Author : BADIAT IBRAHIM Category : African Stories & Novels
ba ƙara zasu shigar. Nayi iya yina ma a kashe maganar a gida, wallahi basu yarda ba..............✍🏻
MRS BUKHARI
Sai jibi in Allah ya kaimu da rai da lafiya "
[10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 13
Bansan sanda na fito zauren kamar zautacciya ba. Idanu muka haɗa da Kaila, ya jefe ni da wani kallon tsana.
"Nayi ɗan daka ce ban je masallacin ƴan taya na ganku a wajan bara ba. Nayi nadamar wannan haɗuwar tamu na farko. Na auro mata marar tarbiyya ƙazama, wacce babu abinda ta sani sai ƙazanta da haihuwa. Ki faɗama Yarki ta bar mun gidana wallahi in ta ƙara shigo mun gida kotu ce zata raba ni da'ita. Ke kuma zaki ga irin mummunan hukuncin da zan yanke miki akan wannan aika_aikar da kishi ya rufe miki ido kuka yi. Nan gaba ni zaku kashe ba ɗana ba ai" Jikina tsuma yake ta ta yi. Kuka kawai nake yi, Yaya Use kuma ta yi kasaƙe tana kallona, bata ce komai ba tasa hijabinta ta ratsa ta gaban Kaila ta fita, har jikinsu na gugar na juna, dan Kaila ya ƙi mazawa, ita kuma na santa da zuchiya, dan Yaya Use asalin irin halin ƴan jagora gareta, girmane yasa ta yi sanyi. Namiji kuma ya ƙara seseta mata nutsuwa. Da harara Kaila ya bi yaya Use.
"Aikin banza aikin hofi. In banda tashanci taya wannan buhun fulawar zata yi faɗa da Hajiyayye ba dai dama shiryawa su ka yi ba. Ke kuma na dawo gareki Shanono." Nuna ni yake yi da ɗan yatsa jikinshi har rawa yake yi, tunda nake ban taɓa ganin Kaila a cikin ɓacin rai makamancin wannan ba. Ba shiri na durƙushe a gabanshi ina kuka. Hannayena na haɗe waje guda cikin sigar ban haƙuri. Amman Wallahi in buɗe baki in yi magana na kasa. Babu irin zagin da Kaila bai yi mun ba, ya buɗe baki yace uwarki Inno da ubanki Nanoma ne kawai baice ba. Amman ya zage su tas. Hakan bai mishi ba yasa ƙafa ya shureni sai da na shige ɗaki. Sai gani a tsakiyar yarana. Kuka na kuma sakawa, ganin ashe kuka suke yi. Hauwa da Balaraba ne kawai basa kuka, amman suma sun yi shiru kamar ruwa ya cinyesu. Ban yi aune ba, Kaila ya shigo da bulala mai baki biyu. Yanda yake dukan Sani da Sulaiman in sun mishi laifi haka ya shiga tabkata. Tsabar zafin duka da gigicewa sai da na kusa tsirara a gaban Isa dake ta faman kokawar ƙwace dorinar a hannun Kaila, amman ya kasa. Amadudu ne ya shigo da gudu da ƙyar suka ɓanɓare kaila a ɗakin.
"Zaki ci ubanki ne ƴar iska ƴar mabarata, ni zaku kashe ma ɗa dan baƙin hali." Allah kawai nake ambato har zuwa lokacin ina jin zugin dukan na ratsa jikina. Yarana duk sun takure a lungon katifa sun cure waje guda sai kuka suke yi. Jaririna dana tumirmushe na ɗauka da sauri. Ashe shiɗewa yayi. Sai da na jijjigashi da ƙarfi sannan ya saki wani irin kuka mai karaɗe kunnuwa. Nima na sake sakin kuka. Ina jiyo Bilkisa tana yima Kaila magana akan rashin dacewar dukana da yayi. Sai faɗa yake yi kamar zai ari baki. Yana ta tsinkani a wajan Bilkisa, yana faɗa mata a kwaroro ya tsinceni ya wankeni ya aureni ina bazawara mai aure huɗu, shi kuma yana saurayi fil. Jaririna na duba, sai ajjiyar zuchiya yake yi, nono yake ja a hankali. Su Sani na duba, haƙiƙa ƙaddarar zuwansu duniya ne ya haɗa aurena da Kaila. Dani dashi bamu da tsimi bamu da dabara. Wannan shine karon farko da Kaila ya sa madoki ya dokeni. Ya kan mareni, ko ya sa hannu ya hankaɗeni in faɗi, amman bai taɓa mun mugun duka irin wannan ba.
