Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sanadin KENAN 2 HAUSA READ Complete Hausa Novel by Sumayya Abdulkadir Takori

Author :  sumayya Abdulkadir Takori Category :  Romance

Chapter   2 / 11

3K to 6K   out of 31.5K words

duk abin da ki ke son saidawa, in dai a gida ne. Ni zan tafi, Allah ya ba mu alkhairi. Sai gani na biyu".
Kamar kada ta barshi ya tafi, ji ta yi in za su kwana suna hira ba za ta gaji ba. Mikewar nan da ya yi zai tafi kamar an soki zuciyarta. Babu yadda za ta yi tana ji tana gani ya bace a falon, ya bar mata sassanyan kamshinsa.
Da kyar ta ja jiki zuwa cikin gida, tambayar duniya Innarta ta yi ta fada mata abin da suka tattauna, ta kasa gaya mata komai. Laila ta ce a zuciyarta, wannan ita ce soyayya? Duk da ba wanda zai ba ta amsa ta yarda ta amince ita ce. Ta kuma yi mata mummunan kamu.
A bangaren Maaruf babu wani sauyi a zuciyarsa daga yadda ya zo, ya kuma tafi. Suka yi sallama da Hajiya da Baba Liman, motocinsu suka tashi. A cikin Jigawa suka kwana a hotel, da asuba suka kama hanyar Abuja.
Karfe goma na safe itama Hajiya direbanta ya dauko ta, sai Bauchi.
***
Amina na nan jiya-i-yau, sai ma baki da ya karkace. Ta samu Doctor da nosis suna yi mata gashin bakin. Hajiya ta daga hannunta sama, ta ce, "Ya Allah! Ka dubi wannan kankanuwar baiwa taKa, Ka ba ta lafiya. Lafiyarta kwanciyar hankalinmu ce nida mahaifinta da al'umma masu yawa, domin ubanta warkewarta kadai ce za ta sanya mishi nutsuwa ya ci gaba da ayyukan alherinsa ga al'umma".
Bai kara tunawa da Laila ba yana Bauchi ya tare wajen Amina, in ka ga ya fita sallah ce da wanka da canza kaya ya fitar da shi. Don bacci kan kujera rike da hannun Amina ya riga ya saba da shi. Hajiya na gefe kan sallayarta tana lazimi tana tausaya musu su duka. Tana ganin in ya yi auren nan maraicin zai ragun musu, za su samu wadda za ta rungume su su duka biyun, ta rage musu maraicin da suke ciki. Don haka ta yi wa Liman magana a tsaida daurin auren cikin sati mai kamawa, ta kuma umarci Ma'aruf ya kara zuwa wajen Laila su kara fahimtar juna.
Sai a lokacin ya tuna da ita. Bai yi musu ba, ya tsakuri lokaci cikin muhimman lokutansa ya je ya kara ganin Laila.
Sai dai hirar ba ta yi armashi kamar wancan zuwan ba. A dalilin wasu tsare-tsare na shagulgulan biki da Laila ta lissafo masa har guda bakwai. Shi mamaki ma abin ya ba shi, tana kauyen kayau kamar Ji-Kas don ta je birni karatu shi ne ta samo wannan budadden idon haka? To ina ga ta shiga manyan birane irin Bauchi da Abuja? Shi ba abun ya ce zai janye ba, Hajiya ba za ta yarda ba. Sai ya ga bari ya ba ta duk abin da ta ke so don a zauna lafiya, amma da sharadin babu keyarsa cikin shagulgulan nata.
Laila ba ta so haka ba, amma da ya tura mata leda cike da kudaden da ta bukata sai ta amince. Suka yi sallama ya tafi zuciyarsa cike fal da tunane-tunane masu sosa zuciya. A hankali ya tambayi kansa,
"Yaushe zan samu matar da za ta so ni don Allah ba don wadannan takardun ba? Yaushe zan samu matar da zan so kamar A isha? Yaushe zan kara jin soyayyar wata diya mace a zuciya ta bayan Aisha? Yaushe? Yaushe?? Yaushe???"

