Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

GIMBIYA BALARABA Kauna, Iko, da Yaudara by Bintubatula

Author :  Bintubatula Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 7

9K to 12K   out of 19.4K words

ya hau yi masa gaisuwa, ko kallon su baya yi

*********
Tafiya take fakam-fakam!! sak'e-sak'e kawai take a zuciyarta da tunanin d'aukar fansa kan, d'an burni,sunan da ta sama sa kenan, wallahi bai dake ta a banza,sai ta rama duk hanyar da zata bi ta sani, leb'anta ta tab'a da hannunta, cire hannuta tayi tana girgiza kai! a fili tace."Wallahi he na rama idan ubanka ne shugaban k'asa he na rama, nima sai na fasa maka baki,hummm!! Zaka san ka tab'o Ladidi jikar Mai koko, bana barin takwana kuma bana manta ranar d'aukar fansa." Da tafiyar ta ya gane i tace jiki na rawa ya k'wala mata kira,"Ladidi" da sauri ta juyo tana waigen idan taji ana kiranta. Kakanta ne D'an fulani, yake tawo wa inda take, yana can gurin kiwo labari ya same shi na mutuwar ta,shine ya tawo cikin tashin hankali! Abun mamaki kuma sai gashi ya ganta a hanya, yana k'arasowa inda take ya damk'i hannuta, bai ce mata komai ba suka fara tafiya, zub'uro baki tayi tace." Ni ka sake ni ka rik'e min hannu da k'arfi ai gida zani ba wani guri ba." D'an Fulani yayi mata shiru, shi dai k'okarin shi kawai yaga ya danganata da gida,hankalin kowa ya kwanta. Tun daga nesa jama'ar dake gurin suka hango tawowar su, sai aka fara kallon-kallo tsakanin su, da suka tabbatar da cewar itace sai kowa ya fara zura silafas d'insa yana guduwa, D'alha ya juya yaga wayam! babu kowa a gurin, girgiza kai kurum yayi yana jin wani d'aci cikin zuciyarsa wato Ladidi ta zama abun tsoro kenan? D'an Fulani ya d'amk'ata a hannunsa yana fad'in"Gatanan can wajejan titi na gano ta tana tafiya ita kad'ai." D'alha ya sauke ajiyar zuciya yace."Alhamdullahi, dama ni jiki na bani yarinyar nan tana raye,amma jama'ar gari suna ta fad'in ta mutu a cikin ruwa,Allah nagode maka daka bayyana mana ita ko hankalin Mai koko ya kwanta." Sai sanan Ladidi ta tuna da abunda ya faru d'azu tsakaninta da Mai koko, dariya ta kece dashi,hahahaha! D'alha ya gaura mata mari! Yana fad'in"Rufe miki don buhun ubanki, shashasha, shakatafe, naga ranar da zakiyi hankali dai" D'an Fulani kuwa a'lamarin Ladidi ya fara bashi tsoro,don haka yace."D'alha mu shiga cikin gidan sai mu San abun yi." Kai tsaye cikin gidan suka shiga.




*Tofaa ko ya zata kasance idan jama'ar gidan sukaga Ladidi Wanda suka dauka ta mutu cikin rijiya,ko yaya Mai koko zatayi in taga Ladidi? To Ku cigaba da bina dai cikin labarin domin in warware muku*






*COMMENT VOTE AND SHARE*
[10/1, 10:04 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻





~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*





*MARUBUCIYAR*


```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
```LADIDI K'WADAGA```




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_

_____________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________




*ALHAMDULILAH*

*HAUWA S ZARI'A*
_Maman Usuwan_

*Ina taya ki murna na kallama littafin ki HAKA ALLAHA YA NUFA* _KADDARA TACE_ *UBANGIJI ALLAH YA K'ARA BASIRA YA SA SAK'ON KI YA ISA INDA KIKE SO*
_________________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_





