ganta babu mayafi a wannan gidan sai ko a gidan Goggonta. Ganin irin nutsuwar da yayi yana sauraron ta itama ta zama serious ta soma magana cikin matsanancin ladabi.
 Da alama baka yi rayuwar karkara ba Mai girma Gwamna. Koko ince,  Special Adviser for Rural Development din ka bashi da idea. Kauyukanmu sun fi maraya bukatu nesa ba kusa ba, amma kunfi mayar da hankali ga  urbanization . Kananan hukumominmu tun daga Itass, Ganjuwa, Shira, Tafawa Balewa, Ningi, Toro, Katagum, Misau, Darazo, Jama are, Warji, Dass, Dambam da sauran wadanda ban ambata ba babu wadatar ruwan famfo sai na rijiyoyin burtsatse, babu tituna masu kyau, babu wadatar malaman makarantun firamare da sakandire sai a makarantun cikin birni, babu wadatar wutar lantarki, babu wadatar likitoci da malaman jinya a asibitocin su. Babu hannun gwamnati (tallafi) cikin sana o in da sukeyi duk kokari ne na kai da kai kawai a tsakaninsu.
Ba yau na fara bibiyar ayyukan administration dinka ba, sau tari ina budo (BATV) da Bauchi TV ina gani. Maganar gaskiya Your Excellency, gwamnatin ka tafi bada karfi ga raya maraya wai kara wa mai karfi karfi, kauyukanmu dake karkashin kananan hukumomi kuwa ko oho! Basu san ana yi ba wai kunu a makota! .
Da gama fadin hakan ta ja bakinta tayi shiru, ta maida duban ta ga talbijin, anyi sa a kuwa a daidai lokacin an nuno ya je bude wani estate da ya gina don bada haya ga ma aikata akan hanyar fita garin Bauchi. Amina ta juyo ta dube shi ta nuna t.vn da dan alinta ta ce
 you see.....? .
Ga mamakin ta har zuwa lokacin sauraron ta yake da  attention da dan murmushi akan fuskarsa. Ko zantukunta sun masa ciwo fuskarsa

8 / 11