****
An daura auren Ma arouf da Lailah ranar lahadi, uku ga watan Fabrairu. Laila ta yi duk shagulgulanta a Dutse da kawayenta na jami'a, wunin biki kawai aka yi a Ji-kas.
Ya bada motoci don dauko amarya kamar yadda Hajiya ta umarce shi. Nan gidansa na Bauchi aka sauke su. Ya rufe bangaren Aisha domin a can duk wasu memories na rayuwar farin cikinsa ke ajiye. Sashen baki ya bai wa Laila, shi kuma da ma yana da nasa bangaren.
Dangin Laila sun yi dukkan kauyancinsu sun gama, an kwashe su an mayar Jikas, ya zama sai ita kadai cikin wannan katafaren gida. An tabbatar mata ba aikin da za ta yi, akwai ma'aikata, girki wannan sai ta ga dama, ba abin da ya fi wannan dadi ga Laila, domin da ma ita makiwaciya ce. Inda duk kuma aka samu makiwaciyar mace za a samu kazanta. To Allah ya fishshe ta.
Da daddare tana ta shirye-shiryen tarbar ango shiru ba ta ganshi ba. Ta yi kwalliya kamar-kamar-me, ta sha turaruka ba irin nata na gida ba, wadannan na cikin kayan lefenta ne da Hajiya ta sa aka hada mata. Tun tana zuwa gaban madubi tana kara gyara kwalliyar da daurin kallabin, har gyangyadi ya soma dibanta.
A lokacin ta ji alamun shigowar mutum dakin ta hanyar sauyawar kamshin da ta ke shaka a hancinta, da wani nau'in kamshin na daban da jefi-jefi ta kanji har ta gane na mutum daya ne, wato mijinta Engnr. Ma arouf Habibu Ji-kas. Ta ware ido tana dubansa da sassanyan kallo, shi kuma da alama wanka ya sha, ya zuba farar shadda, yana balle 'links' din hannun rigarshi. Suka hada ido, ya yi murmushi.
"Sannu da bakunta, ya ya ki ka samu gidan da ma'aikatanshi?"
Ta yi far da idanunta.
"Komai lafiya kalau".
Ya ce, "Madalla. Ni yanzu zan tafi asibiti ne, sai gobe zan dawo da safe sabida Hajiya ba ta dawo daga Ji-kas ba, da sai ta karbe ni".
Cikin mamaki Laila ta ce, "Asibiti? Me ake a asibitin? Waye ba lafiya?"
A hankali ya ce mata, "My Little daughter AMINA!".
Bai ja bayanin da nisa ba, ita ma ba ta tambaya da nisan ba, duk suka yi shiru. A zuciyarta tana fadin,
 Ranar  first night dina ita ce ranar jinyar 'ya? Mafari kenan da tsanar yarinya Amina ya shiga zuciyar amarya Laila. A tashi zuciyar yana sauraro ne ya ji ta ce 'mu je tare in raka ka'. Ko kuwa  me ya sameta? Da ya ga babu alamun ko daya cikin hakan daga gare ta sai ya sa kai ya fita.
"Night".
Ya furta a hankali. Yana mai daga mata hannu hadi da janyo mata kofar.
Tun daga wannan rana Laila ta ji ta tsani wannan 'ya ta Ma'arouf don ta lura an kar-maciji ne ba a sare kansa ba, babu uwarta amma za ta zame mata kishiya.

Duk da cewa bayan dawowar Hajiya daga Ji-kas da komawarta asibiti ya bata lokutansa yadda ya kamata, an barji amarci Laila ba ta gode ba. Wannan 'ya ta Ma'arouf mai shanyayyen barin jiki ta tsaya mata a makogaro kwarai da gaske, ganin yadda yake ba ta muhimmanci fiye da ita. Kai zata iya cewa fiyeda komai nasa. Ba ta taba zuwa ta duba ta ba, ba ta taba cewa a gaishe ta ba. Ma'arouf din ya kullaci wannan a zuciyarsa, bai dai nuna mata ba ne, ya zuba ido ya ga kamun ludayin ta akan  yarsa.
Baba da Alhaji mansur kan zo duba jikanyarsu lokaci zuwa lokaci. Zabe na karatowa, kamfen na kara tsananta gare su. Ya zamana ba shi da lokacin kansa, sau tari mantawa yake da Laila a cikin gidansa, sai ta kira shi a tafi-da-gidanka, amma hakan bai sa ya daina kula da 'yarsa a asibiti ba, amma yana mancewa da Laila a gida.
***
(Tenure) dinsu ya cika sun sauka daga kujerunsu na 'yan majalisar tarayya, 'yan rikon kwarya sun hau. Ana gab da yin zabe.

