Author : BADIAT IBRAHIM Category : African Stories & Novels
wuta da humra setine mai bala'in kyau. Kunsan dai Kanuri mune turaren wuta da humra, namu da banne, ke kanki in kika yi amfani da waɗannan set zaki gode mun. Akan farashin 10k kacal na bar muku farashin promo domin ku. Mutum ishirin kaɗai zan cire suke da damar mallakar wannan setin mai sanyin daɗi. Kuma iyakar ƴan paid group ɗina ne kaɗai zasu samu wannan garaɓasar. Ku yi hanzari duk mai buƙata ta kasance a cikin mutum ashirin da zan ɗiba.)*
Da sauri na miƙe tsaye kamar ba ni bace na wuni sukuku. Baki na riƙe kawai ina kallon Kaila. A guje Bilkisa da Hajiyayye suka fito. Hajiyayye tana ganin abinda ya faru taja wani irin dogon tsaki tayi komawarta ɗaki. Dama ɗakin nata cike yake da ƴan uwanta. Kamar yinwataccen zaki haka Kaila ya dira a wuyan Sani ya far mishi da mahaukacin duka, tamkar yana dukan ƙato. Dama haka yake musu irin wannan dukan. Bilkisa ta isa a guje ita da Hindatu, amman sun kasa ƙwatar Sani a hannun kaila. Har ya fashe mishi ɗan bakin nashi. Tsam na miƙe na koma ɗaki. Yaran suka biyoni ɗuu. Zaunar dasu nayi, ni ko na kasa zaune na kasa tsaye, ina jiyo Sani yana kirana.
"Umma ki ceceni zai kasheni, wayyo Baba wallahi bansan kana zuwa bane, wayyyooo" Kuka na fashe dashi, har muryar Sani ta dashe. Baban Mustapha ne ya burmo gidan namu. Ina jiyo muryarshi tun daga zaure. Shine ya ƙwaci Sani a hannun Kaila. Da mugun gudu Sani ya shigo bakinshi na zubar da jini da yawu, gefen idanshi ya kumbura. Ƙanƙameni yayi tsam sai cusa kanshi yake a jikina. Hannuna na ɗaura a saman kanshi ina shafawa.
Ya'isa kayi shiru kaji Yaya. Babu komai, ai mahaifinka ne hukunci yayi maka. Muje in wanke maka bakinka, ku ci dumame ku kama hanyar makaranta, kayi shiru ya'isa" Da ƙyar a ranar nasa Sani ya yarda ya tafi makaranta, bakin shi ma ya aune sosai. Ko bayan tafiyar su Sani makaranta na jima a ɗaki ni kaina bansan zaman me nake yi ba. Ni ba tunani ba, ni bansan adda'ar da zan dinga yi domin kore damuwa da baƙin ciki ba. Habiba Bala ce ta sanyaya mun raina data kira take sanar dani an yi ma Dauda tiyata cikin nasara, amman yana bacci a lokacin. Wani irin farin ciki ne ya sauka a zuchiyata. Kawai na sau ma Habiba Bala kukan farin ciki, sai jero mata godiya nake yi, ita kuma tana ta rarrashina, da haka mu kai sallama. Ina dai zaune, bani na fito ba sai wajajen goman safe. Kiki_kiki na ɗaura miyar dare, tana tafasa na kaɗa. Miyar kuɓewa nayi bushasshiya, Sai na mayar da ruwan wanka kan wutar, na soma yanke farata na, waɗanda suka cika da datti, sunyi baƙiƙƙirin dasu. Tas na yanke farcen ƙafata dana hannuna, na faɗa bayan gida, ina cuɗawa na bi da ruwa na fito. Misalin dayan rana sai ga su Sani sun shigo hajaran majaran sai warin rana suke dokawa."
"Umma yinwa" Cewar Shafi'i dama shi kam ba mai jurar yinwa bane sam. Sani da Sulaiman ne dai masu dama dama. Balaraba ita bata zuwa boko, islamiyya kaɗai take zuwa. Abinci na zuba musu su ka ci, dan zumudi ni ko abincin na kasa ci. Ƙarfe biyu bata cika ba na saka inifom ɗina har nayi goyo. Yara suka kalleni suka kwashe da dariya, Sani har yana ƙwarewa. Nima dariyar nayi bance uffan ba. Farin hijabina na saka na rataye jakata.