*DEDICATED*
~*TO*~
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿113*




K'ok'arin futa take daga d'akin, ba tare da ta k'ara kallon inda yake zaune ba, cikin nutsuwa yace." Ina zakije kuma"? D'an juyo wa tayi tace."Zan je in kawo maka abun kari" k'asa yayi da kansa cikin so da k'aunarta yace."Na huttashe ki dawo ki zauna, domin yau bana jin yinwa saboda kin cika min ciki da so da k'aunar ki, hak'ik'a ina alfahari dake cikin matana Balaraba kece Gimbiya ta." Lumshe idonta tayi tana jin wani yarrr! a jikinta gaskiya taji dadin yabon da yayi mata, itama yanzu ta fara jinsa cikin zuciyarta, yace." Dawo ki zauna muyi hira" Simi-simi ta dawo ta zauna nesa dashi,sai kauda kai take cike da kunya, shi kuma ya k'ura mata ido yana sakin k'yatattacan murmushin sa, cikin shagwaba'a tace." Ka daina kallona haka inajin babu dad'i a jikina."Lumshe ido yayi ya bud'e tare sa zuba mata su yace." Haka nake so ai da alama kin fara sona, ko da yake ma, jiya naga alamu daddare an karb'eni hannun biyu" rufe fuskarta tayi ta mik'e da sauri ta bude dakin ta futa cike da kunyar sa. Karo! Suka buga da Halisa ta d'ebe ta ta watsar! tab'e baki tayi tamkar taga kashi tace." Ke kuma wannan shashan cin fa? dube ki don Allah abun tausayi dake wai har kece zaki shigo cikinmi ki nakasa min miji,to bari kiji wallahi Duk irin k'ulunboton ki baki isa ki kashe min mijina ba, domin kici dukiya sai dai Idan mu, mu kashe ki, kar ki manta da cewar mun San kece silar mutuwa d'an uwanmu Moddibo, to wallahi Sarki! Almansur yafi k'arfin ki, jaka kawai, 'yar talakawa"

Wani mugun b'acin rai! Ya turnek'e zuciyar Balaraba, tabbas Halisa taci albarkacin mijinsu da bashi da lafiya, amma da badan wannan ba, da sai ta k'ara nuna mata ita wacece, da alama ta manta karon su da ita na farko, amma taci al'washin duk randa ta k'ara yi mata magana irin wannan tabbas sai ta nuna mata kuskuran ta. Azima ce ta k'araso inda suke tsaye ta buge k'afad'ar Balaraba tana zabga tsaki! Hannun juna suka rike suka wuce ta cikin wata irin tafiya ta k'asaita. Kallo ta bisu dashi zuciyarta tana zafi,! Lallai ruwa ya daki babban zakara, ita kad'ai take fad'in haka a zuciyar ta, idan da ba haka ba wallahi da sai sun gane kuransu.

Yana zaune inda yake tun futar Balaraba, fuskarsa cike da annuri suka same shi, amsa musu sallama yayi ya nuna musu gurin zama, jiki a sanyaye ko waccen su ta zauna, babban abunda ya sa jikinsu yayi sanyi shine ganin da sukayi yana cikin farin ciki da annushuwa kamar yadda suka ga fuskar Balaraba haka, wani irin kishin Balaraba ya damu zuciyarsu, sanin halinsa na rashin d'aukar raini yasa ko wacce tayi shiru da bakin ta, gai dashi sukayi sunayi masa ya jiki, ya amsa da walwala, Azima tace."Yau zaku tafi ne"? " Eh insha Allahu sha biyu na rana" Shiru sukayi. Halisa tace." Tunda ita wannan ta futa daga girkin ta, zan shiga nawa ina ganin ya kamata a tafi dani ko da wani taimakon da zanyi maka." Harararta yayi, ta sunkuyar da kanta da sauri, a hankali yace." Ke ko za'a tafi da wani waye zai tafi dake guri kije kiyiwa mutane shirme" Azima taji dad'in maganar sa, ji wani son kai na Halisa take fada a zuciyar ta, muryar shi sukaji yana fad'in"Duk Ku kwantar da hankalin ku babu da wanda zani, sai kace wani Yaro,ku munje ma ba wani zama za muyi ba."