Yana zaune shi kadai watarana yana tunani. Hajiyarsa kullum girma kara hawanta yake, mijinta ya yi masa karah da duk wata alkunya da ta dace, ya sallama masa matarsa don kula da diyarsa. Ga Amina babu ranar tashi sai sanda Ubangiji ya nufa. Zaman asibitin nan ya ishe su duka daga shi har Hajiya har yarinyar.
Gara ta dawo gida a ci gaba da kula da ita a gida ko su ma hankalinsu ya tsaya wuri guda. Hajiya ta dade tana cewa a koma maganin Hausa za ta mike kan kafafunta yana basarwa. Amma yanzu zai duba shawarar nan tata.
Kuma tunda ga Laila a gida ba ta komai, sai ta dinga kula da ita, zai gwada na Hausan tsayin wata biyu a gani, in ba nasara a sake komawa asibitin, don ba a hada duka biyun a lokaci guda in ji Hajiya. In yaso Hajiya ta koma wajen mijinta ko na dan lokaci ne haka ta huta, jikin girma amma kullum bisa dardumarta ta ke kwana tana rokon ma Amina lafiya, uwarta gafara.
Sun yi wannan maganar da Hajiya, ta ce, "Ni ai da bakina ban ce maka na gaji ba".
Ya ce, "Na san ba ki gaji ba Hajiya, ba kuma za ki taba gajiya ba in don ta taki ce. Magana ce ta dukkanmu muna da hakki a kanki. Ni, Amina, da Baba Liman. Bai kuma dace a yi ta take nasa ba alhalin ina da mata mai koshin lafiya.
A dauko masu maganin da ki ka yi magana su fara, Laila ta kula da ita, ke kuma ki koma gidanki ki huta. Yadda fa nake son Amina haka nake sonki Hajiya ta. Ina son ki da hutu ko don karin lafiya a gareki. Bana son kowannenku ya jigata, hakkin dan Adam za a ciccire".
Sai ya ba ta dariya, ta ce, "To bari a kira masu maganin. Ita kuma Lailar zan yi magana da ita, amana zan bar mata Amina ba don na gaji ba".
Laila rasa abin cewa ta yi sanda Hajiya ke mata wannan maganar, wai za a bar Amina karkashin kulawarta, ita ina za ta iya wannan wahalar? Cikin yan watanni ta saba da hutu ya bi jikinta.
Gashi shagon kayan kawa na mata ta ke kokarin budewa. Ina taga lokacin aikin wahalar  yar su? Cikin dan zamanta a Bauchi, da Abuja da ta ke bin Ma'arouf lokaci zuwa lokaci ta yi kawaye matan abokansa, idonta ya kara budewa har ta ke ganin karatu wahala ne in dai don a samu abin yi ake yinsa.
Ma'arouf ya cika alkawari, ya ba ta jarin da ya yi alkawari, motoci sai wadanda ta zaba ta ke hawa, ga dankareren gida ita kadai a cikinsa tana juyawa yadda ranta yake so, ma'aikatan gidan duka yanzu tsoronta suke don kuskure kalilan za su yi ta ci mutuncinsu. In danginta na kauye suka ce za su zo cewa ta ke ba ta gari, don ba ta da lokacinsu, har Innarta kuwa. Amma tana mata aiken kudi da duk abin bukata, zuwa inda ta ke ne ba ta laminta. Wannan sai kawayenta matan 'yan majalissa da matan ministoci, ba su da aiki sai maganin mata sababbin fitowa na makudan kudade kuma suna ganin alfanunsu tunda suna ganin yadda suke so daga mazajensu da dukiyoyinsu ba su da shamaki akan komai.