To maza ku yi ku gama mana. Ku je gidan su Mustapha ku yi wasanku, in lokacin islamiyya yayi sai ku je tare. Sani banda zuwa wanka rafi, dan Mustapha ya faɗa mun kana bin yaran gidan Rahilu. Ni zan je makaranta ku yi mun adda'ar samun nasara." Adda'a su kai ta mun. Raina fes na fito zauren, dai_dai Hajiyayye ta rako ƴan uwanta zaure. Turus Hajiyayye tayi kawai tana kallona. Ni ko da ganinsu gabana ya yanke ya faɗi. Dan banso nayo arba da kowa ba. Da sauri na ɗauke kaina, ina rufe ɗakina na jefa ɗan mabuɗin a jakata na fice. Yara su ka bi bayana. Da sallama mu ka shigarma Sabira. Tana ganina ta soma tafa hannaye.
"Ga ƴar makaranta, ga ƴar makaranta" Dani da yara duka muka tuntsire da dariya.
Sabira baki da dama. Ga yarannan. Sabida in na barsu a gida ba lallai suje islamiyyar ba." Sabira tace.
"Yau bana nan na fita, sai da na dawo Abban Mustapha yake faɗa mun irin dukan da Abban Sulaiman yayi ma Sani. Gashi idanunshi sun tara jini." Na ƙwafe wannan dukan sosai a raina. Sosai nake jin zafin dukan, har bana so ayi zancan. Bagarar da hirar nayi ta hanyar juyawa da gudu_gudu. Sai a zaure mu kai sallama na kama hanyar makaranta. Aji ya cika bundin, ni dai bancin ƙarshen aji na samu, mu biyu ne a bincin ni da wata dattijuwa. Mata sai hira suke yi ana tafi. Malami bai shigo ajin ba, shewa kawai kike ji yana tashi. Ni kuma sai kallonsu nake yi, ina mamakin wai yau nice a zaune a aji a karo na biyu. Bayan haihuwa ta takwas, Allah mai iko, Allah ya bani nasarar karatu. Ina cikin tunanin nan sai naji ajin ya yi tsit, ashe malamine ya shigo.
"Sababbin zuwan mu su je ajin ƴan B su mayar da form dinsu da fasfo, za'a rubuta sunansu a rijista. Ni dai na taso amman sai harɗewa nake yi. Duk inda na walga kallona mata suke yi kamar wata baƙuwar halitta. Har na fita na jiyo Muryar wata mata na faɗin.
"Baiwar Allah kuɗin cizo suna bin hijabinki ta baya" Da sauri na waiga bayan nawa ai kuwa na gansu har uku, yatsana manuniya nasa a baki na dangwalo yawu na kamo kuɗaɗen cizonnan na kashesu a ƙasa. Kab ajin ni suke kallo. Ni kuma ina ɗagowa nabi ayarin mata biyun da suka nufi B likas dan mayar da fom. Muka mayar da fom sunanmu ya shiga rijista. Da darasin lissafi muka soma ( maths) Nan dai na shiga rubutu hannuna na kakkarwa, har wani zufa hannuna ke yi dan tsoro. Abubbuwan dai gasu nan ga kamarsu gani nake tamkar ban taɓa shiga aji ba. Ko malamin turanci daya shigo ni dai ina zaune dunkum kawai. Gashi sai aikin gida suke bamu ( home work) Ni dai kwafewa kawai nake yi, wasu abun dai nakan haɗa in furta kamar mai koyon magana. Ana cikin yin darasin gona, agiric Salis ya soma kuka.
"Wacece ɗanta yake kuka? Ta fita waje in ma ta shayar dashi, ko ta rarrasheshi. Ya kamata ku dinga zuwa da mataimaka da zasu dinga kula muku da yaranku, iyakarku dasu ku fita ku basu Mama ko ruwa" Da sauri na fita, dama fitsari nake ji. Sai da na nemi ban ɗakin makaranta, ashe basu da banɗaki sai na malamai, ɗalibai sai dai su shiga maƙota. Nima maƙotan na shiga na soma yo fitsarin. Ina dawowa makaranta ana buga ƙararrawar yin hutu. Gefe na samu na yaye hijabina na dumbulama Salis nono. Yayi maza ya cabka ya shigo tsotso yana sauke ajjiyar zuchiya. hutun minti talatin muka yi. Ina gani mata sai siyayyar ƙwalam suke yi, ni kam inaa. Aji muka koma muka ci gaba da ɗaukar darasi, wallahi ji nayi bana iya fahimta, ƙwaƙwalwata ta toshe sosai. Har ƙwalla sai da na tsiyayar dana tuno ƙoƙarina wajan karatu da naci. Duk abinda ya gagari su Habiba Bala da su Halima Bawa, ni ake kawo ma, har mayya suke ce mun. Dan ina da ƙwaƙwa ko darasi akayi mana komawa ɗaki nake in ta bitar karatunnan, ko kuma in shiga ɗakin karatu na cikin makatanta wanda aka tanada domin ɗaliba, ni dai ku barni da ƙazanta kawai. Kuma ni ban ɗauka abinda nake yi ƙazanta bane, dan a haka na taso na tarar da mahaifana, da yayyena. Amman yau gani a aji bana ko gane komai. Dattijuwar dake gefena ta taɓoni.
"Baiwar Allah an tashi fa, bani wuri in wuce" jakata na raruma na matsa mata, nan na shiga kiciniyar goyon Salis, wannan dattijuwar ta dubeni tace.
"Wannan goyon ai ɗanyene, kuma zai barki kina fahimtar karatun kuwa?" Ɗan murmushi nayi nace.
To zan jaraba dai, amman ban fahimci duk abinda akayi ba ma yau. Ƙila sabida na daɗe rabona da shiga aji "
"To ki dinga tawowa da wacce zata dinga miki renon yaron. Ke kuma sai ki nutsa kiyi karatun dan yana da matuƙar mahimmanci sosai. Kuma nan ai makaranta ce duk wanda kika gani koyo yazo yi. Duk abinda ya shige miki ki yi tambaya ko malami ko ɗaliban ilimi. Sai gobe ko?" Godiya nayi mata, muka fita a tare kowa ya kama gabanshi. Inata ta tafe, kwasham_kwasham bani na samu abun hawa ba har sai da na nazo kan babban titin zangon baƙi tukunna, Minti goma ne ya kawo ni bakin layinmu.
Da shigata gidan nayi maza na buɗe ƙofata na ƙule bana son kowa ma ya ganni. Kayan makarantar na tuɓe na mayar da kayan gida. Salis yana kwance yana baccinshi rai ɗaya. Da Bilkisa naci karo tana riƙe da ƙatuwar leda.
"Umman Sulaiman kin dawo ashe? Nazo har sau biyu baki nan" Yangar maganar Bilkisa burgeni yake yi, harma nake jin kamar tafi kowa iya sarrafa harshe. Duk da naji Habiba Bala ma haka take karya murya.
Na dawo yanzu" Na bata amsa. Kaila ne ya nufo mu sai ƙamshi yake yi, cikin ado da kwalliya yake. Yana ganinmu tare ya dubeta yace.
"Wai me yake kawo ki wajan Shanono ne Ɗanyan gwal? Ni sai in ga kina shige mata da yawa ai" Da zafin harshe ya fesar da kalamin. Wani mugun kallo ta watso mishi tare da ƙare mai kallon sama da ƙasa.
"Kar ka sake ka sake ɗaga mun murya. Ko mun yi da kai duk abinda zan yi sai ka sani ne? Ni fa ko a gida banga uban da ya isa ya takura mun ba." Baki ya sake yana kallon Bilkisa data mugun haɗe ranta, kallona tayi tace.
"Kaya ne dama na fitar suna nayi miki ke da Dady na. Mummy ma tace in miki Barka ranar suna ƙanwata zata zo suna. Allah ya raya Dady." Da dariya na karɓi ledar.
Kai amman na gode sosai Bilkisa amman babu ma suna kar ki wahalar da me zuwa."
"Amman me yasa ba suna?" Ta jefo mun tambayar amman idanunta na kan Kaila wanda ya ƙula ainun. Murmushi nayi nace.
Babu kawai dai, haihuwa bata fari ba, taron bikin suna ai sai ku" Baki ta taɓe ta yi wucewarta. Tana shiga cikin gida nima na faɗa ɗakina. Kaila ya bita fuuu zuwa turakarshi.
KAILA:
Tsabar jaraba har baya iya gani. A hargitse ya shiga ɗakin ya tarar da Bilkisa a tsaye ta riƙe ƙugu.
"Ke Bilkisa yanzu dai_ dai kenan a gaban shanono ki dinga nuna ban isa dake ba? Ni fa duk na soma gajiya da lamarin zaman aurennan wallahi. Mu kenan bama kwana biyu cikin jin daɗi. Jiya ina ji ina gani kika hanani kanki a shinfiɗa............... Dakatar dashi tayi da cewa.
"Dakata mun, ni ba'a mun faɗa, kuma na gaji da aurenka tafiyata zanyi gidanmu, na gama aurenka kenan. Bansan dama kai ba adali bane a gidanka ba da bazan shigo ba ma" Hanyar fita ta shiga nema. Carab Kaila ya riƙeta ƙam. Shine harda tsugunnawa yana roƙonta tayi haƙuri, da ƙyar ta haƙura, da taga kaila na shirin zubar da hawaye. Amman sai ta shiga fishi dashi. Kiran sallar magriba ne yasa ya fice daga ɗakin jiki a mace.
SHANONO.
Ina tsakar gida ina jiran ruwan tuwo ya tafasa in zuba talge. Littafin lissafi ne a hannuna ina duba shafin da akayi mana, ina bin misalan ciki a hankali a hankali. Haya_hayar yara ce tasa na rufe littafin na kallesu.
Yaya akayi yinwa ko Sulaiman?"
"Lefi yayi ma malam shine ya zane shi" Cewar Amina uwar kanzagi kenan. Shi Sulaiman ashe a wuya yake, sai yasa hannu ya shararama Amina mari. Tas naji sauran hannun kaila a fuskar Sulaiman. Yaron ya fashe da kuka ya durƙusa. Tsaki Kaila yayi tare da bin mu da kallo yana muzurai.
"Kizo shanono mu yi magana" Jin yace haka sai Hajiyayye ta ɓata rai daga dariyar data gama yi ina ganinta. Nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ilai kuwa ina zuwa na same shi a tsaye kamar soja.
"Bani kayan da Bilkisa ta baki maza" Suna kan katifa dama. Ɗakkowa nayi na bashi abinsu.
"To daga yau sai yau in kika sake tsaiwar minti uku da Bilkisa ranki zai ɓaci. Wallahi Shanono ki fita sabgarta in kina son aurenki ya tsira" Yana kaiwa nan ya fita. Kaila na lura barazanarshi gareni bata wuce ta saki. Domin yasan babu abinda na ƙi jini irin saki. Kuma yasan wahalhalun da na shiga sanadiyyar mutuwar aure. Wannan dalilin ya riƙa yake tsorata duniyata da kalmar saki. Sabida ya lura zaman auren nake so, burina in zauna da daɗi babu daɗi. Kai na girgiza kawai, na fita nayi talge abuna, na ci gaba da duba littafina.
"Ni da su Gwamma, oh ni Hajiyayye in da ranka ka sha kallo, an koma makarantar balagaggu, dan miji ya auro kishiya likita." Ni dai hankalina yana kan littafina domin na soma fahimtar yadda abun yake, saura ƙiris in gano bakin zaren. Amman in na kwashe tuwo zan leƙa Sabira ta ɗan ƙara ɗaurani bisa layi. Kafin isha na game tuwo na baje ma yara a faranti, nima na zuba nawa. Sai da naci na yi ƙat, na goge miyar a kaina tas na mayar da ɗankwalina. Sai na miƙe na goya Salis.
Yaya ka kula dasu zan je in dubo Sabira. Haka dai kiki_kiki Sabira ta koya mun abinda ya samu, sai taran dare na baro gidan. Duk aikin gida da aka bamu a makaranta sai da mu ka yi tukunna. Ko da na shigo gida yara sun jima da Bacci. Amina harta tsula fitsari tana cikinshi. Salis na sauke a baya a daddafe nima na haye katifar nan nayi kwanciyata.
Gaga_gaga dai anata rayuwa a haka, kullum da sabon tashin hankalin da kaila zai sani a ciki, bayan kwana biyu da kawo sammaci. Habiba Bala tazo mana da lauya. A gidan yaya Use mu ka haɗu, acan muka tattauna, yai mana tambaoyi cikin ƙwarewar aiki. Iyakar abinda muka sani muka sanar mishi. Shi kuma ya ɗaura mu a kan matsaya ɗaya. Habiba Bala bata daɗe ba ta koma, sabida Dauda. Ranar dana kwana bakwai da haihuwa da safe ina ɗaki yara duk sun tafi makaranta. Nima aikin gida da malamar Physics ta bamu nake yi, da kuma aikin gida da aka bamu a islamiyya, Baƙaƙen larabci zamu rubuta daga farko zuwa ƙarshe, inata fama na barbaje sai cin rubutu nake yi. Makaranta da daɗi sosai, naji daɗin makarantar islamiyya dana je sosai, gashi muna da yawa ainun, akwai ƴan mata da matan aure, harma da zawarawa. Ga manyan mata ƴan gayu sosai a ajinmu, ko wacce tas da'ita. A bencinmu mu uku ne, dukkanmu muna da goyon yara ƙanana, kuma naci sa'a suma sababbin zuwanne, sai kowa ya sake da kowa dai.
Kaila ya ɗago labule ba ko sallama yace.
"Ki shirya kaya nan da awa biyu motar ɗiban kaya zata iso. Za'a kwashi kayanku zuwa sabon gida" Kafin in yi magana ya saki labule ya ficewarshi. Ina jiyo dirin lifan ɗinshi." Ba shiri na haɗe littattafan sai gidan Sabira. A falo na sameta tana turarashi da kayan ƙamshi daga Mrs Bukhari. Ko ina tsab sai ƙamshin daɗi.
Ka ga mata ƴan lelen miji. Wallahi kya yi Sabira Abban Mustapha yana yabawa kuma yana ba da gudunmawa" Zama nayi a kujerarta, ita kuma ta ajjiye kaskon tace.
"Yaya karatun, yanzu na kira Habiba Bala na ji jikin Dauda, mun gama wayar kenan na soma turara gidan sai ga ki"
Hmmm yau zamu tashi Sabira. Yanzu ya leƙo ɗakina yake sanar mini. Wai nan da awa ɗaya motar ɗiban kaya zata iso." Waya kawai naga Sabira ta zara, ta yi danne dannenta ta kara a kunne. Jim kaɗan ta soma magana.
"Hello Ahmad kana ina yanzu haka? Kaya nake son ka ɗaukar mun daga gida zuwa masallacin ƴan dankali. Wajan masu sai da kaya na hanu.? " Daga wayar ina jiyo Ahmad na cewa.
"To Anty motar ma tana ƙofar gidanki, in shigo in ɗebi kayanne?" Da jin haka Sabira ta miƙe tsaye.
"Mu je Tani maza bamu da lokaci sosai." Fita mu ka yi, Ahmad ya taimaka mana muka saka katifunnan a mota. Yayi gaba dasu, mu kuma mu ka bi bayanshi a Napep. Da waɗannan katifun guda biyu Sabira ta amsar mun gado 6 by 6. Sai mu ka sai katifu guda biyu a cikin kuɗin da Habiba Bala ta bani. Sabira ta siyamun kafet na hannu mai kyau ja da kuɗinta. Cikin awa guda muka gama siyan komai Ahmad ya dawo damu. Motar mu na tsaiwa motar ɗiban Kaya itama ta tsaya. Kaila ne a gaba a lifan ɗinshi. Kamar bai ganmu ba haka yayi.
"Ahmad ga motar nan, ka zuba kayan a ciki. In ka zuba ka shiga ɗakin su Mustapha zaka ga doguwar kujera ka fito da'ita ka haɗa mata." Godiya naso yi, amman Sabira ta doka mun harara ta ja hannuna zuwa ciki. A lokacin me motar kaya da Kaila, da Amadudu sun soma fitar da kaya waje. Sabira ta zazzage tsunmokaranmu tas a ƙasa ta sake zaɓewa, ta cire mana marasa yawa, sauran kam ni kaina nasan babu amfanin da za'ayi dasu. Tsabar sabo da tulin tsunmokine kawai. A buhu ɗaya ta haɗe ma yara kayansu. Ni kuma nawa ta je gidanta sai gata da katuwar jaka. A ciki ta shirya mun kayana. Ta kirawo Ahmad ya fita dasu. Kayana dana Bilkisa su kai gaba. Kayan Hajiyayye da Hindatu kuma sai an dawo. Hajiyayye ta kai wuya kuwa da ita da ƴan uwanta da tayo gayyarsu. Itama Bilkisa ƴan uwanta biyu sun zo jiya daga Zaria, ga me aikinta kuma. Allah sarki, ni ko daga ni sai Sabira, Yaya Use sai dai waya kawai mu ka yi da'ita nake sanar mata. Habiba Bala kuma, dana kirata ɗazu a wajan siyo katifa tace in yi haƙuri sai gobe zata iya shigowa.........✍🏻
*OUM SOOFEEYYER GRAPHIC AND DATA*
*INA