Author : BADIAT IBRAHIM Category : African Stories & Novels
Marubuta da masu business*
*Maza ku hanzarta mun shirya tsaf domin kayatar da ku da graphics kalakala Kuma cikin farashi me sauki*
Logo
2d Logo
Flyer
Invitation card
Invitation vedio
Save the date card
Save the date vedio
Book cover
Account sticker
Makeup Flyer
Business Flyer
Da dai sauransu
Sannan Kuma Ina koyarwa ga duk me bukata cikin sauki
08069638776
*All netwk Data is available*
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻
[10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 17
Ana cikin wannan Gaga_gaga sai ga ƴan makaranta sun dawo. Ganin mu a tsakar gidane yasa suma suka shigo ɗu. Amina ta kusan murjema ƙanwar Hajiyayye ƙafa. Ai kuwa ta lailayo ashariya ta mako mata ta ɗaura da cewa.
"Shegiya mai kama da uwarta, dangin ƴan maula, masu kwana a bakin masallaci" Wani zafi naji a zuchiyata, nasan haushi suke ji da abinda ya faru da Yaya Use da Hajiyayye, da kuma haushin an soma tafiya da kayana ita nata gasu nan jibge a tsakar gidan. Ina ganin haka na miƙe dan take takensu so suke a tanka su yi buyagi a tsakar gidannan. Su ja mun sale salin tsiya.
Sabira mu soma yi ma maƙota sallama, kafin lokacin tafiyar tamu tayi, yau dai ba zuwa islamiyya sai kuma gobe." Fita mu ka yi a gidan har da yaran. Bilkisa tana ɗakin Kaila ita da ƴan uwanta. Muna fita mu ka samu isa a waje isowarshi kenan da matarshi uwar gidanshi Jamila. Itace muke mutunci, amaryarta kuma ƙawar Hajiyayye ce unguwarsu ma ɗaya.
Jamila kece a tafe? Gashi kin zo zamu shiga yawon sallama da maƙota" Ɗan dariya tayi tace.
"Ai sai mu je. Da fatan ba ki yi fishi ba. Kin haihu ko barka banzo ba, an muku amarya ma banzo ba"
Babu komai. Isa barka da rana" Muka gaisa da Isa tare da mun murnar komawa sabon gida.
"Kaila ne yace in soma kai ku can gidan. Ku shiga maƙotan ku fito sai mu wuce in soma ajjiyeku, sai in kwashi sauran matan nashi" Tare da Jamila mu kai ta bin maƙota muna musu sallama. Sai Allah sanya alkairi suke yi mana. Muna fitowa Isa ya figemu a mota sai sabon gida. Kaila ne ya buɗe mana get da sauri, ni naga sai dariya yake yi. Muna haɗa idanu ya gintse dariyar tashi, ya sau get ɗin. Masha Allah gida yayi kyau ya sha fenti mai ruwan ƙasa, ga filin tsakar gida masha Allah. Muna firfitowa Kaila ya soma masifa.
"Haba isa dana san haka zaka yi mun ai da ni zan ɗauki motar in je in ɗakkosu. Bilkisa baka ganin baƙine suka zo mata daga Zaria? Da direba ma suke tafe, direban nasu yaje Bauchi ɗakko wani saƙone. Da sai ka bar su Shanono su zama ƙarshe." Isa ya hararashi yace.
"Kai dai kaji kunya. Shanonon zan kawo a ƙarshe gidan da tare kuka zaɓi yanda fasalin gidan kuke son ya kasance. Ko ka mance tare kuka dinga zuwa sauke block ne? Duk wani wahalar ginin gidannan da itafa akayi. Dan kawai kayi amarya shikenan sai itace zata zama ƙarshen shiga gidan?" Ni dai ina gefe kamar yajin ƙosai. Yara kuwa guje_gujensu ma suke faman yi a tsakar gidan. Isa ya nuna mana hanyar babban falo, inda shine mahaɗar ko wanne pat na cikin gidan.
"Bismillah ku shiga daga ciki, ai kinsan ɗakinki" Sai lokacin Kaila yayi magana yace.
"In kin shiga ki jirani a falo in na dawo zan nuna miki ɗakin ki. Kai kuma ka bani keyn mota in ka gama soki burutsun zancan" Fisge keyn motar yayi a hannun me shi. Isa ya koma ɓarayin mai zaman banza ya zauna, suka fita a gidan. Mu kuma muka shiga ciki. Masha Allah, ko ina yaji tayil, ga ƴan kayayyakina a gefe a cikin babban falon, amman banga na bilkisa ba. Kuma duk ƙofofin ɓangarorin uku a rufe suke da ƙwaɗo, dan Jamila sai da ta murɗa ko wacce ƙofa ta ji ta gam. Doguwar kujerar da Sabira ta bani akai muka zauna, jikina kamar an watsa ma kaza gishiri haka nake ji. Sai haɗiɗiyar yawu kawai nake yi. Minti ashirin bayan zuwanmu sai ga Kaila da Isa motarsu ta shigo. Sabira ce ta leƙo take sanar mana.
"Gama su nan sun dawo, Amarya a motar da ƴan uwanta suka zo aka kawo su, Abban Sulaiman kuma ya ɗebo Hajiyayye da ƴan uwanta. Ni dai ina zaune jigum, har su Bilkisa da tawagarta suka shigo. Hajiyayye kuma suna wajan motar kaya data shigo yanzu. Ƴan uwanta suka shigo cikin falon da muke, tare da Kaila. Key ya jefo mun cinyata, tare da nuna mun ƙofar ɗakin dake gefe can. Ciki biyu da falo ne ɗakin sai bayan gidu a ko wanne ɗaki in ban manta ba Dan da sunan Amadudu aka yanki ginin ɗakin. Ashe ni zan zauna a ciki. Hajiyayye kuma ya miƙa mata keyn ɗakin da a da nasan turakarshi ne, Bilkisa kuma ya buɗe mata ɗakin da aka gina shi da sunana, ɗaki mai babban falo da ɗakuna har uku, bayan gida biyu, ga kitchen yalwatacce, har kantocin cikin kitchen ɗin ni da kaina na zaɓi samfurin wanda nake so, ashe rabon wata ne. Wannan shine kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Ana cikin haka sai ga Amadudu da Hindatu sun shigo babban falon da sallama. Key ya miƙa ma Amadudu.
"Ɗakunan dake tsakar gida, kai da Hindatu sai ku jera kayanku a ciki. Ɗayan yaranku sai su dinga kwana a ciki. Ɗayan kuma Shamwila sai ta dinga kwana a ciki " Gaba mu ka yi abin mu, Jamila ta buɗe ƙofar ɗakin muka shiga. Dukkanmu tsuru_tsuru mu ka yi a tsakar ɗakin muna kallon abun mamaki, ni ko hawaye ne kawai yake gudana a Idanuna tsabar damuwa har wani jiri ne yake ɗibata. Jan fentin mai kaila ya shirɓinamun a ɗakunan nawa babu ko sofane kalar jinin kare ( maron). Ni ɗakin ma tsoro ya bani wallahi, dan tunda uwata ta haife ni ban taɓa ganin fenti mai kalar jinin kare ido da idoba sai yau. Numfashi na ja mai zafi. Sabira ta kawar da tunanina da faɗin.
"Kai Tabarakalla masha Allah. Waje yayi kyau. Tani Allah ya sanya alheri, Jamila mu soma shigo da kaya ciki ko, mu kafa mata gado?" A tsaye suka fice suka barni ina kalle kalle. Ɗayan ɗakin ma an toshe ƙofarshi da bulo ga halama nan ana gani. Shi yasa naga wata ƙofar a cikin falon, kuma wannan ɗakin da aka toshe yafi girma, bayan gidan ɗakin kuma yafi kyau. A wannan gidan ɗinma a falo yarana zasu dinga kwana kenan, gashi su Hindatu har nasu yaran sun samu ɗakin kwana, Allah mai iko" Kama musu na yi mu kai ta shigo da kaya. Dake kayan nawa babu yawa cikin ƙanƙanin lokaci muka kammala komai. Durowar dake jikin bangon uwar ɗakina Sabira suka buɗe suna ta jera kayan yara. Ni kuma ina saman turmi ina buga labule da ƙusa dan bani da ƙarfen labule amman mancewa nayi da zan siya na hannu a masallaci. Zama nayi a kujera ina ba Salis Mama. Jamila tace.
"Umman Sulaiman me za'a dafa ne ya kamata ace an ɗaura abinci, naga gidan ya soma ɗinkewa da mutane."
To Jamila bari in nemi Abban Sulaiman tukunna riƙe mun yaronnan ina zuwa" Kafin ta karɓi yaron sai ga sallamar Bilkisa daga bakin ƙofa.
"Umman Sulaiman ki kawo kwano a zuba miki abinci ke da jama'arki"
To Bilkisa zan aiko yara su kawo" Komawa nayi na zauna. Sabira ce ta ɗakko wata kwaraɓaɓɓiyar kulata babba ta kira yara ta basu su ka kai. Sai gasu da masa da miyar gyaɗa, harda sinasir, da lemukan roba har katan biyu, da fiya wata leda biyu. Yaran Sabira ta soma cira ma, su kuma sai da su kai sallar la'asar sannan suka zuba mana namu a tare muna ci suna hirarsu har da dariya. Duniya lallai ta nai musu daɗi. Ga ƴan uwan Hajiyayye ma a babban falo sai shewa da surutu suke yi. Dan Hajiyayye tayo gayya sosai, har maƙotanmu ƙawayenta duk sun zo. Ni ce dai koma baya akan komai, komai nawa yana zuwar mun ba irin na gama gari ba. Yau da Kaila bai hana Yaya Use zuwa inda nake ba da yanzu tana nan, yaranta. Nayi_nayi ta turo mun su ma taƙi gudun fitina, ga shi Yaya Karime tana Shanono sai jibi zasu dawo.
"Tani kayayyakin kitchen ɗinki ina zamu jera miki ne, naga kitchen a falo ko nan ne zamu jera naki kayan?" Cewar Jamila ba tun yau ba na fahimci Jamila tana da son dukan cikin mutum dan taji zance. Murmushi kawai nayi mata nace.
Ku barshi ai kuma kun gaji, kayan kitchen ɗin ba wani kaya ba, ni kaɗai ma in na nutsa zan gyara, dan akwai gyaran da ba'a ƙarasa a kitchen ɗin ba" Ni kuma harga Allah tsoro nake ji in ba da umarni a jera mun kayan kitchen a kitchen ɗin falo in zo Kaila yai mun watsi da kaya a gaban kishiyoyina, ya tsinkani kamar yadda ya saba. Gaga_gaga haka mu ka wuni cur muna abu guda. Sai yamma lis Jamila, Isa ya zo ya mayar dasu gida, ashe Amaryar a gidan ta wuni a ɓarayin Hajiyayye. Har gaban mota na kai Jamila sai godiya nake yi mata. Jamila ta kawo mun gudumawar kofunan roba dozin guda. Ban jima da shigowa ba Sabira ma tai mun sallama, sai kuma gobe in mun haɗu a makaranta. Abun sha'awa yara sai facaka suke da ruwan fanfo a bayan gida, su shiga ciki da gudu, su fito da gudu, wannan rigimar harda Hauwa akeyi. Tana biye dasu tana ihu da dariya. A babban falo kuma ina ta jiyo hayaniyar maza da muryar Kaila. Har zuwa bayan Isha, nan fa yunwa ta soma sasuƙar yara, ni bansan tudun da zan dafa ba. Ragowar masa guda goma sha biyu na basu, na juye musu miyar a kai. Nan da nan suka cinye, ba sai sun ce mun basu ƙoshi ba, ni kaina nasan basu ƙoshi ba. Lallaɓasu kawai nayi.
Ku yi haƙuri babu abinci ne a gidan. Ai kuna gani yau muka dawo sabon gida ko? Sai gobe zamu soma ɗaura sanwa." Buɗar bakin Sani yace.
"Umma Munga su Samira, da Jaxuli suna cin tuwo ɗazu" Sai nayi jigum nace.
To bari in leƙa in tambayo muku in bai ƙare ba." Salis na saɓa a kafadata yinwa kamar zata kayar dani, na nufi ɓarayin Bilkisa. Ashe mugun gyara akaima falon namu. Wasu ɗima_ɗiman kujeru aka baje, da ƙaton kafet, harda kayan kallo, ko ina sai hasken wuta. Gargaɗin dana tuno Kaila yayi mun ne yasa na canja akalata zuwa ɓarayin Hajiyayye. Jama'a sun soma sassautawa a ɓarayin nata. Da sallama na shiga falon. Abun mamaki ƴan uwanta suka watso mun wani kallo. Daga masu jan tsaki, sai masu cewa wari suke ji, harma da masu toshe hanci. Wani ƙududu na haɗiye ya faɗa cikina da zafi. Da ƙyar na buɗe bakina, dan jikina yayi mugun sanyi. Da ba dan bana son yarana su kwanta da yinwa ba, da juyawa ma zanyi in haƙura. Amman yaya zan yi, wanda bashi da gata ai yana ruwa.
Hajiyayye dan Allah abinci zaki sanmun in ba yaran yinwa suke ji." Wani banzan kallo tayi mun. Ita da danginta suka saka shewa, kafin tace.
"Wannan abincin ba Kaila bane ya kawo aka dafa. Balle kice suma suna da hakki akai. Daga gidan ubana ƴan uwana abun alfahari na suka yo aka tawo mun dashi kin gane ko? Sabida haka bazan bayar ba." Yayarta Ta Bizaaro tace.
"Zamu haɗu a kotu nan da kwanaki zaki san kishi ba hauka bane. Gobe ba zaki sake yin kisan kai ba. Tani baki ma da kunya, kinga ƙannenmu sai haƙuri aka basu dan dakaki ma su ka so yi, nice na taushesu" Daurewa nayi dan bana fatan suga zubar hawayena. Juyawa kawai nayi da sauri. Kiciɓis nayi da Kaila a ƙofar shigowa ɓarayin Hajiyayye. Idanu muka zuba ma juna. Sai lokacin hawayen da na shanye suka shiga suntiri a kumatuna. Ƙur yayi da idanunshi a kaina, bai tanka ba, nima ban tanka ba muna tsaye dukkanmu. Kaina na sauke ƙasa nace.
Yara yinwa suke ji Kaila. Bansan da wanne kitchen zanyi amfani ba. Sannan bansan kuma inda kayan abincin suke ba waɗanda aka ɗebo daga can gidan..
"Dakata Shanono. Wannan gidan ba irin wancan tsohon gidan da muka baro bane. Duk wani tsari ya canja. Zuwa gobe zan tara ku kuji sabon tsarin da zan fitar. Kayan abinci kuma ki tambayi Hajiyayye yana store ɗin kitchen ɗinta. Kitchen ɗin falonnan zaki iya jera dattin tarkacenki, amman ki sani ba kitchen bane na kunna gawaye ba. Yana da ƙofar waje, sai ki dinga fita da gawayin ta waje. Wallahi muddin naga wani ƙazanta a cikin kitchen ɗin, to zaki koma girki a cikin ɗakin ki zai fi mun sauƙi." Yana kaiwa nan ya wuce ni, bai faɗa mun yanda zanyi da yaran ba. Nayi iya dubana ko gawayi babu ban gani ba. Haka dole na koma ɗakina. Na samu ma yara mazan sunyi bacci a katifarsu wacce aka sa ma rigar leda. Ajjiyar zuchiya na sauke, ina shiga ciki na tarar da matan ma sun yi bacci. Ni ko a darennan tunanika babu irin waɗanda basu zo kaina ba. Na gaji da irin wannan rayuwar ƙasƙancin da nake yi a gidan kaila. Na fahimci tozarcin da nake fuskanta shafi_shafi ne, kuma ko wanne shafi da salon shi. Rayuwa kenan. Babu damuwa watarana sai labari, zaman gidannan inayine domin goben yarana kawai, amman nayi imani baƙin ciki da ciwon zuchiya su za sui ajalina. Haka na kusan raba dare ina kuka da tunano rayuwar da nayi a baya. Da irin mazajen dana aura, da irin jarrabawar dana fuskanta, dama darasi, da ƙaddarar dake cikin ko wanne aurena biyar. Aure da sha'anin maza ya gama fitar mun a kaina sam.
Washe gari.
Haka gari ya waye muka tashi cikin yinwa, ni kuwa cikina ƙullewa yayi sosai, da ƙyar na tashi, na tashi yaran dan su ɗauraye jikinsu su yi sallah. Ni kuma na shiga aikin fitsari. Ruwa na yayyafa a katifun duka biyu, nasa tsumma na goggoge,abun daɗin, rigar ledar da aka rufe katifar bai ba fitsarin damar taɓa katifar ba. na fito dasu, ruwan fitsari na yarari. Kaila da Hajiyayye suna babban falo, da dukkan halama Hajiyayye itace da Kaila. Ta ɗauki wanka tayi kyau abinta. Da idanu suka bini harna fice da katifun duk biyu, na wanke zannuwan gadon da zallan ruwa na yaɓa a katanga. Ina shigowa Hajiyayye tace.
"Ruwan fitsarinnan kisa tsumma ki gogeshi, wallahi Baby bazan iya ba. Yanzu ta babban falonnan zata dinga fitar da katifa kullum?" Ina tsaye ina kallon Hajiyayye, da irin kallon tsanar da kaila ke jifana dashi. Ko da ya tashi, da zagi ya rufeni, idona ya bushe babu ko sofanen hawayen ma. Tsumma na ɗakko na goge, na basu haƙuri dukkansu na koma ɗaki. Salis na tarar a hannun Sani sai kuka yake yi. Tun cikin dare yake jan nono, amman babu ruwan nonon, kukan yinwane kawai. Sauran yaran ma sun yi jigum sai kallona suke yi, irin kallon ki yi mana rai" Salis na saɓa a baya. Idanuna duk kwantsa, kumatukana duk busassun yawun bacci na fice a gidan da karamar jakata. Jefa ƙafata kawai nake yi bansan inda ma na dosa ba. Wannan masifa dame tai kama. Ni dai na kama tafiya sai nausawa nake yi, kafin in zo titi ma ba ƙaramar tafiya bace, haka nai ta fama, ina tafe faram_faram Salis sai kuka yake yi........✍🏻
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻
[10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA.
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 18
Na ci tafiya sosai. Ƙafafuna su kai busu_busu dasu. Da ƙyar na