****
Hajiya ta turo masu maganin gargajiya tun daga Maradi ta Nijar. Sun fara yi wa Amina magani a gida, har tsawon kwana goma. Amina dai ba ta mike ba, Ma'arouf ya sallame su suka tafi, aka samo wasu daga Kauran Namoda, suma sun buga irin tasu rawar ba nasara, amma dai bakin Amina da ya gicciye ya koma daidai. Su wadannan ya kara musu ihsani fiye da na baya. Haka kowa ya yi ta zuwa yana kwasar rabonsa daga wurare daban-daban har watanni biyu da Engnr. Ma'arouf ya diba wa masu maganin gargajiya akan Amina suka cika, don haka ya dakatar da zuwansu haka.
Tafiya ta gaggawa tal kama shi zuwa Abuja a washegari, ya bar Amina karkashin kulawar Laila.
Bayan tafiyarsa, Laila ta kira kawarta Nazi a waya.
"Wannan gawa-ta-ki-ramin ya dauko daga asibiti ya kawo min gida, uwarsa ta gaji da wahala ta gudu balle ni, na kasa gane me yake nufi, in bar harkokin da ke gabana in zauna da ita ko ya ya? A pampers fa ta ke kashi da fitsari, ni ina zan iya wanke ta? Abinci sai an ba ta a baki, wanka sai an yi mata, brush sai an yi mata. Na rantse da Allah Nazi ba zan iya ba, ya ya zan yi ne?"
Nazi ta tuntsire da dariya,
"Ki barta da masu aiki kawai, ki yi harkokin gabanki".
"Masu aikin gidan nan duk maza ne, ga shi yarinyar mace ce (I'm confused), ki ba ni shawara".
"Na ba ki ai kin ce ba haka ba, ina ruwanki da wani maza ne ko mata, ba biyansu ake su yi aikin ba? Kuma me za su dauka a jikin shanyayye? Ke ni rabu da ni ina da abin yi yau (container) ta za ta iso, taki sai jibi, mu wuni lafiya".
Nazi ta kashe wayarta.
Laila ta tashi zuwa dakin Amina, wanda don matsayi yana kallon dakin barcin Babanta.
Ma'arouf yadda ya tsara gidansa na Bauchi babu (space) na karin mace. Katon falo ne shi da Aisha, ga dakinsa, ga na Aisha ga na yaran da za su haifa yana kallon dakin barcinsu. Kicin da store a kasan bene suke da wani katon falon da ciki a kasan. Sai bangaren ma'aikata a can waje kusa da (gate) din gidan.
Dakin dake falon kasa wanda don baki akayi shi shi ya zama na Laila, na yaran da ma can na Amina ne tun mahaifiyarta na raye, yanzu da ta baro gadon asibiti ma nan aka dawo da ita. Ya rufe dakin A isha.
Laila ta daga ido tana kallon irin tsarin da aka yi wa dakin. Daki ne na 'yan gata wanda aka kashewa dukiya ba kadan ba. Kamar na 'ya'yan Turawa, ga wani gadon yara mai matattakala ga (teddy Bears) nan da can, ga (computer game), ga duk wani nau'in wani abu da yaro mai gata zai bukata. Fentin dakin da komai da ke cikinsa (light blue and pink), toilet din kuwa ba a magana don kyau da ban sha'awa ko dakin dan shugaban kasa sai haka.
Ta jinjina kai, wani bakin ciki ya kule ta. Ta sa hannu ta shafi cikinta, ita har yau ko kyankyaso bai shiga ba, da ta kawo su nan su ma ta rage takaici. Ta daga kai ta dubi Amina a gadonta tana kwance tana kallonta. Kyakkyawar yarinya mai kama da ubanta kamar ya yi kaki ya tofar.
Tun safe ko ruwan shayi ba ta bata ba, ba ta canza mata (pampers) ba, ba ta dauko ta ta sanya ta a (wheel-chair) da Babanta ke sanya ta a ciki ya dan zagaya harabar gidan da ita ba, ko ta samu canjin iska.