Azima tace." Nima dai abunda nagani kenan." Halisa kuwa sai yak'e take ta lura mutumin nata haushinta yake ji, domin yak'i sakin jiki da ita hirarasu suke da Azima tamkar babu ita a gurin. Wayar shi tafara k'ara ta mike da sauri ta d'auko masa, karb'a yayi ba tare da yace mata komai ba, Governor na ne, suka gaisa yace." Fatan jikin da sauk'i, duk wasu shirya-shirye angama insha Allahu da kaina zan zo in d'auke ka cikin mota har filin jirgi" Sarki! Yace." Jiki alhamdullahi ni kam bani da matsala sai ta rashin k'afafu shima na wani lokaci ne insha Allahu, zamu zauna cikin shiri insha Allahu" Governor yace." Naji muryar ka rad'au da alama kana cikin nishadi kasan fa duk namiji da yake da mace sama da daya to mutukar suna kula dashi da kwantar masa da hankali babu Wanda ya kaishi dacewa". Murmushi yayi yace." maganar ka haka take, Aboki" dariya Governor yasa yace." Dole dai na koya maka surutu ko"? Yace." To ya na iya fa halin ka." Haka dai sukai barkwamci kafin suyi sallama suka kashe wayar, Azima da Halisa kuwa ganin babu fuska ko wacce taje zata je tayi Wanka, suka sauka babu wacce ta kara kula 'yar uwar ta.
[10/2, 9:21 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻





~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*





*MARUBUCIYAR*


```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
```LADIDI K'WADAGA```




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_

_____________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________






*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_





*DEDICATED*
~*TO*~
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿114*




To Balaraba ma lokacin da suka rabu dasu Halisa gurin ta, ta nufa wanka ta shiga a gurguje ta futo ta kimtsa jikinta, ta kasance mace me son atampa duk ya wanci kayan ta itace doguwar riga, da Riga da siket da zani basu da yawa, yanzu ma wata 'yar Ghana ta saka doguwar riga ce, sosai kasa ya bud'e daga iya kwankwanson ta ya matse da kirjin rigar komai ya futa har madauri ne da ita daga baya, d'ankwali ta d'aura dai-dai misali ta shiga kicin dinta dole tana ganin sai tayi masa abu motsa baki, cake ta fara had'a ma, zuciyar ta tace ki had'a masa Dambu nama ko yana so, nan take ta futo da zallar tsokar Neman sa cikin firji ta Dora kan wuta bayan ta sanya albasa da kayan k'amshi, ta cigaba da had'a cake din ciki k'warewa.


