SANADIN KENAN 2 HAUSA READ BY TAKORI.doc

Author :  sumayya Abdulkadir Takori Category :  Romance

Chapter   1 / 11

1 to 3K   out of 31.5K words

??????>??  2?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????.?

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F3WordDocument?????
0Table?????????!Data
?????????????????? P???KSKS??
vnr???????kkkk8??dkQ!g!:?!g!'!=! I!?!?!$o?!*kk? ? @kkkk?!K?OKg!O?!KOQ!Q!kO ?^`??^Normal d??,CJmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJhA`???hDefault Paragraph Font$mH sH nH tH _HOJPJQJ^J?i`???? Normal Table0:V 4?4?l4?4?la?6 $mH sH nH tH _HOJPJQJ^J(k`???(No List X`?Xheader

?H?$$mH sH nH tH _HOJPJQJ^J??o??0Header Char_34457df9-d6f7-4f81-9850-48c6ddbb647d,CJmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJX `Xfooter

?H?$$mH sH nH tH _HOJPJQJ^J??o?!?0Footer Char_f8179cde-3f89-4ca3-aa0e-ebb39081e3d5,CJmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJZU`?1Z Hyperlink0>*B*
mH sH nH tH _HOJPJQJ^Jphc??n<??
T v??8"\%'*(,?.V2 4>59?;H=A?BNE?JM?O?PbVY?\:_Zb?f4j?k?l?p2s?w?yr{?~?4?8????????????B???4??????????T?B?????????J???h?h??????????P?@?f?l???h? ???F????????????b?????
D? ? @?R?4??\???? ?!?"$?$?&\(?)? SANADIN KENAN!











2














Sumayyah Abdulkadir
takorikabara@gmail.com
 HYPERLINK "mailto:Babbangoro2015@yahoo.com" Babbangoro2015@yahoo.com

SADAUKARWA
Sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, Allah ya hada mu cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.
DON TUNAWA DA
Domin tunawa dake marigayiya Kakata kuma Goggo na HAJ. HAWWA ABUBAKAR WALI.
GARGADI
Ban yarda a kwafi wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ko karanta shi a rediyo ba tareda iznina ba, hakan zai kaimu ga tsayawa gaban hukuma, wadanda bansan inda kuke ba kuma zamu hadu a kotun Allah ranar da bawa bashi da abin biyan hakkin dan uwansa sai kyawawan ayyukan sa. Takori.
TUNASARWA
Littafin SANADIN KENAN! Kirkirarren labari ne don fadakarwa da nishandantar da mai karatu kamar sauran littattafan TAKORI. Bashi da nasaba dani ko wani nawa ta kowacce fuska, SANADIN KENAN! Kirkirarren labari ne don haka a kiyaye.
SANADIN KENAN-2
Sun isa Ji-kas lafiya, wadda ke karkashin karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa. Maigidan Hajiya Malam Halilu, shi ne babban limamin garin Ji-kas, saboda haka gidan na Hajiya ba boyayye ba ne. Ga kuma gyaran da Ma aruf ya yi masa ya zama abin kwatance, in za a yi kwatance za a ce gidan Hajiya Saude farin Gida, kamar ita kada ke da gidan babu kishiya.
Hajiya ba ta kara haihuwa ba tun haihuwar Ma arouf, wannan kuma tsarin Allah ne, kuma hakan bai sa Malam Halilu ya taba canza mata fuska ba ko sau daya, don shi yana da  ya yan har takwas duk maza wadanda ya haifa tareda matarsa ta lalle Lami wadanda ke karatu karkashin kulawar Ma arouf. Tafiya da Hajiya ke yi ta huta wajen Aisha bai taba damuwa ba. Haka yanzu da ta ke jinyar jikanyarta
Akwai kyakkyawar fahimta tsakaninsu. Kishiyarta Lami ba wai ba ta kishinta ba ne, kawai wutsiyar rakumi ce ta yi nesa da kasa, don gabadayansu har maigidan kamar karkashin inuwar Hajiyar suke, shi ya sa ta shafa wa kanta salama, ta kwantar da kai ta ke cin arziki hankali kwance.
Yaran makota suna ta tsalle suna murna Hajiya ta dawo, don sun san tsarabar chaculet ta zo, suna ta kwaso kayanta daga mota suna direwa kofar dakinta. Ta sa mukulli ta bude dakinta, ya yi kura sosai, kwana arba in da biyu ba kwana biyu ba. Ta rasa me za ta ce musu, tunda yau daga asibiti ta ke ba ta da alawa. Sai ta sa mai aikinta Tambai ta gyara dakin, ita kuma ta sallami yaran da kudi ta ce su je su sayi alawar. Ta fada kewaye ta yi wanka, ta yi sallar la asar da ta riske su a hanya. Ta kwanta tana hutawa, Tambai na ba ta labarin abubuwan da suka faru ba ta nan na suna, biki da mutuwa. Hajiyar ta jajanta, ta ce, in ta huta duk za ta leka, koda yake kwana uku kacal za ta yi, Aminatu na asibiti har yanzu.
Tambai ta gama abinci lafiyayye ta zubo mata. Lami ta shigo suka gaisa ita ma da nata kabakin abincin. Hajiya ta yi godiya ta zauna tana jajanta jikin Amina, a hakan Malam Halilu ya dawo ya riske su.
"Yau babbar bakuwa gare mu ashe?"
Abin da ya fara fada kenan yana ta fara'a, da gani ya yi murnar ganin matar tasa.
Ta ce, "Ga ni nan dai, duk da ba zama zan yi ba zan koma, har yanzu Mamar Manzo na kan gadon asibiti".
ya ce, "Assha! Allah sarki uwata, Allah ya kara afuwa. To yaushe za ki koma ke nan?"
Lami da ta ga sun manta ta a wajen sai ta fita ta ba su waje, dan kishi-kishi na cin ranta. Don in ka ga maigidan nasu na wannan fara'ar to tabbata a gaban Hajiya Saude yake.
Bayan sallar isha ya dawo daga masallaci ya ci abincin dare, duk a dakin Hajiyar tunda ita zata karbi girki, ta ke gaya masa abin da ya taso ta rana tsaka, wato nema wa Ma'aruf aure na gaggawa.
Malam Halilu ya gama sauraronta, ya gyada kai.
"Kirawo min shi mu yi magana yanzun nan, akwai kuskure cikin al'amarin nan".
Hajiya ta dauko wata katuwar (cellular) wadda ake amfani da ita a wancan zamanin, duk da haka sai masu hannu da shuni ke iya rikewa. Ta danna kiran Ma arouf.
Yana dakin tattaunawa da dukkan 'yan majalissar Najeriya, ya manta bai kashe tafi-da-gidansa ba, kiran Hajiya ya shigo da sunan da ya yi 'saving' dinta 'MA MERE' wato  uwata da harshen Faransa. Sai ya fito waje ya amsa saboda dukkan uzurinsa ba ya (ignoring) kiran Hajiya.
"Karbi, Imam ke son magana da kai".
Ya karba suka gaisa da Malam.
Malam Liman din ya tambaye shi, "In kana kan uzuri mu bari sai ka koma gida ka samu nutsuwa".
"Babu komai, mun gama. Yanzu kowa zai tafi".
Malam Liman ya ce, "Madallah.
Wato na ji kuna son yin wani shirme ne kai da uwarka, aure ba abin wasa ba ne, ba kuma wasan yara ba ne. Umarnin Ubangiji ne, don haka dole a tsarkake niyya wajen yinsa.
Kuna so ku ce don siyasa za ku yi aure, wanda wannan aure ba karbabbe ba ne a wurin Ubangiji. Ka sanya ikhlasi a zuciyarka, cewa za ka yi auren sabida Allah ba don ka yi siyasa ba, sannan ka ga matar sau uku don ka tabbatar da lafiyarta kalau kamar yadda Manzo (S.A.W) ya yi umarni. Ku tattauna, ku aminta da juna, a yi baiko sannan a sanya lokacin aure, wannan shi ne aure, amma ba ka ce ta zo ta nema ma aure kai babu ruwanka ba ko ganin matar ba ka yi ba, wannan aure bai yi ba".
Haka ya yi ta jawo masa nassi na Alqur ani da hadisi masu nuni da tsarkake zuciya wajen yin aure ba don cimma wata manufa ta duniya ba.
Jikin Ma arouf ya yi ligib, yana son dattijon ko don farke gaskiyarsa a kan komai tsakaninsa da Allah ba irin malaman da ke ba da fatawar son rai don a ba su wani abu ba.
Ya ce, "Malam, na yi niyyar aure da zuciya daya, ku zaba min mata kowacce iri ce, zan zo mu ga juna. Amma ni ba zan iya zaba da kaina ba, sai in ta ganin kamar na ci amanar A isha".
Maganarsa ta karshe ta baiwa Liman tausayi, shi kansa ya girgiza da gushewar A isha a doron kasa, ya sha tunanin a ina Ma arouf zai samo mata kamarta? Sai ya yi saurin kauda tunanin, ya ce,
"Allah zai dubi kyakkyawar zuciyarsa da kyawawan halayensa ya ba shi mace tagari tamkarta, ko fiye da ita".
"Babu wani cin amana Ma arouf, A ishar za ta so ka samu nutsuwa a bayan ranta, ba ka yi ta ragaita ba. Yanzu na ji magana, za a bincika, insha Allah Allah zai dubi zuciyarka da halayenka na kyautayi ga kowa, Ya ba ka mata ta gari".

Washegari Hajiya da maigidanta sun gama tunaninsu tsaf! Sun kuma tsaida kan 'yar maigarin Ji-Kas, wadda ke karatu a jami'ar Jigawa. An sa ranar aurenta har za a yi watannin baya mijin ya ce ya fasa. A ganin Hajiya da Baba Liman, zai fi dacewa su nema masa 'yar birni mai ilimin zamani, ba irin yaran su na kauye ba, Ma arouf din zai fi son hakan.
Hajiyar ta shirya da kanta ba aike ba da yammacin washegari ta tafi gidan Maigari, shi kuma Liman ya tafi wajen mahaifinta.
Kowanne ya fadi abin da ya kawo shi. Amsa iri daya suka samu. Yaransu 'yammata uku ne, Sadiya, Laila da Asiya. Wadda duk suke so za a ba Ma aruf ba tare da jan dogon lokaci ba.
Amsa daya su ma suka samu daga Hajiya da Liman, a ba shi wacce aka ce ta ke jami'a, suka ce, Laila kenan. To Allah ya sa a yi a sa'a.

Uwar Laila guda ce kawai ba ta rangada ba, amma ta taka rawa a tsakar dakinta, 'yar ta aka zabarwa attajiri dan Hajiya Saude farin gida. Nan fa kishi ya tashi, da ma matan uku ne, kuma kowacce na da 'ya budurwa, wato Asiya da Sadiya, sai dai su bana suka kammala makarantar sakandire. An zabi ta Jami'a an bar su. Wannan abu ya yi musu ciwo.
Laila kuwa da ma ba dama ce wajen iya yi da kidifiri. Jin mijin da Allah ya kawo mata rana tsaka bayan Mahadi ya fasa auranta kan laifin tara samari barkatai, ta ce da uwarta, "Ashe gaba ta kai mu?"
Uwar ta ce, "Gobarar titi a Jos ba!".
Ta ba ta hannu duka kashe tare da rungume juna suna murna, babu godiya ga Allah, sai ka dauka wasu kawa da kawa ne ba uwa da 'ya ba, kai ka ce wata ajiya ce suka yi yanzu suka dauki abarsu ba nufin Allah ba. Ita kadai ce mace cikin 'ya'yanta, don haka ba karamin buri ta ci a kan Laila ba, ga shi tun ba a je ko'ina ba Allah ya fara cika mata.
Kwanan Hajiya uku ta ce Ma arouf ya baro ayyukansa ya zo su ga juna da matar da suka zabar masa, don a bar sahihiyar magana kafin su bar Ji-kas, dukkansu hankalinsu ya koma kan Amina. Sai a lokacin ya gano Hajiya hannun likitoci ta bar Amina, hankalinsa bai tashi da yawa ba, don ya yarda da kokarin Dr. Umar Bolori a kan Amina da kaunar da yake masa.
Motoci uku suka biyo shi a baya zuwa Ji-kas ban da securities dinsa guda biyu da suke tare da shi daga Abuja har Jigawa. Mutane dankam sun yanyame kofar gidan Hajiya Saude kamar yadda suka saba duk sanda ya zo Ji-kas, to yau ma hakan. Da kyar ya samu ya shige dakin mahaifiyarsa bayan ya sa sakatarensa Idris ya sallame su.
Ya yi sallah ya ci abincin da Hajiya ta tanadar masa, sai da duhu ya shigo bayan magriba Liman ya karasa da shi gidan Maigari, lokacin babu idon mutane. Ya sanya 'dark-shade' wanda ya boye kwayan idanunsa, yana sanye da shadda (getzner) ruwan siminti da hula zanna kalar shaddar, an yi ma rigar ado da zaren (silver) wanda ya kayatar da shaddar sosai. Da kafafunsu suke tafe suna hira har gidan Dagaci, wanda ya karbe su hannu bibbiyu, ya shigar da su turakar da yake saukar bakinsa. Ma arouf ya gaishe shi cike da ladabi ya amsa cike da kauna, ya rike hannunsa cikin nashi yana fadin,
"Sai ka yi hakuri da ita fa, duk cikin 'ya'yana ita ce mai giggiwa".
Abin ya ba wa Liman dariya, ya ya kai da aka zo neman auren 'yarka ka ke fadar halinta mara kyau? Shi kam maigari iyakar gaskiyarsa ya ke fadi, don kaunar da yake wa Ma arouf ba tun yau ba bazata bari ya yaudare shi ba.
Engnr. Ma'aruf Ji-kas, yana so ya tambayi Maigari,
"Giggiwa wace iri?"
Amma ba zai iya ba, saboda karamcin dattijon. Ko dago kai ya kasa saboda tsabar girmama manya.
Maigari da Liman suka fita kofar gida, suka dasa hira bayan Maigari ya shiga gida da kansa ya yi kiran Laila.
Laila ta yi dauri ya kai sau goma tana warwarewa, ta sa kaya ya yi sau takwas tana canzawa. Ta fesa turare ya yi kala biyar, amma har yanzu ba ta ji tana kamshi ba. Uwarta na kara zuga ta.
"Ta ina zai ganki ya ce ba ki yi ba? Ai karyarsa ta sha karya".
A can falon bakin Maigari, Ma arouf ya fara kosawa. Har ya fara duban agogo. Ba ya son jira a rayuwarsa. Ko wanne minti daya mai amfani ne a wurinsa. Rayuwarshi a kayyade ta ke cikin tsara lokaci, minti goma sha biyar ya tsara zai yi tare da ita, ga shi ta ci minti talatin ba ta ma fito ba.
Ya dan ja tsuka, ya murza zoben tsari na azurfa da ke hannunsa, wanda Baba Habibu ya sanya masa da jimawa, don a cewarsa rayuwa irin tashi sai da neman tsarin jiki. Yana son zoben don a kowanne lokaci yana tuna masa da Baban, ya kira shi a waya ya ji lafiyarsa, ko ya zo ya ganshi, ko ya aika a dauko masa shi a duk inda yake (kafin rasuwar Aisha).
Sai lokacin ya ji takun takalmi kas-kas-kas, Laila tsayawa ta yi a soron gidansu hancinta na sirnano mata wani kamshi mai sanyaya zuciya da bata taba jin irinsa a rayuwarta ba. Sai ta ji turarukan da ta gumbudo sun hau mata kai kamar ta juya ta canza kaya. Wata zuciyar ta ce koma canza kaya ki dawo ki tarar ya yi tafiyarsa, duk lokacin da ki ka bata bai ishe ki ba?".
Sai ta fasa komawar, ta yi sallama a dakin tare da daga labule ta shiga.
Fitilar aci bal-bal ke ci a dakin, haskenta ya haska mata Ma arouf Ji-Kas wanda ya dago ido daga kan agogon (Rolex) da ke daure a fatar hannun hagunsa ya dube ta cikin hasken a ci bal-bal din, sai ta ga kamar idanun sun tara hawaye ne. Amma da ta kalle shi sosai, sai ta gane ba hawaye ba ne, halitta ce. Dogo, mara kauri, yana zaune bisa doguwar kujera kafafunsa a mike yana murza wayar hannunsa. Shaddar jikinsa sai maiko ta ke da alamun ba ta (squeezing) sam-sam. Tafin kafarsa fari sol kamar ba ya taka kasa.
Laila ta tuno yadda kullum ta ke fama da goge kaushin tata kafar da dutsen kaushi. Kai Allah mai kyauta da kari, wannan sardidin miji Allah ya dauko ya ba ta har gida. Labban bakinsa jazur da su kamar yankan reza, fuskarshi (intact) cikakkiya, komai ya zauna daf a muhallinsa; wato ido, hanci, gira kowanne daidai yake a inda Allah ya halicce shi. Ba fari ba ne can, sannan ba za a kira shi baki ba. Kamar tsafta ce ta bayyanar da haskensa, amma ba shi da hasken fata sosai. Ga wani saje ya kwanta tun daga gefen fuskarsa sai sheki yake, da gani yana samun (extra) kulawa.
Ta ga in ta tsaya kallon mijin nata zai dauke ta sakarai, dole ta kama kanta, ta zauna a kujerar da ke fuskantarsa, ashe ta manta kushin din kujerar a rarake yake sabida tsufan kujerun tana zama ta burma ciki.
Tana kokarin fitowa ya ce, "Sorry". Da murya mai nuna kulawa.
Ita dai kunyar duniya ta hana ta magana duk da ba ta ga alamun ya yi mata dariya ba. Ta bar kujerar ta koma wata duk suka yi shiru. Ya gaji da shirun ga dare yana yi, kuma cikin Jigawa za su kwana a hotel.
Ya ce, "Ba ki iya gaisuwa ba?"
A dan daburce ta dago domin ba ta zaci zai yi maganar ba kamar daga sama ta ji ta.
"Iyee, na'am?"
Ya maimaita, "Ba ki iya gaida na gaba da ke ba?"
Da sauri ta ce, "Ka yi hakuri, ina wuni?"
Ya basar, "Ya ya sunanki?"
"Laila!"
Ta amsa.
Ya maimaita sunan cikin ransa. Ko ba komai sunan ya dace da ita, kyakkyawa ce da kuma alamun mai son ado ce, uwarta bafullatana ce don haka fara ce tas!
"Ni sunana Ma arouf". Ya fadi a gajarce.
"Na sani". Ta ba shi amsa.
"Ya akai ki ka sani?"
Ta dube shi da kyawawan idanunta kamar ta ce waye bai sanka ba a garin nan? Sai kuma ta kama kanta, ta ce,
"Baba ne ya fada".
Ya gyada kai. Cikin sakakkiyar murya ya soma magana sosai duk da ba ta fi layi biyu ba a ganinsa ya yi cikakken bayanin da ya dace.
"To ni Laila na zo ne don mu ga juna, mu kuma fahimci juna kamar yadda iyayenmu suka yi umarni. Na ganki na karbe ki a matsayin matar aure na ta biyu. Na taba yin aure har ina da 'ya. Wannan shi ne".
Jimlar nan 'kamar yadda iyayenmu suka yi umarni' bata yi mata dadi ba. Wato ba soyayya ta kawo shi ba, umarnin iyaye ne. Wata zuciyar ta ce, 'Ban da abinki Laila yaushe akayi daren har garin zai waye? Yaushe ya ganki har da zai yi zancen soyayya? Tunda ya riga ya zo a hankali za ki sa ya so ki, ki mallake shi ke kadai, ki mantar da shi tunanin kowace 'ya mace har matacciyar da aka ce yana masifar so'. Wannan tunanin ya sa ta yin murmushi, har ya zaci shi ta yi wa murmushin.
"Sunana Laila, ta biyar wajen Baba, ta farko wajen Innarmu. Ina karatu a jami'ar Dutse ina karantar home-economics, yanzu ajina biyu. Na amince ni ma, Allah ya tabbatar mana da alkhairi".
Ya gyara zama kamar ya gaji da zaman yana son mikewa ko jijiyoyin bayansa sa warware daga zaman jiran da ta sa shi. Bai yi shiru ba ya ce,
"Me ya sa ki ka bar ni na yi ta jiranki? Ko kin san jira na daya daga cikin abubuwan da na tsana a rayuwa ta?"
Da hanzari ta amsa laifinta, ta karyar da kai ta ce, "Ka yi hakuri".
Ya ce, "Na yi. To ga shi kina karatu a Jigawa, ni kuma Bauchi zan ajiye ki. A can gidana yake, kuma can na fi zama, ko ya ya za a yi?"
Laila ta kasa jan ajin a wannan lokacin cewa ta yi, "In za ka bar ni in yi business zan ajiye karatun".
Ya dan dube ta na sakanni, "Business kuma? Karatun naki fa?"
Ta girgiza kai, "Barinshi zan yi. Na fi so in yi kasuwanci".
Cikin mamaki ya ce, "Bauchi ba a karatu?"
"Ana yi, ban so ne kawai".
Bai ja da yawa ba, ya zunkuda kafada irin ko ohon nan.
"Za ki saida

1 / 11