Ta karasa gaban yarinyar tana kare mata kallo a yatsine.
"Ni ba zan iya wahalar da ubanki ke yi da ke ba, kakarki kanta ta gaji ta gudu shi ne ni za a hada ni da jangwam. Tashi ni su zo su wanke miki kashi".
Ta danna kararrawar ma'aikatan gidan, nan da nan mutum biyu suka zo. Samari ne guda biyu masu share-share.
"Ku dauke ta ku kaita toilet ku yi mata wanka, ku cire mata (pampers) din tun dakin bai soma wari ba".
Matasan biyu suka kalli juna kamar masu yin shawara, ta galla musu harara.
"Ko ba za ku yi ba ne?"
Da sauri suka ciccibo yarinyar, daya ya riko kai, daya ya riko kafafu suka yi toilet da ita, suka tube ta suka cire pampers za su soma wanke ta. Kamar an jefo shi, Ma'arouf ne ya shigo babu zato babu tsammani. Ya yi (missing flight) dinsa ne mai zuwa Abuja ba da son ransa ba.
Ashe da rabon zai ga bacin ran da bai taba shiga kwatankwacin sa ba.
Cikin matsanancin mamaki ya dubi Laila. Muryar sa kamar ta wanda zai fashe da kuka.
"Maza balagaggu ki ka sa su tsiraita 'ya ta haka Laila? 'Yar tawa kwalli daya? Laila ko auren kiyayya ki ka yi da ni ba za ki iya taimakawa mara lafiya marainiya ba? Kina nufin su sanya hannu a (private part) din diya ta? Ban taba dukan mace ba, bana fata in fara a kanki.
Ki je duniya ce, kuma in gaya miki wannan yarinyar ta fi min komai da duk abin da na mallaka a duniyar baki dayanta. Ke ma mace ce, kuma za ki haifa, ba ki san ya ya kaddara za ta yi da abin da ki ka haifa ba kina raye ko ba kya raye".
Kallo daya ya yi wa ma'aikatan suka saki (pampers) din da suke cirewa suka yi waje cike da addu'a a cikin zukatansu, kada Allah ya sa wannan ya zamo sanadin hanyar abincinsu. Su ma sun ji umarnin da aikin da aka sanya sun 'odd' to amma su me ye laifinsu? Salin-alin suka fice.
Laila ta rasa abin cewa, ba ta taba tsammanin zai dawo ba sai bayan kwana uku kamar yadda sukayi dashi. Ta kulla a zuciyarta ko 'cangal' ba za ta yi wa yarinyar ba har ya dawo. Maganganun da ya gasa mata ba su ta zata ba, ta fi zaton dan banzan duka daga gare shi in tayi la akari da yadda ta lura yana son yarinyar.
Da sauri ya nade hannun riga ya wanke Amina, da kansa ya yi mata wanka da soso da sabulu mai kamshi, ya nado ta cikin shawul ya fito da ita. Har zuwa lokacin Laila a tsaye ta ke bakin (toilet) ta kasa ko kwakkwaran motsi, tana kallo ya shafe Amina da basilin, ya sanya mata sabuwar (pampers) da sababbin riga da siket masu kyau, sannan ya yi waya kicin a kawo masa 'tea' da 'pancake'.
Da kansa ya rika bai wa Amina har ta koshi ta ture. Jiki ba kwari Laila ta wuce, don ganin yadda ya baiwa banza ajiyar ta (ya yi kamar babu ita a dakin). Ya sumbaci Ameena a goshinta ya mayar da ita ya kwantar.
Ya fito ya zauna a daya daga ni'imtattun kujerun falon. Ya kai hannun damansa ya dafe kansa dake sara masa, ji ya yi dan son da ya soma yi wa Lailar na decreasing gradually (raguwa a hankali). Zufa ta shiga karyo mishi da ya

2 / 11