Da ƙyar na lallaɓa na rarrashi yaran su kai shiru. Ina zaune ina karanta wasiƙar jaki har wajajen sha biyun dare, na rasa inda zan tsoma raina, fargabar abinda kaje kazo nake yi. Na san zaman gidannan ya ƙaremun, to yarana fa wazai riƙe mun su? Jibi rayuwar Dauda yadda ta samu giɓi sakamakon rashin uwa majingina a tare dashi. Taya zan tafi in bar gidannan, in tsallake yarana ababen alfaharina? Ina cikin wannan taɗin zuchi wayata tayi kuka Yaya Use ke kira da sauri na ɗaga"
"Tani ince dai babu wata matsala data biyo baya ko?"
Babu Yaya Use, kiyi haƙuri da abinda Kaila yayi miki"
"Hmmm Tani kenan, akwai ranar da zan mayar ma da Kaila wannan cin kashin da yayi mun. Halin da kike ciki shi yafi damuna a yanzu, rintsawa wannan na kasa yi. Baban yara sai tambayata yake yi, jikina yayi sanyi. Ki yarda dani Tani wallahi ban daki Hajiyayye a ciki ba, makircine kawai irin namu na mata. In ce dai ƴan uwanta basu zo ɗaukar fansar dukan ƴar uwarsu da akayi ba ko?" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
Basu zo ba, amman a cikin zulumi sosai nake Yaya Use, dan ƴan uwanta sunce ba zasu yarda ba. Kuma Yaya Use makircin Hajiyayye yafi da haka wallahi, tayi mun abubbuwan da bansan iyakarsu ba a rayuwa. Amman babu komai, kema nasan kin yi ne domin ki ƙwatar mun ƴanci ba dan ki jefa ni cikin matsala ba. Amman tsorona tsinuwar da Baffa zai mun in ya ji mutuwar aurena a karo na biyar. Dan ina da yaƙinin Kaila sakina zaiyi, Ɗa ba wasa bane yaya Use " Mun jima muna tattaunawar da ba zata fisshemu ba, face mu ɓata bakunanmu da ƙone katin waya kawai. A taƙaice kwana nayi kusan a zaune, kafin asuba jikina ya kumbura yai suntum, ko idona bana iya buɗewa sosai. Kasancewar jikin nawa ɗanyene kuma gashi na daku iya duka. Ko da na tashi yara su yi Sallah, da suka ga fuskata sai tambayata suke yi banda lafiya ne? Ni kuwa shiru nayi musu kawai, Dauda kuma yayi ƙuri abun tausayi. A ranar dai a ɗaki nayi ma Dauda wankan magani a cikin bawo, na shafe mishi takashinshi da man da mai maganin ya bamu. Abun tausayi har wani ajjiyar zuchiya Dauda yake ta saukewa, wari kuwa ya cika ɗakin fam. Ruwan wankan na fita dashi a bawo na zubar. Nan da nan tsakar gidan ta kaure da ɗoyi ina jiyo Amadudu daga ɗaki yana faɗama Hindatu.
"Ina bara gurbi ne ya fashe a maƙota kinji wani azabar wari?" Ina jin haka na koma ɗaki da gudu gudun karma su fito su ganni. Ina cikin yima jaririna wanka na jiyo tsaiwar mota a dai_dai windo na, ni dai na jiyo muryar mace tana cewa.
"Ga gidannan, mun yi waya da mai gidan yana ciki" Sai muka jiyo sallama a zaure da wata ƙatuwar murya. Ba'a jima ba na jiyo takun tafiyar Kaila. Ni ko gudawa harya taru mun. Yara su kai tsuru_tsuru duk a cikin tsoro muke. Kaila ne ya bankaɗe labulen ɗakina. Ba shiri ya toshe hancinshi harda runtse idanunshi. Tabbas na san warin da Dauda yake yi ya kai ayi fin hakan ma. Nima dake uwace shi yasa ko a jikina.
"Ke kam ba dai ƙazanta ba. Ji warin da ɗakinnan yake yi. Ashe dama warin da Ɗanyan gwal tace mun ta jiyo a tsakar gida daga nan yake fitowa? Ko da yake ba abinda ya kawo ni ba kenan. Ƴan sanda na jiranki a waje sai ki goyo ɗanki ku je, nima zan biyo bayanku" Miƙewa tsaye nayi a zabure ina kuka nace.
Kaila kayi mun rai dan Allah. Wallahi Allah Yaya Use bata naushi Hajiyayye a ciki ba. Kaga jego nake yi banda lafiya, ka tausaya mun dan Allah kar ka bari su tozarta ni"
"Kinga dakata Shanono. Dangin Hajiyayye suna da hakkin yin shari'a daku akan ƴar uwarsu. Dan baki san girman laifin naku bane shi yasa ma har kike wannan magiyar ai. Wuce dallah" Kaila ya hankaɗoni waje, sai gani a zaure kusa da wata ƴar doka macr. Goyona ya miƙo mun na ɗamare shi, jikina fa bai daina kakkarwa ba. Yara suka fito suna kuka. Sai a lokacin kaila ya kula da Dauda.
"Shi kuma wannan yaron fa Shanono daga wacce duniyar yake?" Ruɗun sai ya ƙaru mun, in yi magana na kasa. Ƴar doka ce ta katse mana uzuri, wanda ni hakan yayi mun daɗi.
"Wannan kuma maganarku ce ta cikin gida. In ta dawo kwa tattauna, muje baiwar Allah " A gaba ƴar dokar nan ta tusani, ina jiyo kukan Hauwa a kunnuwana, dukkansu yaran kuka suke suna ambaton.
"Umma Umma" Babbar yar su Hajiyayye na gani a ƙofar gidan, da ƙaninsu Namiji. Haka aka sani a motar ƴan sanda kamar ɓarauniya. Kai tsaye hanyar gidan su Yaya Use muka nufa. Labarin daya sake tunzura tashin hankalina. Damuwata ta ƙaru ainun. Ai kuwa sai gamu a ƙofar gidan su Yaya Use. Basu jima da shiga gidan ba, sai gasu da ita an taso ƙeyarta. Ganin Fatima yasa nace.
"Fatima ki je gida ki kula mun da su Sani. Dauda ma yananan, Saudat ta kula da su Inno" Yaya Use sai kuka take yi. Ni ko idanuna a bushe, haka mu kai ta tafiya tiryan tiryan har caji office. Bamu taɓa shiga caji office ba sai yau. Haka aka zube mu bayan kanta. Suka ci gaba da aikinsu. Mu dai muna zaune jigum.
"Tani me ya same ki, naga jikin ki yayi ja ja ja halamun shatin bulala kaddai Kaila ne ya dokeki da ɗanyan jego a jikinki? Kinga yanda halittarki ta canja kuwa Tani. Ga wajan da Baffa ya kwaɗa miki sanda ma ya sake aunewa" Kafin in bata amsa Babbar yar su Hajiyayye ta shigo ita da ƙaninsu, Kaila na biye dasu. Ya ɗau wanka sai ƙamshi yake yi, ba ka ce kaila mijina bane. Shi yasa ma bai son a dangantasho dani, na sani yafi karfina nesa ba kusa ba."
Zuwansu ne yasa har aka kulamu. Nan yar Hajiyayye ta shiga ba da labari ma ƴan doka. Yaya Use tace.
"A'a Ta bizaro kar ki bada wannan shaidar. Wallahi ban naushi Hajiyayye a ciki ba. Tsautsayine da ƙaddara su ka kashe abinda ke cikinta" Buɗar bakin Kaila yace.
"Zaki ga tsautsayi ganin idanki. Tsautsayi da ƙaddara su zasu kai ki gidan kaso kema" Yaya Use tai ma Kaila kallon banza tace.
"In aka sani a gidan kaso a baka mukullin a jefa a bahar maliya. Kaga in ba zamu tsaya a gaban Ubangiji ba... Wata ƴar sanda ce ta daki teburi tace.
"Kuyi mana shiru anan. Ke kina bayan kanta amman bakin ki bai mutu ba ko? Zaki yi bayani ai. Ku taso ko wacce ta rubuta statement, kuma ku sani duk abinda kuka rubuta zai iya zama hujjarku a gaban kotu. " Cikina ne ya juya da naji ta ambaci kotu. Yaya Use tace.
"Mu bamu iya rubutu ba" Ƴar sandar nan tace.
"Zan dinga rubuta muku kuna faɗa mun. Sannan in kuna da lauya ku neme shi, dan ba ma zamu ba da belin ku ba, dan maganar kisa akeyi. Ita kanta me jegon bama tasan in da kanta yake ba har yanzu. Dan haka ku nemi lauya dan tattare bayananku zamu yi mu miƙa ku kotu." Muryata na rawa na dinga karanto iya abinda na sani. Ƴar sandar nan nata rubutu. Haka na gama Yaya Use tayi nata. Ana cikin haka sai ga Sabira da Baban Mustapha sun shigo. Sabira ƙawa ta gari tana ganina ta fashe da kuka. Baban Mustapha kuma yayi iyakar ƙoƙarinshi a bashi ko da belinane wallahi su ka ƙi. Sha'anin hukumomin ƙasarnan sai adda'a.
"Tani ki bani jaririn in tafi dashi, kema ki samu kiji da kanki. Zan dinga bashi madarar yara. Su Sani ma suna gidana, harda yaronki Dauda"
"Dauda yaronta? Kut lallai Shanono kin ci ƙarya kin kwana da yunwa, nine ɗan iskan da kike tunanin zam riƙe miki agolan ɗanki, bacin ubanshi yana da rai? Ai ko bashi da rai wallahi bazan riƙe agola ba, kina fitowa daga gidan yari ki tattare ki mayar da yaro gidan ubanshi. In kuma kina son ku koma gidan uban nashi tare ne ai shikenan Shanono" Yana dasa aya ya fice. Baban Mustapha ne ya bishi da sauri. Ni kuma na sunto goyona na ba Sabira.
Sabira wayata tana ɗaki, ki duba zaki ga number Habiba Bala a ciki. Ki kirata ki mata bayanin halin da nake ciki dan Allah, nayi imani zata zo yau ɗinnan."
"Shikenan Tani, zan kirata. Kuma in Allah ya yarda ba zaku kwana a tsare ba" Keyarmu aka tasa cikin. Zama nayi a ƙasa ina murmushi kawai. Yaya Use tace.
"Sai da na faɗa miki kar ki ɗakko Dauda Tani. Kinga yanzu abinda ya faru ko. Yanzu yaya yaronnan za'ayi dashi? In kika ce gidansu Inno zaki mayar dashi bara zai dinga zuwa kema kin sani. Mu ma kuma kinga halin da muke ciki. Amman wacece ita Habiba Balan da kika ce a kirata?" A taƙaice na faɗa mata wacece Habiba Bala.
"To Allah ya rufa asiri. Baban yara yana ciki fa. Amman Sabida ɓacin rai ko kallona yaƙi yi. Shi yasa ma baki ganshi ya fito ba. Kuma nasan ko ɗaureni za'ayi igiya tayi saura bazai zo ba...........
[10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 15
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*(Assalamu alaikum masoyana. Haƙiƙatan naji daɗin yanda kuke yaba rubutuna, da yanda nake tafiyar da salon labaraina. Babu abunda zance daku sai kodiya. Yau na tashi sai wasu uziri suka same ni, wanda bazai bani zarafin yin typing akan kari ba. Sai na yanke hukuncin sanar da masu bibiyar rubutuna cewar su yi haƙuri ina da uziri, ba zasu samu jina ba har sai na samu al'amura sun warware mun. Allah cikin ikonshi jim kaɗan da yin wannan maganar, saina soma samun kiraye_kirayen waya daga masoyana. Na kuma dinga cin karo da saƙonninsu wanda in na karanta wani ban isa na karanta wani ba. Duk dai ƙorafinsu shine, in taimaka zasu yi kewar Shanono. Wata tace tana cikin ɗakin jarabawa amman hankalinta na kan wayarta. Duk wanda zai yi ma rubutunka haka ai ba ƙaramin masoyinka bane. Ummu nabeeha, da su Khadija Amarya, Maman Amal, Khadija mai doki, Salma musa, Mamagee, da duk members na cikin zauren NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA. duk sun tashi hankulansu. To ga page 15 na baku. Amman zai iya kaini mako guda kafin in gama uzirin dake gaba. In sha Allah zan dawo da zafi. Nagode)*
SHANONO
Bance da Hajiyayye komai ba, sai buyagi take yi. Nazo nayi wucewata ko sake kallonta ban yi ba. Ina jiyo Yayarsu tana ƙunduma manyan zagi a tsakar gidan. Sabira ce ta shigo ɗakina da sallama, hannunta riƙe da kwanon abinci. Wayata ce ta shiga ruri a karo na biyu. Yaya Karime ce take kirana, dagawa nayi tare da kara wayar a kunnena.
Yaya Karime ina wuni?" Daga cikin wayar akace.
"Inno ce Tani. Yaya kun isa gida lafiya dai ko?"
Lafiya lau Inno yaya biki?" Dariya tayi tace.
"Ƴan uwanki sun so ganin ki. Barinma ƙawarki Shafa, yaranta goma fa yanzu, jin labarin kin shigo Shanono sai gata a gidan biki. Yaya Kaila ya yarda da zaman Dauda ba wata matsala ko?" Tsintar kaina nayi da cewa.
E ya yarda Inno." Baki ta washe tace.
"To barka ni dama dalilin da yasa na kira inji kenan. in na dawo zan zo in ɗaukeshi. Sai mu yawata dashi muna bara ina nuna ma mutane ciwon nashi. Ba karamin kuɗi zamu samu ba, kinga muma ma samu a jikinshi. In muka tattare kan kuɗin ko asibitin miya barkatai ai sai a kaishi su yi mishi aikin ko Tani?" Idanu na lumshe na tuno lokacin da muka sauka a Bamaina dake jihar jigawa, Inno ta ɗaure mun ƙafata, ta samo jini a kwata ta kwara mun a kafata, haka mu ka fita mu kaita neman kuɗi a haka. Na sha wuya sosai, Amman mun samu kuɗi sosai. Watanmu biyar kullum sai Inno tayi mun haka
A'a Inno ai Dauda wata ƙawata da mu kai karatu a Bauchi ta ɗauki nauyin biyan kuɗin aikin nashi. Yanzu haka ma suna Bauchi tare." Inno ta yi sanyi da murya, a maimakon taji daɗi, sai ma ta nuna irin ita tafison ta yawata da Dauda, sabida ba karamin kuɗi zata samu ba. Yaya Karime ce ta karɓi wayarta muka gaisa. Daga ƙarshe su kai mun sallama tare da kashe wayarsu.
"Tani ga abinci maza kici. Wai Hauwa tana Shanono ne a wajan su Inno?"
Hmm tana can, sai sun dawo zasu kawo mun ita. Nagode da hidima Sabira " farfesun kan saniya ta zuba mun da farar shinkafa. Ai kuwa naci sosai, ta bani magungunana na sha suma. Sannan nace mata.
Habiba Bala ta bani kuɗi in koma makarantar islamiyya, da boko. Kuma nima dama na riga na ƙuduri niyyar hakan. Dama jira nake in haihu, zaman rashin karatu bazai fissheni ba Sabira. Kinga kuɗin" Ƙasan fulon da nake kwance na bankaɗa na ciro kuɗin, na ba Sabira a hannunta.
Kinga kuɗin ko. Tace abinda ya ragu sai in soma ƴar sana'a domin dogaro da kai. Ke meye shawararki akan hakan? Wacce makaranta kike ganin ya dace in shiga?" Sabira dake riƙe da kuɗin a hannunta tana jujjuyasu tace.
"To tunda naga kuɗin da yawa. Inaga a shawarce ki shiga islamiyyar matan aure *UMMAHAT* Ta cikin al'iman. Kinga Mrs Bukhari ma makarantar tayi, nima gashi ita nake zuwa. Jumma'a, asabar, lahadi ne ranakun zuwan, kinga bazai taɓa makarantar bokonki ba. Kuma zaki ji larabci sosai dan ba'a Hausa, ( Allah sarki malama musriyya, malama Hajara, malama Zarah, mun sha larabci) zaki haɗu da mata wayayyu ƴan ƙarya. Nima gaskiya makarantar ta sake gogar dani na sake fahimtar yanda zan mallake Baban Mustapha. Bokon kuma zamu bincika wata makarantar matan aure dake cikin shaƙura, can unguwar rogo ƴan kwaba. Akwai wata makarantar matan aure masu jajayen wando sai mu bincika. Maganar islamiyya kuma zan sa Baban Mustapha yai ma abokinshi magana suna ɗarasawa da munir director ɗin makarantar asamu a saki a aji ɗaya. Kinga in kika gama makarantar nan har zuwa aji shida? To zaki samu takaddar zaria, zaria suke kiran takaddar, da wannan takaddar zaki iya