Balaraba ta k'aware sosai gurin had'a dambun nama shiyasa sam bai bata wahala ba, nan ta had'a komai cikin abunda bai fi awa guda ba, k'amshi ne kawai yake tashi kicin d'in, zuba shi tayi cikin warmers ko wanne ta aje ta samu wani had'ad'an akushi irin na gidan sarauta ta cika shi da cake d'in da Dambu nama,wannan ta aje shi ne sai zasu tafi zata bashi, ruwa ta d'ora a wuta ta zuba kayan tea masu sa kamsh gahwa na'ana'a citta kanifari kimba da dai sauran su sai da ya gaja da tafasa sannan ta kashe gas d'in ta tace sosai ruwan tea d'in yayi kyau sai kamshi yake ta juye cikin fulas mai kyau. D'auka tayi ta kai falonta ta aje ta dawo ta gyara kicin din tas! Sannan ta dawo ta d'auki, d'auki abunda ta aje, kai tsaye part din shi ta nufa. Lokacin har su Shahid sun zo sun d'auko dashi k'asa yayi wanka shar dashi kana ganinsa kaga ango sosai yake walwala Shatima na tsokanar sa wai farin cikin me yake, shi kuma yana basarwa.
A nutse tayi sallama ta shigo, da sauri ya dago kanshi yana kallonta, saurin sunkuyar da kanta tayi, cikin mamaki ya bi hannuta da kallo, yana kallon yanayin tafiyar ta, Shatima ya amsa yana fad'in"Gimbiya sannu ki da zuw..... Katse shi yayi ta hanyar fad'in"Ka tsaya kana surutu ka karb'i abun hannuta mana,bata da lafiya" Balaraba tayi saurin kallonsa, cikin mamaki, da sauri ta wuce Shatima ya bi bayanta yana fad'in"Ayya! Gimbiya sannu da kokari kawo in aje miki daining d'in." Murmushi k'arfin hali tayi tace." Ka rabu dashi don ni lafiya talau fa." 'Yar dariya yayi yace." Ai naga alama gashi kin sha aiki domin ki faranta ran maigidan ki mybe yana so ki huta ne shiyasa Yace in karb'e ki" Shiru kawai tayi masa tana sunkuyar da kanta cike da kunya,wato Dole dai sai ya tona mata asiri gurin abokan shi,kome amfanin fad'a musu haka oho masa. Gyara gurin tayi sosai, Shahid ya kawo shi har gurin, idonsa a kanta yace." Wato nace kije ki huta shine kika wahalar da kanki ko." K'asa tayi da kanta kurum domin bata so tayi wata magar ya lafto wacce zai sa har su Shatima su gane. "Jimana" yafad'a yana tsare ta da ido, a nutse ta watsa masa wani kallo, Wanda ya shiga jikinsa,amma da yake ya saba karb'arsa sa'i da lokaci a gurin ta,sai ya dake! Yace." Bayan wahalar da kika sha jiya shine zaki na wahalar da jikin ki yanzu,wai ke bakya son hutu ne." ? Taikacinsa ya hanata cewa komai, sai aukin futo da warmers take, Shatima ya doki kafad'arsa yana fad'in." Kai kanai mata bak'in cikin ladan da zata samu ne, ina ruwan ka."? Shahid ya b'oye dariya yana fad'in"Lallai hausawa da sunyi gaskiya cikin karin maganar su, inda suke fad'in"Gurgu yafi...........Sarki! Ya galla masa harara! Dariya suka saka Shatima ya bashi hannu suka taga!Balaraba kamar ta nutse don kunya, simi-simi tabar gurin tana da ta sanin dawo da tasan tonan silili zai mata da bata dawo ba, dab da zata futa sai ga Mama ta shigo da jama'ar ta, sai ta tsaya tana murmushi , itama Mama murmushi ne a fuskarta, suka zauna cikin kujera Balaraba ta durkusa har kasa ta gaishe ta, cikin sakin fuska mama ta amsa tana tambayar me jiki, tace "Jiki alhamdullahi wallahi gashi yana k'okarin Mama muna sa ran samun nasara wannan tafiyar insha Allahu, Mama tace." Hakane dama babu abunda yafi k'arfin addu'a ai, jiya munyi waya da aminiya ta, Matar Sarkin Yalwa sosai mahaifinta dake Malami ne yasa yara 'yan makaranta na addu'a jiya an sauke al'kurani babu adadi"

Mama ta cigaba da cewa." Insha Allahu tanan zuwa itama,kin san bata samu damar zuwa gurin bukin ku ba tun dai da tazo lokacin mutuwar me Martaba." Balaraba tace." Kai angode sosai wallahi ai Mama alk'urani mai girma yana tattare da waraka ko wace iri ce ,mutukar mutum zai rike shi, to ya rike babban kundi." Mama tace." Haka maganar ki take Balaraba." Su Shahid ne suka k'araso gurin cikin nutsuwa suka tsuguna suna gaishe da ita, ta amsa musu da walwala a fuskarta tace." Ya mai jiki? Domin Ku zan tambaya." Shahid yace." Jiki alhamdullahi Mama kin ganshi zaune k'alau dashi,wannan kuma aikin Gimbiya ne ga tanan kusa dake." Cikin farin ciki Mama tace." Nasan zata aikata fiye da haka, k'okarin tura while chair d'in yake, da sauri Shatima yace." Kabari mana inzo." Ko saurarensa baiyi ba ya cigaba da turawa ya k'araso kusa dashi gami da kama while chair din yana fad'in"Da ka bari an turaka." "Akan me zan bari hannuna aikin me yake." Yafad'a ciki-ciki murmushi kawai Shatima yayi yana fad'in" Dama kai ai babu me iyawa da kai sai Balaraba."
[10/4, 12:54 AM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻





~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*





*MARUBUCIYAR*


```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
```LADIDI K'WADAGA```




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_

_____________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________






*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_





*DEDICATED*
~*TO*~
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿115*



Shiru yayi masa har suka k'arasa kusa da Mama,ya fara k'okarin saukowa Mama tace." A'a kayi zaman ka kawai mu gaisa a haka lallai jiki yayi kyau,naji dadin ganin ka cikin walwala ubangiji Allah ya k'ara lafiya." Suka amsa da "Ameen" Cikin kauna irin ta d'a da uwarsa yace." Mama kin tashi lafiya."? Tace."Lafiya lau na tashi amma na kwanta da tunanin ka, shiyasa da na shigo na ganka cikin koshin lafiya naji dad'i kuma na godewa Balaraba." Sunkyar da kai kurrum yayi yana murmushi,tace." Ina fatan ka karya ko."? Balaraba tace." Ga kayan karin can kan daining." " To maza je ki d'auko masa in ga yaci a gabana." Kallon ta yayi yace." Mama sai kace wani k'aramin yaro." Murmushi tayi tace." K'aramin Yaro kake a gurina." Shahid yace." Wallahi hakane Mama mu yara ne a gaban iyayemu, Sarki! Shiru yayi yana kallon ikon Allah Mama tasa Balaraba ta had'a tea me kauri tace."fara bashi ya d'umama cikinsa." Balaraba ta mik'a masa kofin tae sai yak'i karb'a Mama tace." Ki cika ladanki mana." Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya ta nufi bakinsa da cup d'in, a hankali ya bud'e bakinsa ya fara kurb'ar tea d'in, ji yayi sugar yayi yawa ga madara tayi yawa baya son k'arni, a hankali yace." Ki aje Wannan ki had'a min bak'i." Ajewa tayi kamar yadda yace ta fara had'a masa wani,hannu ya mik'a ya d'auki cake guda d'aya ya fara ci, sosai yayi masa dad'i a baki sai da ya cinye guda uku kafin taga ma motsa tea d'in yadda zai fi masa dad'i a baki ta fara bashi cike da kunya a idon Mama da su Shatima, Mama sam hankalin ta baya Kansu tana can tana magana da Jakadiyar ta, Su Shahid sai tsokanar sa suke yak'i tanka musu, a hankali ta dinga bashi yana kurba yana gutsirar cake d'in, sai da ya ci guda shida sannan ya d'aga mata hannu alamun ya ishe shi, tissue yake k'okarin yagowa, ta ya ciro masa mik'ewa tayi tana goge masa gefan bakinsa,ya tsura mata ido yana kallo, ita ko taki yadda su had'a ido dashi, Halisa da Azima ne suka shigo cikin wannan hali, turus sukayi ganin abunda yake faruwa kowacce jikinta yayi sanyi ga Mama a zaune ga uban tafiyar zaune cikin shiri Balaraba ta had'u sosai domin shigar ta ta yau tayi mata kyau, tana tsaye kusa dashi tana goge masa gefan bakinsa . Suka zazzauna jiki babu k'wari suna gaishe da Mama ta amsa musu a sake tana tambayar su me jiki, Azima da yake tafi Halisa wayo ta b'oye damuwar ta ta saki jiki suna hira dasu Shatima,har tana sa

4 / 7
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted