Author : Bintubatula Category : African Stories & Novels
yake." Hararsa tayi kad'an tace." Kana da Neman magana ko." Murmushi yayi tare da lakuce mata hanci yace." Gaskiya ne ai." While chair d'in ta kama tana k'okarin tura shi domin ta futa dashi farlo, yace." Bari ki gani da izinin Allah yanzu zan taka k'afafuna." Balaraba ta matsa gefe tana kallon ikon Allah, ya yunkura bakinsa d'auke da Addu'a sai gashi tsaye da kafafunsa, cikin mutukar farin ciki ta furta "Alhamdullahi ala kullu halin." Shima cikin farin ciki yace." Allah ne abun godiya." K'okarin futa take yi ya rike hannunta da sauri yana fad'in " INA zakije kece 'yar jagora ta fa." Cike da farin ciki tace." Wallahi duk na rasa ya zanyi saboda farin ciki,hak'ika ubangiji naji rokan bawansa ne." Yace." Hakane mutukar bawa zai mik'a lamarin shi ga ubangijinsa to babu shakka dukanin Matsalar sa ta kare." Rungume shi tayi sosai tana sauke ajiyar zuciya, cire ta yayi daga jikinsa yana Dan murmushi yace." In kika karya min alwala fa , zamuje massalaci yanzu in mun dawo kiyi min tanadi me kyau." Ta sinne kanta kafadar shi suka futa a haka
Su Shahid na zaune suna jiran futowar sa,kawai suka ganshi ya futo da k'afafun sa,tare suka mike tsaye cikin mamaki ! Shatima yace." Alhmdullahi Alhmdullahi ala kulli halin, yaushe ka mike ka fara tafiya." Suka fada a tare. Balaraba tace." Yanzu ne kamar da wasa wallahi ya mike." Shahid ya zube gurin yana sujjadar godiya ga Allah,shiko Shatima waya ya futo da ita zai kira mutan gida, Yace." Ka bari tukkuna muje mu dawo ko meye sai ya biyo baya in ka kira mutane yanzu zasu hana mu ibada." Shahid yace." Hakane bari muje mu dawo kawai, tare suka futa har da Balaraba tana sanye da dogun hijabinta fari tass dashi mijinta ya rike mata hannu suka fara tayi,dake gidan da suke bashi da nisa da harami da kafa suka tafi,
Bayan an idar da sallahr jama'a suka zauna massalaci suna add'a tare da karatun alkur'ani me girma.
**********
Waziri Zayyanu kuwa yana futa fadawansa suka rufa masa baya tare da kareshi da lema saboda rana sai baza babbar riga sukeyi, kamar daga sama yaji wani irin ihu!! A kunnensa ,zabura! Yayi yana kalle-kalle, wani ihun yaji Wanda yafi na d'azu, can yaji gurnanin Mak'asudu sama-sama yaji muryar shi yana fad'in "Aiki ya lalaceee!!!!! Ka janyo min ka janyowa kanka, ihuuuuuuuu!! Shikadai yake jin wannan ihu,ya tsaya yana dira-dira Wani bafade yace." Gyara kimtsi daiiii!!! Allah yaja zamaninka ko kayi mantuwa ne." Waziri ya girgiza masa kai a mutukar tsorace!! Yake, tuni jikinsa ya fara tsiyayar da gumi! Ya juya zai goma gida, k'afafun sa suka sark'e suka lauye suka kwalmad'e ba tare da bata lokaci ba ya zube a gurin, yanda k'afafun sa sukayi haka hannuwan sa sukayi, bakinsa ya kar kace idonsa ya wurkile, hallitunsa suka sauya gaba ki daya. Fadawansa suka saka salati tare da d'aukar sa domin kai shi cikin gida.
Ko da suka shiga dashi cikin gidan suka tarar da tashin hankali domin sauran 'yayan ne tsaye kan Mahaifiyar su suna k'okarin ceto rayuwar ta.
*********
Shamsiyya ce cikin kuryan d'akinsa tunda ta tashi da safe take jin ciwon ciki tayi shiru bata fada ba,sai da taga wani abu me kama da jini yana zubawa daga gabanta shine fa ta kira mahaifiyar ta ta fada mata, Uwa ta kira Lantana hankali a tashe! Tasan haihuwa CE,nan suka fara bata taimako ganin yadda take yunk'urin da alama haihuwar a kusa take.
********
Tashin hankalin da iyalin Waziri suka shiga ba a fad'ar sa, ganin yadda hallitun ubansu ya sauya ya munana ya jirkita sai kace ba mutum ba, tuni wasu suka fara kuka mussaman mata, da k'yar aka samu Kattime ta dawo hayyacin ta, ta kallin mijinata da ya koma kamar tsumma! Lokaci guda ubangiji ya tagayarashi tace." Alhamdullahi Allah na gode maka da ya mayar da kai haka hak'ika mutuwar ita tafi amfani da RAYUWAR ka, ka cucu ni ka cuci 'yayanka saboda son zuciya irin taka, ka kashe rai Wanda bamu San adadi ba, hak'ika nayi nadamar auranka bana fatan ko a lahira ubangiji ya had'a fuskoinmu"
Tana gama maganar ta fashe da kuka me cin rai!
Nan fa fadawan da suka kawo shi suka dinga silalewa suna futa cike da kunya.
********
Cikin hukuncin ubangiji Shamsiyya ta haihu lafiya inda ta haifi d'anta namiji yaro lafiyyaye dashi me kama da ubansa sak!!! Kuka sosai take uwa na tayata wai yau itace zata Goya Dan shege rayuwa kenan, haka Lantana ta dafa ruwan zafi tayiwa jinjiri Wanka tas ta shirya shi cikin kaya,ta goyashi tana daure zuciyarta itama amma kukan zuciya kam kullum sai tayi shi.
******
To ranar bayan sun dawo daga massalaci Shatima ya kira wayar mama ya Sanar mata halin da ake ciki, murna sosai Mama tayi ta dinga godewa Allah da ya kawo wa yaron ta sauk'i cikin lokaci kankani lallai duk Wanda ya dogara ga Allah yayi dace duniya da lahira
Me girma governor kuwa yana ganin kamar yafi kowa farin ciki, don haka nan take yasa mutanan sa afara shirye-shiryen nad'i domin a cewarsa me Martaba Sarki!Almansur na biyu na dawowa za'a fara shagalin nadin sarauta, aikuwa gari ya d'auka da murna,dama labarin halin da Waziri yake ciki ya karad'e ko ina cike da waje harda wajan gari ma kowa yaji wasu na turr dashi wasu kuma na tausaya masa halin da yake ciki.
Yau Litinin Wanda yayi dai-dai da sati uku kenan da tafiyar su saudi'a a yau din ne kuma suke d'aura niyyar dawowa gida cikin farin ciki da samun nasara, Balaraba tayi wani fresh da ita kyallin ciki duk ya bayyana a tattare da ita, ta kara cika da kwarjini sosai duk Wanda yasan mace me ciki ya kalleta a lokacin sai ya gane, shiko uban tafiyar tamkar ba Wanda yaje jinya ba ya had'a wata kiba fatarshi tayi sumul-sumul sai shek'i take,shida Balaraba har nasara Wanda yafi wani kyau da gogewa
******
Can gida kuwa ya hautsine da shagali gami da kid'e-kid'e da busa ko INA ka kalla jama'a ne suke kai kawo kowa yana cike da farin cikin dawowar me Martaba cikin aminci da koshin lafiya.
Halisa da Azima sai kintse-kintse sukeyi kowacce tana k'okarin tayi abunda zata fi 'yar uwarta dashi, Azima kokari kawai take tana ji ajikinta kamar asirinta zai tuno tunda dai gashi Waziri yana cikin wani hali shine dama ya yaudare ta, gashi yanzu tana mutukar son auranta addu'a kawai take Allah ya rufa mata asiri.
Fili jirgi a cike da a yarin gidan sarauta tare da ayarin me girma governor suna jiran saukar jirgin su, Sha biyu dai-dai jirgi ya sauka Shahid da Shatima ne a gaba, sai Sarki! Da BALARABA a bayansu ya rungomo ta jikinsa, tuni gadawan gurin suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa, cike da kunya take k'okarin kwace jikinta ya ki s'akinta,cikin walwala suke gaisa da jama'arshi su Governor da Galadima da sauransu mota ta mussaman aka bude masa ya shiga ya zauna Balaraba ta shiga direba ya shiga domin su Kansu su Shahid wata motar daban suka shiga, direba yaja su suka nufi gida
*****
Tsabar hayaniya jama'a tasa kansa ya fara ciwo nan take yace. da Babu direba su huce can shashen Maman shi, amma duk da haka jama'a bin motar suke suna banbadan ci tare da roko da kid'a kowa na fadin albarka cin bakinsa, Sarki ya futo cikin walwala ya dinga daga musu hannu ya rike hannun matar shi tamm!!fadawa suka dunga sanya duka da bulala da k'yar dai ya samu ya tattatka suka shige gurin Maman shi, wacce take tsaye gurin wani k'aton window tana ganin abunda yake faruwa, ganin yaron ta yayi kiba da lafiya gashi kamar ba Wanda ya tafi jinya ba,yasa ta godewa Allah sosai yana shigowa ya rungume ta, Balaraba ta koma gefe tana murmushi, Mama ta rik'o hannunta tana fadin"Zonan yarinyar ta hak'ika ke alkairi ce a tare damu kin zama Wani jigo na rayuwar mu, Balaraba ina jinki a cikin jinana tamkar nice na haifeki ubangiji Allah ya sauke ki lafiya." Balaraba tayi saurin sunkuyar da kanta cike da kunya, lallaima ashe sai da ya fadawa Mama halin da take ciki" Mama ta cigaba da cewa." Duk irin dawainiyar da kikayi da mijinki ina da labari, babu abunda zan iya saka miki dashi sai dai addu'a ladan ki na gurin Allah domin kinyi ibada kin bautatawa mijinki ubangiji Allah ya jikan iyayaenki yayi miki albarka a rayuwar ki." Balaraba ta sunkuyar da kai kasa tana amsawa da amin kwalla duk ta cika mata ido.
Sadiya da Usuman ne tsaye can gefe suna kallonsu Mama ta kirasu tace." Kuzo ga aunty ta dawo,. " BALARABA ta daga Kai tana kallon yaran sunyi kyau sosai sun murje sun kara girma Sosai Mama take kula dasu, makaranta suke zuwa me tsada su saka suttura masu tsada babu. Shakka babu abunda zatace da Mama Fulani bisa alkairin ta a garesu.
Nan b'angaran Mama suka biyo shi Halisa da Azima kowacce tana wace wannan gurin ado gwal sai walwali yake a jikinsu, Balaraba ta basu gurin ganin yadda sukeyi I junansu tamkar su bangaji juna,duk wannan k'awancan babu shi, kowacce ta kwaci kanta, Halisa duk ta kanainaye shi, a cewar ta ai girkin ta ne yau don haka duk su matsa gefe, shidai kawai kallonsu yake, yana tunanin halin da zai shiga zai kwana ba tare da gimbiyar sa ba, ya Riga ya saba da dumin jikinta da shagwaba shi da take sosai da soayyarsu duk dare, to itama b'angaran ta hakan take duk tayi sanyi tana tunanin ta yaya zatayi bacci bataji kanta a kirjinsa ba yana mata wassanin kamar yanda suka saba a saud'ia.
*Daga wannan pege din sai na k'arshe Ku zauna cikin shiri*❤❤❤❤
[10/7, 12:25 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*
*MARUBUCIYAR*
```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
```LADIDI K'WADAGA```
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_
_____________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________
*JAN KUNNE⚠*
_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_
*DEDICATED*
~*TO*~
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*🅿115*
Da k'yar ya samu ya kufce daga hannun Halisa ya gudu part d'insa inda su Shahid suke zaman jiransa,nan kama kafin ya tafi sai ya gargade su kar wacce ta bishi, saboda hutawa zaiyi Balaraba cikin zuciyarta tace." Dama ni ko ka neme ni ba zuwa zanyi ba, zama zanyi inyi jinyar zuciyata da zatayi kwana hudu ba tare da Kai ba.
Nan gurin Mama suka zauna dukaninsu, kallon Balaraba sukeyi a fakaice ganin yanda tayi Wani mugun kyau, tayar ta kamar ka tab'a jini ya futo ta kara cika da kwarjini, wani kyashi da bakin ciki ya damu zuciyarsu babu abunda ya kara daga musu hankali sai yanda Mama take kula da ita, tana kaf-kaf da ita da tayi motsi zatace "Ya akayi in dai akwai abunda kike sha'awar ci kiyi magana akawo miki." Girgikai kai kurum take cike da kunyar Maman, Halisa ta kalli Mama da jiki a sanyaye tace." Bata da lafiya ne."? Murmushi tayi tace." Cutar ta arziki ce ai insha Allahu kun kusa samun baby." Ita da Azima ban San wanda yafi wani shiga rud'u da tashin hankali ba, neman miyau tayi ta rasa abakin ta, idonta ya ciko da ruwan hawaye, Balaraba na da ciki,cikin kuma na masoyinta Wanda taci burin ita zata fara Haifa masa 'yaya, to wai abun tambaya anan, shine mutumin da ya tafi Neman lafiya ta yaya har ya iya kwanciyar aure babban abun tambaya yaya akai shi da bashi da kafa ya sarrafa kansa.
*Dariya nayi nace lallai Halisa kin cika hamaguwa😄*
To tunani da take shi Azima take duk sun shiga tashin hankali Lallai BALARABA tayi musu fintinkau tayi musu zarra,yanzu meye abunyi? Halisa take tambayar zuciyar ta, wani b'angare na zuciyar tata Yace mata,kawai yau kema ki matsa masa yayi miki ciki ki haihu, aikuwa ta yarda da wannan shawarar ta zuciyar tata.
*******
Walidi ne ya siyowa Shamsiyya atamfa guda biyu dinkakkau ya siyo rago ranar suna yaro yaci sunan mahaifin su,wato Sallau, Salihu kenan, a ranar ne kuma labarin Mabaruka ya same su, ta hanyar k'afafun yada labarai, an nuno ta kwance gadon asibiti babu k'afafu, ana cigiyar danginta harda Lamar waya aka kawo wa Walidi aikuwa atake ya kira wayar yayi musu kwantan inda suke, ba tare da bata lokaci ba aka sako Mabaruka a mota tare da keken guragunta tana kuka tana da tasani abunda tayi, Ranar kwana sukai kuka Iya da Sadiya matar Maman suna ta tausar zuciyar su.
******
Ana kiran idar da sallahr Isha'i Halisa ta dura a part din Sarki! Cikin shirin ko ta kwana, tayi kwalliya iya kwalliya, sama ta hau domin baya farlo,shima tunda su Shahid suka tafi ya hau sama domin ya huta, bude kofar tayi ta shiga bakinta d'auke da sallama ya amsa babu yabo babu fallasa, zama tayi kusa dashi, tana sak'e-sak'en maganar da zata yi masa, yace." Halisa mun same Ku lafiya ko."? Cikin dauriya tace." Lafiya lau Yallab'ai." Shiru yana sauraron ta yasan da akwai magana a bakinta, yace." Wane tanadi kikayi min."? Yake tayi kawai tace." Ni wane tanadi zanyi maka,nice ma Nazo kayi min tanada kamar yanda kayiwa Balaraba." Bai gane hausarta ba yace." Wane tanadi nayi Mata." Inda-inda ta fara yace." Ke nake saurare." Tace.'Nima ciki nake so kamun.' Cikin mamaki yake kallonta. Yace." Ciki Allah ne ke ba dashi ba mutum ba, sai kice ni in zama silar shi." Kuka ya fara yi sosai harda sharb'ar majina." Yace." Meye abun kuka, kuma." Tace." Ina jin takaicin yadda wata zata fara haihuwa dakai bani ba." Tsaki yaja yana girgiza kai yace." Matsalata dake rashin wayo da dubara ni dake da balaraba babu Wanda ya Isa ya hana Allah ikonsa akanmu Balaraba zata fara haihuwa dani haka Allah ya tsara.'' Kuka sosai takeyi takasa cewa komai ta kwanta kan bed din tana Jan ajiyar zuciya, tausayinta ne ya kamashi,ya kashe futal dakin tare da aje k'aramin littafin hannunsa ya rungume ta yana fada mata daddadan kalamai, nan labari ya sha BABBAN, na futo na barsu ina fatan samun nasara da 'yaya masu albarka.
To sarki! Ya biya Halisa domin dai jiya ya kashe ta da soyayyar sa mai wahalar mantawa lokaci kad'an ta manta da damuwar ta,ta cigaba da kyautatata masa.
******
Tsito ne ya dura a gidan kamar tsohon mahaukaci ya nufi b'angaran Hajiya Kulu me dakin kudu, yazo domin ya karb'i sauran kud'in aikin sa. Nan ya samu babu. Kowa a shashen nata sai hadiman ta, suka ce masa satin ta biyu bata gida,hakanan yaranta suma ba kullum suke kwana a gida ba, haka ya futo yana tunanin ina zashi,domin yanzu duk aljanun da suke kanshi sun dare sun gudu baya iya yin aikin komai watarana ma da yunwa yake kwana, ya tabbatar da cewa abunda suka aikata da Waziri ne ta shafe shi, zuciyarsa ta bashi shawarar kawai yaje ya nemi afuwar iyalin Waziri ko Allah zai sa ya gama da duniya lafiya, sannan suyi masa iso gurin Sarki! Almansur domin ya nemi gafarar sa Halin da yaga Waziri a ciki ya bashi tsoro bakinsa ya dinga rawa ya rasa abun cewa,Hajiya Kattime tace." Bawan Allah daga ina haka domin banga ne ka ba."?
Tsito ya fashe da kuka yana fad'in." Yanzu haka Waziri ya koma oo ni Tsito." Kattime tace." Kayi min bayani mana, yace." Nine Tsito wanda nayi ma mijin ki aiki duk Dan yayi mulki nan ya warware mata duk abunda ya faru, yaran ta suka taso domin suyi masa duka ta hanasu, tace." Ku kyale shi shima zai ga karshen sa, nan Tsito yayi dasu su masa iso gurin me Martaba Kattime ta hana, haka suka tarkatashi suka futa dashi fadawa suka tasa keyarsa har waje, yana futa ya kasa gane hanya kawai sai ya dauki wata haya ta daban yana tafiya yana tsayawa bola-bola yana tsince-tsince duk ledar da ya gani sai ya d'auka ya sa a bakinsa yana taunawa.
*Ubangiji Allah kasa muyi kyakyawan k'arshe*
*******
Kwana biyu da Halisa tayi ta samu kulawa sosai a gurinsa ganin yanda ta kwantar masa da kai tana kula dashi komai sai tace idan BALARABA ta haihu za'ayi kaza da kaza, hakan ne yasa ya Sakar mata jiki suka sha soyayya.
Azima ya ta karb'i girki sai girin gidishi take tasha magunguna mata kamar banza mararta sai kullewa take jira kawai take dare yayi ta shiga part din Yallab'ai a kashe boss.
*****
Hajiya Kattime ce tayi sallama ta shiga a nutsue Mama ta amsa Jakadiya ta gyara mata gurin zama,sannan ta futa ta basu guri, Kattime ta gyara zama tana fadin ." Fulani magana nake tafe da ita." Mama tace." Ai tunda naga fuskar ki nasan akwai magana."
Kattime tace." Wallahi kuwa, jiya na samu wani labari da bakin da ya fada min bazai k'arya kai asalima shine ya asassa al'amarin." Mama ta zuba mata ido, Kattime ta cigaba da cewa." Kin san Azima da ita aka had'a baki gurin cutar da Almansur." Mama ta mike zaune sosai tana kallon ta cikin mamaki! Kattime ta cigaba da cewa.' Jiya Tsito mashirikin da yayi aikin yazo ya warware min komai, saboda haka Nazo na fada miki auran Azima da Almansur dama da wata manufa aka had'a shi don haka ki umarce shi da ya rabu da ita tun wuri."
Mama jikinta yayi sanyi sosai da sosai tace." Dama ni kaina banyi na'am da wannan hadin ba wallahi oh! Mugu bashi da kama yanzu Azima itace ta bawa yarona guba yaci domin ya nakasa."? Kattime tace." Kina mamakin wannan duniyar wallahi."
Mama tace." Yanzu zan sanya ayi min kiran su ki zauna a gaban ki za'ayi komai, Jakadiya ta kira ta umarce ta ta kira mata Azima da Halisa BALARABA
Wayar ta ta d'auka ta kira uban gayyar, suna tare